Join Our WhatsApp Group

ALKIBLA Complete Hausa Novel Document by ALKIBLA


ALKIBLA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 124659ALKIBLA

Reading Time: 10 Hours

Added On: 10, Apr 2023

Author: Safiyya Abdullahi Huguma ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 686.64 kb

File Type: txt

Views: 6414+

Download: 6488+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: 23/10/2021, 08:34 - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more.
23/10/2021, 08:35 - 👍🏻👍🏻: *ALKIBLA*
_(THE BATTLE OF LOVE)_

*_HUGUMA_*

01


*_Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai_*


*dukkan godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki daya bamu aron rai da lafiya,tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu annabi muhammad S A W*


*_littafin ALƘIBLA,labari ne dana qirqeshi mafi rinjaye kan soyayya,saidai kuma hausawa sukance ba'a rasa nono a ruga,akwai wani sashe na matsalolin da mafi yawan 'yammata ke fuskanta a wannan zamanin game da samarinsu,wanda kusan basu san daga inda matsalar take ba_*

_a wannan karon ina neman afuwan masu karatu,littafin alqibla bazai kai yawan littafin siradin rayuwa ko alqawarin Allah,saidai ina fatan zai nishadantar ya kuma qayatar daku in sha Allah,ASHA KARATU LAFIYA_

*ALLAH YAYI RUQO DA HANNAYENMU🙏🏽🙏🏽🙏🏽*

☝🏾☝🏾 *KIJI TSORON ALLAH,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BA*☝🏾☝🏾☝🏾

____________________________*GOVERNMENT GIRLS UNITY COLLAGE KACHAKO*Makekiyar harabar makarantar 'yammatan ta kwana dake garin kachako wato government girls unity collage cike take da dandazon al'umma,wanda mafi akasarinsu dalibanta ne,da kuma wasu daga cikin iyayen yaran dake ta faman qoqari dakai kawon kwashe yaransu zuwa gidajensu don gabatar da hutun zangon karatu na uku wato third semester.


Daga can gefe daya na harabar makarantar kana iya hangen yadda matashiyar ke tsaye goye da hannayenta sanye cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm da suka amsheta sosai,ta zubawa harabar makarantar tasu idanu,kamar wadda aka baiwa aikin qididdige yawan al'ummar dake karakaina a wajen,kyakkyawar fuskarta babu alamun fara'a ko kadan.


Duk da cewa duka duka shekarunta ba zasu haura goma sha biyar ba,amma kana iya tantance kyan zubi diri gami da siffa da Allah ya bata.


Mai matsakaicin tsaho ce,ma'abociyar doguwar fuska da fata wadda bata cika haske ko duhu ba,ta yadda ba zaka iya kiranta da baqa ba,hakanan ba zaka kirata fara kai tsaye ba,tana da manyan idanu wanda ba'a fiya gane girmansu ba idan ba budesu tayi sosai ba duk sadda taso hakan,daga cikar girarta kawai zai gaya maka tana da yalwar gashin kai,Allah ya yi mata ado da dimple guda biyu a kumatunta hagu da dama,wadanda sukan bayyana duk sanda ta bude baki da niyyar magana,walau tayin ko bata yi ba.


Sake gyara tsaiwarta tayi idanunta na tara ruwan hawaye,duk da basu kai ga xuba ba amma duba daya zakayi mata ka gane hakan,iya damuwa ta damu ta kuma matsu,burinta kawai ta ganta a gida,Tana da burin son ganin mutane a rayuwarta da suke da gurbi na musamman a zuciyarta,duk da cewa ta rasa babban bango kuma jigo a rayuwarta,amma duk da haka bata rasa wasu daka iya xama makwafinsa ba bawai madadi ba.


Abinda ya qara mata zaquwa da son ficewa daga makarantar tunda wurwuri kamar sauran dalibai shine,komawar 'yar uwa kuma qawa a wajenta gida tun lokacin yin hutu da fitar dalibai baiyi ba,sakamakon lalura data sameta,wadda ta tilasta aka maidata gida,banda haka,bata da wata damuwa mai yawa kan jimawar tata.


"Fatima sa'id dabo,fatima sa'id dabo" daga bayanta taji ana kwarara kiran sunanta,a nutse ta waiwaya tana duban mai kiran nata,daya daga cikin 'yan ajinsu ce ladifa hamza,ci gaba tayi da dubanta har ta iso dab da ita
"Anzo daukarki,tun dazu 'yan gidanku ke nemanki" da mamaki ta maida dubanta farfajiyar da take tsayen sannan ta dawo da dubanta kan ladifa,tayi tsammanin inda ta tsaya din zata iya ganin shigowar motar da tazo daukar nata,bata tanka ba saita fara takawa kawai don barin wajen,ladifa ta rufa mata baya tana tsokanarta kan rashin kuzarinta,da yadda ta zama wani sukuku kamar ba ita ba tun tafiyar munira gida ta barta.


Tunga taja ta tsaya lokacin data kusa isa dab da motar da akace tazo daukarta din,mamaki bayyane qarara a fuskarta,wannan ba daya daga cikin motocin gidansu bane,duk wani ahali na gidansu yasan wannan motar waye,ya kuma san da zaman motar,yaushe yazo?,ya akayi ya yarda ya bada motar a daukota?,shine da kanshi?,saita girgiza kanta da sauri,bashi bane,don ko a mafarki tasan bazai taba zuwa daukar wani daga cikinsu ba.


Murfin motar da aka bude yasa ta maida hankalinta sosai ga motar,wani matashin saurayi ne ya fito,wanda dukka a qalla shekarun haihuwarsa ba zasu rufa ashirin da biyar zuwa da shida ba
"Ko baki shirya komawa gidan bane?" Ya dan daga murya yana fadi idanunsa a kanta,hakanan fuskarsa babu yabo ba fallasa,kai ta kada tana son tambayarsa da yaren kurame kan shi da waye sukazo?,saidai bata kai ga tambayar ba murfin sit din baya ya bude shima,wata matashiyar ta sake fitowa,wadda a qiyasce suna iya yin shekaru daya da ita,fuskarta washe da fara'a tana duban zahra dake tsaye.


"Suprise ko?" Matashiyar ta fada cikin sautin qyalqyala dariya,ba tare data shirya ba itama qaramar dariya mai qaramin sauti ya kubce mata,wadda hakan ya baiwa dimple din dake kumatunta damar bayyana,sa'annan kamar wadda aka qarawa qaimi ta doshi motar,tunda taga hafsat cikin motar ta tabbatar ba abinda take zargi bane
"Wallahi kun shammaceni,na farko na zaci daga gidan abban gwammaja za'azo daukana shi yasa na zauna jiran motar gidan,na biyu kuma saina ganku anan,ya akayi haka...?" Cikin dariya hafsat tace
"Shigo daga ciki kisha labari....dama naci alwashin koda gold akayi motar nan saina shigeta ai"
"Mayya....saida kika shiga din kuwa" zahra ta fada tana dariya
"Sarakan surutu...zaki kama mata sauran kayan ku shige mu tafi ko kuwa har sai lokacin da ya diba mana ya cika bamu koma ba?" Cewar daya matashin saurayin dake a mazaunin driver,cikin shadda dinkin zamani.


Leqensa zahra tayi ta window,saita fashe da dariya tana cewa
"Wai,congratumatur ya musty.....yaudai an dana,kaga ko yadda motar tama kyau kamar taka?,anya ba zakayi ratse ba kaje kadanyi shawagi ka dawo ba?" Murmushi mai kama da dariya shima ya saki yana cewa
"Bari kawai.....don dai kawai nasan yana sane da lokacin daya bamu ne,wallahi yau da sai na tsatse motar nan son raina...ke kinga yadda 'yammatan makarantar nan ke wani kallona....."
"Basusan duk bige bane baba" zahra ta fada tana qyalqyalewa da dariya gamida shigewa gidan baya,ya soma qoqarin tada motar bayan duk sun rufe murafun yana cewa
"Aina miki dare xakimin rana,tunda na kankaroki nazo daukarki a wannan dalleliyar motar ba"langabar dakai tayi ta koma kalar tausayi
"Haba ya musti,ni dakai fa bata baci,kada kasa 'yan uba suyi mana dariya"
"Dariya kuma ta nawa?" Wancan saurayin dake daya site din ya fada yana sake kwanciya sosai jikin kujerar motar
"Kaji ko?" Zahra ta fada tana bata fuska
"Rabu dashi,duka adawa ce,ba wanda zai ganmu a rana" mustapha ya fada yana harar shamsu dake gefansa zaune,wanda bai sake tankawa ba ya yamutsa fuska kawai gami da cewa
"Oho dai,maji ma gani".


Kusan wannan 'yar tsamar ba wani sabon abu bane a wajensu,sun riga da sun saba da hakan,wanda ba komai bane ya kawo haka ba face fahimtar juna da sabo dake tsakaninsu,duk da cewa akwai banbancin iyaye,duka sun fito daga mahaifa daban daban.


Saida suka hau titi sosai sannan ta gyara xama tana duban hafsat
"Wai ya akayi ne haka?" Dariya hafsat tayi kafin tace
"Wallahi ya hajja ce tace ya bada a daukoki,da yaqi ma tace to bari ta kira mas'udu ya bada tashi tunda shi ta isa dashi,to sai da yaji haka sannan ya bayar......zahra ma tana kusa sai data saka baki" tabe baki zahra tayi tana juyar da kanta xuwa window,tadan dubi titi kadan sannan ta dawo da dubanta ga hafsat
"Sai kace xai mani gafara motarma sai an roqeshi,ni wallahi ya hajja data sani bata roqa ba.....bama wannan ba,na dawo hutu da farinciki da burin samun sake,musha soyayyarmu nida hafiz,zuwansa nasan komai saiya rushe wallahi,babu wani sauran sake,bayan shi har gida ake biyoshi,ya kuma baje kolin soyayyarshi babu jin kunyar kowa,amma mu ya hanamu katabus babu gaira babu dalili,bayan yafi kowa sanin tsarin gidan,yanzu daka yi candy za'a zuba maka idanu ka kawo wanda zaka aura,idan babu ya zama jarraba,yanzun kuma kana tsaiwa dasu shiya hana ruwa gudu,haba" ta qarashe masifar dajan tsaki,dariya hafsat keyi abinta tana qarawa,kafin tace komai shamsu ya waiwayo yana dubanta
"Ke yarinyar nan da gaskene fa zaki qone tun kafin ki tafasa" hararar wasa ta jefa masa
"Saimu zauna ai ku jiqamu kusha,kunfi kowa daga murya idan bamu tsaida miji ba...."
"Meye a ciki,sadaka kawai zamu bada ku a masallacin malam ayuba" ya fada cikin shaqiyanci yana qyalqyalewa da dariya,wanda ya saka mustapha ya dara shima,baki ta tsuke ita kuwa kana tace
"Allah ya kiyaye ya sawwaqe,wuce nan wallahi".


Da ire iren wadan nan hirarrakin suka ci gaba da tafiya cikin motar,tana tambayar hafsat wasu abubuwa da bata nan akayi,da kuma wadanda ta tafi ta bari,shamsu dai bai gaji da tsokanarta ba ya sake cewa
"Sai tambaya kamar makahon daya warke daga makanta,kamar wadda aka sallamo daga gidan yari" fuska ta narke wanda da alamu lokaci zuwa lokaci tana da dabi'ar shagwaba wanda batasan ita kanta tana dashi ba,kusan a jininta abun yake
"To ya shamsu don Allah meye maraba,kowa an barshi yana jeka ka dawo amma ni an turani boarding saboda shawarar da wannan mutumin ya bada,kuma wai aka amince masa"
"To ya za'ayi sai haquri,kinsan shi,idan ya kafe akan abu,amma kuma da wuya idan ya kafe din a kasa ganin alfanun hakan" baki ta zumburo tana mita
"Kaidai kawai kana goyuwa da bayanshi ne a fakaice"
"Ko kadan,ke dince kin fiya qorafi a kan lamuransa,bayan dukka mun riga mun saba da halayyarsa"
"Ai shikenan" kawai ta fadi,don batason zancan yayi nisa,saita kamowa hafsat wani zancan suka shiga.


Tafiyar a qalla awa daya harda wasu mintuna masu dan dama a kai suka isa unguwar gadon qadon qaya dake qwaryar birnin kano,bakin wani gida mai manyan kagantu tsaho da kuma fadi suka tsaya,wanda kallo daya zaka masa tun daga waje kasan cewa ba mace ko mutum daya zuwa biyu bane kawai ke zaune cikin gidan.


Zaka sake gasgata hakan lokacin da gate din gidan ya bude motarsu ta kunnu xuwa ciki,sassane daban daban qunshe cikin gidan,a qalla akwai sashe hudu zuwa biyar,kowanne na mazaunin gida mai xaman kanshi.


Kamar mai jira,tun kafin ya kammala daidaita tsaiwar motar ta balle murfin motar ta kwasa da gudu tamkar qaramar yarinya ta nufi daya daga cikin gine ginen dake tsakiyar gidan,madaidaicin gini guda daya dake hannun dama.


Baki dukka suka sake suna dubanta,duk da cewa sun sani ba tun yau ba halin xahra din na daban ne,quruciya da rawar kai kamar bata qara komai cikin shekarunta.


Da sauri saurinta take kutsa kai zuwa sassan 'yar tsohuwar,burinta kawai ta cimmata,don ba qaramar kewarta tayi ba,sabo da shaquwa ne mai yawa tsakaninsu,wanda babu makamancin irin wannan tsakaninta da kowanne jika nata koma bayan zahrar.


'Yar kyakkyawar dattijuwa tsaye gaban freezer tana yunqurin ciro wani abu tana magana da wata matashiyar budurwa dake xaune kan daya daga cikin kujerun falon sanye da hijabi mai hannu kalar blueblack,kallo daya zaka mata kasan shekaru sun fara tura mata,saidai yanayin tsafta da son gayu irin nata ya qawata tsufan nata sosai,don kana iya hangen ragowar jan lalle dake qafarta wanda bai gama fita ba,da tajajjiyar sumarta dake cikin dankwali,wadda ke cike da furfura,saidai kuma awanke take fes cikin tsafta da tsari,sam bata lura da shigowar xahra cikin falon ba sai sautin muryarta daya karade ilahirin falon.


"Hajja!" ta fada cikin nuna zallar farinciki tana nufarta,kafin takai ga juyowa tuni zahran ta isa gareta,ta kuma cukuikuyeta gami da rungumeta tsam ta baya tana dan tsalle
"Yan makaranta....barka,barka" ta fada fuskarta na fadada da fara'a,wanda ke bayyana farincikin dake cikin zuciyarta,yake kuma alamta tarin qaunar dake tsakaninsu
"I miss you my hajja" zahran ya fada tana dariyar farinciki
"A'ah,sauya harshe dai,ni ba gane wannan surkullen naku nake ba,yanzu yayanku ya gama nashi ya fita" dariya zahran ta saki tana sakin tsohuwar,saidai sautin 'yar dariyar da taji daga gefanta yana hankalinta ya kuma hanata furta abinda tayi niyyar fada din,ta waiwaya tana duban sashen.


Kusan a tare suka sakarwa junansu murmushi
"Kicemin keda kishiyarki ne hajja......anty takwara ina yini" ta fada tana qarasawa inda matashiyar ke zaune,wadda fuskarta ke fadade da fara'a tana duban zahran gami da gyara mata wajen xama ta hanyar tattare hijabinta zuwa jikinta ta duban zahran itama
"Lafiya lau takwara.....ya makaranta?"
"Alhamdulillahi....gamu yau mun samu 'yanci"
"Aikuwa dai kam,gida akwai dadi" daga haka ta maida dubanta ga ya hajja wacce ta samu waje ta zauna
"Hajjata....me dame aka tanadarmin?" Tayi maganar a shagwabe kamar yadda ta saba
"Duk abinda takwarata keso" hajjan ta fada tana dariya,qaramin tsalle najin dadi ta doka ta fada saman kujera tana cewa
"Allah yabarmin hajjata"
"Eh qwarai,kafin ki shukamin wata tsiyar taki ba" da sauri zahra tadan bata rai tana wulqita idanu,kana ta maida dubanta ga hajjan
"Haba hajja....Allah yasa ba gaban 'yan adawa kika fada ba,da kin saka sunmin dariya,musamman su o'o" ta fada tana dan satar kallon zahra.


Sarai zahran ta fahimci wa take nufi,saita murmusa tana qunshe dariyarta gami da girgiza kai,kasancewarta mai sauqi da sanyin hali,marason yawan magana da rashin daukar al'amura da zafi
"Inna wuro....inna wuro rigima" ta ambaceta da sunan da yawanci akafi kiranta dashi cikin gidan,saita waiwaya tana duban zahran
"Eh ai nasan kin fahimta.....don nasan bakison laifinsa" ta fada tana sake bata fuska kamar wadda aka zaga,hakan ya sanya zahra yin dariya dole tana kada kai cikin jin nauyin ya hajja dake zaune a wajen.


"Sarkin neman magana,idan ya jiki kuma ya hukuntaki kice wani abu daban,shin kin shiga ma cikin gidan ma kin gaisa da mutane ko kuwa kkka zauna neman magana...." Kafin xahran ta baiwa hajja amsa hayaniyar 'yammatan gidan ta soma dosowa falon
"Tofa,Allahumma salli ala,aikin dawo,yanzu zaku taru ku dinga hanani sakat,sauqin abunma dodonku yana gari shima"
"Ni wallahi hajja ki dinga hanashi zuwa duk sanda zanzo hutu,tsakani da Allah fa hanani sakewa yake,hutun wata daya kacal din da nake samu saina qareshi cikin rashin jin dadi" baki hajjan ta kama tana dubanta,ta rasa wanne irin abune haka irin na zahran,qara kusantowar hayaniyar tasu alamun suna bakin falon yasa ta dauke kai ba tare da tace komai ba har suka qaraso cikin falon riqe da hannuwan jakankunan zahra guda biyu,wanda ta barsu a farfajiyar gidan bata samu daukosu ba saboda tsabar zumudi.


Kyawawan matasan 'yammata su biyar rigis sanye da unifoarm,wanda...


Read / Download ALKIBLA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On ALKIBLA
avatar
halimat-6

8 months ago

Reply

Alkibla

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album