Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DAYA CIKIN BIYU Complete Hausa Novel Document by DAYA CIKIN BIYU


DAYA CIKIN BIYU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 85798



DAYA CIKIN BIYU

Reading Time: 7 Hours

Added On: 28, Nov 2024

Author: Aisha Abbas Mrs Isham ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Jarumai writers association

Author Phone : 08166018849 or 09024503194

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 443.7 kb

File Type: txt

Views: 1066+

Download: 977+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: ⚔️👑👑 ƊAYA CIKIN BIYU 👑👑⚔️

( ⚔️THE CHOSEN ONE ⚔️ )


🔥A story of love,hatred and violence ⚔️🔥




🤍*Story and written*🤍

~By~

Aisha Abbas (*MRS 🌹 ISHAM 🌹*)
(*Yar lelen jarumai writers*).




Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN KAI,ME KOWA ME KOMAI.ME RAYAWA,ME KASHEWA.ME YIN YANDA YA SO KUMA A LOKACIN DA YA SO. TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU ƘARA TABBATA GA MASOYIN MU ANNABIN RAHAMA,FIYAYYAN HALITTA DA BABU KAMAR SA ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM❤️💯*

Ina sake miƙa godiya ta ga Allah Madaukakin sarki da ya nuna min wannan lokaci haɗe da banI damar sake rubuta wani labarin.
Masoyana ina farin cikin sake kasancewa da ku a cikin wannan littafin nawa me Suna ƊAYA CIKIN BIYU. ina fatan yanda ku ka bani hadin kai a sauran littatafai na wannan ma zaku bani. to akafta kawai,wannan littafin yazo da Salo daban-daban, Wanda ban taɓa kawo muku shi ba. Ku kasance dani Mrs isham dan Jin wannan kayitacciyar labarin.🔥😍❤️❤️❤️

Ina masu son tallata hajarsu?,masu son a yi musu tallar kayan sana'ar su domin samun kostomomi to Kar ku yi Kasa a guiwa ku garzaya ku Kira wannan layin nawa 08166018849 Mrs isham.



🤍Date: 01/07/2024 💘📚🖊️







❤️🔥Page 1__2




*KUWAIT*


Ƙasar Kuwait, ƙasa ce a yammacin Asiya,tana arewacin gefen gabashin larabawa a bakin tekun Farisa,tana iyaka da Iraki zuwa arewa da Saudiyya a kudu. Kuwait ƙasa ce ta larabawa.an san Kuwait don al'adar wasan kwaikwayo na gida, Kuwait ita ce kawai ƙasar Larabawa a yankin gulf Farisa masu al'adar wasan kwaikwayo, kungiyar wasan kwaikwayo ta labarci a Kuwait ta kasance wani babban bangare na rayuwar al'adun larabawa na ƙasar.
Dinar Kuwaiti wato kudin Kuwait, ita ce mafi girman darajar kudi a kaf faɗin duniya,a cewar bankin duniya, Kuwait ita ce kasa ta biyar mafi arziki a duniya.

Yawancin yan ƙasashen waje suna Ƙaura zuwa Ƙasar Kuwait,suna samun sha'awar yawan albashin su ne,domin suna daya daga cikin manyan Ƙasashen da suke bada albashi me tsoka da gwabi, sannan kasantuwar babu haraji da za'a biya da ze cutar da yan kasar.masu ƙaura zuwa ƙasar kuwait sun yarda cewa ƙasar na iya bada kyakyawar rayuwa tare da duk abubuwan jin dadi domin ƙasa ce da Allah ya albarkaceta ta fannin arziki me tarin yawa.


MASARAUTAR BAYAAN DAKE ƘASAR KUWAIT.


Masarautar Bayaan babban Masarauta ce da babu irinta akaf faɗin nahiyar ƙasashen Larabawa, Masarauta ne da yake riƙe da al'adu na gargajiya da kuma ilimi da wayewa akan harkokin rayuwa,masarauta ce me karfin gaske wanda suke faɗa a ji a ko ina,tana da rundunar sojojin mayaƙa masu tarin yawa. sannan akwai arziki sosai a cikin masarautar Bayaan.akwai su da doka me tsanani .hallau masarauta ce me adalci da kuma sanin hakkin bayinsu da suke mulka,duk da ako ina ba'a rasa ɓata gari ,amma sarakunan da duk suke mulkar Bayaan to sun kasance masu adalci da kuma kwazo da jarumta.
tun daga kan sarki na farko har izuwa kan sarki na takwas wanda shine yake mulkar kasar a yanzu, abubuwan da masarautar suke dashi kuma suke tunkaho dashi shine,yawan dukiya da mafi yawancin masarautu suna zuwa gare su karɓar bashi domin ciyar da bayinsu,suna da yalwatacciyar abinci da suke wadata bayinsu dashi shisa inde ka ga bawa babu alamun yunwa a jikinsa tofa daga masauratar Bayaan yake,suna da tsaro da kuma sojojin yaƙi masu yawa da kuma tsorata abokan gaba an horasu ne domin bada rayuwar su da kuma karfin su bawa masarautar Bayaan kariya,sun samu horo me tsananin gaske kuma dukkansu gwarazane masu jini a jika,ma'abotan tsorata zuƙata.
masarautar tana da albarkar ruwa me dadi da kuma yawa wanda suke amfani dashi domin yin noman abinci,ga kuma girma da ƙa wa da masarautar take dashi.ga kayan ado na gwala-gwalai na danyen lu'ulu'u hatta kujerar sarautar na lu'ulu'u ne,duk wani wanda ya shiga masarautar baya taɓa kwadayin fita .saboda yanda aka ƙawatar da lungu da saƙo na masarautar da zallar fari,game da haɗi da jan lu'u-lu'u.suna da riko da addini duk da acikin Bayaan akwai wa'yanda suka kasance ba Musulmai ba haka zalika babu bambancin addini a masarautar.
Babban abinda ma'abota rayuwa a masarautar basu sani ba shine Bayaan tana samun kariya da tsaro ne daga wajajen rauhanan aljanu da suke lura da komai na Bayaan.


A shekata ta dubu ɗaya da sittin da shida,sarki Mustapha Abdullah Rahman shine sarki na farko a masarautar Bayaan,sarki ne me adalci da imani,haɗe da tausayi.yana da ahalinsa da suka kasance matarsa ɗaya se ya'yan sa maza guda biyar wanda sune sulaiman Abdullah Rahman, Muhammad Abdullah Rahman, Abraham Abdullah Rahman,nooradeen Abdullah Rahman, Yousuf Abdullah Rahman. Dukkanin su sun taso ne masu kaunar mulki har sukayi aure suka hayayyafa,a lokacin da sarki Mustapha Abdullah Rahman ya tsufa sosai nan ya sauka daga kan karagar mulkin sa,domin bawa daya daga cikin ya'yan sa saboda yanzu ya yi tsufar da baze iya cigaba da mulki ba,kuma dole a samarwa Bayaan sabon Sarki haka yasa aka duba wanda yafi chanchanta a cikin ya'yan sa guda biyar din man.domin masarautar Bayaan bata bi ta kan cewa waye babba waye karami wanda yake da tausayi da kuma nagarta shine wanda ake bawa sarauta.hakan yasa aka ga Yousuf Abdullah Rahman yafi ko wannensu cancanta yasa aka naɗasa a matsayin sabon sarkin Bayaan,wasu daga cikin yan uwansa sun yi farin ciki wasu kuma sun ji haushi sosai saboda yanda suke kwadayin hawa kan karagar kuma babban takaicin su shine koda a ce ya mutu ya bar duniya.
Su bazasu taɓa samun wannan kujerar ba,har se in beyi aure ba kuma be haihu ba,amma muddin yana da yara ko mace ko na miji to dole ɗan sa za'a bawa Sarautar,wannan shine doka da kuma tsarin Bayaan. duk Sarkin da yake mulki ya zamana ya mutu ko kuma yanason ya yi murabus tofa baza'a bawa dan uwansa ba ko kuma wani bare ba, dole ya'yan cikinsa ne ze mulki Ƙasar. Hakan yasa wannan sarautar da aka bawa Yousuf Abdullah Rahman ya yi wa dayawa zafi a cikin su da har suka yi wani nufi a ransu.
Bada jimawa ba kuwa sarki na biyu wato sarki Yousuf Abdullah Rahman ya fara mulki kamar yanda mahaifin su yai yi cike da gaskiya da amana,har lokacin da sarki Mustapha ya mutu.

A haka rayuwa yaci gaba da tafiya a yayinda mulki yake tafiya kan ya'ya da kuma jikokin Mustapha Abdullah Rahman domin yanzu haka ana kan sarki n biyar wanda ya kasance jikan jikan Yousuf Abdullah Rahman,wato Khalid Mudassir Rahman haka shima yana gabatar da mulkinsa yanda ya dace,a yayinda zuriyar Rahman suke cigaba da haɓaka to ko ina domin aure suke yi kuma haihuwa suke kowa da matansa da ya'yensa har ma da jikoki.

Bayan shekara ɗari huɗu,wanda ya zama shekara ta dubu biyu da daya(2001) a wannan karnin Sarki na takwas ne yake mulki waƙo sarki TAIFUR MUZZAM RAHMAN shine wanda yake mulkar masarautar da yake sa'ke haɓbaka.komai ya sauya kamar yanda zamani ya sauya,Sarki ne me ƙima da daraja wanda yasan kan mulkin da yake yi.kowa yana son shi saboda yanda yake da adalci da kuma tausayin talakawa da kuma kyautata musu.wannan ne ya sake wanzar da soyayyar sa a zuciyar talakawan sa.

Sarki TAIFUR MUZZAM RAHMAN yanada mata kwalli daya me suna Sarauniya Fatima.kuma ita din yar Sarkin yammacin ƙasar Yemen ce,yanda mijinta yake da hali nagari haka itama domin ko a Masarautar su na Yemen kowa na kaunar ta,kuma bugu da ƙari jaruma ce.suna matukar son juna ita da sarki TAIFUR har Allah yasa ta samu cikinta na fari sosai suke nunawa wannan cikin so da kauna,basu damu da menene a ciki ba ko mace ko namiji su de suna kaunar cikin.haka talakawa da bayi kowa yana iya kokarin sa wajen nuna bajintar sa ta hanyar yin kyauta da iya karfin su wajen matar sarkin su me adalci .kuma hakan na faranta musu rai sosai, haka suka cigaba da renon wannan cikin da ko da yaushe girman sa ƙara wuce misali yake.


Tun lokacin da Sarauniya Fatima ta samu ciki ta ke wasu irin munanan mafarkai marasa kan gado,kuma masu caza kwakwalwa in de aka bi komai da ki-da ki,sede waye ya wani damu da ya san ma’anar mafarki?.wannan dalilin yasa bata taɓa sanarwa da sarki ire-iren
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DAYA CIKIN BIYU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album