Join Our WhatsApp Group

ABDULAZEEZ SADAUKI Complete Hausa Novel Document by ABDULAZEEZ SADAUKI


ABDULAZEEZ SADAUKI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17017



ABDULAZEEZ SADAUKI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 25, Nov 2023

Author: Ummu Khaleel ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : 08088002574

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 98.74 kb

File Type: txt

Views: 660+

Download: 172+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: [1/7, 3:28 PM] FIRST CLASS: .سم الله الر حمن الر حيم

*ABDUL AZEEZ* (sadauki)

*1/1/2020*


By ummy Khaleel

1&2

*WANNAN FAGE ƊIN SASAUKARWA NE GAREKI 'YAR UWATA AMINIYA UMMU AFAN(TWINS SIS) INA GODIYA GAREKI DA KULAWAR KI GARENI, ALLAH YABAR ƘAUNA, ALLAH KUMA YARABAKI LAFIYA DA ABIN DA KE JIKIN KI*

_____________________________________

*☀FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION☀*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*


______________________________________


*FREE PAGE*


Gamai buƙatar cigaban labarin sai ya biya naira 100 ta wannan number

08088002574


............Yaro ne ɗan kimanin shekaru goma sha biyu yashigo gidan da gudu yana kiran, "Umma Umma, yau nasayar da talle na gaba ɗaya."
Umma wacce ke zaune a bakin murhu tana hura wuta da uban tsohon ciki ta juyo ta kalle shi tace, "alhamdulillah yanzu kuwa nake maganar ka acikin zuciya ta, ashe ma kana hanya."
Abdul Azeez yace, "eh Umma yau kasuwar a cike take da jama, agurin ƴan saida dabbobi ruwan yaƙare, yanzu bari na ɗauki leda biyu na koma."
"Da ka tsaya tukunna nagama abinci kaci sai ka koma, kaga tun safe bakaci komiba."
"A'a Umma kinga yanzu fa akwai mutane akasuwa kuma kinga akwai rana gara nayi naje ko Allah zaisa ya ƙare."
"To Allah yaba da sa'a *SADAUKI* "
Har ya juya zai tafi yajuyo ya kalli ummar tashi yace, "Umma na ina jin daɗin wannan sunan da kike kirana dashi, natafi sai nadawo."
"Adawo lafiya."

Akowani ranar laraba ake cin kasuwar wannan ƙauye dake cikin garin Bauchi wato *DAƁE*
Kasuwar daɓe kasuwa ce wanda akafi saida dabbobi ire-iren su shanu, tumakai, awakai sai ƙananan dabbobi ire-iren su kaji, agwagi, zabbi, talo-talo da dai sauran su.
Awannan rana Abdul Azeez (sadauki) yakan fasa zuwa makarantar boko dan yaje ma mahaifiyar sa talle sabida wasu dalilai wanda zankuji anan gaba.
Abdul Azeez sawunshi huɗu yana fita tallen pure water kuma yana ƙarewa, ana biyar ɗin ne umma tace, "idan ka sayar da wannan kasai abinda ranka yake so."
Abdul Azeez yana fita akaro na biyar tun kafin yakarasa cikin kasuwa aka saye ruwan, da murnar shi yashiga cikin kasuwa inda ake sayadda ƙoyayen zabbi ya tambaya, "nawa-nawa ake sayarwa?"
"Naira ashirin-ashirin guda nawa kake so." Inji mai sayar da ƙoyin.
"Guda biyar nakeso zansa ma kazata da take ƙwai."
Guda biyar ya kirgo yabashi acikin baƙin leda, Abdul Azeez yabashi kuɗin shi Naira ɗari.
Yamma liƙis Abdul Azeez yadawo gida yasami mahaifiyar tasa tana jan ruwa arijya, ajiye robar tallan ruwan yayi yace, "umma kawo naja miki, kije kizauna ki huta."
Larai dake bayan gida tana jinshi tace, uban kini bibi ahaka dai za aƙare a talla."
Zaiyi magana umma tayi mishi da hanu alamar karyayi magana, yakarɓi gugar yaci gaba da iba mata ruwa.

Da daddare misalin ƙarfe takwas bayan yadawo daga masallaci, yanufi ɗakin umman tashi, saida yayi sallama ta amsa mishi kafin yashiga yasameta akan sallaya ta idar da Sallah tana lazimi.
Zama yayi agefe saida tajira tashafa addu,ar da takeyi suka shafa tare, ta kalleshi tace, "sadauki kadawo?"
"Eh umma abinci nafa?"
Nuna mishi tayi da hanu a inda yake, sadauki yatashi yaje ya ɗauka a kusa da wani ƙaramar kujerar tsakar gida.
Ɗakkowa yayi yazo yazauna akusa da ita, hanu yasa acikin aljihu yaciro mata ƙunshin nama yace, "umma ga wannan kici kinji, akasuwa nasayo miki."
Murmushi tayi tasa hanu ta karɓa tace " Allah sarki sadauki ubangiji Allah yayi ma rayuwar ka albarka, Allah yasa kacigaba da kyawawan halayyar ka."
"Ameen umma na, Baffa bai dawo bane yau naji shi shiru har yanzu, Allah dai yasa lafiya?"
"Insha Allah yana hanya kasan ranar kasuwa bai cika dawowa da wuri ba."
Ahayye munafurci dodo, daga tsakar gidan sukaji Larai da Inna wuro suna faɗi, Inna wuro cikin harshen ta na fulani tace, "hande enboni, (ni nashiga uku) ashe mutum batajin kunyar yarinyar farinshi, tasa yarinya agaba suyi ta hira kamar kanwarshi, kai Allah ya shawake jamani."
Larai tace, "yo inbanda abinki ina kunya awajen kaɗo, kinsanfa sheda yaga firamare kafin yayi aure aidole yayi rashin kunya."
Haka dai suka rinƙa yaɗa habaici ma umman sadauki.
Sallaman baffa ne yasa Larai da Inna wuro suka kalli juna suka sheƙe da dariya, Larai tace "agama wahala ashiyar damu da mazajem mu da yaran mu."
Inna wuro tace, "keda kika shan doka, aradu anemo abamu da iyalinmu, inbahaka tsinuwar jatuma tabi mutum."
Baffa baice musu komi ba yanufi ɗakin matar sa, sallama yayi suka amsa yashiga ya samesu suna hira irin na ɗa da mahaifi.
Umma tana ganin shi tayi ƙoƙarin tashi dan kawo mishi abinci da ruwa, "zauna kihuta baiwar Allah, sadauki tashi ka miƙo min abinci na kaga mahaifiyar ka tana fama."
Tashi yayi yaɗakko abinci acikin wani kwanon tuwo da miya yakawo mishi ya ajiye, ruwa yaje ya kawo mishi a irin kofin ƙarfen nan na da ya ajiye, yakoma ya zauna.
Umma tace, "Baffan sadauki ya kasuwan dai, yau kayi dare sosai?"
Saida yakai loman abinci baki ya haɗiye ya kalleta yace, "kasuwar yau sai addu,a saniya ɗaya na sayar, kinsan dabbobi sun sauka."
"Allah yayi ma wanda aka sayar albarka."
"Ameen" ya amsa.
Girgiza kai kawai yayi yana tausaya ma halin da take, ciki wata goma shaɗaya har yanzu bata haife ba, gashi mahaifiyar shi tahana shi yakaita asibiti.

****
Kasancewar yau Alhamis, sadauki da rana yake zuwa makaranta, dan haka yana idar da sallan asubah yanufi inda garken shanun su yake, da toci (touch) yake haska wajen yana zuba musu abinci a manya manyan fanteka, Muryar baffa yaji yana kiranshi, ya ajiye kwanon abincin da sauri yanufi inda yake, yana isa ya tsuguna har ƙasa ya gaishe shi cikin halayen fullanci.
Baffa yace, "baka gajiya da asuban nan tun haske baifara fitowa ba kashiga cikin dajin nan kana ba dabbobi abinci?"
Sadauki yace, "Baffa gani nayi gara abasu abincin da wuri kaima ka huta, kana gajiya da yawa."
"Allah ya maka albarka sadauki, kai yaro ne amma kana da tunani irin na manya, kaje ka huta kaima anjima saikaci gaba da basu abinci."
Sadauki yace, "to Baffa."
Salamu alaikum, salamu alaikum, "wai ko bakowa ashikin gidan ne ina ta sallama babu wanda ya amsa, Inna wuro, Larai, ko bakwanan ne?"
Umman sadauki tana jin sallaman gabanta yafaɗi dam, ahankali tayi ƙoƙarin tashi ta fita tana amsa sallaman, Yadado ta banka mata harara tace, "yo dama kina shiki ina ta sallama kinyi shiru, ke game shiki ko, to bari kiji shikin ki baida dameni ba kaɗo kawai tashige ciki tana masifa."
Umman sadauki ta girgiza kai kawai, tanufi Kitchen tafara ƙoƙarin yi mata girki, dan batasan da dawowar ta ba.
Yadado tana shiga ɗaki ta ciro ƙunshin fura acikin wani bakko tasa a kwano, tafara damawa da nono.
Tuwon dawa umman sadauki ta tuƙa ma Yadado, dama suna da sauran miyar ɗanyen kuɓewa ta ɗumama tazuba mata awani kwano takawo mata.
Harara Yadado ta banka mata tace, "anshe miki zanshi wannan abincin naki, ne maza kifita min da wannan kayan mayun.
Harta ɗauki kwanon zata fita, Larai da Inna wuro sukace ajiye mana mu zamushi, ai munsha maganin mayu tun muna shiki, Yadado kin dawone?"
Cikin sakin fuska Yadado tace, "i nadawo ina ta sallama ashe wannan shanuwar tana shiki bata amsa ba, shine wai yanzu takawo min abinshin mayu."
Larai ta kece da dariya tace, "da yunwa muka dawo dan haka muzamu shi ko ya kikashe Inna wuro?"
Inna wuro tatashi ta karɓi kwanon tuwon ahanun ta tace, 'mushi ko Larai dan aradu da yunwa nadawo daga gidan sunan nan, Yadado zuba mana fura musha."
Komawa ɗaki tayi ta zauna ta zabga uban tagumi, a cikin zuciyar ta tace, "wai yaushe ne uwar mijin ta zata so ta ne, yaushe ne matan kannen mijinta zasu jata ajiki su ɗauke ta kamar ƴar uwarsu, yaushe ne Abdul Azeez zai samu ƴanci agidan agidan ubanshi?"
Tunanin da tarinƙa yi kenan, hawaye ne suka gangaro mata a idanu, bata ankaraba taga mutum atsaye a kanta, tana ɗago kai suyi ido huɗu da Abdul Azeez (sadauki)


*Ummy khaleel*

*Taku ce*
[1/7, 3:28 PM] FIRST CLASS: بس ا لله الر حمن الر حرم

*ABDUL AZEEZ* (sadauki)

*2/1/2020*

By ummy khaleel

*3&4*

*Sadaukar wa gareki my Dr herly, Ina MATUƘAR jin daɗin comments naki, Allah yabar ƙauna*

________________________________________

*☀ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION☀*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*

Karki karanta idan baki biyaba


________________________________________

...............Tsugunawa yayi akusa da ƙafafuwan ta yace " Umma na kiyi haƙuri a makarantar mu malamin mu yace mai haƙuri yana shiga aljanna."
Kallon shi tayi tace, "kaci abinci kuwa?"
"A'a Umma, Baffa yace naɗakko mana abincin muci acan."
Tashi tayi ta ɗakko tuwo da miya tasaka a tiren silver da ruwa acikin kofi tabashi tace, kayi sauri ka kai mishi."
Harya ɗauki abincin zaifita yaji hayaniyar yaran gidan sunshigo da ihu.
Sadauki yace, Umma wallahi yaran nan basajin magana, kullum inayi musu magana akan surinƙa shigowa gida da sallama, amma basaji, da zanyi magana kuma saikiji Inna Larai sunfara faɗa wai nacika iyayi."
"Kaci gaba da yi musu magana, in Sha Allah watarana zasu gane."
Fita yayi yana mata sai ya dawo.
A tsakar gidan yagansu ko wanne da sandar sa ahanu suna hira cikin halshen fullanci, zai wuce mauɗe yace, "kai ɗan shegiya zonan ka ajiye abincin nan kaje ka kawo mana ruwa."
Kallon shi yayi baice komiba yayi hanyar fita, mauɗe ya tashi ya iske shi yace, ina maka magana kayi kunnen uwar shegu ko, aradun Allah matuƙar baka ijiye abinshin nan ba sai mun maka jina-jina."
Kallo ɗaya Sadauki tayi mishi yace, kabani hanya nawuce Baffa najirana agona."
Mauɗe yasa sanda ya buge tiren abincin ya zube, Abdul Azeez yace, "Wallahi kaci darajar abu ɗaya, badan hakaba da nanuna maka cewa kai ƙaramin ɗan iska ne."
Mauɗe yayi wani ihu irin na ƴan farauta yace, "aradun Allah idan kasan shewa wannan hegiyar matar ta haife ka da jini bismillah."
Umma ce tasoma fitowa taga abincin da tabayar akai ma Baffa anzubar, batace komi ba tanufi wajen ta kwashe kayan tanufi Kitchen, sauran yaran suka tuntsure da dariya suna kallonta.
Hakan ya sa Abdul Azeez zuciyar shi ta Fulani ta motsa, ya wawuri mauɗe da ƙarfi yamaka a ƙasa, sauran yara ukun suka soma ihu wai Abdul azeez zai kashe mauɗe.
Laure da Inna wuro suka fito da gudu suka nufi kansu, Larai ce ta ɗauki itace tana ƙoƙarin kwaɗa ma Abdul azeez yayi saurin matsawa ta kwaɗa ma mauɗo.
Ihu yasaka yana faɗin wayyo Allah.
Inna wuro ce ta nufi inda yake tana ƙoƙarin ɗagashi.
Yadado ce tashigo gidan ɗauke da karare tana faɗin, "wai meke faruwa tundaga waje nake jin hayaniya?"
Ganin abinda yake faruwa tayi saurin zubar da kararen hanun ta tanufi inda mauɗe yake akwance yana ihu wayyo kayi na.
Yadado tace, "hande enboni wanene ashikin ku yakeson kashe mauɗo?"
Bala yace, "faɗa sukeyi shida Abdul Azeez shine yaɗauki ƙaton ishe ya narke mashi aka, kuma uwar shi yana kallon ta."
Yadado tasoma masifa, "bazai yuwu ba akashemin jika, ina shi Manu yake, maza kuje garke kunshe ina neman ta."
Bala da suleh suka fita da gudu suna murna yau za aduke Abdul azeez.
Larai ce tasa kuka tana faɗin, "wallahi idan yarona ya mutu kaima saika mutu."
Yadado tace, "yi shiru ai uban nashi zaidawo yau sai yayi maganin mayyar uwarshi."
Bala tare suka dawo da Baffa.
Yadado tana ganin shi tace, "yau ko ni ko wannan mayyar matar taka, tunda naga alama so take takashe ɗan masu gida dan taga ita bata aihuwa."
Baffa cikin sanyin murya yace, "mai yafaru Yadado?"
"Shiga ciki kaga abin da yafaru, Kuma yau inason ka saki wannan shegen matar naka."
Ɗakin Yadado yashiga yasami mauɗo a kwance sai faman ihu yake wayyo kaina.
Zama tayi kusa dashi yace, "sannu mauɗo ya akayi haka ta faru?"
Mauɗo yace, "innar Audu ce tasa yabigeni da sanda, dan natambaye ta abinci na."
Baffa yasan cewa wannan sharri ne kawai aka kulla ma Umma danhaka yace, "yi haƙuri anjima zansiyo maka kifi da burodi kaji."
Mauɗe jin yace zai siya mishi kifi da burodi yace, "yawwa Kawu nagode, kai kana da kirki."
Girgiza kai kawai yayi yafita daga ɗakin yadawo cikin gidan yasamesu atsaye cirko cirko.
"Wani mataki ka ɗauka Manu?" Yanzu ashe yaro ya aikata ba dai-dai ba ka ƙyaleshi."
Manu wato Baffa yace, "Yadado kiyi haƙuri zansan abinda zanyi."
"Banyarda ba, matuƙar baka ɗau hukunci akan Habi ba (umma) zanyi maganinka, yanzu abinda nakeso dakai ɗauki tarfon ka kiramin iyayen yaron nan."
Baffa yace, "Yadado dan Allah kiyi haƙuri, wannan matsalar ba wani babban matsala bace."
Larai tasa kuka tace, "dama haka zaka faɗa mana, dan kaga yaron ka yacutar da nawa yaron, to wallahi bazan yardaba." ta zauna tamiƙe ƙafa tayi ɗai-ɗai tana rusa uban ihu.
Umma tana ɗaki tanajin sharrin da akayi musu, addu,a tayi akan Allah yakawo sauƙi awannan zaman da sukeyi.

*****

Bayan sallar isha,i kowa ya halarta acikin gida, manya da yara.
Inna tace, "dama yau ina da magana daku."
Bello saifaman huci yake cike da izza yace, "Yadado karfa kishe zaki ban haƙuri, dan aradun Allah abinda yaron Manu tayima yarona yasin saina rama mata, yo ai aihuwa batafi aihuwa ba."
Inna tace, " yi haƙuri Bello ai hukunshi nakeson yanke wa yanzu, kuma muddin Mutum yaƙi bin shawarana billahil lazi saina ɗaga mishi nono."
Jafaru yace, "Inna yasin wannan karon dole Manu ya saki wannan mayyar matar tashi."
"Biba inason kisani daga yau kinfita ashikin dangin mu, dole manu ya sawwaƙe maki, dan haka manu kasaki yarinyar nan saki uku."
Baffa ji yayi ƙirjin sa yabuga dam,...


Read / Download ABDULAZEEZ SADAUKI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album