Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

UBANA NE KO KISHIYATA Complete Hausa Novel Document by UBANA NE KO KISHIYATA


UBANA NE KO KISHIYATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 83070



UBANA NE KO KISHIYATA

Reading Time: 6 Hours

Added On: 18, Oct 2024

Author: Nernah Maryam (Martey Bee) ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 406.85 kb

File Type: txt

Views: 826+

Download: 1152+

Last download: 3 days ago

Description/Story: 😭😔UBANA NE KO KISHIYA NA💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

Gargadi........

Wannan littafin mallaki Na ne kuma bana yi shi don cin zarafin wani ko wata bane hasalima duk wanda ya ga ko ta ga labarin yayi daidai da tsarin rayuwar ta ko makamancin hakan to ina me bada hakuri,

Sannan ban yarda wani ko wata su juya mun labari Na ko su canza ba tare da neman izini Na,

Da sunan Allah me rahma me Jin kai,Allah yanda Na fara rubuta labarin nan lafiya Ubangiji ka sa Na gama shi lafiya,

..............
Page one

**********Bauchin Yakubu

GRA

Karan hayaniyan mutane tare da bugun gate in wani tangamemen gida ne yayi alarming securities in gidan kan bakin da me gidan ke expecting tun safe sun iso,

Sunday ne ya mike tare da kallon mal Iro yace Iro I think they are here already make I do quick and open this gate before oga change am for me,dariya mal Iro yayi tare da bantaran goron sa domin shi Sam ba gane wanga turanci na Sunday yake yi ba,normal turanci ma ya ya kare da shi balle wata broken,

Shi ko Sunday cikin sauri ya tashi tare da nufan black gate in saida ya bude kofar ya leka ganin dandazon yan jarida ne ga sanya shi saurin bude gate in gaisuwa suka yi exchanging bayan sun shigo cikin premises in gidan,

Masha Allah Na fadi sakamakon karewa gidan kallo da nayi,wata gida ne Wanda ya amsa sunan sa gida babban duplex building ne wanda aka kawata wajen gidan da flowers kaloli daban daban,kallo daya za ka yi wa gidan ka san mamallakin sa ba karamin attajiri bane domin duk layin zan iya cewa gidan Sen RILWANU AUDU WAZIRI .... Ya fi Na kowanne kyau,

Sa'eed ne ya fito daga cikin main house in gidan sanye da black and white uniform, shine mafi kusanci da Senator Rilwan,

Cikin fara'a ya karasa gurin yan jarida domin an riga an San da zuwan su,sun zo ne domin tattaunawa da Sen RILWANU AUDU WAZIRI wanda aka tsayar a partyn su domin yin Takaran Gwamnan jahar Bauchi,ganin zabe ya karato ne ya sanya ya hada zaman shi da kanshi domin bayyanar da wasu raayoyin shi tare da amsa wasu yan tambayoyi da suke ta son masa,

Ba karamin lucky da dadi yan jaridan da suka samu zuwa suka yi ba domin sun San ko banza bara su koma hannu Na dukan cinya ba domin Sen RILWANU an san shi da halin kyauta da son jamaa ka'ida ne duk wani Wanda ya zo ganin shi to baya zuwan banza,

Iso Sa'eed yayi musu zuwa ga wani babban Hall dake cikin gidan Wanda an yi shi ne daman domin taro,

Hall ne babba me kyau dauke da kujeru da Dan karamin tables Wanda ke dauke da snacks and drinks a kai,

Bismillah have a seat Sa'eed yace yana murmushi su din ma murmushin suka yi tare da fara kokarin zama,baran sanar da Sen zuwan ku kafin nan ku fara shan ruwa,

Ya wancin gurin ba karamin dadi suka ji ba domin ka je inda za a karbe ka a mutunta ka har a baka abun makulashe ma wani abu ne,nan suka hau Dan ciye ciye da dan shaye shaye kun san mutanan mu ba a ganin bati a bari lol....

Kusan 15 mints da fitan Sa'eed suka fara Jin alamun tafiya tare da magananganun mutane Wanda ya tabbatar musu gwamman goben su ne ke tafe,da sauri suka yi arranging kansu tare da kokarin setting cameras in su domin kowa so yake ya fara daukan sa a hoto,

Kofar aka bude Wanda securities in sa ne kusan su biyar a gaba sanye da irin same kayan da ke jikin Sa'eed sai wasu biyar in a baya sai kuma wasu mutane su uku a tsakiya ko wannan su ya hade cikin dakkakiyar shadda sai kyalli kawai suke zuba wa da kamshi,

Da sauri yan jaridan suka Mike suka fara daukan su a hato,daya daga cikin mutanan ke kirarin Senator Rilwan sai kayi gwamman mu Na gobe insha Allah sai ka mulki jahar Bauchi...

Wanda ake kira da Senator RILWANU AUDU WAZIRI Na bi da kallo,masha Allah na furta sakamakon ganin babban mutum me kamala sanye yake cikin farar shadda Wanda ta ji aiki da brown zare ta ko xauna masa damas a jiki duk da shi din ba ramamme bane ba kuma za a kira shi da kato can ba,

Brown hula takalmi tare da links ne a jikin sa,saidai duk gayun nan da ya ci yayi lacking Abu daya shine murmushi,

A cikin yan jaridun ne daya ya kalli daya yace Salman ya haka yau kamar abunda ke damun Sen domin daga fitowan sa jikin shi a sanyaye and ka dubi fuskan shi ko digon faraa babu bayan kuma shi mutum ne me yawan faraa,

Hmm Tahir manta kawai ni kaina jiki Na yayi sanyi domin tun duban farko da nayi masa na gano damuwa lulube a fuskan sa,ni dai ko ma miye ke damun shi Allah ya sa kar yayi affecting Alkhairin da zai mana,

Daya daga cikin yan jaridan ne ya tashi tare da mika gaisuwa bayan Alhaji Rilwan ya zauna tare da manyan Aminan sa guda biyu,Alhaji Salis da Alhaji Kabiru,

Nan suka shiga masa tambayoyi akan zaben da ke tahowa ya yake ganin abun zai kasance tunda yana da abokan hamaiya dukda ma shi din mutum ne me Alkhairi hannun sa a bude yake ya sanya mutane ke kaunar sa sosai,

Mikewa yayi sai a lokacin Na ga yayi murmushi farko dai da sunan Allah ya fara sannan ya mika godiya sai kuma ya fara jawabin sa kamar haka......

Hakika farin jini da soyayyan da ya samu a gurin mutane daga Allah ne domin in za a tuna sanda ya fito neman senator haka nan mutane suka yi ta kauna shi,ya gode wa Allah da irin daukaka da nasarorin da ya samu a rayuwar sa sannan ya Na mika godia ga dumbin jamaar garin Bauchi bisa yadda da kaunar da suke nuna masa kuma in sha Allah muddum ya zama Gwamma to zai yi mulki bisa tsoron Allah zai kaunaci talakawan sa zai.nan dai yayi ta jero irin cigaban da zai kawo wa garin Bauchi,

Nan ko aka sanya tafi ana fadin sai kayi Gwamma in sha Allah uban marayu kuma gatan Bauchi,

Dan gurban ruwa yayi sannna ya cigaba da jero jawaban sa ,yanda Hall in yayi tsit baka Jin muryan kowa sai nashi,

Kamar daga sama suka ji an banko kofar Hall in kafin securities su kai ga sanin waye har ta shigo,

Sanye take da ash in dogon rigan material kanta ko dankwali babu dogon bakin suman kanta ya kwanto har kafadun ta,kafafunta ko slippers babu,da gudu ta hayo kan stage in,

Kallon Sen Salis yayi yace Alhaji kamar Princess nake gani lafiyan ta kuwa??

Wata kallan gumi ne ya tsattsafo wa Sen a fuskan shi wanda ya sanya bayan hannun sa ya goge ji yayi wani irin balain ciwon ciki da zafi ya durnuke shi lokaci daya duk da uban AC's in da ke cikin Hall in,

Tafi ta shiga yi hannuwa bibiyu tana yi tana fadin wow wow nice one, so tsayawa kuka yi don kuma baku da aikin yi irin sa yana cika ku da maganganun karya da yaudara ku kuma kuna saurara kuna cewa sai yayi sai yayi me.ta kare cikin murya me karfi idanun ta jajjawur hawaye Na zuba,

Wannan mutumin ne wai har kuka tsayar matsayin Dan Takaran ku wai wannan mugu mara mutuncin mutumin Wanda babu ko dikon tsoron Allah a tattare da shi kuke so yayi mulkin jahar Bauchi inalilahi wa ina ilaihi raju'un da kuwa masifa da bala'i ta afku a garin nan,

Cikin sauri Alhaji Kabiru ya tashi yace keeee NADIYA kina da hankali kuwa wani irin shashanci da iskancin banza ke damun ki ko dai kin yi shaye shaye ne in to hauka kike to kiyi maza ki dawo hankalin ki uban ki mahaifi kike jefa da irin wanna kalmomin,

Cikin sauri ta katse shi da ka dakata mun karamin Dan iska ai ba da kai nake ba sarai Na san waye shi, Dan juyi tayi tare da nuna SEN in tace wai ko ba the greatest SEN RILWANU AUDU WAZIRI ba the most richest man in Bauchi ko ba shi ba,Wanda a idanun duniya yake Na Allah amman a badini fa,Allah Ubangiji ya tsine maka Daddy ya Allah Na roke ka,ka hada shi da masifan duniyaa da ba lahira babu masifa kamar kasancewa yar ka da nayi I regret being Ur daughter you are indeed a disgrace to all fathers around the world da yardar Allah bara ka
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download UBANA NE KO KISHIYATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album