Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR AZIZU DA AZIZA Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR AZIZU DA AZIZA


HIKAYAR AZIZU DA AZIZA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 19570



HIKAYAR AZIZU DA AZIZA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Prof Ibrahim Malumfashi ,Bukar Mada ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 95.9 kb

File Type: txt

Views: 717+

Download: 199+

Last download: 2 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

01 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO

Waziri ya ce, madalla, sa’annn ya fara " ka sani wannan labari ne na mai bege da da abin begensa. Ka sani ya kai sarki mai arziki cewa labari ya same ni na mai bege da abin begensa da mai zance tsakaninsu da abin da ya gudana gare su na al'ajabi mai gangarowa abin da ke gusar da bakin cikin zuciya.
A wani lokaci mai tsawo da ya gabata, an yi wani birni da duwatsu suka kewaye shi ana ce da shi Koren Birni, sarkin birnin ana kiransa Sulaiman Shah. Ya kasance mai kyauta ne da kyautatawa, mai adalci da aminci da alheri da karramawa. Yana da kwarjini da mutunci da karramawakyautatawa, mai adalci da aminci da alheri da karramawa. Yana da kwarjini da mutunci da karramawa, ga shi yana son jama'a matafiya su rika shiga kasarsa. Sunansa ya yadu a ko'ina cikin duniya, domin ya jima sosai a bisa gadon sarauta yana yaki da aminci ga masoyansa. To sai dai shi wannan sarki gwauro ne, ba shi mata balle d'a. A tare da shi akwai wazirinsa wanda yake tarayya da shi wajen kyawawan halaye. Suna zaune a kan haka wata rana ya aika waziri ya zo ya same shi ya ce masa, "ya waziri, zuciyata ta baci, hakurina ya gaza, jikina ya raunana, na kasance yanzu nan ba ni da aure, ba ni da mata ballantana na samu magaji. Wannan kuwa ba ka'idar sarauta ba ce, idan saraki suna mulki sun fi jin dadin su mutu su bar magadan da za su hau gadon sarauta ko bayan ransu. Son samu a samu zuriya mai yawa saboda su kara karfi. Kuma manzonmu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa, "ku yi aure ku hayayyafa ku zama masu yawa, domin na yi alfahari da ku ranar lahira." Yanzu me kake gani waziri? Ina dabara?" Da waziri ya ji haka, hawaye ya zubo daga idanunsa, ya sa hannu ya shafe sannan ya ce, "Allah ya ja zamanin sarki, ni kam na nesanta kaina da jaye - jayen ubangiji mai rahama mai jin kai ba. Ko kuwa kana so na jefa kaina ciki azabar Allah? Ina ba ka shawarar ka sayo kuyanga." Sarki ya yi ajiyar zuciya ya dubi waziri ya ce, "Waziri ka sani cewa idan mai mulki ya sayi baiwa ya maida ita sad'aka bai san asalinta ba, bai san danginta ba, ba zai gane aibunta balle ya guje mata. Idan ya sadu da ita ta samu ciki ta haihu da shi, ta yiwu a samu yaro mara jin magana mai zubar da jini, mai girman kai. Ita mace kamar kasar gona take, inda yake juji ne mara kyau zai fitar da shuka mai kyau amma ba za ta yi karko ba. Inda yake akwai fako da yumbu za a sha wahalar tattalin shukar kafin ta girma, amma za ta zama mai karko a karshen lamari. To haka nan dan matar na iya gadon halinta har ya zamana Allah ya yi fushi da shi. Saboda haka, ni ba zan sayo kuyanga na mayar da ita sad'aka ba, nufina shi ne na samu 'yar sarki daga sarakunan kasashen musulmi wadda take kyakkyawa mai hankali kuma mai asali. Idan ka san wata daga 'ya'yan sarakuna to ka fada min na tafi na nemi aurenta a gaban shaidu wadanda za su zama mana masu albarka da iznin mai duka. Waziri ya ce, "Allah ya ba ka nasara, kuma ina addu'ar Allah ya sa ka cimma burinka." Sannan ya kara da cewa, "ka sani ya sarkin zamani labari ya zo min cewa Sarkin Farar kasa, Zaharshahu na da wata 'ya wadda ta kai matuka wajen cikar kyau da kyawon hali. Kalamanta na rudar da mai sauraro, ganinta na gigita masu gani, babu tamkar ta a zamaninta. Ta cika duk wasu siffofi na cikar halitta, kwayar idanunta baki suduk fuskarta na sheki, tana da manyan nonuwa masu gigita mai gani da manyan kuturi sun zauna inda ya dace. Idan ta matso kusa sai mai gani ya fitinu, idan ta juya baya sai mutum ya suma. Ita ta kasance tamkar yadda mawaki ke cewa:
Ita ta kasance mai kuturi mai kyawo,
Mai hasken sharaba da fuska mai haske
Hasken wata bai kai ya haske nata ba
Ya zarce yakutu da zinariya a haske
Hakoranta na walkiya in tai dariya,
Jikinta ko na walkiya ba sassake
Manemanta da yawa sun hallaka,
A wajen kallonta sun mace babu ke
Da waziri ya kare waka, ya dubi sarki Sulaimanu Shah ya ce, "ina ba ka shawarar ka aika da wani mutum mai girman daraja da sanin wayon zaman duniya zuwa ga mahaifinta ya nema maka auren ta. Kuma wanda za shi din ya zamana mai iya magana domin sarkin yana da zafin rai. Domin kuwa hakika ita ce ta dace da kai, babu tamkar ta a nan kusa da nesa. Za ka ji dadinta sosai yadda ya kamata, kuma da sannu sai ka ga Allah ya cika maka burinka game da ita." Sarki ya ji dadin wannan kalami, kirjinsa ya cika da farin ciki, bacin ransa ya gushe. Ya dubi waziri ya ce, " wannan bayani naka daidai ne waziri, kuma babu wanda ya dace ya tafi wajen sarkin nan sai kai. Domin na yaba da kwazonka da mafificiyar dabararka. Yanzu ka tafi gida ka shirya ka tafi gobe da duk wadanda suka kamata ka nemo min auren wannan matar. Da fatan kuma ba za ka dawo ba sai da ita." Waziri ya amsa, "na ji na yarda."
Waziri ya tafi gida ya shirya kayan tafiya, ya samu kyaututtuka manya – manya wadanda ake yi wa sarakuna na daga duwatsu masu daraja da tufafi da sauran su. Ya shirya ingarmun dawaki na hawa da kayan fada da sulken yaki irin kirar Annabi Dauda. Sannan ya shirya akwatunan dukiya mai yawa wadda baki ba zai iya lissafa ta ba. Sannan ya kawo rakuma da alfadarai da kuyangi dari. Sannan ya shirya da hakimai dari su raka shi. Aka kawo laima bias abin hawan waziri jama’a suka riki tutoci suka rankaya. Kafin tashinsu sai da sarki ya yi masa nasihar kada ya jima ya dawo da wuri da zarar bukata ta biya. Bayan sun tafi sarki ya zauna cikin kaguwar su dawo masa da labari mai dadi, kullum yana zuba ido da kasa kunnen dawowar waziri. Ayari kuwa suka yi ta tafiya dare da rana safe da yamma, har ya zamana bai fi tafiyar wuni guda ba zuwa birnin Baira’a, nan waziri ya yi umarnin a sauka gefen wani kogi. Daga nan ya tara makusantansa yatabbatar wannan aure bisa kayyadajjen sadaki. Sannan aka yi addu’a kowa ya shafa. Waziri ya tashi ya fito da kayayyaki na kyaututtuka da na ado da na kamshi duka ya shiga rarrabawa mahalarta bayan wanda ya ajiye wa sarki. Sarki ya shiga domin kintsa ‘yarsa da kuma hidima ga waziri da mutanensa domin yin biki don nuna jin dad’in faruwar wannan al’amari. Aka yi ta shagalin biki Waziri ya yi ta rabon kyaututtuka iri – iri ga manya da kananan fadawa. Suka wanzu cikin wannan sha’ani na biki har wata biyu cur ana ta annashuwa da jin dadi mai ban kaye da tausasa zukata.
Bayan wannan aka shirya komai da komai na bukatar amarya, sarki ya shirya wata babbar rumfa a nan kofar fada, aka yi ta shirya wa kayanta wadanda ke cikin akwatuna manya – manya. Sannan aka hada da kuyangi na kasar Turkawa da na Girkawa da Rumawa kuma aka tanadar wa amarya wata babbar ma’ajiya ta dukiya da sauran duwatsu masu daraja. Aka sa alfadarai biyu su dauke su. Sannan aka kawo darbuka mai kyau mai cike da ado na musamman aka dibiyawa taguwa. Sarki ya zo da kansa ya yi musu rakiya farsakai masu yawa, sannan ya yi mata nasihar bin miji da hakkin aure. Sannan ya yi sallama da waziri ya juyo gida cike da farin ciki.
Waziri da ‘yar sarki Gimbiya, amarya da sauran jama’a suka rankaya suka yi ta tafiya ba dare da rana har ya kasance tsakaninsu da birnin bai wuce kwana uku ba. Sannan ya tashi wakili ya garzaya domin yin albishir ga zuwansu tare da amarya. Sarki ya cika da farin ciki mai yawa, ya yi wa jakadan nan karimci mai yawa gami da sutura da sauran kyaututtuka, ya umarci manya fadawa su shirya domin zuwa taryen wannan tawagar amarya. Kowa ya shiga cikin kayan adon sarautarsa sannan suka dunguma da tutoci masu kayatarwa zuwa bayan gari. Sarki ya yi umarnin kowa da kowa ya fita babba da yaro namiji da mace su fita domin taryen amarya. Lokacin da mutanen gari suka ji haka fa sai mamaki ya kama su, duk suka fito da hanzari, amma Sarki ya ce kada a shigo da ita cikin gari, sai da dare. Manya manyan mutane, su ne suke yi wa wannan amarya ta Sarki kowace irin hidima, kafin ta iso cikin garin. Har wa yau kuma Sarki ya sa aka caba wa hanyoyin cikin gari ado ko’ina.

ZANCI GABA02 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO

Ita kuwa hanyar da amarya za ta biyo kuwa, sai aka rufe ta da zannuwan alharini masu alfarma, sauran hanyoyi kuwa aka yi musu ado da dardumai, aka daura fitillu masu launi iri iri. Sa'an nan a kofar fadar aka daura wata irin makekiyar fitilla mai hasken gaske,amma hasken nata kore ne shar, a gefen hanyar da amarya za ta shiga zuwa gidan Sarki aka daza mutane. Can sai ga amarya ta dumfaro, kuyangi na gabanta, barori suna biye da ita a baya, amaryar kuwa ta ci ado irin na zamani mai kayatarwar gaske, musamman mahaifinta ya hada ta da wadansu 'yan moren matansa, don su rika shirya mata ado, su kuwa wadannan 'yan moren sai da Sarki ya tura su wata kasa mai nisa don su koyo yadda ake yin ado, suka gwanance sosai. Sa'an nan suka dawo gida, suka ci gaba da yi wa 'yar nan tasa hidimar ado.
A daman amarya kuwa askarawa ne wadanda ake cewa sai baba-ta-gani ke kewaye da ita haka ma a gefen hagunta, ita kuwa tana tafe a cikin darbuka kan taguwa har ta isa gidan Sarki, mutanen gari duk suka yo caa suna kallonta, ko’ina sai bushe-bushen bigila da kade-kaden ganguna ke tashi, mazaje sai karkada masu suke, suna jefa su sama, suna cafewa, abin gwanin ban sha'awa. Kamshin turare ya bice wurin ko’ina Dawakai kuwa sai barade ne ke sukuwa da su, wuri duk ya rude babu masokar tsintsiya, babu irin adon da ba ka samu a wurin. Dabbobi kuwa har na daji an hau kansu rannan, ga giwaye, ga damisu, ga zakoki, da dai sauransu birjik. Mai tutsu yana yi, mai ruri yana yi, mai yakuta yana yi, har dai aka isa filin kofar fada, sa'annan Waziri ya bi da amarya ta wata kofar asiri, wadda aka fasa musamman saboda amaryar.
Lokacin da amaryar nan ta sauka, sai duk wuri ya haske, saboda kyawon fuskarta, da kyallin kayan jikinta. Fili ya haske saboda kayan lu'u-lu'u, da ya ke jikinta, sai ka ce wata ne ya sauko kasa. Sa'ar da dare ya yi aka sake bude kofar nan ta asiri za a fito da amarya zuwa gidan da Sarki ya sa aka shirya mata. Barori suka jeru cikin layi, amarya kuma ta iso da kuyangi a gaban ta sai ka ce wata a tsakanin taurari, ko kuma goran lu'u-lu'u a tsakanin kananan duwatsun lu'u-lu'u, wanda aka shirya a zare. Bayan an shigar da amarya cikin gida, sai kuma aka shirya kayayyakinta cikin daki, su gadon lu'u-lu'u, wanda aka zuba wa shimfid’a mai daraja, an kuma zayyana bangon dakin da zane na yakuti, amarya ta shiga daki ta zauna kan gado. Sarki kuma ya shigo wurinta, Allah ya sanya son ta a zuciyarsa, nan take a wannan ranar ya dauke budurcinta, hankalinsa ya kwanta daga jarabarta da ya sha fama a kai, domin kuwa duk watannin nan da Waziri ya yi a wurin neman aure can a garin Madinatul Baila'a, tun ran da ya tafi Sarkin sai ya kasa barci, ya kasa zaune, ya kasa tsaye, yana tunani kan wannan yarinya da Waziri ya ba shi labarinta tun kaftn ya gan ta ya fada jarabar son saduwa da ita.
Bayan da Sarki ya dauki budurcin yarinya sai ya fito filin fada ya sa aka shirya bidi'a kasaitacciya, aka kuma shirya walima muhimmiya, a wurin walimar nan babu nau'in sha da babu wurin, balle na wajen abinci, su naman 'ya'yan shila, da na sauran tsuntsayen daji, da dabbobin daji. A bangare kayan sha kuwa ga su zuma, ga giya iri daban-daban. Sarki ya sa aka nemo gwanayen masu kade – kade suka yi ta yi, ana annashuwa. Wasu kuma suka hau dawakai suka yi ta sukuwa suna nuna bajinta iri - iri. Haka aka yi ta biki da wasanni har kwana uku sannan kowa ya watse.
Bayan amarya ta yi kamar wata guda sai ciki ya soma bayyana a cikin gida da wadanda ke tare da ita. Tun zuwanta kuwa Sarki bai sake fitowa fada ba, sai bayan watan nan guda, sa'annan rannan ya fito fada aka ci gaba da zaman majalisa, aka ci gaba zarafin mulki. Kwanci tashi har watannin cikin yarinya suka cika, wata tara daidai. Rannan sai ta shiga nakuda, Allah ya saukaka mata wahalar nakuda, a cikin sauki, ta haifi da namiji, mai shaidar arziki a goshinsa, yana ta kyalli, aka yi sauri aka sami Sarki a Majalisa aka ba shi labarin haihuwar. Kada ka so ka ga fuskar Sarki a rannan, ta cika da fara'a, ya yi farin ciki matuk’a, ya kawo kurfi da kayayyaki na alfarma ya bai wa masu albishir, nan da nan aka rufe zaman Majalisa. Sarki ya tashi ya shiga cikin gida ya iske Sarauniya, ya dube ta, ya dubi yaron da aka haifa, ya ga hasken nan a fuskar yaro, ya sake dubar yaro, ya yi makakin irin kyawon wannan yaro, ya tabbata ya dace da wak’ar shahararren mawaki da yake cewa a wasu baituka:
Allah ya ba shi kyau, ya ba shi daukaka,
Zaki na sansani, na daula, tauraro, tsinin
Mashi da kaifin takobi da askarawa da mayaka
Dole duk sun durkusa yayin da ya zo,
Amma fa kada ka dora shi kan mama mai tudu,
A’a kai dai dora shi bayan doki shi ya fi a gare shi
Domin kuwa shi jinin mazaje ya fi dadin sha a gun sa.
Bayan da Sarki ya kare wa jinjiri kallo sai Unguwarzoma ta zo ta dauke shi ta yanke masa cibiya ta saka masa tozali, da rana ta kewayo aka rada wa yaron suna Tajul Maluki Harun. A ranar bikin an yi shagali mai yawa, har ya fi na lokacin tarewar amarya. Shi ke nan...


Read / Download HIKAYAR AZIZU DA AZIZA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

6 Comments On HIKAYAR AZIZU DA AZIZA
avatar
hamadou-8

7 months ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

7 months ago

Reply

Telecharger

avatar
hamadou-8

7 months ago

Reply

Download

avatar
hamadou-8

7 months ago

Reply

Download

avatar
taskar

7 months ago

Reply

Replying to hamadou-8

idan ka gagara downloading ne zaka iya karantawa anan kyauta ai

avatar
hamadou-8

7 months ago

Reply

Hamadou saadia

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album