Join Our WhatsApp Group

BAKAR DAULA Complete Hausa Novel Document by BAKAR DAULA


BAKAR DAULA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 71910



BAKAR DAULA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 06, Oct 2023

Author: Ameera Adam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : FIRST CLASS WRITER'S ASSO

Author Phone : 0706 206 2624

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 365.84 kb

File Type: txt

Views: 841+

Download: 500+

Last download: 1 hour ago

Description/Story: [11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

1

A duk lokacin da Allah (S.W.A) ya ƙaddara wanzuwar hallitar Ɗan adam a doran ƙasa, ko ya ƙi ko ya so akwai waɗansu abubuwa da suke yin jerin gwano a gangar jiki da ruhinsa. Inuwa! Wata aba ce da Ubangiji ya ke ƙaddara wanzuwarta manne a jikin kowanne abu, walau mai rai ko akasin haka. A kodayaushe tana bibiye da su matuƙar bawa zai zuba maganansa zai lura da haka. Kalmar ƙaddara! Kalma ce mai ɗauke da rassa biyu walau ƙaddara mai kyau ko kishiyarta. Ƙaddara abokiyar tagwaitakar inuwa ce domin bawa ba ya taɓa shallake wa ƙaddararsa, sanin haka ya sa na fahimci karin maganar Malam bahaushe ta: 'Tun ran gini tun ran zane." ta zauna ɗaram kwatankwacin yadda ake ɗora ƙwarya a gurbinta.

10/06/1022
Shekara Dubu Ɗaya baya.

Hankalinsa ya fi na kowanne lokaci kai wa matuƙar ƙolokuwar tashi, yana tafe yana taku da sandarsa Waziri da sauran muƙarraban cikin daular suna take masa baya. Tamkar waɗanda saƙon mutuwa ya dirar wa haka fuskokinsu suka fasalta saƙon da ke ƙunshe cikin birnin zuciyoyinsu. Sarki Damina yana kai ɗora ƙafarsa kan jan dutsen da ke a matsayin matattakalar benen hawa tsauni tsidik! Wani gajiyayyan talakansan ya dira a gabansa cikin firgice da tashin hankali, kuka yake tamkar hawayen idanunsa za su ƙare. Ya ruƙo ƙafafuwan Sarki Damina a ɗimauce yana faɗin, "Ya kai babban Sarki, Sarkin sarkunan duniya bakiɗaya sarkin da yake share mana hawaye. Ka taimaka ka roƙar mana afuwa wurin Sarauniya Sha-kundum, yanzu haka ɗana Rabo yana can yana aman jini ta hanci ta baki don mai ɗakina naƙuda take jini ya ɓalle mata tana gangarar..." Tun bai rufe baki ba Sarki Damina ya daka masa razananniyar ƙarar da sai da hantar cikinsa ta kaɗa, yana shirin sake magana Sarki ya fisgi takobin da ke maƙale a kafaɗar Waziri kafin Bawan ya yi wani yunƙuri tuni ya sauke kansa ƙasa. Da sauri wasu ƙaratan Dogarai suka ƙarasa wurin suka zube suna yi wa Sarki godiya, "Godiya muke Sarki Damina mai masoya da yawa, Sarauniya Sha-kunduma ta yi ruƙo da hannayenka. Haushin zuciyarta ya gushe domin ta faɗa mana hanyar maganin samun lafiyar Yarima, idan wannan bai wadatar da kai ba ka yi mana umarni mu kawo maka wani ko da a cikin mu ne ka sake datse rayuwarsa matuƙar zai sanyaya zuciyarka" Bai tanka musu ba ya miƙa wa Waziri takobin da ke ɗigar da jini, har sun cicciɓi gawar bawan da kansa tuni ta samu mutsuguni a gefen wata bishiya, Sarki ya dube su yana cewa. "A gaggauta ƙone gangar jikinsa tare da yaron nasa da ba shi da lafiya. Ita kuma mai ɗakinsa a zaro jaririn cikinta a kai wa babban dodo sannan a salwantar da gangar jikinta" Yana gama magana ya haye kan tsibirin maƙarrabansa suna biye da shi a baya.

Kamar yadda yake farillah a wurinsu duk lokacin da za su shiga cikin kogon dutsen a yanzu ma sai da suka aiwatar, sai da kowannensu ya saka ƙanƙanuwar aska ya yanki gefen ɗan yatsan hannunsa suka yarfar da jinin a jikin wani sassaƙaƙƙaen gunki, hannun gunki ɗauke yake da kwari da baka daga bayansa an jingina masa takobi a jiki. Kansa a sunkuye yake alamar ƙasƙantar da kai ga wani dungulmin kan mace da suka ɗora masa a gadon bayansa. Sarki Damina ne ya fara yin gaba sannan su Waziri suka rufa masa baya, daga bakin shiga dutsen suka tsaitsaya don sun san ko karan hauka ne ya cije su ba za su taɓa haure bakin ƙofar dutsen ba. Kai tsaye Sarki Damina ya kutsa ciki sandarsa ta zame masa abokiyar tafiya. Daga tsakiyar kogon dutsen ya hangi Boka Mai zamani zaune da wasu ƙanana tukwane a gabansa, daga shi sai ganyen ayaba wanda ya yi makari don rufe al'aurarsa.

"Yau ba ranar zuwan ka ba ce kamar yadda yake a bisa al'ada, me yake tafe da kai don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa." Boka mai zamani ya faɗa yana karkatar da hankalinsa wurin Sarki Damina. Duk tsananin izza da taƙama irinta Sarki yau ya sauke ta a gefe ya fusakanci Boka yana mai bayyana damuwarsa, Sarki Damina ya zube gwiwowinsa kamar wanda ya aikata wani mummunan zunubin da yake neman gafara. Murya ɗauke da damuwa ya furta, "Ya kai Boka Mai zamani lamarin halin da talakawanmu suke ciki tabbas tura ta fara kai bango. A yau mun wayi gari da samun ɓillar annobar haɓo a cikin gari fiye da tsammani, babban abin da ya ɗugunzuma hankalina abin bai tsaya iya waje ba hatta ahalina na fuskantar wannan barazanar, a taimaka a roki Sarauniya Sha-kundum ta yafe mana tun da laifin wani ba ya taɓa shafar wani." Boka mai zamani ya miƙa masa busasshen hannunsa mai ɗauke da zaƙwa-zaƙwan farata, taurin hannunsa tamkar busasshen katako sannan ya ce, "Ina tukwicin ziyarar Sarauniya Gunki Sha-kundum kafin na san abin yi? Domin sanin kanka ne tuni bakin alƙami ya riga da ya bushe." Sai a lokacin Sarki Damina ya tuna da ƙoƙon tukwicin ziyara, cikin sake ƙanƙan da kai ya furta. "Sha-kundum ta dafa aikinka ta shiga lamuranka boka mai dogon zamani. Ka ga taka ka ga ta kakanninmu, iyayenmu duka sun wuce sun barka. Ya kai wannan boka mai dauwamamman ruhi da dogon zamani a yi mini afuwa bisa mantuwar da na yi, amma duk wani hukunci da Sha-kundum za ta yanke ni mai biyayya ne." Boka na gama jin haka ya miƙe ya tunkari bakin wata rijiya wacce faɗinta ya fi girman ƙaramin ɗakin, yana zuwa ya fara taka matattakalar da ke cikinta ya shige. Shigarsa ke da wuya bakin rijiyar ya shafe tamkar ba a taɓa wanzar da komai a wurin ba. Yana shiga kai tsaye ya tunkari gunkin wata mace da ke tsaye da tulelen tsohon ciki a jikinta, hannunta ɗaya tallafe da tsohon cikin ɗayan kuma yana riƙe da garkuwa alamun ta kare kanta da shi. Sai da ya sunkuya ya miƙa gaisuwa sannan ya furta, "Ya ke Sarauniya sha-kundum! Ya ke mammallakiyar wannan Daular a yau ma na sake dawowa da neman yafiyar al'ummarki.Na tabbata kina saurarena kamar yadda kika daɗe kina jina. Haƙiƙa talakawanki sun dawo da wata buƙata domin a yau sun wayi gari da samun annobar haɓo shin wane taimako za ki yi musu?" Hawayen ne ya ziraro daga cikin idanun gunkin, boka ya ƙarasa ya kanga kunnensa a jikin ƙirjinta. Ya jima a haka sannan ya ɗago cike da girmamawa ya ce, "Tabbas zan isar musu kamar yadda kika buƙata, ki ƙara haƙuri nan ba da jimawa ba za ki dawo cikin ainihin hallitarki ta zahiri. Za ki ci gaba da mulkar al'ummarki kamar yadda kika mulke su a ɗaruruwan shekarun da suka gabata. Komai ya zo ƙarshe tun da ke kika tabbatar min da haka, sarauta da izzar mulki na baibaye da rayuwarki. Taɓewa da hallaka tana ga Maharba da Mafarauta har ƙarshen rayuwarsa." Yana gama maganar ya juya jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da gishiri, yana taka matattakalar bene ɗaya rijiyar ta fara dawowa kamar yadda take da farko a wurin.

Kan shimfiɗarsa ta farko ya koma ya zauna ya dubi Sarki Balarabe yana faɗin, "Ta faru ta ƙare..." Da sauri Sarki ya katse shi da cewar, "Allah sa ba laifinmu ne ya sake hauhawa ba."

"Ka buɗe kunnenka da kyau ka saurari abin da Sha-kundum ta gaya min game da ku." Boka mai zamani ya faɗa fuska babu walawa. Shiru Sarki ya yi yana sauraron Boka. "Tabbas Sarauniyarmu Sha-kundum ta sake dawo wa kamar yadda ta faɗa a lokacin da numfashin zai ɗauke..." Baki na rawa Sarki ya katse boka da cewar, "A ina aka wanzar da ruhinta? A wane yanki ne mu sa a kawo mana ita? Idan ta kai bangon duniya na rantse da hatsabibanci Sarauniya da izzar mulkina sai na sa an ɗaukota a faɗin duniya." Boka ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya har yana birgima a ƙasa tamkar jakin da yake birgima a cikin sahara. Sarki sai da ya fusata ya doki ƙasa da tafin hannunsa sannan Boka mai zamani ya koma kan buzunsa ya furta, "Haba Sarki Damina ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu, haka duk mai niyyar yin sammako ya bari duhun dare ya gifta. Sarki Damina a kwai gaggarumar matsala, kamar yadda duk faɗin garin nan babu wanda ya taɓa gani ko jin sautin Sarauniya Sha-kundum sai ni, to tabbas a wannan karon ko ni ba ni da masaniyar a ɓangaren da wannan sabuwar sarauniyar take. Babban abin baƙincikin ma waɗanda suka sulwantar mana da ruhinta a cikinsu halitar Saruniya ta sake wanzuwa..." Tun bai ƙarasa magana ba jikin Sarki Balarabe ya fara rawa kamar wanda ake kaɗa wa gangi, a fusace ya miƙe tsaye yana huci tamkar kumurcin macijin da ke tsaka da fusata. A fusace ya furta, "Boka mai zamani ka na nufin Sarauniyarmu ta ɓullo daga cikin zuri'ar maharba da mafarauta ne?" Boka ya jinjina kai yana faɗin, "Ba harsashe ba ne Damina domin Sha-kundum ta tabbatar mini kuma kai shaida ne bata taɓa yin ƙarya, ta ba ni muhimmin saƙo gare ku na farautar Maharba a ko ina suke a faɗin duniya. Sai dai babban tashin hankalin ta yi alƙawarin ba za ta sake magana ba har sai na sada da ta da ainihin ruhinta. A sanyaye Sarki Damina ya furta, "Tirƙashi! Ana dara ga dare ya yi. Bayan wannan ina tafe akan buƙatar Yarima Nomau, babban boka lamarin ciwon yaron nan a kullin ƙara ta'azzara yake. A da muna haɗa shi da ƴan mata ɗaya zuwa biyu a rana amma yanzu har ta kai ga mata biyu ba sa iya gamsar da shi, kafi kowa sanin shi kaɗai na mallaka kuma har abada ba zan sake haihuwa ba. Idan na tuna ba ni da magaji lamarin na sake ɗugunzuma hankalina." Boka mai zamani ya hura ƙasar gabansa nan take wata ƴar ƙorama ta bayyana a wurin, sai da ya barbada wani garin magani sannan ya zura hannunsa ya warasu haɗe da runtse idanunsa tare da fara karanta waɗansu irin ɗalasuman tsafi, ƙirjin Sarki Damina ban da bugawa babu abin da yake yi saboda fargabar abin da Boka zai sanar da shi. Boka mai zamani ya jima a haka sannan ya buɗe idonsa yana kallon Sarki Damina haɗe da furta, "A kodayaushe maganar ɗaya ce! Kamar yadda na sanar maka Yarima Nomau ba zai taɓa warkewa ba matuƙar bai sadu da da inuwar wannan macen da nake gani a tattare da shi ba. Tabbas zai warke sai dai bazan taɓa ce maka ga wa'adin lokacin da zai ɗauka cikin wannan tuburewar ba. Na ga haske jingine da su daga inuwar yarinyar nan na ga akwai rabo a tsakani, sai dai ka fi kowa sanin yadda aka yi aka samu Yarima Nomau don haka idan har ya samu rabo da wannan yarinyar Ɗa ko Ƴar da za su haifa dole zai zama mallakin Babban dodo ne, idan ba haka ba duk daren daɗewa za su zama masifa a daular nan. Kuma wannan hasken ba komai yake bayyana mini ba illa kusantowar warakarsa, don na lura akwai yuwuwar samun waraka nan ba da jima wa ba." Ajiyar zuciya Sarki ya yi don tun da yake zuwa wannan kogon bai taɓa jin labarin da ya faranta ransa kamar na wanan ranar ba Ya dubi Boka fuska ɗauke da murmushi ya furta, "Ya kai babban malamin madogararmu shin zan iya sanin wacece yarinyar nan kuma a wane yanki take?" Boka Mai zamani ya girgiza kai yana cewa, "Lamarin Yarima Nomau ya wuce duk yadda kake tsammani, daga ni har bokayen duniya babu wanda yake da wannan amsar don haka ina mai baka shawara kar ka wahalar da gangar jiki da ruhinka akan abin da babu takamaimar amsa. Wani hanzari ba gudu ba, daga bayan wannan inuwar na hango wata baƙar ƙura wacce ta lulluɓe sarararin samaniya sai dai ni kaina ban fahimci wacce irin ƙura ba ce koma dai wacce iri ce ina fatan za ta zame mana alkairi." Sarki Damina ya miƙe ya fara zagaye cikin kogon dutsen sai da ya zagaye boka mai zamani sannan ya ce, "Wannan ba zai zame mana matsala ba domin mun dogara da Sarauniya Sha-kundum da babban dodo na tabbata su za su kawo mana waraka a rayuwa. Yanzu wanne irin magani ta ba mu wanda za mu aiwatar mu da al'umnarmu?"

Boka mai zamani ya miƙe ya ƙarasa bakin rijiyar ya miƙa hannu ciki nan take ruwan cikinta ta kawo har sama sannan ya ɗebi ruwan da ƙoƙo ya miƙa wa Sarki Damina yana faɗin, "Wannan ruwan a je a zuba shi cikin kogon Ɗanbille duk wanda wannan annobar ta same shi ya ɗauka ya sha kai koda bata kama mutum ba zai iya wanka domin yin rigakafi. Wannan ce iya maganar da ta umarce ni na sanar da ku don haka za ka iya tafiya ya sarkin sarakunan duniya." Sanin ƙa'ida da dokar Sarauniya ya sa Sarki bai musa ba ya miƙe ba tare da ya furta koda kalma ɗaya ba, har ya je bakin ƙofa ya ji muryar Boka yana faɗin, "Ka da ka manta a kai wa Babban dodo Mai tsohon ciki biyu da idanun dattijai biyu." Gyaɗa kai kawai Sarki ya fice daga kogon dutsen.

Garin Dabur

Daga cikin bukkar da nake kwance ina bacci na fara jin hayaniya sama-sama, ina yunƙuri tashin na ji muryar mahaifiyata ta karaɗe majiyar sautina da cewar, "Yau wacce baƙar rana muke gani da yammacin haka? Ya abar bauta kada ki yi fushi da wannan mummunan zunubin domin ba mu da sa hannu a ciki, ka hukunta masu wannan zunubin da gaggawa don sun cutar da ƴar tsintuwar da bata ji ba bata gani ba." Ihun da Kandala take jerawa ne ya sa ni fito wa saboda duk wanda ya ji kukan nata ya san ba na lafiya ba ne. Jikina ne ya ɗauki tsuma sakamakon ganin halin da take ciki kace-kace da jini, a gefe ɗaya mutane daga jinsin maza da mata sun yi carko-carko a kanta suna kallon halin da take ciki. A gabanta na tsugunna raina ya kai ƙololuwar ɓaci, na dube ta fuska babu walwala na furta "Waye ya yi miki...


Read / Download BAKAR DAULA

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album