Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

1

A duk lokacin da Allah (S.W.A) ya ƙaddara wanzuwar hallitar Ɗan adam a doran ƙasa, ko ya ƙi ko ya so akwai waɗansu abubuwa da suke yin jerin gwano a gangar jiki da ruhinsa. Inuwa! Wata aba ce da Ubangiji ya ke ƙaddara wanzuwarta manne a jikin kowanne abu, walau mai rai ko akasin haka. A kodayaushe tana bibiye da su matuƙar bawa zai zuba maganansa zai lura da haka. Kalmar ƙaddara! Kalma ce mai ɗauke da rassa biyu walau ƙaddara mai kyau ko kishiyarta. Ƙaddara abokiyar tagwaitakar inuwa ce domin bawa ba ya taɓa shallake wa ƙaddararsa, sanin haka ya sa na fahimci karin maganar Malam bahaushe ta: 'Tun ran gini tun ran zane." ta zauna ɗaram kwatankwacin yadda ake ɗora ƙwarya a gurbinta.

10/06/1022
Shekara Dubu Ɗaya baya.

Hankalinsa ya fi na kowanne lokaci kai wa matuƙar ƙolokuwar tashi, yana tafe yana taku da sandarsa Waziri da sauran muƙarraban cikin daular suna take masa baya. Tamkar waɗanda saƙon mutuwa ya dirar wa haka fuskokinsu suka fasalta saƙon da ke ƙunshe cikin birnin zuciyoyinsu. Sarki Damina yana kai ɗora ƙafarsa kan jan dutsen da ke a matsayin matattakalar benen hawa tsauni tsidik! Wani gajiyayyan talakansan ya dira a gabansa cikin firgice da tashin hankali, kuka yake tamkar hawayen idanunsa za su ƙare. Ya ruƙo ƙafafuwan Sarki Damina a ɗimauce yana faɗin, "Ya kai babban Sarki, Sarkin sarkunan duniya bakiɗaya sarkin da yake share mana hawaye. Ka taimaka ka roƙar mana afuwa wurin Sarauniya Sha-kundum, yanzu haka ɗana Rabo yana can yana aman jini ta hanci ta baki don mai ɗakina naƙuda take jini ya ɓalle mata tana gangarar..." Tun bai rufe baki ba Sarki Damina ya daka masa razananniyar ƙarar da sai da hantar cikinsa ta kaɗa, yana shirin sake magana Sarki ya fisgi takobin da ke maƙale a kafaɗar Waziri kafin Bawan ya yi wani yunƙuri tuni ya sauke kansa ƙasa. Da sauri wasu ƙaratan Dogarai suka ƙarasa wurin suka zube suna yi wa Sarki godiya, "Godiya muke Sarki Damina mai masoya da yawa, Sarauniya Sha-kunduma ta yi ruƙo da hannayenka. Haushin zuciyarta ya gushe domin ta faɗa mana hanyar maganin samun lafiyar Yarima, idan wannan bai wadatar da kai ba ka yi mana umarni mu kawo maka wani ko da a cikin mu ne ka sake datse rayuwarsa matuƙar zai sanyaya zuciyarka" Bai tanka musu ba ya miƙa wa Waziri takobin da ke ɗigar da jini, har sun cicciɓi gawar bawan da kansa tuni ta samu mutsuguni a gefen wata bishiya, Sarki ya dube su yana cewa. "A gaggauta ƙone gangar jikinsa tare da yaron nasa da ba shi da lafiya. Ita kuma mai ɗakinsa a zaro jaririn cikinta a kai wa babban dodo sannan a salwantar da gangar jikinta" Yana gama magana ya haye kan tsibirin maƙarrabansa suna biye da shi a baya.

Kamar yadda yake farillah a wurinsu duk lokacin da za su shiga cikin kogon dutsen a yanzu ma sai da suka aiwatar, sai da kowannensu ya saka ƙanƙanuwar aska ya yanki gefen ɗan yatsan hannunsa suka yarfar da jinin a jikin wani sassaƙaƙƙaen gunki, hannun gunki ɗauke yake da kwari da baka daga bayansa an jingina masa takobi a jiki. Kansa a sunkuye yake alamar ƙasƙantar da kai ga wani dungulmin kan mace da suka ɗora masa a gadon bayansa. Sarki Damina ne ya fara yin gaba sannan su Waziri suka rufa masa baya, daga bakin shiga dutsen suka tsaitsaya don sun san ko karan hauka ne ya cije su ba za su taɓa haure bakin ƙofar dutsen ba. Kai tsaye Sarki Damina ya kutsa ciki sandarsa ta zame masa abokiyar tafiya. Daga tsakiyar kogon dutsen ya hangi Boka Mai zamani zaune da wasu ƙanana tukwane a gabansa, daga shi sai ganyen ayaba wanda ya yi makari don rufe al'aurarsa.

"Yau ba ranar zuwan ka ba ce kamar yadda yake a bisa al'ada, me yake tafe da kai don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa." Boka mai zamani ya faɗa yana karkatar da hankalinsa wurin Sarki Damina. Duk tsananin izza da taƙama irinta Sarki yau ya sauke ta a gefe ya fusakanci Boka yana mai bayyana damuwarsa, Sarki Damina ya zube gwiwowinsa kamar wanda ya aikata wani mummunan zunubin da yake neman gafara. Murya ɗauke da damuwa ya furta, "Ya kai Boka Mai zamani lamarin halin da talakawanmu suke ciki tabbas tura ta fara kai bango. A yau mun wayi gari da samun ɓillar annobar haɓo a cikin gari fiye da tsammani, babban abin da ya ɗugunzuma hankalina abin bai tsaya iya waje ba hatta ahalina na fuskantar wannan barazanar, a taimaka a roki Sarauniya Sha-kundum ta yafe mana tun da laifin wani ba ya taɓa shafar wani." Boka mai zamani ya miƙa masa busasshen hannunsa mai ɗauke da zaƙwa-zaƙwan farata, taurin hannunsa tamkar busasshen katako sannan ya ce, "Ina tukwicin ziyarar Sarauniya Gunki Sha-kundum kafin na san abin yi? Domin sanin kanka ne tuni bakin alƙami ya riga da ya bushe." Sai a lokacin Sarki Damina ya tuna da ƙoƙon tukwicin ziyara, cikin sake ƙanƙan da kai ya furta. "Sha-kundum ta dafa aikinka ta shiga lamuranka boka mai dogon zamani. Ka ga taka ka ga ta kakanninmu, iyayenmu duka sun wuce sun barka. Ya kai wannan boka mai dauwamamman ruhi da dogon zamani a yi mini afuwa bisa mantuwar da na yi, amma duk wani hukunci da Sha-kundum za ta yanke ni mai biyayya ne." Boka na gama jin haka ya miƙe ya tunkari bakin wata rijiya wacce faɗinta ya fi girman ƙaramin ɗakin, yana zuwa ya fara taka matattakalar da ke cikinta ya shige. Shigarsa ke da wuya bakin rijiyar ya shafe tamkar ba a taɓa wanzar da komai a wurin ba. Yana shiga kai tsaye ya tunkari gunkin wata mace da ke tsaye da tulelen tsohon ciki a jikinta, hannunta ɗaya tallafe da tsohon cikin ɗayan kuma yana riƙe da garkuwa alamun ta kare kanta da shi. Sai da ya sunkuya ya miƙa gaisuwa sannan ya furta, "Ya ke Sarauniya sha-kundum! Ya ke mammallakiyar wannan Daular a yau ma na sake dawowa da neman yafiyar al'ummarki.Na tabbata kina saurarena kamar yadda kika daɗe kina jina. Haƙiƙa talakawanki sun dawo da wata buƙata domin a yau sun wayi gari da samun annobar haɓo shin wane taimako za ki yi musu?" Hawayen ne ya ziraro daga cikin idanun gunkin, boka ya ƙarasa ya kanga kunnensa a jikin ƙirjinta. Ya jima a haka sannan ya ɗago cike da girmamawa ya ce, "Tabbas zan isar musu kamar yadda kika buƙata, ki ƙara haƙuri nan ba da jimawa ba za ki dawo cikin ainihin hallitarki ta zahiri. Za ki ci gaba da mulkar al'ummarki kamar yadda kika mulke su a ɗaruruwan shekarun da suka gabata. Komai ya zo ƙarshe tun da ke kika tabbatar min da haka, sarauta da izzar mulki na baibaye da rayuwarki. Taɓewa da hallaka tana ga Maharba da Mafarauta har ƙarshen rayuwarsa." Yana gama maganar ya juya jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da gishiri, yana taka matattakalar bene ɗaya rijiyar ta fara dawowa kamar yadda take da farko a wurin.

Kan shimfiɗarsa ta farko ya koma ya zauna ya dubi Sarki Balarabe yana faɗin, "Ta faru ta ƙare..." Da sauri Sarki ya katse shi da cewar, "Allah sa ba laifinmu ne ya sake hauhawa ba."

"Ka buɗe kunnenka da kyau ka saurari abin da Sha-kundum ta gaya min game da ku." Boka mai zamani ya faɗa fuska babu walawa. Shiru Sarki ya yi yana sauraron Boka. "Tabbas Sarauniyarmu Sha-kundum ta sake dawo wa kamar yadda ta faɗa a lokacin da numfashin zai ɗauke..." Baki na rawa Sarki ya katse boka da cewar, "A ina aka wanzar da ruhinta? A wane yanki ne mu sa a kawo mana ita? Idan ta kai bangon duniya na rantse da hatsabibanci Sarauniya da izzar mulkina sai na sa an ɗaukota a faɗin duniya." Boka ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya har yana birgima a ƙasa tamkar jakin da yake birgima a cikin sahara. Sarki sai da ya fusata ya doki ƙasa da tafin hannunsa sannan Boka mai zamani ya koma kan buzunsa ya furta, "Haba Sarki Damina ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu, haka duk mai niyyar yin sammako ya bari duhun dare ya gifta. Sarki Damina a kwai gaggarumar matsala, kamar yadda duk faɗin garin nan babu wanda ya taɓa gani ko jin sautin Sarauniya Sha-kundum sai ni, to tabbas a wannan karon ko ni ba ni da masaniyar a ɓangaren da wannan sabuwar sarauniyar take. Babban abin baƙincikin ma waɗanda suka sulwantar mana da ruhinta a cikinsu halitar Saruniya ta sake wanzuwa..." Tun bai ƙarasa magana ba jikin Sarki Balarabe ya fara rawa kamar wanda ake kaɗa wa gangi, a fusace ya miƙe tsaye yana huci tamkar kumurcin macijin da ke tsaka da fusata. A fusace ya furta, "Boka mai zamani ka na nufin Sarauniyarmu ta ɓullo daga cikin zuri'ar maharba da mafarauta ne?" Boka ya jinjina kai yana faɗin, "Ba harsashe ba ne Damina domin Sha-kundum ta tabbatar mini kuma kai shaida ne bata taɓa yin ƙarya, ta ba ni muhimmin saƙo gare ku na farautar Maharba a ko ina suke a faɗin duniya. Sai dai babban tashin hankalin ta yi alƙawarin ba za ta sake magana ba har sai na sada da ta da ainihin ruhinta. A sanyaye Sarki Damina ya furta, "Tirƙashi! Ana dara ga dare ya yi. Bayan wannan ina tafe akan buƙatar Yarima Nomau, babban boka lamarin ciwon yaron nan a kullin ƙara ta'azzara yake. A da muna haɗa shi da ƴan mata ɗaya zuwa biyu a rana amma yanzu har ta kai ga mata biyu ba sa iya gamsar da shi, kafi kowa sanin shi kaɗai na mallaka kuma har abada ba zan sake haihuwa ba. Idan na tuna ba ni da magaji lamarin na sake ɗugunzuma hankalina." Boka mai zamani ya hura ƙasar gabansa nan take wata ƴar ƙorama ta bayyana a wurin, sai da ya barbada wani garin magani sannan ya zura hannunsa ya warasu haɗe da runtse idanunsa tare da fara karanta waɗansu irin ɗalasuman tsafi, ƙirjin Sarki Damina ban da bugawa babu abin da yake yi saboda fargabar abin da Boka zai sanar da shi. Boka mai zamani ya jima a haka sannan ya buɗe idonsa yana kallon Sarki Damina haɗe da furta, "A kodayaushe maganar ɗaya ce! Kamar yadda na sanar maka Yarima Nomau ba zai taɓa warkewa ba matuƙar bai sadu da da inuwar wannan macen da nake gani a tattare da shi ba. Tabbas zai warke sai dai bazan taɓa ce maka ga wa'adin lokacin da zai ɗauka cikin wannan tuburewar ba. Na ga haske jingine da su daga inuwar yarinyar nan na ga akwai rabo a tsakani, sai dai ka fi kowa sanin yadda aka yi aka samu Yarima Nomau don haka idan har ya samu rabo da wannan yarinyar Ɗa ko Ƴar da za su haifa dole zai zama mallakin Babban dodo ne, idan ba haka ba duk daren daɗewa za su zama masifa a daular nan. Kuma wannan hasken ba komai yake bayyana mini ba illa kusantowar warakarsa, don na lura akwai yuwuwar samun waraka nan ba da jima wa ba." Ajiyar zuciya Sarki ya yi don tun da yake zuwa wannan kogon bai taɓa jin labarin da ya faranta ransa kamar na wanan ranar ba Ya dubi Boka fuska ɗauke da murmushi ya furta, "Ya kai babban malamin madogararmu shin zan iya sanin wacece yarinyar nan kuma a wane yanki take?" Boka Mai zamani ya girgiza kai yana cewa, "Lamarin Yarima Nomau ya wuce duk yadda kake tsammani, daga ni har bokayen duniya babu wanda yake da wannan amsar don haka ina mai baka shawara kar ka wahalar da gangar jiki da ruhinka akan abin da babu takamaimar amsa. Wani hanzari ba gudu ba, daga bayan wannan inuwar na hango wata baƙar ƙura wacce ta lulluɓe sarararin samaniya sai dai ni kaina ban fahimci wacce irin ƙura ba ce koma dai wacce iri ce ina fatan za ta zame mana alkairi." Sarki Damina ya miƙe ya fara zagaye cikin kogon dutsen sai da ya zagaye boka mai zamani sannan ya ce, "Wannan ba zai zame mana matsala ba domin mun dogara da Sarauniya Sha-kundum da babban dodo na tabbata su za su kawo mana waraka a rayuwa. Yanzu wanne irin magani ta ba mu wanda za mu aiwatar mu da al'umnarmu?"

Boka mai zamani ya miƙe ya ƙarasa bakin rijiyar ya miƙa hannu ciki nan take ruwan cikinta ta kawo har sama sannan ya ɗebi ruwan da ƙoƙo ya miƙa wa Sarki Damina yana faɗin, "Wannan ruwan a je a zuba shi cikin kogon Ɗanbille duk wanda wannan annobar ta same shi ya ɗauka ya sha kai koda bata kama mutum ba zai iya wanka domin yin rigakafi. Wannan ce iya maganar da ta umarce ni na sanar da ku don haka za ka iya tafiya ya sarkin sarakunan duniya." Sanin ƙa'ida da dokar Sarauniya ya sa Sarki bai musa ba ya miƙe ba tare da ya furta koda kalma ɗaya ba, har ya je bakin ƙofa ya ji muryar Boka yana faɗin, "Ka da ka manta a kai wa Babban dodo Mai tsohon ciki biyu da idanun dattijai biyu." Gyaɗa kai kawai Sarki ya fice daga kogon dutsen.

Garin Dabur

Daga cikin bukkar da nake kwance ina bacci na fara jin hayaniya sama-sama, ina yunƙuri tashin na ji muryar mahaifiyata ta karaɗe majiyar sautina da cewar, "Yau wacce baƙar rana muke gani da yammacin haka? Ya abar bauta kada ki yi fushi da wannan mummunan zunubin domin ba mu da sa hannu a ciki, ka hukunta masu wannan zunubin da gaggawa don sun cutar da ƴar tsintuwar da bata ji ba bata gani ba." Ihun da Kandala take jerawa ne ya sa ni fito wa saboda duk wanda ya ji kukan nata ya san ba na lafiya ba ne. Jikina ne ya ɗauki tsuma sakamakon ganin halin da take ciki kace-kace da jini, a gefe ɗaya mutane daga jinsin maza da mata sun yi carko-carko a kanta suna kallon halin da take ciki. A gabanta na tsugunna raina ya kai ƙololuwar ɓaci, na dube ta fuska babu walwala na furta "Waye ya yi miki haka Kadala?" Ilahirin jikinta rawa ya ke don haka na kama hannunta na haɗa su da nawa na sake furta, "Babu abin da zai faru da ke ki gaya min waye ya yi miki haka?" Cikin yanayin azaba ta furta, "Ban san sunansa ba amma na ji wasu suna ce masa Barde." Ban jira ragowar maganar ta ba saboda tun farkon ganin halin da take ciki shi ne mutum ba farko da ya fara faɗo min a rai, saboda sanin hali ya fi sanin kama. Barde riƙaƙƙen ɗan akuya ne baya iya kwana biyu ba tare da ya kusanci wala macen bil'adam ko dabba ba.

Ina miƙe wa na riski muryar Goga ya fara fito yana busa ƙaho wanda yake alamtawa sauran ƴan uwa na nesa da na kusa akwai fita ta gaggawa. Kafin ya gama busar da yake tuni gidanmu ya cika damƙam da sauran ƴan uwa maharba da mafarauta kowanne yana tafe cikin shirin dawa, ɗaya bayan ɗaya na kalle su kowannen su yana jiran umarnin da zan bayar. Jin na yi shiru ya sa Goje ya ɗaga gorarsa sama da hannun ɗaya, ɗayan hannun mai riƙe da kwari da baka ya sauke ya fara zabga mini kirari. "Burugu ce da kanta ba aike ba mace mai kamar maza ko cikin maza sai an tona. Cau cau cau cau ƙurungu mugun kifi sa'a a dawa sa'a a cikin gari wani aiki sai jan wuya makutsa daji, a lafiya uwar gidan kere amanar kura kyaci da gashi. Dawa dai, dawa gidan maza tsanani yana dajin Gurɓu ku bar faɗa musu wahalar sanar da su daɗin maza na cikin dawa mata na gida suna yin girki, wuya a dajin gwiɓau wuya a dajin fatalaki wuya ta ƙare a kan Barde yau ya taɓo ajalinsa." Ilahirin jikina ban da rawa babu abin da yake yi saboda tsumin da ya tayar min har nake jin da ace Barde na gabana babu abin da zai hana ban tsarge ruhinsa gida biyu ba, duk da kowa ya san Barde a cikin garinmu ba kanwar lasa ba ne.

Da sauri na faɗa bukkarmu na ɗabo gurun damatsan hannuwana da wuya, na kunce fatar mesar da ke ɗaure a ƙuguna na ɗaura ta damisa sannan na ɗauko kwari da baka haɗe da zabgegiyar adda na fito wurin da su Goga suke tsaitsaye. Suna ganina suka yi yunƙurin saka kai a hanzarce na dakatar da cewar, "Wannan fitar ba taku ba ce saboda Barde gidanmu ya taɓo ba ku ba, na yi rantsuwa da abar bauta ba zan dawo gida ba sai na sauke kan Barde daga gangar jikinsa, weeeehuuuuhuuuuu sai ni sarauniyar baka jikar marigayi Baushe amanar kura kawanciyarka ka huta muna tafe idan dabbobi sun ƙare. Sai ni yaƙi ban san wasa ba Abar bauta ta buɗa mana matuƙar na saka kai ko yau ko yanzu ban san namiji ba sai na ga tabo a jikinsa, wahala a hanyar tugu wuya a hanyar badake wuya ko da magani babu daɗi ko ana ha maza ha mata sai na dawo da kan Barde a hannuna." Ina gama zabga kirari cikin haɗin baki tawagar da ke wurin suka furta, "Dawa dai Sarauniyar kwari da baka, Abar bauta ta buɗa miki a dajin Gurɓu." Har na saka kai zan fita na dawo wurin Mahaifiyata na russuna saitin kunnenta ina faɗin, "Ki roƙar mini abar bauta da ta rinjayi ɗayan ruhin kar ya ziyarce ni ina tsoron kada Barde ya yi nasara akaina." Cike da ƙwarin gwiwa ta furta min, "Sa'a dai Sarauniya abar bauta ta buɗa miki ɓoyayyan ruhi ba zai ƙara ziyartar ki ba." Ina gama sauraronta na fice daga cikin gidan cike da ƙwarin gwiwa na nufi wurin da na tabbatar Barde na zama da ƴan koronsa.

Daular Sarki Damina.

Daga kogon boka mai zamani ya so kai ziyara bukkar babban dodo amma sai ya ga mafi dacewa ya fara zuwa wurin al'ummarsa ya umarci rundunar mayaƙansa da su fita yi masa farautar duk wata halitar bil'adam, musamman daga tsagin maharba da mafarauta kamar yadda suka saba yi a baya. A tsaitsaye suke dubbanin mutanen daular don a zatonsu maganin warakar annobar da ke damunsu aka kawo musu, Waziri ne ya yi gyaran murya sannan ya furta, "Ya ku waɗannan jama'a ya kamata kowa ya nutsu don jin saƙon da Sarauniya sha-kundum ta aiko." Tamkar ɗaukewar ruwan sama haka wurin ya yi tsit, Sarki Damina ya yi gyaran murya sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya ya sanar da su duk yadda suka yi da boka Mai zamani sannan ya ɗora da cewa, "Ina umartar manyan mayaƙan dakarun daular nan da su hanzarta fita cikin gaggauwa don yi mana farautar bayi kamar yadda suka saba a baya, kuma su yi sani cewa ya zama wajibi su farmako mana La'anannun hallitar can ta maharba da mafarauta a ko ina suke a faɗin duniya. Wannan umarni ne daga Sarauniya sha-kundum idan ba haka ba bala'in da muka shiga da wanda muke ciki a yanzu shafar mai ne akan abin da zai faru da mu a gaba." Yana rufe baki zaratan dakarun mayaƙan suka fara fita a guje zuwa mahallansu kowanne na fito wa da manyan makamai, runduna guda suka yi tsaya a gaban sarki Damina. Sai da ya ƙare musu kallo sannan ya kasa su gida huɗu, manyan zaratan mayaƙan ya ce su bi gabas hanyar da za ta sada su da ƙasar Dabur. Runduna ta biyu ya ce su bi Yamma hanyar da za ta sada su da ƙasar Baƙasud, runduna ta uku ya ce su bi kudu hanyar da za ta sada su da ƙasar Mubali sai tawaga ta huɗu da ya umarce su da Arewa wacce za su isa da Ƙasar Surima. Lokaci ɗaya suka bazama a yunwace da farauto kowanne irin bil'adam kamar yadda Sarkin da yake mulkarsu ya ba su umarni.


*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananjn ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu

Please Login or Register in order to submit comment