Join Our WhatsApp Group

RUWAN RAYUWA Complete Hausa Novel Document by RUWAN RAYUWA


RUWAN RAYUWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 3186



RUWAN RAYUWA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 26, Aug 2023

Author: Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08162600700

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 17.49 kb

File Type: txt

Views: 496+

Download: 83+

Last download: 10 days ago

Description/Story: RUWAN RAYUWA
===============

__
Allah Yana da wani ruwa wanda duk wanda ya sha shi to ba zai mutu ba, saidai in shi ne ya roqi mutuwa da kan sa.
.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah. WhatsApp 08162600700.
.
Wata rana Annabi Zulqarnaini ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
suna hira da wani Mala'ika mai suna Zayafiylu ﺯﻳﺎﻓﻴﻞ , sai Zulqarnaini yake cewa da shi "Ya kai Zayafiylu! Shin yaya kake ganin irin bautar da Mala'iku suke yi wa Allah Madaukakin Sarki idan an kwatanta ta data mutane?"
Sai Mala'ikan nan ya fashe da kuka, sannan ya ce "Ya kai Zulqarnaini!, ibadar mutane ba komai bace idan aka hadata data Mala'iku a sama. Domin a cikinmu akwai Mala'ikan da a tsaye yakewa Allah ibada, kuma ba zai zauna ba har a tashi Alqiyama. Wani yayi sujjada kuma ba zai dago kan sa ba har abada. Wani ya yi Ruku'u kuma ba zai dago ba har a tashi qiyama. Wani kuma ya daga kansa sama, ba zai sauke kansa ko ya waiwaya ba har abada. Suna cewa "Sub'hanal Malikul Quddusi Rabbul Mala'ikati war Ruhu Rabbana ma abadna Ka haqqa ibadatiK"
ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﺍﻟﻘﺪﻭﺱ ﺭﺏ ﺍﻟﻤﻼﺀﻛﺔ ﻭﺍﻟﺮﻭﺡ ﺭﺑﻨﺎ ﻣﺎ ﻋﺒﺪﻧﺎﻙ ﺣﻖ ﻋﺒﺎﺩﺗﻚ "
Da jin haka sai Zulqarnaini yay kuka mai tsanani sannan ya ce "Gaskiya ina so in samu tsawon rayuwa yadda zan dade ina bautawa Allah sosai da sosai kuma nay maSa biyayya"
Sai Mala'ikan ya ce "Da gaske kana son tsawon rayuwa ya kai Zulqarnaini?"
Sai ya ce "E"
Sai Mala'ikan Ya ce "Ai kuwa Allah Yana da wani ruwa a duniyar nan, wanda duk wanda ya sha shi to ba zai mutu ba. Saidai in shi ne ya roqi mutuwar da kan sa"
Sai Zaulqarnaini ya ce "To ka san a inda ruwan yake?"
Sai Mala'ikan ya ce "A'a, amma dai mu Mala'iku muna yawan yin hirar cewa Allah yana da wani duhu a cikin qasa wanda Mutum ko Aljan ba su ta6a zuwa wajen ba. To ina jin a cikin duhun wannan ruwan yake"
Da jin haka Sai Sarki Annabi Zulqarnaini yasa aka tara masa Malaman duniya gaba dayansu da ma'abota karance-karancen littattafai da masu bincike akan guraren da Annabawa suka zauna, sai ya tambaye su ya ce
"A cikin abubuwan da kuke karantawa na tarihin Annabawa da Hadisai da sauran littattafai, shin kun ta6a jin cewa Allah yana da wani ruwa da ake kira RUWAN RAYUWA?"
Sai suka ce "A'a"
Sai ya sake cewa "To kuna da labarin Yana da wani duhu wanda mutum da Aljani basu ta6a takawa ba?"
Sai suka ce "A'a"
Sai wani Malami a cikinsu ya ce "Ya kai wannan Sarki! me yasa kake tambayarmu akan wanna?"
Sai Zulqarnaini ya gaya masa yadda sukay da wannan Mala'ikan.
Sai Malamin nan ya ce "Ya kai wannan Sarki! hakika na karanta wasiyyar Annabi Adamu ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
to a cikin na ga cewa Allah Madaukakin Sarki Ya halicci wani duhu a duniya, wanda mutum ko Aljani basu ta6a zuwa wajen ba"
Sai Zulqarnaini Ya ce masa "To a ina ka samu labari duhun yake?"
Sai ya ce "Duhun yana inda qahon rana yake"
Sai kuwa Zulqarnaini ya tara mutane da masu basirar cikinsu da manya-manyan mutane da Sarakuna sannan suka doshi inda rana take, sukay tsawon shekara goma sha biyu suna tafiya.
Sai ga su kuwa a kusa da wannan duhu.
Saidai shi wannan duhun ba kamar duhun dare yake ba, shi wani duhu ne mai kamar hayaqi.
Sai suka sauka a wajen.
Sannan ya tara Malaman ckin tawagar ta sa ya ce "To ni fa zan shiga cikin duhun nan ne"
Sai suka ce " Ya kai wannan Sarki! Haqiqa tun kafin kai akwai Annabawa da Sarakuna da suka wuce, duk cikinsu ba wanda ya nemi shiga cikin wannan duhun. Don haka kai ma kada ka shiga. Saboda muna gudun kada wani mugun abun ya same mu sannan kada hakan ya zamo wata sabuwar haryar fitina ga mutanen duniya"
Sai Zulqarnaini ya ce "Ni fa sai na shiga"
Sai Malaman suka fadi sukay gaiauwa suka ce
"Ya kai wannan Sarki! Ka haqura da shiga wajen nan, da mun san in ka shiga zaka samu abinda kake nema da sai mu kyaleka. To mu muna gudun kada fushin Allah ya kama mu ko wani abu mara dadi ya same mu. Sannan muna tsoron kada wannan abu ya zama sanadin lalacewar mutanen duniya"
Sai Zulqarnaini ya ce "Ni fa sai na shiga"
Sai suka ce "Girman kujerarka"
Sai ya ce "Wane nau'in doki ne ya fi gani da daddare?"
Sai aka ce masa "Macen doki, mai kananan shekaru"
Sai yasa aka tara masa matan dokuna masu kananan shekaru guda dubu shida.
Sai ya za6i mutum dubu shida masu hankali da ilimi a cikin jama'arsa, ya baiwa kowanne doki.
Sannan ya baiwa wani mutum jar tuta shi ne Annabi Khidr (wato mutumin nan ma'aboci Annabi Musa ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ) ya hada shi da mutum dubu biyu ya jagorance su. Shi kuma Zaulqarnaini ya jagoranci mutum dubu shida.
Sai ya cewa ragowar jama'ar da suka taho tare "Kuy jiran mu a nan wajen tsawon shekara goma sha biyu, idan mun fito shikenan, idan kuma ba mu fito ba ku koma gida"
Sai Annabi Khidr ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ya ce masa "Ya kai wannan Sarki! Hakika zaka shiga cikin wannan duhu, kuma baka san tsawon nisan tafiyar da ke cikinsa ba kuma duk cikin mu babu wanda yake iya ganin wani. To ya za muy idan wani ya 6ace?"
Sai Zulqarnaini ya ba shi wata qararrawa ya ce "Idan duhu yay muku yawa to ka jefar da wannan a qasa idan tay qara sai kowa ya dawo inda take"
Sai suka shiga cikin duhun don neman RUWAN RAYUWA.
★Dag shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islam it yah★
To shi Annabi Khidr ya san abinda Zulqarnaini yake nema a cikin duhun nan shi ne RUWAN RAYUWA, amma Zulqarnaini yana 6oye musu.
To bayan sun yi nisa a cikin duhun, sai jama'ar Khidr sukay karo da wani kwari, sai sukay zaton cewa a ciki Ruwan rayuwa yake. Da suka gangara ciki sai yacewa jama'arsa "Ku tsaya, kada kowa ya motsa"
Sai suka tsaya. Khidr ya dauko tutar nan da Zulqarnaini ya ba shi ya jefa ta. Kawai sai ya ga ta fada kan kogi na ruwa.
.
.
Shi kuwa Zulqarnaini da wadanda suke tare da shi sai suka 6ace hanya, suka bi inda ba anan Ruwan Rayuwa yake ba. Sukay ta tafiya a cikin duhun har kwana arba'in. Sai ga su sun shigo cikin wani haske, shi dai ba irin hasken rana ba kuma ba na wata ba sannan kasar wajen kuma ja ce.
Sai suka hango wani dogon gini an gina shi bene akan bene madaukaka.
Sai Zulqarnaini ya tsayar da rundunarsa, ya ce su jira shi anan. Sannan ya fita shi kadai har ya je inda wannan ginin yake. Sai yaga an gina shi ne da baqin karfe ta ko ina.
Sai yaga wani baqin tsuntsu an rataye shi a tsakanin sama da qasa bakinsa yana jikin baqin karfen.
Lokacin da Tsuntsun ya ji tafiyar Zulqarnaini sai ya ce "Waye wannan?"
Sai ya ce " Ni ne Zulqarnaini"
Sai Tsuntsu ya ce "Yanzu duk abinda ka gani a baya bai ishe kaba saida ka qaraso inda nake?" Kuma ya ce "Ya Zulqarnaini! ba ni labari"
Sai yace masa "Tambayi abinda kake so in gaya maka"
Sai ya ce "Shin gine-ginen bulon Siminti (cement block) sun fara yawa a duniya?
Sai ya ce "E"
Sai Tsuntsun nan ya matsa daga kusa da Zulqarnaini, yay ta matsawa yana yin nesa, har sai da ya hau daya bisa ukun ginin baqin qarfen nan.
Sannan ya sake cewa "Ba ni labari Zulqarnaini"
Sai ya ce "Tambayi abinda kake so"
Sai ya ce "Ya Zulqarnaini! shin shaidar qarya ta fara yawa a duniya?"
Sai ya ce "E"
Sai Tsuntsun nan ya sake matsawa yay nesa. Har ya je biyu bisa ukun ginin"
Ya sake cewa "Ya Zulqarnaini bani labari, shin kayan kida sun yawaita a duniya?"
Sai ya ce "Na'am"
Sai Tsuntsun ya sake matsawa har saida yay wa Zulqarnaini nisa mai yawan gaske ya zamto wannan ginin ya shiga tsakaninsu.
Sannan ya ce "Ya Zulqarnaini kar ka ji tsoro. Ba ni labari"
Sai ya ce "Tambayi"
Sai ya ce "Shin mutane sun dena fadar La ilaha illAllahu ( ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ )?"
Sai ya ce "A'a, suna fada"
Sai Tsuntsun nan ya matso kusa da taku uku. Ya ce "Ba ni labari ya kai Zulqarnaini"
Sai ya ce "Tambayi"
Sai ya ce "Shin mutane sun dena salloli biyar da aka wajabta musu?"
Sai ya ce "A'a, basu bari ba"
Sai Tsuntsun ya sake matsowa, ya ce "Ba ni labari"
Zulqarnaini ya ce "Tambayi"
Sai ya ce "Shin mutane sun dena wankan janaba?"
Sai ya ce "A'a"
Sai Tsuntsun ya dawo kamar yadda suke da farko, sannan ya ce "Ya Zulqarnaini hau benen nan can sama"
Sai Zulqarnaini ya kama bene da hawa, yana tafiya a tsorace har ya isa kan benen. Sai yaga wani matashi mai kama da mutum yana sanye da fararen kaya, yana tsaye ya daga kansa sama, ya saka hannuwansa a cikin bakinsa.
Lokacin da ya ji tafiyar Zulqarnaini sai ya ce "Waye nan?"
Sai ya ce "Ni ne Zulqarnaini!, kai kuma waye?"
Sa ya ce "Ni ne ma'abocin qaho (Mala'ika Israfiylu, wanda Allah Ya wakilta ya busa qaho a tashi alqiyama)"
Sai Zulqarnaini ya ce "To ya na ga ka saka hannunka a bakin ka kuma ka daga kanka sama?"
Sai yace "Hakika Alqiyama ta kusa. Ni dai kawai ina jiran umarnin Ubangijina ne in busa qaho"
Sannan ya dauko wani abu kamar dutse ya baiwa Zulqarnaini. Ya ce "Ungo wannan ya kai Zulqarnaini, in ya qoshi to kaima zaka koshi. In kuma ya ji yunwa to kaima zaka ji yunwa"
Sai ya kar6i dutsen sannan ya dawo wajen mutanensa.
.
.
Shi kuwa Annabi Khidr ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ lokacin da ya ga wannan ruwa sai ya sauka ya cire kayansa ya shiga ruwan.
Sai yaga ruwan kogin ya fi nono fari, kuma ya fi zuma zaqi. Sai yasha yay alwala yay wanka sannan ya fito, ya saka kayansa.
Sannan ya jefa qararrawar nan inda jama'arsa suke. Sai tay qara jama'ar suka hadu. Sannan ya ce "To mu tafi da sunan Allah"
Sai suka wuce har suka karaso inda su Zulqarnaini suka a tsaye a cikin haske.
Lokacin da Zulqarnaini ya dawo wajensu sai ya basu labarin Tsuntsunnan da abinda ya faru a tsakaninsu. Sannan ya ce musu "Kuy min bayanin wannan dutsen, me yake nufi?"
Sai Malamai suka kar6a suka dora shi akan sikeli. Suka dora wani dutsen a daya 6angaren sikelin mai kamar girman wanda Mala'ika ya baiwa Zulqarnaini. Sai dutsen Zulqarnaini ya rinjaye shi.
Suka dinga kara dutsina amma dutsennan da Zulqarnaini ya zo da shi yana rinjayarsu. Har sai da suka dora dutsina guda dubu daya amma yana rinjayarsu.
Sai Malaman nan suka ce "Ya kai wannan Sarki! gaskiya ilimin mu ya qare akan wannan"
To shi Annabi Khidr yana kallon abinda suke aikatawa amma bai musu magana ba. Sai Zulqarnaini ya ce masa
"Shin kana da ilimi akan wannan?"
Sai ya ce "E"
Sai ya dauki dutsen nan ya dora shi akan sikeli, ya dauko wani dutsen mai kamar girmansa ya dora shi a daya hannun sikelin. Sannan ya debo qasa ya zuba akan wannan dutsen da Zulqarnaini ya zo da shi har ta rufe shi gaba daya.
Sai kuwa dutsinan nan sukay dede akan sikeli, ba wanda ya rinjayi wani.
Sai Malaman sukaywa Allah sujjada suka ce "Sub'hanAllahi. Wannan ilimin ya wuce sanin mu"
Sai Zulqarnaini ya ce "To yi min bayani. Me wannan yake nufi?"
Sai Annabi Khidr ya ce " Ya kai wannan Sarki! lallai mulkin Ubangiji ya fi qarfin bayinSa kuma lamarinSa ya zarce tunaninsu. Kuma Allah Ya jarrabi bayinSa, sashinsu zuwa sashi. Ya jarrabi Malami da Malami, Jahili da Jahili. Kuma Ya jarrabi Malami da Jahili, Ya jarrabi Jahili da Malami. Kuma lallai Allah Ya jarrabe ni da kai, Ya jarrabeka da ni"
Sai Zulqarnaini ya ce "Ya isheka haka. Gaya min me wannan dutsen yake nufi?"
Sai Khidr ya ce "Ya kai wannan Sarki! , wannan wani misali ne Mala'ikan nan ya buga maka.
Hakika Allah Ya danqa garuruwa da yawa a hannunka, Ya baka abinda bai baiwa kowa ba amma baka qoshi ba har saida son ranka ya saka ka yin kutse a cikin Mulkin Ubangiji ka nemi abinda ba wani Mutum ko Aljan da ya ta6a yunqurin nemansa (wato Ruwan Rayuwa)"
Ya cigaba da cewa "To wannan dutsen, misali ne Mala'ikan yay maka cewa shi dan Adam baya qoshi har sai an rufe shi da qasa tukuna".
Da jin haka sai Zulqarnaini ya ce "Ka yi gaskiya ya Khidr wajen fassara wannan dutsen. To wAllahi ba zan sake binciken wani abu a duniya ba har in barta"
Sai ya hau dokinsa ya juya suka koma baya.
Har saida suka dawo tsakiyar duhun sai suka ji suna tafiya akan wani irin abu. Sai jama'ar suka ce "Ya kai wannan Sarki! Menene haka dokunan mu suke takawa kamar duwatsu?"
Sai Zulqarnaini ya ce in kuna so ku diba, wanda ya diba se yay nadama. Wanda bai diba ba ma se yay nadama"
Sai wasu suka diba wasu kuma basu diba ba.
Sai suka zo suka wuce ta kusa da RUWAN RAYUWA amma Zulqarnaini bai sha ba.
Lokacin da suka fito haske sai suka ga ashe abinda suka diba dinnan Zubarjadi ne, don haka sai wadanda suka diba sukay nadama. Wadanda basu diba bama sukay nadama.
Sannan Zulqarnaini ya koma garin Daumatul Jandal ya zauna har ya rasu acan.
.
.
Nan gaba insha Allah za mu kawo muku yadda Zulqarnaini ya je inda rana take 6ullowa da kuma inda rana take faduwa da kuma yadda ya gina katangar bayan duniya don kada Ya'ajuju da Ma'ajuju su shigo duniyar nan ta mu.
.

__
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah.
WhatsApp 08162600700.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also...


Read / Download RUWAN RAYUWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album