Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

NI DA GIDANA Book 1 Complete Hausa Novel Document by NI DA GIDANA Book 1


NI DA GIDANA Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 50204



NI DA GIDANA Book 1

Reading Time: 4 Hours

Added On: 06, Jun 2024

Author: Zainab Ilyas Mazawaje ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : KAINUWA WRITER'S * *ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 271.77 kb

File Type: txt

Views: 293+

Download: 268+

Last download: 26 minutes ago

Description/Story: *🏤 NI DA GIDANA 🏤*


*_Littafi na daya_*


*NA*



*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*



DAGA Marubuciyar👇

```Mubarak KO Mujahid?
Rashin Danga na
Kayan aro
Ni Da Gidana
Sab'anin Zato
K'addarar Iman
Nadamar aure na```

*_Wannan littafi Ni da gidana free ne 1&2 ga makarantan littattafan Hausa a ko'ina suke._*

__________________________

( littafi na d'aya)



1🗻 Labarin rayuwa ta d'auke yake da amsoshin tambayoyin wasu mataye. Haka zalika d'auke yake da warwarar matsalolin wasu mataye. Kuma yana d'auke da mafita ga dubban matayen aure da suka Shiga takunkumin Ina mafita ga damuwar su.


Sumayyya, duk ke wad'an nan furutai ga manyan a minan'ta biyu Laila da Aliya da suka Sata a gaba, suka zuba mata idanu, game da tambayoyin da suke ta yi mata a kan rayuwar'ta. Ta dubesu tayi murmushi.

”Ni ba 'yar kowa bace, ni 'yar talaka ce lis. Kuma ni ba kyakykyawa bace, Amma na auri Mijin da ko a mafarki, ban tab'a zaton zan aureshi ba. Na Shiga daula ta arzik'i nayi ninkaya a ciki da Sai d'ai, d'ai kun mata a duniya ke rabautar irin sa. Na mallaki kadarori da dukiya da ni kaina bazan zayyano su cikin sauk'i ba. Kuma shaida ne, da zaku labarta kowa wacece sumayya.

Taja dogon numfashi ta d'ora.

Duk da wannan jin dad'in duniyar da daula da sa'ar Miji na kerewa sa'a da na rabauta, Ina tare da wani tabo na mikin ciwo a zuciya ta da ya kasa warke wa da a ka jarrabeni da shi, da Sai Jifa Jifa yake motsamin yayi ta d'an zugi idan na tuno jarraba ta, a rayuwa. Babu kuma Wanda yake fahimtar wannan damuwa tawa, sai Mijina da muka zama han'ta da jini.

Laila ta dafa kafad'ar sumayya Sannan tace.

"Sumy, yanzu nan har kina da Wata damuwa ko
matsala a rayuwa da bata kau ba?. Zato na ai kin gama shan kwana."

Aliya ta karb'a.

"Wallahi yarda kika zama a bar Sha'awa ga mata a ko'Ina babu Wanda Zai yarda kina da Wata damuwa ko Yaya a rayuwa sumayya.

"Idan kuka fad'i haka, kun jahilci sanin ita kan'ta rayuwar. Babu yarda za'a yi a ce Wai mutum burin sa a rayuwa ya cika d'ari bisa d'ari, ko bashi da matsala ko d'aya, dole a tab'a shi, ta wani b'angaren ko a hanashi ta wani fannin. Cikakken musulmi, zai ce yayi imani, Sannan a ce Wai ubangijin'sa bazai jarrabi imanin sa ba? impossible."

"Gaskiya ne, dole ne Kam." A cewar Aliya.

Laila ta muskuta, ta k'ara matsawa dab da Sumayya, tayi d'an duba kad'an cikin katafaren falon da samun irin sa zai wahalar.

"Sumayya, don Allah ki daure ki bamu labarin rayuwar nan taki domin na tabbatar a Kwai a bubuwa da yawa da mata zasu amfana da shi, domin ke d'in nasan bata wasa bace, Sai dai a d'au co's a wurin'ki a komai, tun da ga mai gida ma duk kin mallake, kullum tunanin'sa yana gareki."

"Tabbas, tun da daga Zaman Mu a nan, ya kiraki a waya ya kai sau biyar." Inji Aliya.

Sumayya tayi 'yar dariya tace.

"Bazan ce ba haka ba ne a minai na, sai dai nayi k'ok'arin mai da tunanin Ku can baya, domin Kusan gwagwar mayar da sumayya tasha kafin ta samu wannan matsayin wurin Mijinta da wurin dangin'sa, har ma da Ku da duk wad'an da nake burgesu da basu Sha'awa. Duk Wacce zata iya kwaikwayo na wurin juriya da Hak'uri da dangin sa da dogaro ga Allah, da iya tafiyar da Miji da juriyar irin d'abi'un sa duk hutsancin'sa, to tabbas zata iya dace da irin rayuwar Sumayya ko ba duka ba.
Sai Dai matsalar dole idan Ina baku labarin za'a zo wurin da zan yi ta kuka, k'arshe ma na sare na kasa ci gaba. Saboda haka domin komai yazo min da sauk'i zan rubuta muku a rubuce Kawai. Na yarda Ku yad'a shi ma, ko ya zama littafi, domin na tabbatar 'yan uwa na mata zasu k'aru da yawa ma. Ku bani Sati d'aya, saboda Kunsan Mijina yanzu bai fiye yin nisa ba sosai, kuma yana d'an jimawa bai yi tafiya ba. Kunga kuwa Sai ya fita zan samu dama ko?".

"Wallahi da gaskiyar'ki . Mu dai godiya muke sosai, muna jira ." Cike da zumud'i Laila ta fad'a.ita ma Aliya jinjina tayi mata.
"Allah yaja da ran gimbiyar mata, Allah ya k'aro twin's biyu bayan su Abalkhair. "

Murmushi Kawai tayi. Saboda sun jima suna yi mata nacin labarin rayuwar'ta saboda ta zamewa kowa kamar One in town. Amma fa ga Wanda ya San'ta ko ya gan'ta ko labarin'ta da ya shahara ya riski Mutum.

Bayan Sati kuwa Sumayya ta cika alk'awari ta basu rubutaccen labarin'ta. Ga daga kuma in'da ta soma.


_________________________

JIGON AL'AMARIN


_______ Had'uwa ta da Fa'iz Bukar, daga nan k'addarar ta soma.

************************

_____ Ajin ya kaure da hayaniya saboda rashin malami. Dama kuma al'adar 'yan a jin na Mune surutun, koma da malamin, saboda sunci sunan mun mun GAGARA.

Ni da nake monita na tashi na duba time table, domin naga wani malamine da mu a lokacin. Naga English teachear ne, wato malamin turanci. Na Mik'e na nufi taff room in da mukaci karo da malam Abba class teacher d'in Mu. Na rusuna nace.

"Sir, babu malami a ajin, Sai hayaniya kuma suke sunk'i yin shiru."

"Wani malami ne daku bai shigo ba?". Yace.

Nace "English teachear ne sir, kuma anyi masa transfer. Sabon malamin da a kace yau Zai soma zuwa kuma bai zo ba."

Da sauri yace.

"Ai kuwa yazo. Malam Fa'iz sunan sa, Yana ma staff room suna ganawa da princepal na baro su. Muje na nuna Miki shi, ki fad'a masa period d'in sa ta Shiga, bai Sani ba ne."

Ban'da shi malamai uku ne a staff room d'in biyu maza, Sai malama wasila dake aikin sa hannu a test a gefe guda.

Yana gefe d'aya shi kad'ai a zaune yana duba wani text book. Dole da ka Shiga, shi zai fara d'auke Maka idanu, saboda farar fatar'sa irin ta shuwa a rab. Matashin saurayi ne da duk cikin malaman babu mai k'asa da shekarun sa, Sai dai Sama.


Ni dai Ina yin tozali da shi, na Shiga mamakin sake had'uwa ta da shi a karo na biyu a rayuwa ta, kuma zai zomin a matsayin malami. Ko da yake had'uwa ta da shi d'in ma ta farko, ba wani a bu ya Shiga tsakani na da shi ba, face wayata da na tab'a yarwa ya tsinta ya kawo min. Tsawon Wata tara Kenan.

Amma a bin Mamaki nunawa yayi kamar bai tab'a gane ni ba, da ya d'ago kai muka had'a idanu. Sai da ya wani ja a ji, cikin jin kai, Sannan yace da k'yar.

"Are you a monitor?" Yace.
Na gyad'a kai.

"Yes, sir".

Har ya Mik'e nayi ni kuma gaba, ya kirani yace.

"O K. Jeki, gani nan zuwa.'" Ya koma yayi Zaman'sa.

Ban jima kuma da Shiga ba, Sai gashi ya shigo. Duk da an ga shigowar'sa ba'a saurara da hayaniya ba, kuma duk kuma da jarabar kallon da a ka bishi da shi, kamar bak'on halitta.

A haka ya soma gabatar da kan'sa cikin harshen turanci. Ya dakata. Yace

"Keep Quit. Isaid keep Queit. "Amma ba'a rage Surutu ba. Ai Sai ya daka Mana Wata irin tsawa da dank'ara Mana zagi, ya zarce da.

"Ku wad'an ne irin jakai ne ku, a na cewa Kuyi shiru baza Ku yi ba?"

Ai kuwa Sai tsit kake ji , saboda dalilai biyu. Farko tsorata, na biyu babu wani malami da ya tab'a zagin mu, saboda ji da Mu da malamai suke, koma me muka yi. Amma shi wannan daga zuwa har ya fara yi Mana lugude? Sabida Surutu Kawai ma?

Tabbas da a lamu Zai fita zakka. Domin da jin kai da tsare gida ma ya shigo class d'in. Shiru yayi kuma yana ta harare harare da nufin yaga Wata tayi ko uhum! yaci zarafin'ta. Haka na karance shi. Babu Wacce kuwa ta kuma yin ko tari.

Yayi sanyi kad'an ya soma magana cikin harshen Hausa kuma.

"My name is fa'iz Bukar. Ba...


Read / Download NI DA GIDANA Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album