Join Our WhatsApp Group

EL HAJJ Complete Hausa Novel Document by EL HAJJ


EL HAJJ

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 39940



EL HAJJ

Reading Time: 3 Hours

Added On: 24, Aug 2023

Author: Mrs A.M ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09066728387

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 209.28 kb

File Type: txt

Views: 800+

Download: 383+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: 🤎🤎🤎🤎
*ELHAJJ*
🤎🤎🤎🤎

Free page 1

Written by
Mrs A.M

Marubuciyar
*NOOR*
*TASWIRAR KADDARA*

Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.

Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.
09066728387


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Ta dukufa sosai tana duba littafan addinin dake kan center table, idonta sanye da farin glass din da take sawa duk lokacin da zata karanta abu ko zata yi amfani da waya.

Tana sanye da red lace a jikinta wanda ya haska ta dinkin ya zauna a jikin ta yai mata dass, tayi kyau sosai kasancewar ta fara sol, tana da kyau dai dai nata don baxa a kirata da mummuna ba.

Sam hankalin ta bai fada mata zuwan sa ba, har sai da taji ya dafa ta dagowa tai ta zuba masa idonta da ke nuna tsantsar kaunar sa a tattare da ita, lumshe masa idon tai kafin ta cire glass din idonta, mike wa tai cike da shagwaba tace "ba dai fita zaka yiba ELHAJJ".

Lumshe mata ido yai kawai yana kallon watch din hannun sa, turo baki tai tana bubbuga kafa a kasa tace "kai dai koh, dama nasan baxa kamin magana ba share ni za kayi kawai".

Hannun sa yasa ya shafa kumatun ta, kamar wanda bakinsa yake masa ciwo yake "kin girma fa..h, ki daina abin yara 30 yrs kike fa".

Kwanciya tai akan faffadan kirjin sa tace "haba dai Elhajj ai ni yarinya ce har ynxu a gun ka, bana girma".

Gajeran murmushi yai yace "uhm, na fita".

Matsa wa tai daga jikin sa tace "bye".

Fita yai cikin takunsa dake nuna nutsuwar sa, yana isa compound din security dinsa dake sanye cikin black suit suka mike da sauri, gaishe sa sukai cikin girmamawa, ba tare da ya amsa suba ya shiga bayan motar da suka bude masa, da sauri suma daya ya shiga driver sit dayan kuma ya zauna a kujerar mai zaman banxa.

iPad dinsa ya dauka ya shiga aiki da ita, cikin girmamawa Wanda ke zaune a driver sit din yace "Sir ina zamu je?"

Sai da ya dau wajen 3 minutes kafin ya bude baki da kyar yace "new site".

Daga kai yai yace "ohk Sir"

Tafiyar 15 minutes ya kaisu ga wani building mai masifar kyau, fadar kyaun sa bata lokacin ne amma ya hadu iya haduwa, ta ko ina glass ne.

A gurin da yake ajiye motocin sa security din yai parking, da sauri dayan ya fito ya bude masa kofar, bai jima ba ya fito don yana da meeting din da zai yi mai muhimmanci.

Tafiya yake suna take masa baya har suka iso inda zai hau private elevator dinsa, sai anan suka matsa amma basu bishi na cikin sauri suma suka shiga general elevator wanda kowa zai iya amfani dashi.

Kusan a tare suka fito daga ciki, bayan sun isa 5th floor wanda anan ne meeting room din yake.

Cikin nutsuwar data zame masa jiki ya shiga dakin taron, kowa ya hallara da alama shi kadai ake jira, bai tsaya wani gaishe gaishe ba kawai suka fara magana akan abinda ya tara su.

Sun dauki kusan 2 hours suna magana wanda duk akan kayan da zai shigo dasu ne daga companyn sa dake China, wanda tun kafin zuwan kayan manyan yan kasuwa sun bada kudi su, don kowa yasan Elhajj baya sai da baragurbin kaya.

Office dinsa daya gama haduwa ya shiga bayan gama meeting din nasu, zama yai yana cire hular kansa, a hankali ya dauki remote din AC ya kara sanyin ta kasancewar sa ma'abocin son sanyi sosai.

Bude kofar akai aka shigo, bai bude idon saba don ya riga yasan ba wanda zai shigo masa office kai tsaye sai aminin sa Salim.

Zama Salim yai a kujerar dake kallon tasa yace "Elhajj ina ta fada maka tun jiya Ka kara duba abin nan fa, ni mutumin bai kwanta min ba sam gani nake kamar cutar mu yazo yi kawai".

Bude lulu eyes dinsa yai akan Salim tabe baki yai yana dan gyara zaman sa yace "na riga na fada ma nayi signing, kuma ni banga alamun cutar mu yazo yi ba and wannan deal din fa mai kyau ne ka sani zamu samu profit sosai".

Girgiza kai Salim yai cikin kokarin fahimtar dashi yace "kudade masu yawa fa kasa Elhajj kuma ni banga amfanin sa kudin ba, wannan abin in kana so zaka iya Sawa a fara yi a company ka fah, mai yasa sai Ka basa kudin".

Bottle water ya bude ya kurba kadan kafin yace "taimakon sa nai, kasuwancin sa yana son mutuwa kuma ni banga wani aibun hakan ba, bafa kyauta na basa ba kasuwanci zamu yi tare nida Shi meye damuwar kane Salim".

Shiru Salim yai kafin yace "shiknn tunda har hankalin Ka ya kwanta da wannan business din bkm".

Shiru sukai dukan su sai karar AC kadan kadan, mikewa Salim yai yace "bara naje ina da wasu clients da zasu zo muyi magana".

Daga masa kai kawai yai hankalin sa akan computer dinsa da yake duba wasu design na textile din da zai shigo dasu.


*********
Ihu take tana kuruwa kamar wacce ake yankata, duk mutanen gidan sun fito sai kallon ta suke suna Allah ya kara.

Kara murde mata kunne Baba yai yace "ba tambayar ki nake ba ina kika kaimin kudi na don ubanki".

Zillo tai tana kokarin kwace kanta tace "haba Baba don Allah, ni bani na daukar ma kudi ba wallahi meye hadina da kudin ka kuma fisabilillahi kawai salon dai dole sai an yiwa mutum sharri, wallahi Allah yana sama kuna yana kallo".

Bige mata baki yai yace "rashin kunya zaki min, wa kike zagi ni Umma data fada min ehe".

Turo karamin bakin ta tai tace "da Umma nake ai Baba, Allah yana kallo kuma wallahi baxan yadda ba sai na rama".

Hannu yakai zai kara mangare mata baki tai saurin kauce wa tana turo baki.

Umma dake tsaye a kofar dakin ta tace "don Ubanki *DIJE* ni kike zagi karya na miki na kece kika dau kudin ba, a gabana kika fito daga dakin sa kina boye abu a zani".

Da karfi dije ta fincike kunnen ta daga hannun Baba daya tsaya yana sauraran abinda Umma take cewa, kallon Umma tai da manyan idon ta tace "nidai nasan bani bace kuma duk Wanda ya dauka yasa ake zargina Allah ya isa wuta balbal baxan yafe masa ba".

Inna fure dake zaune a tsakar gidan tana tankade kukar da take siyar wa tace "ai Malam daka kyale ta Ka rabu da tambayar ta don in har wannan fitsararriyar ce baxa ta fada ma gaskia ba, kuma tunda har Yaya tace ta ganta da idon ta tofa ba shakka ta ganta din kuwa".

Hararar ta dije tai tace "Inna fure ba ruwan ki wallahi ba dake muke ba, kar ki shiga fadan daba naki na atoh ki barni kar na shiga harkar ki kizo kina cewa nayi miki rashin kunya".

Janyo ta Baba yai yana dafe kansa yace "wai don Allah baxa ki nutsu bane, sai yaushe zaki yi hankali kullum baki da aiki sai yiwa manya rashin kunya".

Rau-rau tai da idonta tace "toh Baba kana kallon fa, so kake nayi shiru na zuba ido ai ta soka min maganganun da zasu sa hawan jini kama ni ynxu Baba".

"Ikon Allah" Baba ya fada yana kallon, juya wa yai kawai ya dubi Mama dake yiwa Aisha jikar ta kitso, cikin haushin yadda tun da aka fara maganar nan bata sa baki ba yace "ynxu Maman Hajara kina kallon abinda yarinyar nan take amma baxa kiyi magana ba kin mana banxa kamar baki san muna gun ba".

Tabe baki tai ba tare data kalle sa ba tace "Malam mai zan ce ni kuma, ai gani nai dukkan mutanen dake tsakar gidan nan sun isa su hukunta dije shiyasa na kyale ku kuyi mata duk hukuncin da ku ka ga dai-dai ne, abinda na sani shine kawai y'ata baxa ta taba sata ba".

A harzuke Baba yace "kina nufin karya duk ake mata knn?"

Sai a lokacin ta dago ta kalle sa tace "eh toh zan iya cewa haka Kam"

Tsaki yai kawai ya juya don yiwa dije magana sai dai wayam ya gani alamu ta gudu, girgiza kai yai yace "wannan yarinya Allah ya shirye ta ita bata san ta girma ba wai?".

Tabe baki Umma tai tace "ina ta sani kuwa, kullum gata nan tana yawo da hijab sai tsami da take, da anyi magana tace yar islamiyya ce ita".

Inna fure ta cafe da fadin "shiyasa ni ko wanke wanke bana bata toh yarinya ce kazanta ta mata katutu kamar mahaukaciya".

Girgiza kai Baba yai ya sa kai ya fice daga gidan cike da takaicin kudin sa da aka dauke masa.

Ni kuwa tunda na samu na fita daga gidan ban tafi ko ina ba sai hausawa a kafa gidan Yaya Hajara, ina tafiya a hanya a hankali kamar ba dije ba sai dai duk wannan tafiyar da nake mai kama da yanga cikin dauda nake, don ash din hijab dina ya koma dark brown sbd rashin tsafta sosai duk yayi jirwaye.

A hankali na tura kofar gidan ina sallama, Yaya Hajara dake zaune a tsakar gidan ta tana girki tace "wa'alaikumussalam shigo nasan laifi kika yi shine kika lallabo nan, Allah dai ya shirye ki".

Bakina na turo ina shigowa cike da shagwaba nace "kai don Allah Yaya Hajara, wai ba gurin Wanda zanje ya dinga lallaba ni ne, ita Mama kullum tana hantara ta tana cemin kazama, su Umma kuwa dama ai ba'a maganar su kema kuma gashi nan wallahi sai na hada kayana na gudu haba kun ishe ni fah".

Da mamaki Yaya Hajara take kallonta, mike wa tai a hankali sbd cikin ta daga girma tace "ki gudu ki tafi ina Dije?".

Ba tare da shakkar komi ba tace "karkashin gada mana can Lagos".

Salati Yaya hajara ta kamayi tace "ikon Allah, yaushe zaki yi hankali Dije shekaru 15 amma har ynxu dai kullum jiya i yau".

Zama tai akan kujerar katakon dake tsakar gidan tace "nidai ba wannan ba, ki taimaka min ki zuba min abinci wallahi yunwa nake ji, kinsan girkin Inna Fure ne kuma sbd mugunta irin tata baxa tayi girki da wuri ba sai mun lallasu".

Girgiza kai Yaya Hajara tai tace "baxan baki abinci ba sai kin yi wanka kin cire wadannan kazaman kayan naki".

Da sauri na mike nace "tab baxan yiba gaskia haba don Allah taya Zan yi wata wanka kamar wata yar ruwa, shekaran jiya jiya fa nai wankan kuma kice mai wanka ynxu".

Kamar Yaya Hajara zata make ta tace "ni dai na rasa wata iriyar yarinya ce keh Dije kazanta tayi miki yawa wallahi, rabon ki da wanka tun shekaran jiya wata iriyar mace ce keh".

Turo baki nai nace "ba wankan da zanyi gaskia, nifa ina son kamshin da jikina yake in banyi wanka ba".

Tafa hannu Yaya Hajara tai tace "warin kike so dije?"?

Juya manyan idon ta tai tace "kwarai kuwa, har shinshinawa nake naji kamshin baki ji dadin da nake jiba".

Ganin zare ido baxai sa Dije tai abinda take so ba tace "toh ynxu dai in kin yadda zaki cire kayan ki tas kiyi wanka na baki wani kisa sannan ki bude kanki na wanke miki shi ni kuma zan baki 200".

Shiru Dije tai tana tunanin wanna opportunity din, da sauri tace "toh na yadda amma dai zaki fara bani kudin na rike a hannuna don karma ki min wayo".

Daki ta shiga ta dauko dari biyun tace "gashi, karba tai da sauri tace yauwa na ngd, kamar kinsan dama ina kicin matsi ina bukatar kudi".

Banxa tai mata sai kujera data jawo ta zauna, wanke ma Dije kai take da ya dankare sbd datti, ta jigata sosai kafin ta gama wanke kan sai tsaki take ita ba abin tayi mita ba tasan tsaf Dije zata ce ta fasa wankan.

Ruwa ta nuna wa Dije tace "dauki wannan kije ki dirje jikin ki sosai, na ajiye miki sabulu da soso har da sabon brush in baki wanke ko ina ba sai na karbe kudina".

Turo baki kawai Dije tai ta shige toilet din, ta fi minti 20 a ciki sannan ta fito ta don bata tsaya algus ba tunda an biya ta sai data wanke ko ina ta wanke bakin ta sosai.

Zanin da Yaya Hajara ta bata ta daura a jikinta ta fito sai baxa dogon gashin ta yake, taji dadin wanka da wankin Kan don ko ta ina iska shigar ta take yi.

Dakin Yaya Hajara ta shiga a ciki ta same ta tana zaune akan gado ta mike kafafun ta, har zata zauna itama Yaya Hajara ta nuna mata kayan da ta ajiye mata akan gado tace "kar ki sake ki zauna min dauki kayan nan ki sa, ga turare can a kan mirrow fesa a gabana ina kallon ki".

Hararar gefe Dije tai tace "kamar ya na fesa turare nifa kinsan bama shiri da turare Yaya Hajara, in na fesa ji nake kamar numfashi na zai yanke".

Tsaki yaya Hajara tai tace "iskancin banxa, ba wani kamar numfashin ki zai yanke kawai so kike ki dinga hamami kina bugawa".

Kwal kwal da Ido tai tace "ynxu nice nake hamami ina bugawa Yaya Hajara".

"Kwarai ko karya nai miki ne ehe, zaki fesa ko sai na tashi gani kikai ba'a bugun ki shiyasa kike abinda kika ga dama".

Tana zumburo baki ta fesa turaren ta zura sabon pant dn da Yaya Hajara ta ajiye mata, bra tasa wacce Yaya Hajara ta siya in ta haihu tayi amfani da shi, da fushi da komai ta sa doguwar rigar.

Sai kuma ta karasa gaban mirror tana kallon kanta, wankan nan da tai ya kara fito da farar fatar ta, fara ce sol irin farin nan natural, tana da manyan ido wanda suke dake da light brown eye ball, sai siririn hancin ta daya dace da fuskar ta sosai, mai da kallo ta tai kan karamin bakinta da yake jajir kamar yasa jam baki, shafa gashin kanta tai tana nannade sa ta daure, tana da...


Read / Download EL HAJJ

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album