Join Our WhatsApp Group

AKAN KUDI Complete Hausa Novel Document by AKAN KUDI


AKAN KUDI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 85247



AKAN KUDI

Reading Time: 7 Hours

Added On: 17, Nov 2023

Author: Sherntee Ghayu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS

Author Phone : 07064706167

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 490.62 kb

File Type: txt

Views: 509+

Download: 450+

Last download: 21 minutes ago

Description/Story: ο»ΏπŸ’΅πŸ’΄ *AKANKUDI* πŸ’΄πŸ’΅

(A poor lady story)

.... 28th March, 2023

πŸ””πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š

@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°


πŸ…Ώ......... *001*


*KATSINA*

"Ummah Kinga wallahi harna gaji da jiranta ace Idan mutum ya shiga d'aki kamar bokanya" Ummah dake zaune gefen wannan kyakkyawar Budurwar da bazata wuce 17 a shekaru ba tace "hmm Maryam Kenan ai duk Kece kika sangarta ta dayawa ace kullum sekin biyo mata" Ummah ta k'arashe tana tana kallon a gogon y'ar k'aramar keypad din hannunta ta cigaba da cewa "ai gashinan takwas din harta wuce" kyakkyawar Budurwar da aka Kira da Maryam tayi murmushi tace "Ummahmu Kenan ai yanzu zakiga ta fito" ko rufe baki batai ba Sega wata kyakkyawa kuma farar budurwa ta fito fuskarta fayau Babu ko powder natural beautyn ta ya fito tabbas da ace ba'a 9ja naganta ba danace wannan anyi kyakkyawar balarabiya irin quraish dinnan lol 😁
Tanata kiciniyar saka face mask tace "Maryam taso mu tafi kar muyi latti" Ummah tace " *SARAUTA* kofa karyawa bakiyi ba" kyakkyawar Budurwar da aka Kira da sarauta tace "Ummah na k'oshi sena dawo, wai meyasa yau bakiyi waina ba" Ummah na mik'amata kud'in makaranta tace "yau sunan y'ar gidan Badiyya inason naje ne shiyasa" sarauta tace "to kijira Idan na dawo sena rakaki zanje mu muntafi ayi mana addua" Maryam ta amshe dacewa "se mun dawo" Ummah tabisu da addua Har suka tafi.

Highlights college
Anan suke karatu Sanda sukaje anata taron latti dole suka tsaya suka amshi hukuncinsu sannan suka wuce class.

At 10:20am
Gaba d'aya d'aliban suna waje sunata wasansu inka cire wasu Daga cikin SS3 students suna zaune class suna fira, su hud'u ne Akan teburin hira suke sosai suna shewa inka cire sarauta dake gefensu tana zane. Acikin firar tasune d'aya ke cewa "amm Yawwa spincy dan Allah kinsiya wannan littatafin" spincy tace "na siya harma na Gama karantawa" da sauri zeena tace "tsakanin da Allah wayyo dan Allah kiban labari wallahi tunda na gama free pages ban kuma ba" Maryam tace "wai wane littatafin?" meelarge tace "auren wata Tara mana" Maryam tace "Kai Nima inason littafin wallahi marubuciyar tasan sirrin love dana rubutun littafi wai ya aka k'are ne tsakanin MD da XAHRA" meelarge tace "Aini Dama Bana siyan littafi sedai na jira na bati dan Allah spincy Idan kinje gida ki turomin" spincy tayi kicinΒ² da rai tace "Allah ya sawak'e insai littafi infitar dashi kinma ja wallahi tunda na gama gogeshima zanyi" Maryam tace "kudai kuka sani nidai fad'amin complete sunan littafin naje na nema" Zeena tace "gaskiyarki Maryam Nasir" Spincy tace " *AUREN WATA TARA WRITING BY HAJARA L SADEEQ MISS HAJJO*" Meelarge tace "Aina Allah base k'arewa seme dan baki turomin ba a banza zanga Yana yawo a group" Spincy tace "oho Dai aje aita karanta littafin Allah ya isa" "mttsswww" dogon tsakin dasukaji ne yasasu juyawa su kalleta tsakin ta k'arayi kafin tace "Allah dai ya kyauta muku madadin ku zauna kuyi tunani Akan yanda zakuyi suna ko kuma kunemi na kanku shine zaku zauna kuna firar banza da wofi" Zeena tace "hmm *MARYAM SARAUTA* Kenan ai gwara mu zauna muyi firar banza da wofi Akan mu zauna muyi tunanin dakike magana akai mufa matane harmu mutu rik'on mu ake Daga iyayenmu Zuwa mazajenmu daga mazajenmu Zuwa y'ay'a yenmu to Akan me zamu zauna mu b'ata lokacin mu " meelarge tace" gaskiyarki yar uwa" Sarauta tace "Aiko kunji haushi niko kunganni nan neman kud'i se inda k'arfina ya k'are kenifa *AKAN KUDI* ba abunda bazan ba raina ne kurum da bazan bayar ba" kafin wani yayi magana sukaji ringing bell alamar andawo aji daga haka kowa ya wuce mazauninshi Haka aka cigaba da darasi har lokacin tashi yayi.
Kallon Sarauta Maryam tayi tace "yakamata mu tsaida napep mu tai ko" Sarauta tace "haba Maryam nan da d'aki Tara shine Zaki wani ce muhau napep Dan Allah ki koyi economizing rayuwa haba ni band nawa kud'in inyaso kekin hau napep din Ohk" ta k'arashe tana mik'ama Maryam hannu Maryam tace "yanzu Sarauta abunda kikeyi kin kyauta Kenan ke kullum bakida abunda ke faranta Miki se kud'i kin fifita kud'i Akan kowa kin maidani kamar ba k'awarki ba wallahi kiji tsoron Allah kud'i fa halaka ne ashe duk fad'an da Ummahmu take Miki a banza" Sarauta tayi murmushi tace "hmm Maryam Kenan kud'i ba halaka bane kyauta ce kuma baiwace tadaban da Allah keyiwa bayinshi ni bance Miki keba k'awata bace kuma bance fad'an Ummah yatashi abanza ba but am sorry to say gaskiya kud'i sunfimin komai kizo mutafi" ta k'arashe tana tafiya wannan ba sabon Abu bane agurin Maryam Tasha sanar da ita kud'i sun fita a gurinta so bazatayi mamaki ba shiyasa kawai tabita suka tafi.
A gajiye taje gida, ta tarar da Ummah harta shirya sedai me cemata tayi taje kurum ita tagaji Babu inda zata, dama Ummah ta tsammaci hakan shiyasa kurum tayi tafiyar ta.



*JIDDA*

*The emir palace*


Ajere motocin suka shigo masarautar a hankali suke tafiya harsu kayi parking da sauri escorts din suka fito tare da bud'emai k'ofar a hankali yasoma fitowa daga motar kafin kuma gaba d'aya ya bayyana (hasbunallahu wani'emal wakeel tsarki ya tabbata GA mahaliccin wannan halintar) saurayine da baze wuce 29 a shekaru ba Yana sanye cikin k'ananan kaya inda ya d'ora alkyabbarshi me adon zinari a sama gashin kanshi ya sauko har gurin wuya ta b'angaren Dama kyawawan red lips dinshi su suka k'ara k'awata fuskarshi eyesbolls dinshi bak'i wuluk yariman nan dai ya had'u ta ko Ina ga kyakkyawar k'ira da rabbi yayi mishi tafiya yake in a classic way harya k'arasa wani kyakkyawan building daya gama haduwa tundaga yanayin building d'in kasan cikinshi zeyi kyau da dad'in kallo Haka kuwa akai Kai tsaye yashiga cikin k'ayataccen palourn komai yaji ba'a magana a hankali yasoma hawa upstairs d'in d'aki d'aya ya bud' e Acikin jerin d'akunan wani kyakkyawa kuma farin dattijo nagani Wanda daka kalli fuskarsa zaka hango dattijon taka da mutuntawa *SARKI LADTEEF* Kenan sarki masarautar jidda murmushi yayi tare da mik'ewa cikin nuna murna da k'auna yace "you're welcome my darling son" shima rungumeshi yayi tare da shagwab'e fuska kamar k'aramin yaro cikin lafiyayyen larabcinshi yace "ai Nayi fushi bakaje d'aukoni Airport ba koma murnar zuwana bakuyi ba" kyakkyawar matar dake tsaye gaban mirror tana murmushi tace "my baby boy Kadai k'i girma ko" kallonta yayi yace "Ummi Kenan aina gode hardake ko" kusa dashi ta dawo tana zama tace "Tohm munji we're sorry Ohk koba Haka ba JARUMINA" ta k'arashe tana kallon sarki murmushi sarkin yayi yace "hakane mana ayi mana afuwa" saman kafad'arta ya kwantar da kanshi tare dacewa "badan halinku ba anyafe" duk dariya sukayi Ummi ta mik'e tasama me martaba alkyabbarshi tare da fesheshi da turare "Abieyna seka dawo" Abiey yace "Tohm Abiey's boy sena dawo" harya fita yadawo yace " *MUHAMMAD SHUREIM*" dasauri ya juyo yace "Na'ammmm" Abiey yace "kome kakeyi karka bari yau ta wuce bakaje Ka gaida su Neenah ba kaji ko" Muhammad Shureim yace "in sha Allah Abiey" daga Haka Abiey ya fice kallon Umminshi yayi yace "meyasa Abieyna yake hakane Sarai fa yasan halin mutanen nan amma shi yafi son ayita wulak'antani" Ummi tazauna gefenshi tare da d'ora hannunta a saman kafad'aeshi tace "kayi hak'uri my son mahak'urci nawadaci wata rana se labari kaje kugaisa kaji Aidai bazasu cinye namanka d'anye ba ko" Kai ya d'aga mata tace "good boy Shureim" murmushi yayi yace "Humm Ummi Bari naje b'angaren *SHUBAI'A* tun kafin tasamu labarin dawowata tad'au fushi me dogon zango dani" Ummi murmushi kurum tayi tace "gaskiya Kam gwara kaje nasan dishes nasan an shirya maka" murmushi yake harya fice daga d'akin cike da shauk'i da d'okin ganin k'anwar tashi............


Kar ku manta labarin *AKAN KUDI* k'irk' irarren labarine danayishi domin nishad'antarwa dakuma fad'akarwa nice taku me nishad'antar daku a kullum da ko yaushe

@ *sherntee ghayu* πŸ₯°πŸ₯°

Sak'on godeeya ta Zuwa gareku a bin alfaharina
~Miss hajjo
~mom Islam
~Daddy's little girl
~zaituna


07064706167


πŸ’΅πŸ’΄ *AKAN KUDI* πŸ’΅πŸ’΄

( A poor lady story)

..... 19th April, 2023


πŸ””πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š


@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°

πŸ…Ώ....... 002

........... Tunda Yafito ake gaishe shi amma gaba daya hankalin shi ya tafi,
Wani kata farin building yashiga wanda kallonshi kurum Zenuna maka bak'aramin kud'i aka zuba a gurin ba daga ganin tsarin building din zenuna maka Bana mutum daya bane,

Babban falo ne wanda yaji kayan alatu da more rayuwa akwai bene a both side din falon wanda yabada wani style na daban upstairs d'in shima akwai falo dakuma bed rooms, hawa uku ne benen kowane hawa akwai falo bedrooms dinning da kitchen, Babban photo frame din dake a falon shize nuna maka Cewa falon nasune duk zaune suke suna dariya akan kujera su ukku akayi hoton, Yarima Shureim, gimbiya Shubai'a dakuma umminsu ba qaramin kyau sukayi ba.

A hanzarce ya k'arasa hawa na biyun, lek'e yafara kafin yashiga gaba d'aya cike dason nuna bazata yace "surprise" a D'an tsorace ta juyo, wow a gaskiya gimbiya Shubai'a bak'aramin kyau gareta ba, cikin yaren kurmanci take nuna mishi yaushe yazo, yana motsi da bakinshi kuma yana Mata nuni da yanzu yazo ba jimawa,
Rungumeshi tayi cike da farin ciki sundau kusan 3mins ahaka kafin ta sakes shi da hannu take nuna mishi tayi kewarshi,
Ahaka suka D'an tab'a hira kafin tasoma jera mishi abinci, iya farfesun kifi kurum yaci tunda yafara cin abincin yake yabamata harya gama don dama yasan lagon k'anwar tashi, haka suka d'au tsawon lokaci kafin yaje yayi wanka ya shirya ya fito domin ta rakashi b'angaren su
Neenah, da farko Shubai'a bata so rakashi ba amma hakanan ta rakashi.

Tafe suke suna fira gwanin ban sha'awa harsuka qarasa wani building shigen nasu ne amma nasu yafi haduwa shikuma hawa hud'u ne a ciki
B'angaren Neenah, da b'angaren Hajjo Mubeenah, se b'angaren Hajjo Jumaima, se b'angaren gimbiya Khaleesat,
A Babban falon suka zauna, Hajjo Mubeenah itace ta fara saukowa tundaga kallon da take musu zaka fahimci basu karb'u ba a wajenta, cike da izgili take kallon su kafin tace "Allah yasa lafiya??" Shubai'a ce tayi dariya take Mata nuni da Yarima ya dawo yau shine sukazo gaishesu, murmushi Hajjo Mubeenah tayi tace "toh fa su kurma anfara bada ba'asi" kafin wani yayi magana sukaji muryar Hajjo jumaima na cewa "ah ahh yau kuma su kurma ne a part d'inmu" Neenah dake shigowa part din tare da khaleesat tace "maraba da bak'in k'asar turai yaushe a k'asar tamu" yana d'an murmushi yace "d'azu nazo" Neenah tace "Tohm sannunka da dawowa" ta k'arashe tana zama kusa da Shubai'a, kafadarta ta data tana Mata magana da kurmanci yanda zata fahimta tace "shine se yau ake ganinki kin b'oye" Shubai'a tayi murmushi tana Mata nuni da Babu inda take zuwa, Hajjo jumaima tace "toh dama Ina kurma zeje" Neenah tace "Haba Hajjo dan Allah ki kama girmanki Ina ruwanki ba Allah ya d'ora mata ba Kindai San bada shi aka haifeta ba ko to ki kiyaye" sakamakon suna dan shakkarta yasa suka Ja tsaki duk suka koma d'akunan su, a wayence khaleesat ta gaisa da su kafin ta wuce d'akin ta, kusan minti 20 suka dauka suna fira da Neenah wanda jigon firar itace Shubai'a, Shubai'a akwai son hira da labari, kafin sukayi mata sallama suka tafi.




*KATSINA*

Zaune take daga k'ofar d'akin tana danna y'ar k'aramar wayar Ummah, yayinda Ummah ke kitchen tana girki, wani yarone yayi sallama tare da cewa "a bada kub'ewa" Ummah dake kitchen tace "ta nawa?" yace "ta ashirin" tsam Sarauta ta mik'e ta dauko mishi kubewar ta amshi kud'in ta koma ta zauna, Ummah data fito daga kitchen tace "Kwana biyu Sarauta kamar akwai abunda ke damunki duk kin shiga damuwa" a hankali tace "Ummah Maryam fushi take dani yau Kwana biyu batazo gidannan ba kuma kinga na kirata tak'i dagawa" Ummah tayi murmushi tace "Sarauta ta Maryam Kenan to ai sekije kiji me kikayi mata" Sarauta tace "to ai seta d'auka na wani damu da'ita" Ummah tace "Aikin damu da'ita ne Kinga bansan shashanci ki tashi kibani guri" tana kaiwa nan ta koma kitchen mik'ewa Sarauta tayi ta dauki Hijab dinta tayima ummah sallama ta fita, tafiya take cikin salon burgewa seka d'auka yar gidan wani Babba ce a hankali take tafiya harta k'arasa babban titin tananan tsaye kusa da wata mota, a hankali taji ana cewa "yanzu ya zamuyi mu dauko yaron can duba fa kagani akwai mutane dayawa a gurin nidai gaskiya tsoro ya kamani" d'ayan dake gefen shi yace "Haba Nas sokake ka b'atama komai kawai fa fita zakayi ka jawo hankalin yaron mud'aukai" wanda aka kira da Nas yace "gaskiya bazan iya ba" a hankali ta k'araso gefen motar tare da cewa "me zaku bani in kawo muku shi nan"................



Kar ku manta labarin *AKAN KUDI* k'irk'irarren labarine danayishi domin nishad'antarwa da kuma fad'akarwa, nice taku me nishad'antar daku kullum ako yaushe

@ *sherntee Ghayu* πŸ₯°πŸ₯°


Sak'on godeeya da fatan alkhairi ga jarumata
*Zeinerb Ibrahim momy*



07064706167


πŸ’΅ πŸ’΄ *AKAN KUDI* πŸ’΅ πŸ’΄

(A poor lady story)

......... 22nd April, 2023

πŸ””πŸ“š *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATIONS* πŸ“š


*Story & writing*
*By*

@ *sherntee ghayu* πŸ₯°πŸ₯°

πŸ…Ώ......... 003 & 004


................... A razane suka juyo suka kalleta cike da tsoron ko jami'ar tsaroce Nas yace "to ked'in Wacece eye??" cikin halin ko inkula tace "ba damuwar ka bane " Rabiu yace "to shikenan wancan yaron dake tsaye k'ofar makarantar can zaki dauko mana" juyawa tayi ta kalli yaron kafin tace "a nawa?" Rabiu yace "20k" Kai kurum...


Read / Download AKAN KUDI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album