Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

KWAI CIKIN KAYA Complete Hausa Novel Document by KWAI CIKIN KAYA


KWAI CIKIN KAYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 374193



KWAI CIKIN KAYA

Reading Time: 31 Hours

Added On: 27, Aug 2023

Author: Billyn Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 07040727902, 09134848107

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 2.1 mb

File Type: txt

Views: 7966+

Download: 18463+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: *_Typing📲_*





*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*🧺


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ*


_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_Ya rabbi ka bani ikon faɗar abinda zai amfanar da al'ummar MANZON ALLAH (A.S.W), ka tsare harshena da alƙalamina ambaton abinda zai cutar da ni da ku a duniya da lahira.😭🙏🏻_*

*_Ya ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan al'ummar musulmi da suka rigamu kwanta dama, ALLAH ka kawo mana ƙarshen wannan annoba ta corona virus (covid-19), domin rahamarka garemu😭🙏🏻_*

*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na ɗaya_
*______________________________________*


...........Ko wacce kafar yaɗa labarai da ta yanar gizo labarinsu a wannan safiya ta laraba shine sace shahararren mai arziƙin nan *Alhaji Sadi kokino (ba giyar yaro ba)*.
A yanda labaran ke ta yawo an sace Alhaji Sadi kokino ne a daren jiya talata a filin jirgin sauka da tashi na babban birnin ƙasar. Abu mafi ɗaure kai ga wannan lamari shine ta hanyar da mutumin da yay garkuwa da shi ya ƙwamushe sa. Da yawan mutane da suka shigo jirgi ɗaya da Alhaji Sadi kokino sun tabbatar ma jama'a da lafiya lau ya sauka, harma ya gaisa da wasu tsirarun mutane da suka je tarbarsa. Sannan akwai wasu ƴan jarida guda biyu a filin jirgin da har suka ɗauki hotansa da gajeren bidiyo. Kowa ya shaida Alhaji Sadi lafiyar ALLAH ya shiga motar da ɗaya a masu gadinsa ya buɗe masa, sannan amintaccen direbansa yaja motar a gaban kowa. Sai dai a lokacin da motocin suka shiga harabar gidansa aka sake buɗe masa ƙofa dan ya fita sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye, a taƙaice dai Alhaji Sadi kokino yayi ɓatan dabo a hanyar dake tsakanin filin jirgi zuwa gidansa.
Zuwa yanzu dai jami'an tsaro sun bazu ta ko ina nemansa, tare da buɗe kunnuwa da idanu ko za'aji wani abu da ga bakin wannan mai ƙwamushe da ba'a san ta yanda yay siddabarun sace Alhaji kokino ba...


*____________________________________*

A yayin da masu yawun mai da yanda akayi ke kaikawo akan wannan ruɗaɗɗen labari suma talakawa ƴan bani na iya sai tofa nasu albarkacin bakin suke. Ko wane dandalin sada zumunta na yanar gizo ka shiga sai kace nace akeyi. A yayin da wasu ke jimamin lamarin wasu ALLAH ya ƙara suke faɗa, a wani gefen kuwa ma kai tsaye suke ƙaryata lamarin da dangantashi da farfaganda irinta manyan ƙasa ce kawai, ƙilama yana can kwance a gidansa lafiyar ALLAH.
Daga masu ƙaryatawa har waɗanda suka gaskata kowa yana da dalilinsa, dan kuwa a yanda ƙwamishen ya kasance dolene ya bada mamaki, musamman idan mukai dubi da jami'an tsaro da cctv cameras da ke zagaye da filin jirgin, ga haske ta ko ina tamkar rana.

Koma dai yaya abin ya faru lokacine zai bayyana mana hakan😟.


*___________________________________*

Kwance yake a bayan motar idanunsa a lumshe tamkar mai barci, lokaci-lokaci yakan ɗanja guntun tsaki tare da huro zazzafar iska daga bakinsa.
Duk da kasancewarsa gwarzo kuma jarumin mutum mai ƙoƙari da jajircewa a aikinsa kallo ɗaya zakai masa a yanzu ka hango tarin gajiyawa da ɗunbin kasalar dake tattare da shi.
Tsayuwar motar da buɗe murfin da akayine ya tilasta masa buɗe lumsassun idanunsa kaɗan tare da ɗago hannunsa ya kai dubansa ga agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun, kaɗan ya yamutse fuska yana sake huro iska kaɗan kafin ya sauke hannun da maida dubansa ga ƙofar motar da aka buɗe.
Tamkar bazai motsa ba sai kuma ya yunkura a hankali ya ja baƙar rigar sanyinsa jibgegiya dake gefe ya zura kafafunsa waje.
Da sauri wanda ke tsaye a gabansa da alama shine ya buɗe ƙofar yay azamar kai hannu zai amshi rigar sanyin yana sake ƙamewa alamar girmamawa.
Kansa ya girgiza masa ba tare da ya bashi rigarba, ya matse idanu kaɗan saboda sara masan da kansa yake na azabar ciwo, ya sauke numfashi kafin ya fito gabaɗayansa yana tura ƙaramar bindigar hannunsa a aljihun bayan wando.
Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana saukewa akan matasan samari biyu, cikin hanzari suka ƙame tare da sara masa. Hannunsa na dama ya dinƙule kawai yay gaba ba tare da suma yace musu uffan ba. bishin sa sukayi a baya suma ba tare da sheresun da yay ya damesu ba.

Cikin nutsuwarsa ya iso wajen da ake buƙatar ganinsa, da ganin yanayin ɗakin zaka fahimci wajene keɓantacce na jami'an tsaro da sukan tattauna akan wani case ko shawarwarinsu idan sun tado musamman ta fuskar tsaro.
Ba tare da yay magana da kowa ba ya samu waje ya zauna, suma sauran waɗanda suka shigo tare wajen zama suka samu. Ɗakin yayi tsit, bakajin komai sai ƙarar AC da na fitar numfashi, sai kuma ɗan motsin da baza'a rasaba.
Wanda ke tsaye jikin allon bangon yana wani ƴan zane-zane ya ɗago fuskarsa a matukar murtuke yana kallonsu.
“Nasan kowa zaiyi mamakin wannan taron na gaggawa da muka kira, duk da dai dukkan tunaninmu zai iya tsayawa a waje ɗaya game da abinda muka wayi gari da shi na sace babban mutum irin Alhaji Sadi Kokino. Kamar yanda muka sani tun a daren jiya wasu a cikin jami'anmu suna a wajen domin binciko ainahin abinda ya faru, a yanzu hakama daga can muka tado ɗaya da ga cikinsu domin ya bamu bayanai dangane da lamarin, sannan musan mataki na gaba da zamu ɗauka kuma, dan yanzu dai ga agogo ya nuna ƙarfe 7:19am, na tabbata duk inda 8am tayi wannan labarin zai gama baje duniya ne, sanin kankune kuma mune jami'ai na farko da kowa zai maida hankalin ji da ga garemu, tun daga kan jama'ar gari zuwa ƴan jarida da iyalansa dama jama'ar dunaya baki ɗaya”.
A tare suka shiga jinjina kai alamar gamsuwa da bayaninsa.
Cikin gyara tsayuwa ya ke kallonsu, ya sauke idanunsa akansa da har yanzu hannunsa ke dafe da kansa, *“Jawaad!”*.
Jin sunansa da aka ambatane ya sakashi janye hannunsa tare da ɗago manyan idanunsa da ke a jajur ya sauke akan ogan nasa, cikin dakewar murya da ke tabbatar da shiɗin jarumine ma'abocin nutsuwa ya amsa da “Yes sir” tare da miƙewa tsaye yana ƙamewa.
Gaban allon ogan ya nuna masa da biron dake hannunsa.
Cike da kasala mai tare da nauyin jiki ya taka zuwa wajen, ya maido kallonsa gaba ɗaya zuwa ga sauran jami'an tsaron dake cikin ɗakin taron.
Cikin nutsatstsiyar muryarsa mai amo da saka razani ga abokin gaba ya fara faɗin, “Duk abinda zan faɗa game da wannan lamarin a taƙaice zai iya zama gaggawa, dan har zuwa yanzu da na baro filina jirgin da gidan Alhaji Kokino babu wani bakin zare da muka samu a kai sai surutai marasa makama, a cctv cemaras na Airport kuma lafiya lau Alhaji Sadi ya shiga mota tare da masu tsaron lafiyarsa. A ɗan nazarina ta wannan gaɓar ya nuna lallai mai satar yanada matuƙar wayo, kuma ƙwararrene mai aiki da ƙwaƙwalwa...”
Kowa jin jina kai ya shiga yi alamar gamsuwa da bayanin Jawaad da ke riƙe da kansa da ke ƙara ƙarfin sarawa na ciwo.
Wanine cikin waɗanda ke zaune a kujeru na musamman, alamun shima babbane yay gyaran murya tare da gyara abin maganar dake gabansa. “Wato bayanan JAY abin dubawa ne kam tabbas, amma ku wace shawara ce da ku a kan hakan?”.
Wani ne da ga can rukunin kujerun da Jawaad ya taso ya ɗaga hannu, damar magana aka bashi. Bayan ya miƙe...


Read / Download KWAI CIKIN KAYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

6 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album