Join Our WhatsApp Group

D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU Complete Hausa Novel Document by D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU

D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 6837

D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU

Reading Time: 0 Hours

Added On: 03, Nov 2023

Author: Mujahida Matar Malam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07064904617 or 07031012948

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 43.25 kb

File Type: txt

Views: 495+

Download: 113+

Last download: 3 days ago

Description/Story: *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

_26/7/2023 Jully Tuesday_

*BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM*

*Free 🅿️ 1 to 5*

.......Wani Matashin Saurayi nagani Zaune kusa da Ahlinsa sai fira suke cikin k'aunar juna,

"Samar!" Matar takira sunanshi cikin serious voice, Jin hakan yasa ya maida Hankalinsa kanta Domin ba kasafai take Kiran sunan shi ba, saidai tace tace Soja, hakan ya tabbatar masa Abunda mama zata Fad'i Mai Mahimmanci ne,

"Na'am Umma,"

"Soja kanada Aikinyi Yanzu kuma ko mahaifinka nada Arzikin maka Aure Koda Kai bakada Abun kace Abari kasamu Aiki Yanzu shekara 3 kana Aikin kasami K'arin girma kuma kasami Kud'i to yanzu kasamu Wadda zaka Aura,"

"Mahaifiyar ka nada Gaskiya Yanzu kayi shekara 30 fa to ya kamata kayi Aure soja,"Cewar Abba

Hunmmm: Shikenan In Sha Allah Zan k'ok'arin neman Wadda ta dace,"

"Masha Allah, Allah yakawo tagari,"

Wayarsa tafaru ruri sunan Taj ya bayyana Cikin murmushi yad'aga Kiran Yace "Hello my friend Yane,"?

A d'ayan b'angaren Akace "normal kaga sak'o ta email d'inka Major Yana nemanmu da gaggawa Kan wani Assignment zamuje,"?

Gyara Zaman wayar yayi Yace"Assignment kuma? Bayan Munsami hutun 1 months wane Assignment kuma,"?

"Nima ban sani ba wallahi na d'auka ma kaga sak'on da shine zanyi wannan tanbayar Yanzu mukayi magana dasu Sam itama tayi mamakin Abun Amma koma yayane idan muje Abuja Gobe masani,"

Hunm: "Shikenan badamuwa sai mun had'e goben"

Katse Kiran yayi ya duba Email d'in Tabbas Anason ganinsu gobe,

Fad'ama Iyayensa yayi suka masa fatan Alheri sannan ya hau Shirin tafiya............

**********"""""""""''********

"Sam wai kina macce Amma baki zama ki huta kullum cikin wahala kibar Aikin mana kinga Adangi sai zagina Ake wai nice na d'aure miki gindi kike Aikin maza kina cud'anya dasu,"

"Mommy manta dasu kawai cikinsu ba Wanda ya tab'a taimakon mu bayan rasuwar Baba so Yanzu nayi Aiki tuk'uru nasami Aiki gashi harna Samu K'arin girma to baikamata na watsar da damata ba kawai kimin Addu'a Allah ya kareni"

"Addu'a cikin ta nake kullum sam to Amma maganar Aure fa"?

"Aure lokaci nazuwa Mommy Amma in Sha Allah namiki Alk'awari muna dawowa Wannan Assignment da Akamuna Kiran gaggawa to zanyi,"

"Shikenan Allah y kareku"

"Ameen mommy na Ina sonki"

"Nima haka yanzu yaushe zaku"?

"Gobe ne, kawaii na shirya kayana ne nasan bazan dawoba daga can zamu wuce Assignment d'in,"

*********""""'''''''''******

"Jidda Yanzu barina zakiyi kije wannan Aikin? Auren mufa saura sati 3 Amma zakije wani Assignment kibar Aikin mana,"

"Kaga Bash Koda kasanni kasanni da Aikina Kuma Ahakan kaji kana iya Aurena so kayi hak'uri Mana kasani ko badogon Assignment bane,"

"Nifa bazan iyaba Ace wai wadda Zan Aura take cud'anya cikin k'attan maza, indai kikaje Assignment d'in to wallahi ki nemi wani mijin," fuuuu yabar wurin,

Baki sake tabishi da kallo wai kada taje to soyake tarasa Aikinta bayan Tasha bak'ar wuya Kafin takai inda take yanzu,"? Tabbd'i wallahi bazatayi dagegeduwa Aiki Kam saitaje,
Shiga gida tayi wani iri hakan Yasa kaka tanbayar ta lafiya kuwa?

Bata b'oyemata komai ba Dan Batada kowa sai ita iyayenta sunjima da rasuwa take hannun kakar babanta ne,

Tsaki taja Mtssswww "saboda shi kike damuwa manta dashi idan kikaga Auren baiyuba to Allah Bai bufa ba jeki kiyi Aikinki Ai Namiji Banda Tabbas dama ni na fahimce bawani sonki Yake ba, ki kwantar da hankalinki kinji"

"To kaka nagode"

Tana komawa dak'i takira k'awarta Sam tafad'a mata itama hak'uri tabata,.....

***********"""""""""""*******

Wash gari duka sun had'e Abuja A babbar headquarter ta sojojin

Major Sa'id Yafito ya Fara magana bayan Angama zab'ar wad'an da za'ayi tafiyar dasu,

Su 4 ne Abokan juna Samir, Taj, Sam Jidda dama sune suka Jima suna Aiki tare saidai Samir shine babba cikinsu,

"Abunda Yasa namuku kiran gaggawa shine Akwai wata Annoba data fad'a wani gari, kuma ta rutsa da wata Y'ar k'ank'anuwar yarinyar general wadda bazata wuce shekara 3 Shine mukeson kuje ku ceto wannan yarinyar, sanin kunada k'wazo yasa Nasa daku cikin Wannan tafiyar, Wanda Kai Kaine jagoran tafiyar Captain Samir, Amma sanin makamar daji Emanuel ne Dan Haka ko Ina zaku shiga Saida nasa izinin, ga sauran Abokan tafiya ne Duka ku 200 zaku Domin dajin da Hatsari, Akwai makaman YAK'I da muka tanadar muku sosai, sannan duk Wanda Yadawo daga wannan tafiyar to yanada K'arin girma da kyauta ta musamman Wadda kuma shikanshi general zaima mutum babbar kyauta muddin Aka ceto masa Y'arsa kusani tafiyar dolece kuma kada ku kuskura Arasa Y'ar, Magana tak'are zaku iya tafiya yanzu fatan Alheri da nasara"....................

_BASEERA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948

*D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Free 🅿️ 6 to 10*

......."Taj nifa jikina yayi sanyi Anya wannan tafiyar zanyi ta kuwa,"? Cikin sanyi Jidda tayi maganar,

"Haba Jidda kada ki sare Mana kinmanta irin wuyar da kika shiga Kafin kisami wannan Aikin ma? Kuma Kika samu sannan kikayi training ba iyar wuyar da Baki shaba Amma Kika jure har yanzu Kika kawo wannan matakin bugu da k'ari Bakida kowa sai kaka kaka Bata dogara da kowa ba sai ke ki K'arasa cika burinki Mana Zaki iya,"

"Amma Taj kaduba irin Yawan makaman da Aka bayar zuwa Sojojinda Aka had'amu dasu wannan kad'an ya isa ya tabbatar inda zamu shiga wurine Mai had'ari,"

"K'awata kada kisaka tsoro kisa su d'auka macce batada jarumta Mana Zaki iya koma meye,"

Hunmm: "Shikenan Allah yabamu nasara"

"Ameen suka Ansa,"

Tinda Suke zancen Samir kallonsu kawai Yake Amma yasan wannan tafiyar saita banbanta da saura kawai shi ba mutum bane ma'aboci yawan magana shiyasa yayi shuru Amma Yana fatan suyi nasara Kan wannan Aikin,....

Suna fitowa waje inda zasu shiga motar saiga bash Yakira Jidda, cikin mamakin ganinsa Nan taje, "Ya lafaya meya kawoka nan? Tafiyar zamuyi fa,"

"Yanzu Jidda saikin je kenan, bazaki fasa ba,"?

"Kaga mungama wannan maganar tini Anawa tinanin so kabar sauran zancen saina dawo kawai,"

"Idan kikaje bani bake zaj tura A k'arb'o komai nawa, Zan Aure wata daban,"

"Allah ya bada zaman lafiya," tace cikin Jin haushin maganar tashi tawuce,.

Taj kuwa tinda taje wurin bash ya kejin wani irin zafi mara misaltuwa take ya b'ata fuska ya fad'a motar yana danna Mata Hon cikin Haushin kula bash datayi,.

Dariya Sam tayi dama tasani Yana dakon son Jidda kawai ya kasa fad'a Mata ne, domin ganin tana da kayan wani kanta,

Samir kuwa murmushi kawai yayi

Shiga motar tayi tana Fad'in "Kuyi hak'uri"

Cikin d'aga murya bash Yace"Wallahi I'm serious Jidda idan kikayi tafiyar to munrabu kenan!!!,"

Wani irin d'aci taji Yana taso Mata tindaga Zuciyarta har cikin bakin ta, wannan ai to zarci ne,

Luummm shi Ido tayi tana Jin zafin maganar shi,

Taj kuwa dad'in maganar tasa yaji Domin koba komai watak'il nasa rabo ne yasa hakan tafaru,

"Idan d'an iskan baijaye daga Hanyar mu takashi kawai," Cewar Taj cikin d'aga murya,

Satar kallonta yayi still idanta rufe tajingina jikin kujerar motar,.

Tafiya maitsawo sukayi inda suna Amfani da computer zuwa taswirar gano dajin, basu tsaya ba Saida sukayi tafiya Mai Nisan Gaske kusan sai magriba, Sannan Suka tsaya domin sallah Sunshiga daji Anan suka kafa tinti harda bacci Nan zasuyi sai zuwa safiya sannan suci gaba da tafiyar,.

Masuyin sallah Suka fara, wad'an da basayi kuwa suka Fara cin Abincinsu,

Bayan sungama sallah suka Fara cin Abincinsu

Jidda kuwa zubawa Abincin Ido kawai tayi tana tinane tinanenta,

Cikin sanyi Taj Yace"Jidda Aikinki baya buk'atar dogon tinanin balantana keda Kika shigo babban Assignment, ki daure kici Abincin kinji,"

Hunmm: "nagode da kulawa"

Nan suka kwana lafiya k'alau basu had'u da komai na cutarwa ba,

Ahankali Taj yaie shiga Lamarin Jidda harta rage yawan tinanin,

Kwana 7 sukayi suna tafiyar sun shiga manya manyan da zuzzuka sun wuce birane da garuruwa , Computer tana Nuna musu sun kusa Shiga dajin,

Randa suka cika Kwana 12 suka iso wani dajin Wanda mota Bata shiga inda Taswirar ta Nuna zasubi,

Fitowa sukayi Suna nufar dajin datake Wayoyinsu da Computer suka d'auke komai ya daina Halbawa,

Cikin mamaki Samir Yace"kunga Computer tadaina Aiki hakan Yana Nuna muna cewa Cewa inda zamu shiga ba Network duk wani Sadarwa baya Aiki wurin,"

"Yaya zamuyi kenan tinda kusan computer itace d'auke da Abun komawar my dama zuwan namu," Cewar Sam

Taj Yace"Saidai mu d'auke duk wani Abu da zamu iya, Sai kuma muyi Amfani da Taswirar takarda, Yanzu Aikinka zai fara Emanuel"

Cikin Isa da hura Hanci Yafito tsakiyar su Yace, Kowa Yacika wannan cakar da makaman domin kariya wa kansa tinda motar Bata shiga ciki, sannan wannan zagaye nane so dole kumin biyayya," Yana gama Fad'ar Hakan Yafara lodar nasa makaman A jaka, ganin haka yasa kowa Yafara d'iba,

Tsaki Sam tayi Tace"dube shi kamar wani Birin har yake Fad'in Dole A masa biyayya Mtssswwww"

"Rabuda banza dama ni haushi yake ban wallahi," Cewar jidda

Murmushi Samir yayi"Kunga ku manta dashi kawai muje mud'iba Muma,"

Kowa ya d'auke Abunda zai iya Koda na lek'a motar Naga sun kwashe makaman dukan ko wanne d'auke da k'atuwar jaka A bayansa Hannuwansu kuwa d'auke da manyan bindigoginsu Suka nausa cikin dajin, Emanuel ne gaba sai Samir, Taj, Sam, jidda sai sauran tawagar tasu ko wanne rik'e da bindiga Kuma A shirye Koda wani Abu zai taso musu,

Sunyi nisa sosai domin sunshiga tsakar dajin ba Abunda Suka gani, bakajin komai sai sautin kukan wasu tsuntsaye Yan tsiraru, ga manya manyan itace dogaye Wad'an da suka ma dajin k'awanya,

Kwatsam sukaji wani irin gurnani na fitowa ta gefensu Yana nufosu,

Cikin tsorata Suka tsaya can bisa d'aga hannu da Emanuel yayi yana wurwurga idanuwa Dan ganin meke Shirin kawo musu far maki,.

Kamar daga sama saiga wani gabjejen Zaki Ya fito, Wanda Sam baida shawar kallo, sau d'aya zaka kalleshi kasan lalle bawai iya zakin gaske wanda Suka sani bane, Dole wannan SHAID'ANIN ALJANINE Yadawo zaki,

Tsaye yayi yana k'ura musu idanuwansa wad'an da jajir suke hak'uransa Zara Zara masu tsinin gaske, Wani irin Gurnani yayi Wanda Saida dajin Ya Ansa gaba d'aya, kansu Ankara Wasu shirga shirgan zakuna kamar sa suka bayyana bayansa,

Tsorata Iya tsorata sun tsorata domin wasu har sun ja baya,

Cikin rawar muryar Sam tace"Bana tinanin bindiga zata iya Kub'utar da rayukan mu dole mu k'ara da takubba,"

Maida bindigar Samir da Sam sukayi zuwa Taj jidda kuwa iya bindigar kawai zata iya rik'awa,

Ganin hakan yasa SHAID'ANUN ZAKUNAN suka fad'a musu da mugun nufi.......................

Wai koya zata kasance??

Kubiyoni next page Masoyana....

*BASEERATA ITACE ARZIKINA😍*

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948

*D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟‍♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Free 🅿️ 11 to 15*

...

Read / Download D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album