Join Our WhatsApp Group

HAKA NAKE SANKI Complete Hausa Novel Document by HAKA NAKE SANKI


HAKA NAKE SANKI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22708HAKA NAKE SANKI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 29, Sep 2023

Author: Fatima Aminu Ya'u ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09028287218

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 126.69 kb

File Type: txt

Views: 1099+

Download: 282+

Last download: 14 hours ago

Description/Story:  Haka Nake Sanki
Written by
Fatima Aminu Ya'u
F.A.Ya'u


Sauri kawai take kanta akasa dan bata san magariba tai mata juyawar daxatai sukai ido biyu da shi nan taji gabanta ya fadi ayan kwanakin nan tafuskanci kullum setaga wannan mutumin tun bata fara xargin ita yake bi ba harta fuskanta nan take bugun xuciyarta ya karu wani tsoro ya xiyarci xuciyarta sakamakon magari ba tayi ita daya ke tafe seshi dake binta a baya nan ta kara saurinta.
Dasaurinta ta shiga gidan ko sallama batai ba dan yadda taga shima mutumin saurin yake daga bisani ta nemeshi ta rasa haba mesunan manya yaxaki shigo gida ba sallama umma karene ya biyoni kinsan in yanma tayi aikam naga alama toma me kika tsaya yi a hanya se yanxu xaki dawo wallahi malan muktar ne ya tsaidamu yadanmana nasiha to yayi kyau maxa cire kayan kixo ki kaima hajiya karima tuwonnan to umma ta shige daki dan aje jakarta bayan ta shafa doguwar addu'ar tata tafito umma ina tuwon gashinan na samirane ki gaisheta seda taxo xaure ta tuna dashi aikuwa nan gabanta ya soma faduwa kamar yadda ta xata yana kofar gidan azaune bata nuna alamar taganshiba tai gurin da"aka aikeran tai sa'a kuwa me gadi na kusa ya bude tashige.
Bayan sun dan taba hira Aisha ta rakota xuwa kofar gida vayanan ta fada aranta tadanji dadi sukai sallama ta shiga gida.
Shi kansa yarasa me kedamunsa yabi ya rikice yabi ya manta da duk abinda yake ciki yarasa me yasa yake biyema xuciyarsa indai begantaba baya jin dadi duk irin korafin da ake masa a gida da gun aiki yashanye akullum ya tunkareta se yaga tanai masa wani kwarjini xuciyar sa na fada masa yadaure anman ya kasa.
Tafe take cikin nishadi dan yau kam bataga mayenba koma nace aljanin yadda tasama ranta kenan gani harta kawo titi bata ganshi ba yasa ta yadda aljanine addu'arta ta koreshi sedai me wata dalleliyar mota ta tsaya gabanta ya xuge glass din shine tagani yana sakar mata murmushi tai saurin matsawa ya fito kadija ina kwana ya fadi gavanta ya cigaba da faduwa au yama san sunana bata jira ko bashi amsaba ta shige dansahun da ta tsaida.
Waike bakyajin mutanene taji muryar me dansahun yi hakuri vanjika ba ta sauko gami da mika masa kudinsa tunanin abinda ta aikata take mesa bara tsaya ta amsa gaisuwarba aida tsaya watakilma taji shi waye tarokeshi ya kyaleta harra shiga aji tana saka da war wara.
Yau sati na biyu kenan bata ganshi a hanyaba tun bata damuwa har tadamu yakai duk inda tasan tana ganinsa tana bi bashi va dalilinsa wani xubinma har fita take tadan yawata ko xata ganshi abinda yake ba halinta bane tarasa me yasa ta damu dashi haka duda xuciyarta na fada mata kawai tanason ta ganshine ta bashi hakuri vata da wani abin tunawa akoda yaushe banda fuskarsa cikin sanyin safiyarnan yana mata murmushi muryarsa akullum amsakuwa take matq khadija ina kwana.
Kwance take tana kallon fankar dakin maganar vilkisu take tubawa khadija ko kiyarda ko karki yarda u are in love taurin ran xuciyarki yaki yarda wani hawaye suka xubo mata a hankula ta furta nayadda dake wallahi am in love but with whom bansanshi ba nida nai alkawarin baxan tava soyayyaba yaxanyi toma inshi din va sona yakeba xuciyarta tabata amsa tabvas va sanki yake ba yau tsahin kwanaki benemekiba bema tava cewafa yana sankiba toma inyace yanasanki kekinsan ke ko wace tafashe da kuka tunowa datai itadin wace da tunoshi cikin rantsattsiyar motarsa tasan ba kowanne irin iyayene xasu yarda sansu ya aureta ba.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u
Hawayenta ya karu ga wani kunci da ya xiyarce ta ko mai ta tuna oho tai murmushi gami da goge hawayen a hankula tace Allah kaine abin godiya gami da mikewa ta dauro alwala dan bayyanama Allah bukatunta.
Washe gari da sassafe ta kintsa bayan ta gama aikin gida bata ko tsaya bi takan karyawa ba taima umma sallama ta wuce makaranta tai sa'ar shiga sch din da wuri dan haka ya hau aikinta matsayinta na mai dan kwali.
Ko ayauma tasanya ran ganinsa duda tayadda duk abinda tasa aranta be cika xama gaskiya ba duk yadda umaima tai taxo su tafi taki dan ita yau aka tai niyar tafiya ko Allah xaisa taganshi tarasa wacce irin xuciya gareta namiji xai xo da'alamar so tunkan ya furta xata koreshi inya tafi taji duniya shi take san gani daga bisani ta mance sedai fame shi wannan nasa yafi na kowa domin tarasa meyasa har yau takasa mancewa dashi.
Nasir ne xaune gaban gadon yai tagumi abu buwa duk sunbi sun cushe masa gashi mamarsa ba lpy gashi yanasan ganin khadijansa yarinyar data xama wani bari na jikinsa yarinyarda baya minti biyu cikakke se ya tuna ta yasani ita tama mance dashi watakil ma murna take ta dena ganinsa dan ya fuskanci ba tun yau ba bata san ganinsa.
Nasair nasir yaji muryar maman tasa asanyaye ya mike xuwa inda take kaga nadan samu sauki gara kaxo katafi aikinka karsumaka wani abu yai dan murmushin karfin hali ai bakomai abinda nine director anman ai gunka nakasa xasu dauka eh hakane mama anman kibari kisake warwarewa tukunna to shikensn Allah ma albarka ya amsa amin mamata.
Yau kam jikin mamar da sauki dan haka ya yanke shawarar yau da yardar Allah xe gabatar ma da khadija kansa xai cire duk wani abu na tsoro tsoro da gwarjuninta dan hakane ma gaba daya kayan war dropped dinsa ya futo dasu ya xabi wannan yace beba yaxabi wancan secan idonsa yakai kan shadda sky blue me dinki kalarta tai masifar kyau.
Kimanin karfe hudu yafito tsaf dashi yai kyau sosai kai kace sabon angone koda ummansa ta ganshi tai murmushi dan albarka ina xuwa haka xani gidansu najib ne tai dariya to ka gaisheta yadan jiyo yakalleta kunya ta kamashi se nadawo to se kadawa ya fita yana dariya yanasan ummansa musanman yadda take gane duk wani hali da yake ciki koda kuwa ya boye mata.


Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u
Hudu da rabi tai masa kofar gidansu dan yasan yau bata islamiyya yafi mintina goma be samu dan aikeba yarasa yadda xaiyi can ya hango wani yaro xai shiga gidansu Aisha yai kwala masa kira yaron haryai kamar yaki xuwa se kuma ya yaxo yawwa dan albarka shiga gidannan ka kiramun khadija to yace gami da shiga.
Wai khadija taxo maxa jeka kace batanan tafadi da sauri xatonta umma batajiba harya kai xaure umma ta kwala masa kira Abdallah jeka kace tana xuwa yafice waike me sunan manya yaushe ne xaki dai na abinda kike nafara gajiya da halinki ko cemiki akai ahaka xaki dawwama tai narai narai da ido anman umma yimun shuru inkuma ban isa insaki bane seki fadan ta mike gami da xura hijabinta tai kofar gida.
Tsaye yake jikin motarsa sanye da gilas fari yai masa kyau sosai ga sajen fuskarsa ya kwanta luf kallo daya tai masa wani kwarjinsa ya karu kan fuskarsa tadauke idonta.
Ahankula tai masa sallama batama tsammanin yajita ga mamakinta taji ya amsa barka da rana ta fadi ayayinda bata sanma ta fadi ba duk xuciyarta a rikice take karfun hali kawai tai ta daure bata nuna ba duda tana xaton ya fuskanta. Koda shike shidin farin shigane duk ya rasa mai xai ce mata duda tun jiya yake practice tadan dago batare da tabari sun hada ido ba tace ko xamu matsa kan tuduncan ba damuwa.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u
Sun xauna nadan wani lokaci kowa da abinda yake sakawa cikin ransa kafin Nasir ya jarumtar katse musu shurun da fadin khadija ta dago ta kalleshi na'am nasan xaki mamakin ganina tai murmushi ai ban mamakiba yadan kalleta sabida tace bakomai Allah da komai ya fada taidan murmushi gami da yin shiru any way sunana Nasir muhammad Abdulmalik ina aiki a asibitina fa'ams special hospital batun yauba ina ganinki inasan namiki magana sedai bansan ciki kula yarinya kan hanya ba.
Tai murmushi naji sedai gaskiya ban fuskanci abinda kake nufi ba ta fadi dan jin mexai ce yai murmushi haba dja nasan kin fuskanta inba damuwa ni bansan ciki doguwar soyayya awaje ya kike gani tadan kalleshi kamar ya fa ina nufin xan turo iyayena ai mgn lallaifa ta fadi cikin ranta wannan kaine sarkin sauri hango wata shekarar banda abinsa daga haduwa yau kowata mgnr kirki vasuyi ba sai maganar aure tai dariya kadai bari mu fuskanci juna tukunna yai murmushi dan yafuskanci ko bakomai yasamu shiga.
Ledodin da ya sayo nata gift ya dauko mata gashi naxan wuce mene tace inkinje kya gani nidai baxan karba ba dan Allah karki mun haka Wallahi baxan karba ba sabida me kawai to shikenan naji ban no dinki ai banda waya pls karmuyi haka dake.pls kiban wallahi banda waya to naji yaushe xan dawo duk sanda ka shirya ohhhhp ya fadi haba dja.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u
Tai dan murmushi ya nasir kenan yaji dadin rike sunansa datai bakiji ba ta kalleshi nixan wuce anman wata alfarma xaki mun kice mun wani abu mana da xan dinga tunawa dake kafin nadawo toshikenan kagaida gida ah bakamar wannan ba tai dariya to kamar me kamar i love u ta rufe fuska gami da shigewa gida tana murmushu shima yadan murmusa kafun ya mike yabar wajen.
Koda ta koma gida umma naxaune a tsakar gida tadan kalli khadija yakika dade uhum umma daman daman tashigewarta daki umman tai murmushi kawai burinta yau taga auren khadijarta.
Yaukam nasir rageggen bacci yai dan cikin farin ciki yake duk yakasa sukuni ba abinda yaxamar masa abaun tunawa sai firarsu da khadija.
Kafin wani lokaci shakuwa mai xafi da so da kauna ta shiga tsakanin khadija da nasir har basa iya boyewa duk kasan tuwar nasir miskili anman gurin khadija akune.
Ayanxu ba'abinda ke damun khadija cikin soyayayyarsu sai inta tuna da asalinta ta tuna da ita din wace tasani komai daren dadewa sai nasir yaji koya xai karbi lamarin ko watakil ma ya tsaneta ko iyayensa xasu yarda ya aureta.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u
Yau tunda ta tashi take jinta wani irin kamar ma kartaje makarantar dan batasan karya record dinta na rashin fashiba da ba inda xaka haka ta daure ta tafi.
Ko a sch dinma bata wani tabuka abin kirkiba kawai jinsu take yayin da bilkisu kawarta ta takura mata wai sai ta fada mata wanda take so taje ta fada masa sanin halin bilkin natsokana yasa har yau takasa fada mata game da nasir duda kuwa bata da kamarta.
Gaba daya ajin ya rikice surutu kawai kake ji na yan ajin kowanne group kakalla da abinda ke damunsu da abinda suke tattaunawa da alama sunajin dadin rashin shigowar malamin nasu suma yan group dinsu khadija suna hirar da suka saba wato hirar irin labarun da'ake karantawa jokes gaba dayansu cikin nishadi suke inka dauke khadija dabama tasan me sukeba binsu kawai take da ido maryan tadan kalli Fatima wai meke damun kadija ne wayasan mata yan miskikancinne ya motsa inji Aisha haba bawani aiduda jama'a nacewa itadin shuru shuruce munsan karyane tunda kuwa har damunmu take kawai dai da abinda ke damunta Fatima ta fada ku dalla ku kyaleta ninasan me ke damunta bilki ta fada Aisha ta xuro kunne shi yasa nake sanki kawalli guntsa mana anawa ta miko hannu to lashe money kedai kudi kudi tonaji xakumun note eh munji she is in love gaba daya suka hada baki da karfi gami da gwalo ido😳 what love gaba daya idon ajin yadawo kansu inda yai dai dai da dawowar khadija daga tunani suka saka dariya gami da tafawa what a surprise Fatima ta fada tavdi daman anfada ai masu cika baki kan love is nothing basu iya kamuwaba tai dariya wallahi ku yan iskane shikenan mutun baida damuwa seta love banajin dadi ne kunsan wani xubin inna tuna da matsayina gaba daya suka nutsu dan basa san take tunawa da wannan batun kowacce ta hau mata nasiha.
Tana san kawayen nata domin sudin bata da kamarsu basa taba nuna mata tsangwama ko banbanci face ma duk wata matsala fabata fi karfinsuba suke shige mata faba xamowarsu tare tasamu yanci gameda abinda sauran dalibai ke mata tai dariya gami da rungume su shi yasa nake sanku naji yanxu kaina ke ciwo bari na kwanta kafin atashi mudai bamu yardava ki tashi muyi fira Allah kaina ke ciwo ainai muku alkawarin ayau vaxan kuma damuwaba to shikenan bari nakarbo miki mgni inji bilki kema kinsan bansan maganin sch dinnan Aisha tace inada bari akawo ruwa seki sha nifa magninne bana so innadanyi baccin xai sauka to shikenan kowanne malamine yaxo kuce bani da lpy.
Da murmushinta kan fuskarta daga gani tana cikin farin cikin ganinsa ina ya na barka da yanma bai amsaba abinda bata sava ganiba fuskarsa adaure yana ko naima lefine lefi lefi fa kika ce aini abinda kika mun yafi karfin lefi wallahi khadija kin ban mamaki yanxu ace atsakaninmu akwai yaudara da cin amana da ha inci kinban mamaki ban taba xaton kedin munafika bace se yau nasir me nayi ban cancanci wadannan miyagun sunayenba aikin cancanci fiye da haka naji kafadan menai na kare kaina kare kankifa kika ce uhum yawani saki murmushi daga gani na takaici ne kin cuceni khadija dakika sa nai xurfi asanki alhalin kinsan bamu dace ba anfadamin ko ke wace inaso kimun wata alfarma ki mance da kinsanni kamar yadda na shafeki a babina amma anman what ya fada cikin daga murya gami da cewa baki da abinda xaki cemun cutace kin cuce ni ya shige motarsa tai saurin rike mirfir dan Allah katsaya kasaurareni kisakar min mota ko wallahi yanxu nai hajijiya dake dan Allah kasaurareni xaki saki kosaina makeki yako hankadata gami da jan motarsa ya badeta da kura ta durkushe a gurin tana kuka.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u
Haba khadija wannan wane irin saka abu araine kina bacci kina kuka bilkisu tafadi gami da girgizata firgigit ta farka gami da fadin innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wai lafiya bilki ta kuma fade a kagare wallahi wani mafarki nai mara dadin ji to basai kin...


Read / Download HAKA NAKE SANKI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album