Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

SHALELAN BABA Complete Hausa Novel Document by SHALELAN BABA


SHALELAN BABA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 66252



SHALELAN BABA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 06, Apr 2025

Author: Amnah El Yaqub ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Romance 18+ Novels

File Size: 394.38 kb

File Type: txt

Views: 433+

Download: 889+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: [8/24, 10:07 AM] SHALELAN BABA: 💕SHALELAN BABA💕

(Romance)



Story about luv❤

She is a very very poor girl HANEEFA, who fell in love with one person, he is rich man, nd beautiful, miskilin gaske, duk inda kake tunanin masifa tashi ta wuce nan

karku Bari abarku Abaya wajan Jin Yaya wannan story zai kasance

💕SHALELAN BABA 💕

💕SHALELAN BABA 💕

COMING SOON





Mrs Usman ce ✍🏻
[10/8, 10:31 PM] SHALELAN BABA: 💕SHALELAN BABA💕

(Romance)



To wannan karan alqalamin nawa zai fara tabo muku qauye ne

Ina Fata da burin kasance war mu tare my fan's, Allah Kuma yabani ikon gama wannan labari lafiya Kamar Yanda nafara 🙏🏻



Daga marubuciyar :



🌱DANA SANI🌱

(Ahmad&Feenah)



💞BURINAH💞

(Amal&Daddy)



💖WAZAN ZABA?💖

(Iman & Aliyu)



And now 👇🏻



💕SHALELAN BABA💕

Is loading...











Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem



1&2



Tsugunne yake agabanta,hannunsa riqe da Kambos na yara Yan makaranta fari qal dashi Mai kyau, yayinda ita Kuma take atsaye, tayi tsananin kyau cikin uniform dinta na makaranta,wandon dark blue ne, yayinda rigar ta kasance white blue, Dan qaramin hijabi ne ajikinta fari wanda ya Qawata kyakkyawa fuskarta aciki

dago kansa yayi yadubeta da tsananin soyaiya da kulawa yace Shalele nah saka takalmin naki mana banaso kiyi latti wani malamin ya tabamin lafiyarki



Bubbuga kafafunta tafara aqasa cikin shagwaba tace Allah baba ni Bansan wannan Kambos din, baba yaufa zamu gama makaranta, nide saide ka daukomin wannan sandal din daka siyomin jiya, wannan dinfa satinsa daya baba, taqarasa maganar tana turo masa baki gaba



Murmushi inna Marka tayi, ta dafa kafadarta tace haba Shalele, yanzu menene laifin wannan takalmin,?



Rau rau tayi da ido alamar kuka

Murmushi Baba yayi yace "Kinga Marka dauko mata wancen din saita saka"



Duban ta inna Marka tayi tace to jeki cikin kwabet Dina zaki ganshi aciki saiki dauko

Da gudu ta juya tashige dakin inna



Ungo wannan takalman Marka, ki ajiye mata su a'inda yadace

Karba tayi takai shi cikin yar qaramar barandar datake gaban dakinsu, sannan ta nufo wajan baba da wani Kofi ahannunta



Daqyar tagano takalmin nata ta futo dashi, Kai tsaye wajan babanta ta nufa



Baba gashi



Yace to Shalele, Ina safar Taki?



Safar tabashi, ahankali yakama farar kafarta da yatsun kafar suke dogaye Zara Zara dasu gwanin sha'awa, saka mata safar yayi tana Daga tsayen saide ta Dora hannayen ta akafadarsa, Saida yagama saka mata sannan yasaka mata sandal dinta



Yace inyeee yanmatan babanta shikkenan sai hankali ya kwanta Ko?



Tafin hannunta tasa tarufe fuskarta alamun kunya 🙈



Murmushi yayi kawai, cikin ransa yana yaba tsananin hankali da nutsuwa dakuma uwa uba kunya da Allah yabawa yartashi qwaya daya jal



Kinga Shalele karbi wannan kwastadin naki Kisha, kada kitafi da yunwa, inji inna Marka



Babu musu tace to inna, tsugunna wa tayi, ta karbi kofin zata sha, baba yace a a Shalele nah, kawo nabaki da kaina



Daria tayi sannan tabashi kofin

Cikin nutsuwa yake Bata, Saida takusa shanyewa sannan tace baba naqoshi



A a Shalele nah, bakyason cin abinci, daure ki shanye shi duka, bazaki dawo gidaba sai Bayan sallar zuhur



Bata musu da mahaifinta, dole haka ta karba ta shanye da kanta, domin yaji dadi, suna gamawa, sukayi wa inna sallama tace to Maigida a dawo lafiya



Ya amsa da ameen, suka fice, suna Zuwa bakin kofar gidan, taci uban tuntube da bakin kofar gidan, dasauri baba yace yi Ahankali Shalele



To babana muje





Kekensa yadauko yahau sannan itama tahau kan kariyar keken, yaja suka tafi, basu zame ko'inaba sai makarantar su, dalibai dayawa atsaye afilin makarantar wasu Kuma a zaune, Daga saman ginin makarantar Naga an rubuta Government day junior school kuje local government



Tana sauka sukayi sallama dashi tayi wajan sauran daliban, yana tsaye yana kallanta, tareda jiran yaga shigarta ciki sannan yajuya yatafi gida Kamar Yanda yasaba duk ranar Allah



Tana tafiya tana waigensa ta nayi masa bye bye, mutane da yawa dasuke wajan ba qaramin birgesu sukai ba, irin wannan soyaiya ta 'ya da uba



Saida yaga shigarta sannan yaja Kekensa yatafi gida, yana shiga gida ya ajiye Kekensa agefe, inna Marka tana masa barka da Zuwa, ya amsa yana tambayar ta, Marka Ina tsohon gatarin nan nawa?



Tsananin mamaki ya Kamata tace gatari Kuma Maigida? Mezakayi dashi kaida bame faskaren itace ba?



Marka banasan surutu Dan Allah, tashi daukomin shi



Batace uffan ba tatashi ta dauko masa tabashi



Karba yayi, sannan yayi hanyar kofar gida dashi, binsa tayi Abaya domin taga mezaiyi dashi



Yana Zuwa wajan yafara saran kofar gidan nasa da gatarin, duk wani tudu da gangare Saida ya sai tashi yabaje qasar wajan



Haba Maigida, yanzu fisabilillahi kofar gidan nan kalau da ita Amma haka kawai kasa gatari kadinga saran kofa Kamar Allah ya aikoka?



Dagowa yayi, yana goge Dan gumin daya Tara yace, Shalele nah ce tayi tuntube da wajan dazu, shine nake baje qasar wajan, saboda kada naje Garin shige da ficenta, tasake wani tuntuben (😳🙆🏻)



Yanzu Maigida saboda Allah akan wannan shine kake ta haqilo kaida gatari?



Wato Marka Naga alama bakisan Yanda Shalele take arainaba shiyasa kike wannan maganar, to dazu datayi wannan tuntuben jinsa nayi Har cikin Raina, abin baimin dadiba



Um to Allah yabada sa'ah Maigida, tajuya tayi cikin gida



Wani wajan yasake kaiwa duka da gatarin yana fadin ameen Marka, batare daya kalleta ba



** *** **



Su HANEEFA manya, wato de Har yanzu ke bazaki hutar da babanmu ba Ko? Kinsa bawan Allah kullum saiyazo daukar ki Bayan ya kawo Ki da kansa



Wata Daga cikin qawayen ne tace majidah ba HANEEFA zaki Ceba, Shalele zakice, Wai Shalele saikace wata yarinyar goye maishan mama



Cikin damuwa da kalaman nasu tace yau naji jaraba, babanku Ko babana, Shalele shi nakeso danhaka dashi zaku kirani, bawani Haneefa, haka kawai ga sunan da babana yake kirana, Shima yanajin dadin sunan ne shiyasa yake kirana dashi, ai yasan da haeefan



Wata Daga cikin su maisuna nasiba tace, to maji magani, yarinya Gara ma kidawo da ainahin sunanki, bawani Shalele ba, Tunda girma kike kina qara zama yanmata, inba hakaba samarin Garin nan wallahi Raina ki zasuyi

Saikace wata jaririya Wai Shalelen baba



Itama tace eh naji Shalele na nakeso, ai ni Har yanzu inde awajan babane, to a yarinya ta nake, nida zai maidani ciki ma saboda tsabar yarinta da bazan qiba



Sabira tace wanne irin yarinya kike magana Haneefa? Ga qirgen dangi nan akirjinki zaki dinga kawo wa kanki yarinta, to ai kuwa Ana kaiki gidan miji zama zakiyi daram yarinya



Kafin tayi magana Taji saukar Dan karamin duka abayanta, dasauri tajuya, tana ganin fuskar me dukan nata tace Kai Kai kai fadila sani miye Hakan?

Gani tayi duka qawayen nata Suna Daria, nasiba ce tace Rabu dasu Haneefa, Wai so take Taji kokin fara saka breziya shine ta wayance da dukanki Abaya, ashe ke bakisan wannan sarar tasuba



Da mamaki Shalele tace wacce irin brezia Kuma Ana zaune lafiya?



Still nasiban ce ta dubi wadda tayi dukan tace fadila to kinji de abinda Shalele tace, babu ita ba brezia yanzu, inajin sai anyi auren mijin nata zai aunasu da kansa, idan yaji adadin girmansu saiya siyo mata wadda zata mata









Shalele zata sake magana aka kada musu qararrawar shiga aji, danhaka Bata Cewa nasiba da fadila komai ba sai harara data bisu dashi, suka miqe Dukansu suka shiga aji



Suna zama malamai suka fara Raba musu questions paper, sannan aka basu umarnin farawa, daliban na kalla Dukansu bazasu wuce 14 to 15 ba



Suna gamawa kowa yafara futowa, kowa kagani yana dauke da Murmushi a fuskarsa

Kowa nagama futowa Aka fara photuna, maza da mata wannan yakira wannan ayi musu photo wannan ma yakira wannan

Suna murna Ayau sun gama junior



Sai can gab da la'asar suka fara watsewa, itama itada qawayenta suka futo, suna tafiya Ahankali, yayin da suke fira cikin nutsuwa,



Sunyi Nisa sosai akafa ta hango baba yana tunkaro su, cikin Murmushi tace to nide babana Yazo, sai anjimanku dalibai



Dukansu sukayi mata caaa kowa Yana tsokanarta, Daga me Cewa to Shalelen baba sai munkawo Miki ziyara, sai Mai Cewa to Haneefa sai anjima, Sabira cede ta Daga murya tace Yarinya ba sai anjima ba kihau keken nan de Ahankali wallahi kada kiyi wa angon ki asara, Dan me rabaki dashi sai Allah ehe mude ba ruwanmu



Gaba dayansu suka kwashe da Daria, itama murgudawa Sabira baki tayi, sannan tayi wajan babanta, ta Dane keken suka nufi gida, suna tafiya baba yace,Shalele nah ya jarabawar?





(wannan page din na farko zan tura shi akowanne group, duk group din dasuke so naci gaba da sambado musu, sai sumin magana 💁🏻💁🏻💁🏻💁🏻💁🏻)






Mrs Usman Ce✍🏻
💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download SHALELAN BABA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album