Join Our WhatsApp Group

RAYUWAR MACE Complete Hausa Novel Document by RAYUWAR MACE


RAYUWAR MACE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22307RAYUWAR MACE

Reading Time: 1 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Hafsat Rano ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 09032345899

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 117.88 kb

File Type: txt

Views: 978+

Download: 346+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [7/21, 10:52 PM] Mummyn Yara: *RAYUWAR MACE*
_Hafsat Rano_
Free Page (2)

***
A kofar dakin Umma ta tarar dashi, ta nuna masa falon da hannu sannan ta wuce falon Abban. Yana tsaye yana kai kawo a tsakiyar dakin tana shigowa ya bi ta da ido dan yasan abinda ya kawo ta.

"Alhaji.."

Da sauri ya dakatar da

"Maganar ba zata chanja komai ba, muyi mata addu'a kawai bamu san me Allah ya tsara ba."

"Amma dai hakkin mu ne mu nema mata miji na gari, wanda muka yarda da addininsa da nagartar sa, amma Adam fa? Ya cika wannan sharadin?"

Zama yayi a nutse bayan ya cire babbar rigar jikin sa da hula sannan yace

" Mu bar wa Allah komai, ya fimu sanin komai akai, ba zan taba iya hana Yaya Asabe abinda take so ba, ba kuma zan taba kin danta wai don munin halin sa, ni ma ban fi karfin Allah ya jarraba ni da irin sa ba."

" Yanzu shikenan muna ji muna gani saboda kawai muna so yar mu tayi aure za muyi mata zabin tumun dare!?"

" Idan da rabo sai kiga ta dalilin ta Allah ya shirye shi, sai tayi kokari ta sauya masa DABI'AR sa tunda mace tana da matukar tasiri a rayuwar namiji."

Wani abu ne yazo ya tokare wuyan Umman, bata tare da masu ganin cewa mace zata iya gyara wa namiji Hali bayan ta same shi da girman sa, kawai idan kaji an ce haka toh fa lallai an shirya zalintar macen. Tana tsaye ya zo zai fita daga falon, ya kalle ta yana gyara hular kansa sannan yace

" Karki nuna mata wani abu da zai sa taki auren, muyi mata addu'a kawai dan babu abinda zai sa a fasa sai dai idan Yaya Asaben da kanta tace sun fasa, amma muddin bata ce ba, toh babu makawa sai anyi."

Kasa tanka masa tayi har ya fice, ta zauna dabas a wajen tana jin da gaske an cuce ta, ta kuma tabbatar da biyu Hajiya Maman tayi dan ta nuna mata ta isa da Abban da ma duk wani abu da ya dangance shi.
Da k'yar ta mike daga wajen ta fito bayan ta jawo masa falon, ta isa dakin Asma'un ta tarar da ita tana sallar azahar, sai kawai ta wuce dakin ta domin ta gabatar da tata sallar.
Tana idarwa Asma'un na shigowa, bata ce komai ba ta hau gadon umman ta kwanta rigingine tayi shiru tana tuna abinda ya faru bayan taje wajen sa. Kadan ya rage be rungume ta ba da ta shigo, ya hau surutan da ta kasa gane komai akai, haka ya karaci babatunsa ya tafi bayan yace mata zai dawo da daddare.

"Umma wai me ya faru?"

"Aina da?"

"Ya Adam, ban gane ba wallahi. "

" Kinsan kowanne bawa da yadda Allah yake kaddaro masa rayuwar sa, sannan duk dan ta yayi ma iyayen sa biyayya toh fa ba zai taba tabewa ba, mahaifin ki ya yanke shawarar aura miki dan uwanki Adam... "

A yadda ta mike daga kwancen sai da ta bawa umman tausayi,

" Umma Adam kuma? "

Kai ta daga mata

" Innalillah wa inna ilaihi rajiun, umma wallahi tallahi bana son shi, bashi da hali me kyau wallahi Umma, wallahi Allah bana son shi dan Allah Abba yayi hakuri. "

Duk ta gigice ta rikice, hawayen da Umman take ta rikewa ne suka soma saukowa tayi saurin maida su tana karfafar kanta.

" Menene haka? Me kike haka? Ashe ba zaki iya yiwa mahaifin ki biyayya ba?"

" Umma Adam fa? Umma dan Allah kice yayi hakuri wallahi ba zan iya ba. "

Wani kallo umma ta watsa mata

" Ki nutsu ki saurare ni, kinsan waye mahaifin ku, kin kuma san wacece Hajiya Mama a wajen sa, kukan ki da magiyar ki ba zasu taba sauya masa abinda yayi niyya ba sai dai idan su suka ce sun fasa, dan haka ba ruwana wallahi, ba zan bari ki hadu da fushin mahaifin ki ba, kiyi masa biyayya ku rabu lafiya nima na rabu da nawa lafiya, kuma in sha Allah zaki ga ribar biyayya. "

Daga haka bata kuma cewa komai ba, ta fice ta bar ta a dakin tana jin yadda take kuka wiwi, wayar ta ta dauka ta kira babbar 'yarta hadiza ta sanar da ita komai sannan ta kira sauran yan uwan Asma'un da sukayi aure, kafin kace me sai gasu a gidan gaba dayan su, duk kansu kowa be ji dadin labarin ba, amma kuma sai Umma ta hana su fuskar da zasu kushe abun dan ta riga tasan halin Abban su sarai zai iya saba musu akan maganar, sannan tunda tasan babu fashi gwara kawai tayi kokarin ganin basu bawa Asma'un kofar da zata bijire wa mahaifin nasu ba.
Lallashi da ban baki suka dinga yi mata har suka samu ta dan nutsu amma bata bar kuka ba. A haka Abban da yan mazan suka dawo suka tarar dasu, Abban ya danyi fadan dalilin zuwan su haka sai suka ce ai zuwa sukayi su gaishe su, ya ji su ne kawai amma ya riga ya san umma ce ta kira su akan maganar.
Bayan sallar magriba Yaya hadiza ta samu Abban da maganar, ya nuna mata babu fashi su dai kawai su tayata da addu'a, haka ta baro dakin jikin ta a sanyaye bayan ta roke shi ya barta su tafi da Asma'un ya amince amma iya sati daya kawai dan sati uku ya saka bikin tunda babu wani shiri da za'a yi dan kowanne bangare a shirye suke dama.
Mijinta ne yazo ya dauke su wajen tara, a hanya take bashi labarin abinda ya faru, ya dan juyo yana sake bawa Asma'un baki yana tsokanar ta, ta dan yi murmushi kawai amma ita kadai ta san yadda take ji a ranta.

***Washegari bayan an makaranta sun tafi umma ta shirya Abbati ya kaita chan Mandawari gidan su ta samu Hajiyar su da maganar auren Asma'un da lokacin da Abban ya saka, duk basu ji dadin hukuncin Abban ba, da kuma rashin bawa Asma'un dama ta fadi ra'ayin ta dan kawai ana ganin kamar ko an barta ma ba wani ne zaizo neman auren nata ba.

"Toh yanzu dai ya riga ya gama yanke hukunci, namu kawai shine mu bi ta da addu'a, Allah ya basu zaman lafiya ya kade fitina."

Hajiyan tace bayan sun gama magana da Umman.

"Amin, ni na rasa ta ina zan fara ba, sai a aika su miko su sanar da su umman Asiya da su Aunty Falila da gidajen su kawo muntari."

"Eh yana shigowa zan aika shi, sati uku kamar yau ne ai, duk sai a sanar da dangi, Allah ya basu zaman lafiya."

"Amin." Tace a sanyaye.

***Bangaren gidan Hajiya Mama shiri take na ban mamaki, tuni zancen ya karade dangin su bangaren Abban da kuma bangaren Baban su Adam din, mutane da yawa suna tausayawa Asma'un saboda dai sam babu hali na nagarta da zai saka ka dauki yar ka, ka bawa Adam din, ciki kuwa har da yan uwa makusantan su Abban dan wani kawun su sai da yayi wa Abban magana kasancewar kowa ya riga ya san nutsuwa da kamala irin ta Asma'un dan kaf yan uwanta babu kamarta, duk da su ma basu da matsala amma kuma ita din daban ce, magana da koman ta a nutse take yin sa, bata da rawar kan yan mata dan ba zaka taba tunanin ta je jami'a ba ma, bata dauki duniyar da zafi ba haka kuma bata da son kyale kyalen duniya. Haka ya saka mutane suke ganin kamar akwai zalunci a dauke ta a hada ta da Adam wanda ake tunani hatta giya yana sha bayan mugun halin sa na neman mata da yayi shura akai, amma yadda Abban yayi biris da duk wannan ya saka kowa ya shafa ma kansa lafiya aka shiga bin su da addu'ar fatan alkhairi.

Zuwan Adam din uku tare da zugar abokai baya samun ta karshe dai ranar da yazo ya tarar da Abban nan yake gayawa Abba ai yazo baya samun ta, nan fa Abban ya shiga dakin Umma yayi ta mata fad'a sannan ya dauki waya ya kira Yaya hadizan yace ya fasa sati dayan gobe gobe ta dawo gida. Jiki a sanyaye ta amsa masa da toh, bayan ya kashe sai kuma yaga kamar ya zafafa da yawa, sai ya sake kiranta yace ta kyale ta zuwa satin amma zatayi bako gashi nan zaizo yanzo. Nan ma dai toh din tace ya kashe ya koma ya samu Adam din ya yi masa kwantancen gidan Yaya Hadizan sannan ya bashi number wayar Asma'un da ta Yaya Hadizan yace idan yaje ya kira. Bakin sa tamkar gonar auduga ya karba suka dauki hanyar gidan Yaya Hadizan baka jin komai a motar sa ife ifen su irin ma gogaggun yan duniya, burin sa kawai ya nuna musu kalar matar da zai aura ya san ba karamin taya shi farin ciki zasuyi ba, hutu kam zai huta a wajen sosai, yadda yake ji ma kamar sati ukun yayi masa mugun yawa amma haka zai hakura ya lallaba ya cigaba da maneji da su Fido kafin ranar da zai gwangwaje.

Gidan bashi da wahala suna zuwa suka gane, ya dauko wayar sa zai yi kira sai kuma ya fasa ya fito da kafar sa ya karasa gate din gidan ya kwankwasa da dan karfi saboda karar Gen, be jima yana bugun ba mijin Ya Hadizan yazo ya bud'e masa, ya bashi hannu suka gaisa sannan yace ya shigo ciki

"Owk tare muke da guys suna mota bari nayi musu magana."

"Owk." Yace ya wuce ciki ya bar musu kofar a bude, ya samu falon ba kowa an gama jera ruwa da lemo akan dan centre table din, ya dauki remote ya rage volume din tv daidai lokacin da suke shigowa, su hudu ne dukkan su sanye da kananan kaya daya ma daga ciki wandon sa da kad'an yafi guiwar sa, askin kansu kuwa kai kace gobara akayi a wani gefen kan nasu babu kyaun gani, hannu ya basu suka gaisa sannan ya wuce ciki cike da al'ajabin dalilin da zai sa Abba amincewa bayan ya san waye Abban da nagartar sa.
Da k'yar da ban baki Ya Hadiza ta sakata fita dan bata son fushin Abba akanta zai iya hadasu daga ita har Asma'un yayi musu tatas. Hijabi ne burmeme a jikinta har kasa, ta dauko facemasks ta dora akan fuskar ta sannan ta tura kofar falon kanta a k'asa ta shiga. Wata iriyar kunya ce ta kama Adam din da ya ganta da shigar, shi da yaso suga kalar matar da zai aura amma shine zata je ta burma uban hijabi kamar wadda zata zaman makoki.
Dariyar shakiyanci suka fara yi suna kallon sa, ya hade rai sosai yaki kallon ta, a k'asa chan ta rakube ta gaishe su suka amsa cikin dariya dan su basu ga abinda yake ta musu kozozoto akai ba.

"Our wife kina lafiya?"

Daya daga ciki yace yana kunshe dariyar sa.

"Lafiya lou."

Ta amsa a takaice kanta still a k'asa ba zata iya cewa ga adadin su bama balle kamar su, uban gayyar kawai ta gani sanda ta shigo taga ya wani diririce kamar wanda yayi karya aka gano shi, bata kuma kallon sa ba ta zauna. Tana jin su suna ta shakiyan ci suna tsokanarshi amma ko uffan be ce musu ba, sai da suka gama suka fita, ya taso yazo daidai kanta, ya saka hannu ya fuzge facemask din, ta kalle shi da sauri

"Wannan wane irin wulakanci ne na kawo guys dina su ga matar da zan aura shine zaki sako wannan buhun sannan ki wani toshe fuskar ki dan tsabar iskanci."

"Kamar ya? Me yasa zasu ganni ko su din muharramaina ne?"

"Shit! A 21th century dama akwai mata villagers irin ki? Ke baki san civilization ba? Ko baki ga alamar mijin da zaki aura wayayye bane?"

"Ban san duk wannan ba, abu daya na sani shine abinda addinin musulunci ya koyar dani."

Ta murguda masa baki tana jan facemask din zata mayar ya fuzge da karfi sannan ya buge mata baki

"Karki yarda kice zaki min rashin kunya wallahi, dan zan taimaka miki na aure ki, naga ma ai neman kai ake dake na taimaka nace zan aura, so watch your mouth wallahi, kuma na sake zuwa kika zumbulo min irin wannan Hijab din sai na cire shi ta karfi wallahi. Nonsense!"

Ya juya da sauri ya bar falon har da buga kofa, kasa ko da kwakkwaran motsi tayi, bakin ta da ya buge na mata zafi sosai, sai kuma maganganun sa da suka yi mata mugun ciwo, da gaske taimaka mata yayi? Kuma neman kai ake da ita shine ya tausaya mata zai aure ta. Wani kuka ne yazo mata, ta gwammace ta mutu ba aure akan ta auri mutum irin Adam, jinkirin aure ai ba shine zai saka mutum yayi wrong choice ba, gwara ma ace ka aura baka sani ba, amma wannan kowa ya san halin sa.
Ta jima a wajen tana kuka sosai, kafin ta tashi da k'yar bayan ta goge hawayen ta shiga ciki.


RAYUWAR MACE COMMENT GROUP LINK. Meson comment group sai ya shiga link din nan

https://chat.whatsapp.com/EcH31iWkbGnD9DWC8SsuLR


_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_πŸ₯°

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_πŸ₯°

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANANπŸ‘‡πŸ‘‡_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biyaπŸ‘‡πŸΌ

*_09032345899_*

*KATIN MTN*πŸ‘‡πŸ‘‡

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
[7/21, 10:52 PM] Mummyn Yara: *RAYUWAR MACE*
_Hafsat Rano_
Free Page (1)

*******
...


Read / Download RAYUWAR MACE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album