Join Our WhatsApp Group

BABBAR CUTA Complete Hausa Novel Document by BABBAR CUTA


BABBAR CUTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 20360



BABBAR CUTA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 21, Oct 2023

Author: Yar Gatan Huda ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 119.76 kb

File Type: txt

Views: 549+

Download: 147+

Last download: 15 hours ago

Description/Story: [1:21am, 6/29/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)


Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


*Godiya*
Muna godiya ga sarki Allah da yanuna mana wucewar wata Axumi mai girma lpy ,yanuna mna watan sallah lpy ,Allah ubangiji yasa muna da raban ganin wasu shekarun masu Amfani ,ya jikan wayanda muka rasa ,ya rahamshesu ya gafarta musu ,Ameen ,


*jinjina*

Jinjina ga mahaifanmu masu kaunarmu ,Allah ubangiji ya saka muku da alkairi ,ya biya muku bukatunku ,irin tarbiyar da kuka bamu yasa muma mubama yayanmu ,Allah ya kara muku lpy da nisan kwana mai amfani Allahuma Ameen,


*Gaisuwa*

Muna Mika Gaisuwa ga dukkanin makusantanmu da kuma masoyanmu na birni da kauye ,muna kuma yimusu Barka da sallah. Allah ya nuna mna badin badada ,Ameen ya Allah.


*sadaukarwa*
mun sadaukar da wannan littafi ga ,yan uwanmu ,masoyanmu ,kawayenmu kai dukkanin makusantan *EXCLUSIVE WRITES FORUM*mun sadaukar da wannan littafi gareshi ,


*sharhi*

Wannan littafi munyishi ne dan mu nishadantar ,sbda muma mun nishadantu da ganin watan sallah shiyasa muka kawo muku shi a goron sallah ,kuma muna fatan ya fadakar da mutane ,adauki Abu mai kyau na ciki a yada mara kyau wannan shine amfanin karatun novel ,Allah kasa mu dace duniya da lahira ,kai mana kyakkyawan karshe Ameen ya Rabbi


Allah ubangiji kai mana jagora ka tallafa mana a dukkanin lamuranmu ,tare da daukakin al'ummar musulmi ,
Yadda muka fara kawo muku wannan littafi lfy ,yasa mu kare muku shi lfy Ameen ,


da sunan Allah mai rahama mai jinkai,

📝📝📝📝📝📝
*1-5*

malam sunusi babban malami ne a unguwar kawo dake kaduna ,matarsa daya ce rak mai suna sadiya ,Suna da yaya 4 ,2 maxa ,2 mata,

tahir ne babbansu sai maryam sannan Hashim sai autarsu murja ,
duk cikin yayannan nasu sunfi kaunar Hashim ,daga mahaifin nasu har mahaifiyar tasu yashiga ransu sosai ,


Hashim kyakkyawane sosai gashi nitsatstse baida hayaniya ko kadan ,ga rikon addini uwa uba ga gaskiya komai xaiyi yakan kokari yaga yayi gaskiya ,

A yanxu tahir yai aure yana da yaya biyu ,maryam ma nada yara 3,Hashim kwa na ganiyar samar takarsa ,murja ma an dan tasa an xama yan mata,


Komai ya tashi saidai kaji sunce Hashim ,koda shawara ce xakaji ance Hashim , kawa shine babba komai malam ya samu Hashim hakama mahaifiyarsu ,

Hakan na ciwa yan uwanshi rai,sbda irin fifikon da suke nunawa akan Hashim ,Wanda Su a ganinsu ba komai bane dan sunfi nuna kaunarsu ga Hashim ,soyayyar sa ce Allah ya Dora musu ,


Hakan ya jahoma Hashim bakin jini ga yan uwanshi har suka fara hade masa kai ,suna neman abinda xasu raunana soyayyarshi a xuciyar mahaifansa ,

(Tofah Wai ciki dayama kenan,Allah kasa mu dace)


Hashim yana da budurwa hannatu ,yana Santa sosai,itama tana sanshi ,Su malam ma duk sun san da xaman soyayyarsu ,



...........

Yau Hashim bai shigo gida da wuri ba kamar Yadda ya Saba ,yayi dare sosai gurin hannatu sun shagala da soyayya ,

Yana shiga dakinshi ruwa kawai ya watsa dan ya warware gajiya ,ya kwanta sai bayan da ya kwanta ya Tina bai kulle dakinshi ba ,Amma kyuiya ta hanashi mikewa ya bude yai juyi yai kwanciyarsa,



**
Ana kiran assalatu malam ya fito da yar cocilan inshi a hannu ,dama dakinshi na facing in na Hashim ,

Wa xai gani ya fito ,hannatu ce ta fito daga dakin Hashim sai barin jiki take tana dingisa kafa ,



Hasketa malam yai yana kallanta ya kasa motsi ,inna ma da ta fito yin auwala ta ganewa idonta abinda malam ya gani ,ta daskare a gurin da take ta kasa motsi ,


Yayin da hannatu tai sauri ta fice daga gidan....








E.w.f
[3:33pm, 7/1/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*



*6-10*

daki malam ya koma yai dabas ,abin duniya ya isheshi ,yarasa wani irin tunani xaiyima ,komai ya jagule mishi ,


Inna ma dakin ta koma xuciyarta ta shiga cikin kunci ,wannan wata irin lalacewa ce ka kawo yarinya har cikin gidan da iyayanka suke ,dan da suka fi kauna yanxu shi xai musu haka ,kawai saiji tai tana share kwalla ,

Ganin da sukai lokacin sallah na neman shigewa yasa Su fitowa suka daura auwala ,A lokacin Hashim shikuma ya gama daura auwalar ya shige daki , dan ya makara xuwa masallaci ,



gari na wayewa byan Hashim ya gama kimtsawa kamar Yadda ya Saba a kullum ,sai yashiga dakin malam dan yagaidashi ,Amma yanayin da yasameshi Sam yaki kallan inda yake guiwa a sage ya tashi yabar dakin yashiga dakin inna ,itama Hakan take sam taki kallanshi sai Hawaye da ke diga a idonta ,Hankalin Hashim in yai dubu ya tashi fadi yake me yasamu iyayan nashi ,



Shida murja suka tusa inna a gaba suna tambayarta abinda ya faru ,Amma inna tai musu shiru taki magana ,suka tafi dakin malam shima sukai saukai ta tafas baice dasu ba ,

Waya Hashim ya dauka ya kira tahir ya sanar dashi abinda ke faruwa ,yace yaxo ko shi sa sanar dashi abinda ke faruwa ,budar bakinsa sai ca yai "kai basu sanar dakaiba bare ni kuma ,kawai ya kashe wayarshi ,


saiga sallamar maryam ,hankali tashe itama take tambayarsu abinda ke faruwa ,sai a lokacin inna tai magana tacewa murja ta fita daga dakin ,


Byan fitarta inna ta kalli maryam tace "Wai wannan yaron (ta nuna Hashim ) yarasa irin toxarcin da xai mana da rashin mutumci sai yadaukko yarinya ya kawota gidannan ta kwana ,

Budar bakin maryam sai ca tai Alhmdllh gwara da Allah ya nuna muku da idanuwanku ,wannan abinda ya jima Hashim yana aikatawa ne


daga inna har Hashim suman xaune sukai ,suna kallan maryam ,

inna ce tai karfin halin cewar shin kin gane wanda nake magana akai kuwa ?

tace "na gane mna Hashim ,bari na kira miki murja Ki tabbatar ,ta kwalowa murja kira ,ta amsa da saurinta ta tawo har tana tuntube ,

Maryam tace "sanar da inna abinda Hashim keyi a cikin gidannan ,

Murja tace "na jima ina ganinshi yana shigowa da yan mata ,amma yafi shigowa da hannatu ,kuma hannatun tasha gayamun abinda ke wakana tsakaninta da yaya hashim din ,nikuma sai na samu yaya maryam na gaya mata sai ca tai nai shiru da bakina kar na gaya muku ,na bari sai sanda kuka gani da idonku sbda ko na gaya muku bai xama lallai ku yarda ba "


salati inna ta saka ta fashe da kuka ,malam dake tsaye a bakin koda yana jin abinda murja ke cewa shima salatin yake abin duniya yabi ya isheshi ,


Hashim kwa gaba daya ya jike da gumi ,ya daskare a gurin da yake , sai hawaye dake sharara a idonshi kamar fanfo ,kanshi yana juwa jin abin yake kamar a mafarki ,


A haka Tahir yaxo gidan ya taddasu shima ,mai makon ya kashe wutar sai yakara kunnata ,hadda cewa magana ta fara fitowa waje ,


Malam yace "yanxu Hashim soyayyar da muke maka da abinda xaka saka mna daita kenan ,baxan ma baki ba sbda Allah yafi jarabtar bawa da abinda yafi so ,saidai na nema maka shirya gurin ubangiji da yafiya ,Amma ka tattara kayanka ka tafi can kauye dan xamnka a gabana xaisa mun ciwon xuciya ,xai kuma jahomun xagi a gurin mutane ,


Kuka Hashim yasaka sosai ,yana wlh shi bai aikata abinda ake xarginsa dashi ba ,inna tace yan uwanka ciki daya xasu maka sharrine ka aikata shiyasa suka fada ,dan haka hukuncin da malam ya yanke shine dai dai ,



Kuka sosai Hashim keyi duniyar ta masa xafi ,yan uwansa xir sune sukaimai wannan katoton sharrin ,tare da taimakon masoyiyarshi Wacce ya dauki kaunarsa da amanarsa ya bata ,kuka yake sosai ,

Haka yadinga ma iyayan nashi rantsuwa ,Amma Sam ba wanda ya saurareshi ,da rarrfe ya fita yashiga dakinshi ya harhada abubuwanshi ya fito ya koma dakin yana neman yafiyar iyayannashi ,


Malam yace ya yafe masa ,Amma yaje can kauyen hankalinshi xaifi kwanciya ,Akwai yan uwana a can da xasu kula Dakai ,

Haka Hashim ya juya ya fita yana xubda kwalla mai xafi ,


Yayin da yan uwannashi tausayinsa ya kamasu ,suna kaunarshi ,basu so irin hukuncun nan malam ya dauka ba ,Su sunfiso kawai soyayyar da iyayannasu suke masa ta raunana .........









E.W.F
[10:58pm, 7/9/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*


*11-16*

Maimakon Hashim ya nufi kauyansu da malam yace ,sai ya nufi Kano ,sbd gaba daya duniyar taimasa xafi ,in yaje canma baisan me xaice musu ba ,duk da bai aikata abinda ake xarginshi dashi ba Amma kunyar mahaifan nasa yake ,


Acan Kanon Hashim yake samun wani aboki haris ,shi haris Mahaifansa masu haline ,

Shine yake daukan hashim yakaishi gidansu ,

Hashim ya samu karbuwa sosai a gidan Su haris ,har yafara bin mahaifin haris kasuwa ,sosai Hashim na samun kulawa a gun mutanen gidan ,Sam babu hantara bare kyara ,


Tasu taxo daya da harisa kanwar haris , dake karatun business a jami'ar poly technic ,

shakuwar haris da haris tai yawa har suka fada soyayya ,suna son junansu sosai ,mahaifinsu harisah ba kyamata yabawa hashim harisah ,sbda Yadda da yayi da halayen Hashim,dadin dadawa kuma tausayiin Hashim din da yacika masa xuciya ,


domin Hashim ca masa yai mahaifansa sun rasu ,kuma baisan kowa cikin danginsu ba ,bcs baisan aje garinsu aji maganar sharrin da aka masa ,



Ansha shagalin biki sosai ,na haris da harisah ,mahaifin Su harisah ya dankarawa hashim tsaleliyar mota ,gami da dankareran gidah mai kyan gaske ,


A ciki Su Hashim suka tare ,suna nuna kulawa ga junansu sosai ,saidai harisah Akwai xafin kishi ,ita a ra'ayinta bata kaunar kishiya sam🙅🏾,ita da taga ranar da xa'a mata kishiya ,gwara ranar mutuwarta tafi mata alkairi ,

shaukin soyayya ya debi Hashim yaiwa harisah alkawarin babu kishiya har karshen rayuwarsu ,harisah dadi yaisheta ,ta sakarma Hashim gaba daya ragamar rayuwarta ,suna tattalin junansu sosai ,


Hmmmmm Tofah 🤔Anya kuna ganin hashim xai cika al'kawarinnan kuwa ,ya manta Allah ne ke tsarawa bawansa rayuwa..............













E.W.F


haka rayuwa tai ta tafiyar musu cikin kwanciyar hankali ,watansu 3da aure mahaifinta ya biya musu kujerar makah,sukaje suka sauke faralli ,byan dawowarsu harisah tashiga laulayin ciki ,

Hashim yakan leka gidansu yagai da mahaifansa ya tafar musu da aabinda ba'a rasa ba ,na neman albarka har xuwa lokacin,


duk da har lokacin dai gaskiya batai halinta ba ,Amma dai yana dan samun sakin fuska gun mahaifan nasa


*****
Khadijah kyakkyawar yarinyace ,da ta tsinci kanta A rayuwa a cikin gidan marayu ,


ta samu labari gurin wanda ya amsheta ,cewar mahaifiyarta makauniya ce ,ta kasance tanai mata jagora ,mota ce ke bige mahaifiyarta ,ta sanadiyar haka take rasuwa ,

Kuma basu da kowa a cikin garin ,dalilin da yasa aka kawo Khadijah cikin gidan marayu kenan ,


Khadijah tayi rayuwa mai kyau a gidan marayu ,sakamakon Allah ya hada jininta da dukkanin masu kula daita ,duk mutumin da yai toxali da Khadijah sai yaji kaunarta ,haka take tun tana yarinya ,Hakan a jininta yake ,



Ta samu kyakkyawar tarbiya a gun masu kula daita ,duk inda nutsuwa take Khadijah tana daita ,A yanxu Khadijah shekarunta basu huce 17 ba ,da ka kalleta xakaga tsantsar yarinta a fuskarta ,



***
Tafe take ,ta kusa kaiwa gidannasu ,sanye take da doguwar Riga ta material perpul mai adon fari ,ta sanya farin hijabi ,fuskarta sai Annuri take bayarwa,

Khadijah kenan ,hannunta rike yake da bakar ledar ,da uwah (daya daga cikin marikayenta knn) ta Aiketa ta Anso mata ita a gidan da take xaune ,



Hashim dawowarshi daga kasuwa kenan ,yana kan hanyar xuwa gida ,yai toxali da kyakkyawar fuskar Khadijah ,tana sakin murmushi kawa shi takema ,


A lokaci 1 yaji xuciyanshi ta buga yaja burkin da bai shiri ba ,binta yake da kallo kawa wani dolo har tashige cikin gidan marayu............











E.W.F
[12:53am, 7/10/2017] YAR GATAN HUDAH: ♠♣🖤♣♠♣
*BABBAR CUTA*
♠♣🖤♣♠♣

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM♻

( *GORON SALLAH*)



Writing by ;♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*




~dedicated this page to all lovers EXCLUSIVE WRITERS FORUM muna kaunarku a koina kuke ,don mu fadakar daku muke mu nushadantar ,fatanmu Allah yasa Kui amfani da abu mai kyau na ciki ,EXCLUSIVE Proud to all LOVERS inta aduk inda kuke ,ELEYMS😘~




*17-20*


Byan komawar Hashim gida ,Khadijah Sam ta hanashi sukuni a xuciya ,har Hakan yasa harisah cikin damuwa ,sbda ganin haka Hashim yake rage wani abun ,dan kar tai xargin wani abin ,.

Ammafa xuciyar nan tasa ba dadi,kaunar Khadijah ta ma'maye mishi xuciya ,tunaninshi shine ,me yakaita gidan marayu ,

A Yadda hashim yake jin kaunar Khadijah a xuciyarshi ,xai iya karya alkawarin ko waye,



Kwana 3 tsakanin haduwar Hashim da Khadijah ,Hashim yashiga bincike akan Khadijah ,har saida yaji labarinta ,A take soyayyarta da tausayinta ya kara ma'maye mishi xuciya ,
ya nemi ixinin neman auranta ,aka bashi dama ,


****
soyayya sosai ta kullu tsakanin Hashim da Khadijah ,suna matukar kaunar junansu ,Hashim ji yake kamar ko dayaushe kara mai kaunar Khadijah ake ,hkan a jininta yake......



****
Kaduna Hashim yake nufa bai taba xuwa da motarshi ba sai a ranar ,ya cika motarshi fam da kayan arxiki,


Nan yaje ya tadda yayyanshi sun tusa mahaifansu ,suna neman yafiya kan abinda sukai masa ,domin gaskiya tayi halinta ,hannatu taxo ta fasa kwai ,da xuciyarta ta hanata sakat,


Malam da inna girgida kai kawai suke ,domin abin ya girmama ,dan uwanka ciki daya kai masa wannan makeken sharrin ,yanxu Banda Allah ya taimakesu Hashim bai xuciya dasu ba ,ya daina waiwayarsu ,da ina xasu kai hakkinshi ,



Shigowarshi gidan malam ya tashi yaje ya rungumeshi ,yana shafa kansa ,yana shimasa albarka ,yana furta ka yafemu Hashim ,mun dau hakkinka ,


Hawayene ya sirarowa hashim ,na tsabar farin cikin xuwan ranar da yadade yana tsimayinta ,

Yace "naji dadin xuwan wannan rana ,malam na yafe muku dama can ban rikeku a raiba "


byan lafawar komai ,yan uwan Hashim suka nemi yafiyarshi ,sun gane kuskurannsu ,dama can HASSADA ce ke cinsu ,Kuma sun gane HASSADA BABBAR CUTA ce dake tafi da dukkan Aikin al'kairi ,kuma take damun dan Adam a xuci ,kuma warkewarta sai kayi da gaske ,
BABBAR CUTA CE dake cin dan Adam sannu a sannu ,Yayin da Allah xai ta daga wanda kakema hassadar ,kaga mai gari ya waya ,


suma kansu mahaifan nasa ,sun gane kuskurannsu ,wato fifita soyayyar Hashim da sukai ta fito fili sosai ,Su a tunaninsu Ai dukkaninsu yayansu ne ,babu komai in sun fifita kaunarshi ,bacin ba haka abin yake ba ,ita HASSADAH *BABBAR CUTA*ce ba ruwanta da dangar takarka da mutum , baka sanin sanda xata darsu a xuciyarka yayin da ta fara cin mutum a xuci ,sai yayi da gaske kafin yaiya yaki daita ,

Shiyasa iyaye a lura sosai ,Asan yadda xa'a nunawa ya"ya soyayya ,banda fifiko ,dan kuna ganin dukansu ku kuka haifa ,
Maganin kar ayi kar a soma ,domin baxa ku so rabuwar kan yayanku...


Read / Download BABBAR CUTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album