Join Our WhatsApp Group

ZUMUNTA KO MUGUNTA Complete Hausa Novel Document by ZUMUNTA KO MUGUNTA


ZUMUNTA KO MUGUNTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 29361



ZUMUNTA KO MUGUNTA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 25, Aug 2023

Author: Fatima Zara Alhassan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08144066758

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 148.46 kb

File Type: txt

Views: 1139+

Download: 300+

Last download: 2 days ago

Description/Story: ```MARUBUCIYAR...✍️
Bayan Wuya
Ashe ba so ba ne
Zumunta ko Mugunta📚
       Writting-by Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!!
     Kagaggen labari  ne. Ban yadda wani ko wata, su juya mi ni littafi, ba ta re da izini na ba!! Sabo da haka a kiyaye👂!!!
JINJINA
Ina jinjina ga mabiya littafai na, nagode sosai Allah ya barmu ta re🥰💛💙
SADAUKARWA
ga yan' uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma qara hada kanmu, mu yi zumunci🤝❤️
     MY FANS WANNAN SALON NA DABAN NE. 
KAR KU BA RI ABAR KU A BAYA🤪
        Free pages
SHAFI NA 1
        BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Gudu ta ke yi sosai acikin dajii. kafafunta duk sun farfashe, ya yin da kafarta ta hagu jini ke zuba. Da alama wani kwaro ne ya cije ta awajen. kayan jikinta duk sun yayyage, kan ta ba bu dankwali. kallo daya za ka yi wa kan ta, kasan cewa ya yi watanni sabo da daddagewar da kitson ya yi, ba bu kyan gani. Alamu sun nu na cewa ita kan ta yarinyar ba ta san ina za ta je ba.A daidai wurin wata katuwar itaciyar kuka ta fadi, sabo da juuwar da ta dibeta . Nan da nan guguwa ta tashi a wurin ta lullube yarinyar. Bayan dakika biyar guguwar ta laafa.
Tun shigowar ta cikin dajin ya ke kallonta, ta re da mamakin wannan al'ajabi! Tun zaman sa a jejin bai taba ganin wani mahaluki wai shi bil'adama ya shigo jejin ba, sai yau da Allah ya hada shi da wannan yarinya.  Duk gudun da ta ke yi akan idonsa, har kawo yanzu da ta fadi a gabansa.
Ba din da ya yi saurin ta re ta ba,

Allah kadai ya san raunin da za ta ji, idan ta fadi a kasa. Tsura ma ta ido ya yi yana kallonta, dududu ba za ta wuce shekaru shaa shida ba(16 years) wadda ba ta wuce renon iyaye ba, shi ne aka samu wa su  azzalummai su ka gunguntar da rayuwar ta.  Tafaa hannuwan sa ya yi, sai wurin ya koma wani babban falo ta re da kayan alatu na rayuwa. Fadin haduwar sa bata lokaci ne . Tafaa hannuwan sa ya yi akaro na biyu, ta ke duk rauni kan jikinta su ka bace, ta re da canza ma ta kayan jikinta. . Masha Allah, yarinya ce kyakkayawa , alkalami na ba zai iya bai ya na mu ku kyanta ba. sai dai mai karatu ya kiyasta...
Abun tambaya anan shi ne, wanene wannan mutumin? kuma yarinyar daga ina ta fito, san nan me ya faru da ita?
A tunanin ku, wane irin firgici yarinyar za ta shiga, idan ta farka ta ga kan ta a wannan wuri kuma ta re da wannan mutumin?
kar ku damu, ni Fatima Zara Alhassan ashirye na ke tsab domin  kawo mu ku wadan nan amsoshin.
DOMIN GUDUnMUWA KO SHAWARWARI PLS
      08144066758
YAR MUTAN
       ARGUNGU ✍️📚
ya ku ka ji wannan salon,
Ina fa tar salon ya kayatar da ku?
Comments
  Share```








```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺📖?
MARUBUCIYAR...✍️
Bayan Wuya
Ashe ba so ba ne
Zumunta ko Mugunta📚
       Writting-by Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!
     Kagaggen labari  ne. Ban yadda wani ko wata, su juya mi ni littafi, ba ta re da izini na ba!! Sabo da haka a kiyaye👂!!!
JINJINA
  Ina jinjina ga mabiya littafai na, nagode sosai Allah ya barmu ta re🥰💛💙
SADAUKARWA
ga yan' uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma qara hada kanmu, mu yi zumunci🤝❤️
     MY FANS WANNAN SALON NA DABAN NE.  KAR KU BA RI ABAR KU A BAYA🤪
        Free pages
SHAFI NA 2
        BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM
A hankali ya zauna ku sa da ita...
duk da ya san abun da zai yi haramun ne, amma hakan bai ha na shi aikatawa ba. Sabo da ya ga har yanzu ba ta sa ke ba. Hannun sa ya daura akan na ta, ta re da yi ma ta murmushi, nan ta ke jikin ta ya fara rawa, ta re da janye hannun ta, ta na balla mishi harara,cikin tsiwa ta fara yi mishi magana...waye kai? kuma ina ne nan? Meyasa ka kawo ni nan wurin? Miye manufarka nayin hakan?!!!
Tsura ma ta idanuwan sa ya yi, sai da gaban ta ya fadi. Har wani mai ta ke ga ni acikin su, kuma ga dan banzan kwarjini, duk iskancin mutum sai ya saurara idan ya na gaban shi. Murmushi ya yi ganin ta natsu sosai, ANEESA ABDUL-AZIZ ABUBAKAR MAI NOMA. cikin ta shin hankali ta ce, ya aka yi kasan sunana ta re da fashewa da kuka mai tsanani ta na cewa...dan Allah nima ka kasheni kamar yadda ku ka kashe Iyaye na, ko kun barni da raina wallahi rayuwar ba za ta yi min dadi ba!! na rokeka da ka kasheni nima da Allah...!! Sai yanzu duk abubuwan da su ka faru ke dawo ma ta daya bayan daya. Kuma tabbas ta ga mutum biyu daga cikin wadanda su ka kashe ma ta Ummanta ta re da Bappan ta.  "Mamana ki gudu kar su ka ma ki, ba bu imani acikin zuciyoyin su, dan Allah ki kula da kanki, ba kowane za ki yadda da shi ba, kowa kokari ya ke yaga ya ya zai cuce ka, amma kisani ba duka aka zama daya ba, amma dai ki kula da rayuwar ki, kamar yadda akwai mugayen mutane haka akwai nagari acikin ta, har ga Allah na so ace kin yi Aure kafin wannan kaddarar ta zo ma na, sabo da ki samu majingina a ta re da ke, amma bakomai duk abun da ubangiji ya tsara ma na daidai ne, Aneesa ina son kinsan cewa, a wannan duniyar naka shike cutar da kai, inaji a jikina za ki yi tsawon rai, idan har hakan ta kasance ina son ki samomin amsar wannan tambayar "ZUMUNTA KO MUGUNTA"??  A'a Bappa kar kuyi min haka please wlh idan babu ku acikin rayuwa ta aikin banza ne, ya ku ke son inyi da raina!!...Umma ba ki ce komai ba? Umm...umma...umma...Bappa.... dan Allah ku tashi mu yi rayuwar mu cikin farin ciki, kuka ta ke yi sosai ta na jijjiga gawarsu...halbin da akayi ma ta a kafar hagu shi ya dawo da ita haiyacin ta, bishibishi ta ke ganin fuskokin su, ka fin ta sume anan wurin. Tabbas ta tuna komai, amma abun tambaya anan, waye wannan? 
Tun dazu ya ke kallonta ita kuma ta lula duniyar tunani. Abun da ba ta sa ni ba shine, maganar zuuci ta fito waje, na cewa WAYE WANNAN?   KI na son ki san wanene ni? ya katse ma ta tunanin da fadar hakan.
juyowa ta yi ta re da zuba ma sa idanuwan ta, alamun kai na ke saurare...ya gane nufin ta shiyasa ya ci gaba da cewa...
DAN ALLAH KU FADAMIN GSKY, KU NA JINDADIN LABARIN KO KUMA A CANZA WANI?
DOMIN GUDUMUWA KO SHAWARWARI PLS
08144066758```
YAR MUTAN
       ARGUNGU ✍️📚








```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺📖?
MARUBUCIYAR...✍️
Bayan Wuya
Ashe ba so ba ne
Zumunta ko Mugunta📚
       Writting-by Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!!
     Kagaggen labari  ne. Ban yadda wani ko wata, su juya mi ni littafi, ba ta re da izini na ba!! Sabo da haka a kiyaye👂!!!
JINJINA
  Ina jinjina ga mabiya littafai na, nagode sosai Allah ya barmu ta re🥰💛💙
SADAUKARWA
ga yan' uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma qara hada kanmu, mu yi zumunci🤝❤️
     MY FANS WANNAN SALON NA DABAN NE.  KAR KU BA RI ABAR KU A BAYA🤪
        Free pages
SHAFI NA 3
        BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM
Ya gane nufin ta shiyasa ya ci gaba da cewa...
Sunana FU'UD BAQER JAMEEL,dan sarkin Aljanun FARISa. Mahaifina sarki Baqeer ya na da mata biyu, sarauniya AYRA da kuma SARAUNIYA SaMEE. Sarauniya Ayra  ita ce uwar gida,ta na da yara biyu, yarima fu'ud da kuma gimbiya Hoor.
sai Sarauniya Samee, ita ba ta haihu ba,amma ta na rukon dan  uwan ta. Wato  Aasim, kanene a wurin  ta.
Sarauniya Samee, yar uwar sarki Baqeer ce, auren zumunta aka yi mu su, while sarauniya Ayra Auren soyayya su ka yi.  ita yar sarkin misra ce( Egypt).  Ta kuma gaji sarauta gaba da baya, shiyasa duk wata hauka da sarauniya samee ke yi akan mulki ba ya damunta...
lokacin da kakana sarki Jameel ya bar duniya sai a ka nada mahaifi na ya zama shi ne sarkin farisa. Shi kuma kawu Aasim aka ba shi waziri. Wannan abun ya yi wa sarauniya samee ciwo ainun, domin ta so ace kanenta aka ba sarki,ba mahaifi na ba, Shi ne ya cancanci ya yi mulki ba mijin ta ba, sabo da ita tun farko mulkin ta ke so ya dawo hannunta shiyasa ta Auri sarki Baqeer. wannan kenan...
Shiyasa ta hada kai da kanenta su kashe sarki. Haka su ka bi duk dakarun sarki su ka saye su ba ki daya...
Duk wani abu da sarki Baqeer zai yi toh waziri Aasim zai ce be yi daidai ba.  Shiyasa duk wani abu da waziri zai zo da shi, sarki Baqeer zai karba sabo da a zauna lafiya,amma fa matukar bai sabawa addinin sa ba.
Ashe ba nan gizo ke saka ba, duk wani tanadi  na halaka sarki ya ta na de shi.
Wata rana ana zaune a fada, sai ga waziri  Aasim ta re da makaman yakinsa,ya ce lallai sai mahaifi na ya sauka daga karagar sa , shi ya hau. Wannan magana ta bata ran mahaifi na sosai!!! "kai Aasim ka natsu kasan agaban wadda ka ke yin magana!!! Dan haka ka gyara kalaman ka, ko kuma yanzu insa ayi min kasakasa da kai a nan wurin...!!!! Wata yar iskar dariya Waziri Aasim  ya ke yi, ta re da nu na sarki Baqeer  ya na cewa, haba dan uwana kuma sarkin Farisa...waiii  tsohon sarki zan ce, ta re da bushewa da dariya... sai can ya tsagaita dariyar sa, ba dai tun yanzu ka karaya ba? kar ka damu idan ka barmin sarautar zan barka da lafiyar ka amma, matukar ba ka bar karagar nan ba, toh wallahi ni ne ajalinka...!!
     Mai ku ke tunanin  zai faru da sarki Baqeer?  Shin ku na ganin zai sauka daga karagar sa, ko kuma zai yaki waziri Aasim?
DOMIN GUDUMUWA KO SHAWARWARI PLS
      08144066758
YAR MUTAN
   ARGUNGU``` ✍️📚







```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
MARUBUCIYAR...✍️
Bayan wuya📚
Ashe ba so ba ne❤️
ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺? ON TYPING...✍️
WRITTING-BY FATIMA ZARA ALHASSAN ❤️
GARGADI!!!
Ban yadda wani ko wata, su juya min littafi ba ta re da izini na ba, a kiyaye!!!
GODIYA
  ina mika dumbin godiya ta, ga yanne na, da kuma kanne na, Allah ya sa ka mu ku da alkhairi ya kuma kara ma na dankon zumunci❤️💙💛
JINJINA
Ga masoya na, ma su bibiyar littafaina, Allah ya barmu ta re, ya kuma sa ka  mu ku da alkhairi, ya ba mu ikon hakuri da juna💙💛
Iman fatima Ibrahim, ban manta da ke ba, wlh ki na raina, nagode da kokari, Allah ya bar ZUMUNTA 🤝🥰
Gaskiya na ji dadin yadda littafin nan ya samu karbuwa💃kuma insha Allah zan dinga yi mu ku typing akai-akai nagode👌
FREE PAGES 📖
SHAFI NA  4
      BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
Toh wallahi ni ne ajalin ka...
mamaki da al'ajabi su ka hana sarki Baqeer dogon motsi!!  Shi Aasim zai fadawa haka?! Wannan wane irin zumunta ce ko kuma ya ce mugunta!? Amma bakomai zai ba shi mamaki wallahi!! cewar sarki Baqeer...
Cikin izza da takama sarki baqeer ya tafa hannuwan sa, nan ta ke Dakarun sa su ka bai ya na, su wajen dubu dari shidda da hamsin (65000)  murmushi ya yi ta re da umartar su, su kama mi shi waziri Aasim, amma kamar da dutse ya ke magana, kadanne daga cikin su, su ka bii umarnin sa. Cikin fushi ya kalli gefen da dakarun sa su ke, ya nu na su da yatsa... ni za ku cii wa amana?!!! Mai Aasim ya ba ku da za ku bijire min? cikin fushi ya ke wannan maganar!!! Tabbas ya yi sa ke,ya na aikin me har haka ta faru a cikin masarautar sa? Zuciyar sa ce ta ba shi amsa da cewa, sabo da ka yadda da kowa da ke cikin masarautar, ka kuma yi amanna da cewa ba bu wanda zai cuceka, shiyasa ka ba su Amana.! Ba kasan cewa ba ko wa ne abun yarda ba. Ga shi yanzu wanda ka ke kallo dan 'uwa shi ne gaba-gaba wajen yi ma ka MUGUNTA 👺"  Tabbas gaskiya zuciyar sa ta fada mi shi,toh amma muddin ya na numfashi ba zai bar Aasim ya hau wannan karagar ba!!!  Umarni ya yi ga sauran mabiyan sa, da su kyale Aasim, su bar shi da shi, wannan fadan su biyu ya kamata su gwabza shi...
Dariya waziri Aasi ke yi, hahhh..."ai dama na fada ma ka, ka ga ma zamanin ka, yanzu na wa zai fara ,mutukar ina numfashi  a duniyar nan ba zan bar ma ka wannan mulkin ba, sai dai duk murasa!!!"
   Murmushi sarki Baqeer ya yi, sannan ya ce " ka yi kokari sosai Aasim, toh amma ai wannan fadan na mu ne mu biyu, ba sai an sa ka dakaru na aciki ba, sabo da haka ga fili ga mai doki...kowa ta sa ta fissai, sabo da bazan taba barin azzalumi irin ka ya rike sarautar nan ba... A fusace Aasim ya fara kai ma sa mugayen hari, ba ta re da sarki Baqeer ya shirya ba...amma a haka ya ke ta ka re kansa. Wasa-wasa sai da su ka shafe sa'o'ii su na gumurzu, ta re da zubar wa junansu jinainai.  Abu fa ya kankama, kwana biyu su na filin da ga ba bu ji ba bu gani, a rana ta uku ne labari ya sha bamban....✍️
MA SU CEWA IN KARA YAWAN RUBUTU, INSHA ALLAH ZAN KARA YAWAN SA. NAGODE DA KULAWAR KU❤️💛
   DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA PLs
08144066758
    yar mutan Argungu``` 🥰❤️💙









```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
       MARUBUCIYAR...✍️
***Bayan Wuya***
***Ashe ba so ba ne***
***Zumunta ko mugunta*** On typing...✍️
WRITING BY- FATIMA ZARA ALHASSAN ❤️💙💛
GARGADI!!
Kagaggen labari ne. Sabo da haka, ban yadda wani ko wata su juya min littafi, ba ta re da izinina ba, a kiyaye!!!
         JINJINA:
Ga yan uwana👍 Allah ya barmu ta re, ya kuma kara ma na son yin zumunci 💛💙❤️
GODIYA:
Ina miika gaisuwa ta zuwa ga masoya na, ma su bibiyar littafai na, Allah ya sa ka mu ku da alkhairi 👌
          Ita din kanwata ce, kuma kawa ta ce, wani bangaren kuma Uwa ta ce FATIMA IMAN IBRAHIM 🥰❤️
FREE PAGES
SHAFI NA 5
         Bismillahir Rahmanir- rahim
A rana ta uku ne labari ya shaa bamban...
*************************
  **********************
Sanadiyyar halaka junan su da su ka yi. Hakan ya sa garin ya yi tsit...ba ka jin motsin komai, sai koke-koken iyalan sarki Baqeer.
Bayan kwana uku, garin ya laafa. Sarauniya Samee ta hau kan karagar mulki,sabo da ba wanda ya isa ya ha na ta,a cewar ta, ita ke da karfin dakaru, duk abun da ta sasu,  shi su ke yi. Hawanta karagar ba wu ya ta dinga shinfida zalunci, da mugunta, ta re da kuma ka fa dokoki tsaurara a cikin mulkin ta.  Daga karshe kuma ta koori Sarauniya Ayra ta re da yaranta daga cikin masarautar, kuma da gargadin kar su kuskura su waiwayo wannan...


Read / Download ZUMUNTA KO MUGUNTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album