Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

```MARUBUCIYAR...✍️
Bayan Wuya
Ashe ba so ba ne
Zumunta ko Mugunta📚
       Writting-by Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!!
     Kagaggen labari  ne. Ban yadda wani ko wata, su juya mi ni littafi, ba ta re da izini na ba!! Sabo da haka a kiyaye👂!!!
JINJINA
Ina jinjina ga mabiya littafai na, nagode sosai Allah ya barmu ta re🥰💛💙
SADAUKARWA
ga yan' uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma qara hada kanmu, mu yi zumunci🤝❤️
     MY FANS WANNAN SALON NA DABAN NE. 
KAR KU BA RI ABAR KU A BAYA🤪
        Free pages
SHAFI NA 1
        BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Gudu ta ke yi sosai acikin dajii. kafafunta duk sun farfashe, ya yin da kafarta ta hagu jini ke zuba. Da alama wani kwaro ne ya cije ta awajen. kayan jikinta duk sun yayyage, kan ta ba bu dankwali. kallo daya za ka yi wa kan ta, kasan cewa ya yi watanni sabo da daddagewar da kitson ya yi, ba bu kyan gani. Alamu sun nu na cewa ita kan ta yarinyar ba ta san ina za ta je ba.A daidai wurin wata katuwar itaciyar kuka ta fadi, sabo da juuwar da ta dibeta . Nan da nan guguwa ta tashi a wurin ta lullube yarinyar. Bayan dakika biyar guguwar ta laafa.
Tun shigowar ta cikin dajin ya ke kallonta, ta re da mamakin wannan al'ajabi! Tun zaman sa a jejin bai taba ganin wani mahaluki wai shi bil'adama ya shigo jejin ba, sai yau da Allah ya hada shi da wannan yarinya.  Duk gudun da ta ke yi akan idonsa, har kawo yanzu da ta fadi a gabansa.
Ba din da ya yi saurin ta re ta ba,

Allah kadai ya san raunin da za ta ji, idan ta fadi a kasa. Tsura ma ta ido ya yi yana kallonta, dududu ba za ta wuce shekaru shaa shida ba(16 years) wadda ba ta wuce renon iyaye ba, shi ne aka samu wa su  azzalummai su ka gunguntar da rayuwar ta.  Tafaa hannuwan sa ya yi, sai wurin ya koma wani babban falo ta re da kayan alatu na rayuwa. Fadin haduwar sa bata lokaci ne . Tafaa hannuwan sa ya yi akaro na biyu, ta ke duk rauni kan jikinta su ka bace, ta re da canza ma ta kayan jikinta. . Masha Allah, yarinya ce kyakkayawa , alkalami na ba zai iya bai ya na mu ku kyanta ba. sai dai mai karatu ya kiyasta...
Abun tambaya anan shi ne, wanene wannan mutumin? kuma yarinyar daga ina ta fito, san nan me ya faru da ita?
A tunanin ku, wane irin firgici yarinyar za ta shiga, idan ta farka ta ga kan ta a wannan wuri kuma ta re da wannan mutumin?
kar ku damu, ni Fatima Zara Alhassan ashirye na ke tsab domin  kawo mu ku wadan nan amsoshin.
DOMIN GUDUnMUWA KO SHAWARWARI PLS
      08144066758
YAR MUTAN
       ARGUNGU ✍️📚
ya ku ka ji wannan salon,
Ina fa tar salon ya kayatar da ku?
Comments
  Share```








```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺📖?
MARUBUCIYAR...✍️
Bayan Wuya
Ashe ba so ba ne
Zumunta ko Mugunta📚
       Writting-by Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!
     Kagaggen labari  ne. Ban yadda wani ko wata, su juya mi ni littafi, ba ta re da izini na ba!! Sabo da haka a kiyaye👂!!!
JINJINA
  Ina jinjina ga mabiya littafai na, nagode sosai Allah ya barmu ta re🥰💛💙
SADAUKARWA
ga yan' uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma qara hada kanmu, mu yi zumunci🤝❤️
     MY FANS WANNAN SALON NA DABAN NE.  KAR KU BA RI ABAR KU A BAYA🤪
        Free pages
SHAFI NA 2
        BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM
A hankali ya zauna ku sa da ita...
duk da ya san abun da zai yi haramun ne, amma hakan bai ha na shi aikatawa ba. Sabo da ya ga har yanzu ba ta sa ke ba. Hannun sa ya daura akan na ta, ta re da yi ma ta murmushi, nan ta ke jikin ta ya fara rawa, ta re da janye hannun ta, ta na balla mishi harara,cikin tsiwa ta fara yi mishi magana...waye kai? kuma ina ne nan? Meyasa ka kawo ni nan wurin? Miye manufarka nayin hakan?!!!
Tsura ma ta idanuwan sa ya yi, sai da gaban ta ya fadi. Har wani mai ta ke ga ni acikin su, kuma ga dan banzan kwarjini, duk iskancin mutum sai ya saurara idan ya na gaban shi. Murmushi ya yi ganin ta natsu sosai, ANEESA ABDUL-AZIZ ABUBAKAR MAI NOMA. cikin ta shin hankali ta ce, ya aka yi kasan sunana ta re da fashewa da kuka mai tsanani ta na cewa...dan Allah nima ka kasheni kamar yadda ku ka kashe Iyaye na, ko kun barni da raina wallahi rayuwar ba za ta yi min dadi ba!! na rokeka da ka kasheni nima da Allah...!! Sai yanzu duk abubuwan da su ka faru ke dawo ma ta daya bayan daya. Kuma tabbas ta ga mutum biyu daga cikin wadanda su ka kashe ma ta Ummanta ta re da Bappan ta.  "Mamana ki gudu kar su ka ma ki, ba bu imani acikin zuciyoyin su, dan Allah ki kula da kanki, ba kowane za ki yadda da shi ba, kowa kokari ya ke yaga ya ya zai cuce ka, amma kisani ba duka aka zama daya ba, amma dai ki kula da rayuwar ki, kamar yadda akwai mugayen mutane haka akwai nagari acikin ta, har ga Allah na so ace kin yi Aure kafin wannan kaddarar ta zo ma na, sabo da ki samu majingina a ta re da ke, amma bakomai duk abun da ubangiji ya tsara ma na daidai ne, Aneesa ina son kinsan cewa, a wannan duniyar naka shike cutar da kai, inaji a jikina za ki yi tsawon rai, idan har hakan ta kasance ina son ki samomin amsar wannan tambayar "ZUMUNTA KO MUGUNTA"??  A'a Bappa kar kuyi min haka please wlh idan babu ku acikin rayuwa ta aikin banza ne, ya ku ke son inyi da raina!!...Umma ba ki ce komai ba? Umm...umma...umma...Bappa.... dan Allah ku tashi mu yi rayuwar mu cikin farin ciki, kuka ta ke yi sosai ta na jijjiga gawarsu...halbin da akayi ma ta a kafar hagu shi ya dawo da ita haiyacin ta, bishibishi ta ke ganin fuskokin su, ka fin ta sume anan wurin. Tabbas ta tuna komai, amma abun tambaya anan, waye wannan? 
Tun dazu ya ke kallonta ita kuma ta lula duniyar tunani. Abun da ba ta sa ni ba shine, maganar zuuci ta fito waje, na cewa WAYE WANNAN?   KI na son ki san wanene ni? ya katse ma ta tunanin da fadar hakan.
juyowa ta yi ta re da zuba ma sa idanuwan ta, alamun kai na ke saurare...ya gane nufin ta shiyasa ya ci gaba da cewa...
DAN ALLAH KU FADAMIN GSKY, KU NA JINDADIN LABARIN KO KUMA A CANZA WANI?
DOMIN GUDUMUWA KO SHAWARWARI PLS
08144066758```
YAR MUTAN
       ARGUNGU ✍️📚








```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺📖?
MARUBUCIYAR...✍️
Bayan Wuya
Ashe ba so ba ne
Zumunta ko Mugunta📚
       Writting-by Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!!
     Kagaggen labari  ne. Ban yadda wani ko wata, su juya mi ni littafi, ba ta re da izini na ba!! Sabo da haka a kiyaye👂!!!
JINJINA
  Ina jinjina ga mabiya littafai na, nagode sosai Allah ya barmu ta re🥰💛💙
SADAUKARWA
ga yan' uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma qara hada kanmu, mu yi zumunci🤝❤️
     MY FANS WANNAN SALON NA DABAN NE.  KAR KU BA RI ABAR KU A BAYA🤪
        Free pages
SHAFI NA 3
        BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM
Ya gane nufin ta shiyasa ya ci gaba da cewa...
Sunana FU'UD BAQER JAMEEL,dan sarkin Aljanun FARISa. Mahaifina sarki Baqeer ya na da mata biyu, sarauniya AYRA da kuma SARAUNIYA SaMEE. Sarauniya Ayra  ita ce uwar gida,ta na da yara biyu, yarima fu'ud da kuma gimbiya Hoor.
sai Sarauniya Samee, ita ba ta haihu ba,amma ta na rukon dan  uwan ta. Wato  Aasim, kanene a wurin  ta.
Sarauniya Samee, yar uwar sarki Baqeer ce, auren zumunta aka yi mu su, while sarauniya Ayra Auren soyayya su ka yi.  ita yar sarkin misra ce( Egypt).  Ta kuma gaji sarauta gaba da baya, shiyasa duk wata hauka da sarauniya samee ke yi akan mulki ba ya damunta...
lokacin da kakana sarki Jameel ya bar duniya sai a ka nada mahaifi na ya zama shi ne sarkin farisa. Shi kuma kawu Aasim aka ba shi waziri. Wannan abun ya yi wa sarauniya samee ciwo ainun, domin ta so ace kanenta aka ba sarki,ba mahaifi na ba, Shi ne ya cancanci ya yi mulki ba mijin ta ba, sabo da ita tun farko mulkin ta ke so ya dawo hannunta shiyasa ta Auri sarki Baqeer. wannan kenan...
Shiyasa ta hada kai da kanenta su kashe sarki. Haka su ka bi duk dakarun sarki su ka saye su ba ki daya...
Duk wani abu da sarki Baqeer zai yi toh waziri Aasim zai ce be yi daidai ba.  Shiyasa duk wani abu da waziri zai zo da shi, sarki Baqeer zai karba sabo da a zauna lafiya,amma fa matukar bai sabawa addinin sa ba.
Ashe ba nan gizo ke saka ba, duk wani tanadi  na halaka sarki ya ta na de shi.
Wata rana ana zaune a fada, sai ga waziri  Aasim ta re da makaman yakinsa,ya ce lallai sai mahaifi na ya sauka daga karagar sa , shi ya hau. Wannan magana ta bata ran mahaifi na sosai!!! "kai Aasim ka natsu kasan agaban wadda ka ke yin magana!!! Dan haka ka gyara kalaman ka, ko kuma yanzu insa ayi min kasakasa da kai a nan wurin...!!!! Wata yar iskar dariya Waziri Aasim  ya ke yi, ta re da nu na sarki Baqeer  ya na cewa, haba dan uwana kuma sarkin Farisa...waiii  tsohon sarki zan ce, ta re da bushewa da dariya... sai can ya tsagaita dariyar sa, ba dai tun yanzu ka karaya ba? kar ka damu idan ka barmin sarautar zan barka da lafiyar ka amma, matukar ba ka bar karagar nan ba, toh wallahi ni ne ajalinka...!!
     Mai ku ke tunanin  zai faru da sarki Baqeer?  Shin ku na ganin zai sauka daga karagar sa, ko kuma zai yaki waziri Aasim?
DOMIN GUDUMUWA KO SHAWARWARI PLS
      08144066758
YAR MUTAN
   ARGUNGU``` ✍️📚







```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
MARUBUCIYAR...✍️
Bayan wuya📚
Ashe ba so ba ne❤️
ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺? ON TYPING...✍️
WRITTING-BY FATIMA ZARA ALHASSAN ❤️
GARGADI!!!
Ban yadda wani ko wata, su juya min littafi ba ta re da izini na ba, a kiyaye!!!
GODIYA
  ina mika dumbin godiya ta, ga yanne na, da kuma kanne na, Allah ya sa ka mu ku da alkhairi ya kuma kara ma na dankon zumunci❤️💙💛
JINJINA
Ga masoya na, ma su bibiyar littafaina, Allah ya barmu ta re, ya kuma sa ka  mu ku da alkhairi, ya ba mu ikon hakuri da juna💙💛
Iman fatima Ibrahim, ban manta da ke ba, wlh ki na raina, nagode da kokari, Allah ya bar ZUMUNTA 🤝🥰
Gaskiya na ji dadin yadda littafin nan ya samu karbuwa💃kuma insha Allah zan dinga yi mu ku typing akai-akai nagode👌
FREE PAGES 📖
SHAFI NA  4
      BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
Toh wallahi ni ne ajalin ka...
mamaki da al'ajabi su ka hana sarki Baqeer dogon motsi!!  Shi Aasim zai fadawa haka?! Wannan wane irin zumunta ce ko kuma ya ce mugunta!? Amma bakomai zai ba shi mamaki wallahi!! cewar sarki Baqeer...
Cikin izza da takama sarki baqeer ya tafa hannuwan sa, nan ta ke Dakarun sa su ka bai ya na, su wajen dubu dari shidda da hamsin (65000)  murmushi ya yi ta re da umartar su, su kama mi shi waziri Aasim, amma kamar da dutse ya ke magana, kadanne daga cikin su, su ka bii umarnin sa. Cikin fushi ya kalli gefen da dakarun sa su ke, ya nu na su da yatsa... ni za ku cii wa amana?!!! Mai Aasim ya ba ku da za ku bijire min? cikin fushi ya ke wannan maganar!!! Tabbas ya yi sa ke,ya na aikin me har haka ta faru a cikin masarautar sa? Zuciyar sa ce ta ba shi amsa da cewa, sabo da ka yadda da kowa da ke cikin masarautar, ka kuma yi amanna da cewa ba bu wanda zai cuceka, shiyasa ka ba su Amana.! Ba kasan cewa ba ko wa ne abun yarda ba. Ga shi yanzu wanda ka ke kallo dan 'uwa shi ne gaba-gaba wajen yi ma ka MUGUNTA 👺"  Tabbas gaskiya zuciyar sa ta fada mi shi,toh amma muddin ya na numfashi ba zai bar Aasim ya hau wannan karagar ba!!!  Umarni ya yi ga sauran mabiyan sa, da su kyale Aasim, su bar shi da shi, wannan fadan su biyu ya kamata su gwabza shi...
Dariya waziri Aasi ke yi, hahhh..."ai dama na fada ma ka, ka ga ma zamanin ka, yanzu na wa zai fara ,mutukar ina numfashi  a duniyar nan ba zan bar ma ka wannan mulkin ba, sai dai duk murasa!!!"
   Murmushi sarki Baqeer ya yi, sannan ya ce " ka yi kokari sosai Aasim, toh amma ai wannan fadan na mu ne mu biyu, ba sai an sa ka dakaru na aciki ba, sabo da haka ga fili ga mai doki...kowa ta sa ta fissai, sabo da bazan taba barin azzalumi irin ka ya rike sarautar nan ba... A fusace Aasim ya fara kai ma sa mugayen hari, ba ta re da sarki Baqeer ya shirya ba...amma a haka ya ke ta ka re kansa. Wasa-wasa sai da su ka shafe sa'o'ii su na gumurzu, ta re da zubar wa junansu jinainai.  Abu fa ya kankama, kwana biyu su na filin da ga ba bu ji ba bu gani, a rana ta uku ne labari ya sha bamban....✍️
MA SU CEWA IN KARA YAWAN RUBUTU, INSHA ALLAH ZAN KARA YAWAN SA. NAGODE DA KULAWAR KU❤️💛
   DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA PLs
08144066758
    yar mutan Argungu``` 🥰❤️💙









```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
       MARUBUCIYAR...✍️
***Bayan Wuya***
***Ashe ba so ba ne***
***Zumunta ko mugunta*** On typing...✍️
WRITING BY- FATIMA ZARA ALHASSAN ❤️💙💛
GARGADI!!
Kagaggen labari ne. Sabo da haka, ban yadda wani ko wata su juya min littafi, ba ta re da izinina ba, a kiyaye!!!
         JINJINA:
Ga yan uwana👍 Allah ya barmu ta re, ya kuma kara ma na son yin zumunci 💛💙❤️
GODIYA:
Ina miika gaisuwa ta zuwa ga masoya na, ma su bibiyar littafai na, Allah ya sa ka mu ku da alkhairi 👌
          Ita din kanwata ce, kuma kawa ta ce, wani bangaren kuma Uwa ta ce FATIMA IMAN IBRAHIM 🥰❤️
FREE PAGES
SHAFI NA 5
         Bismillahir Rahmanir- rahim
A rana ta uku ne labari ya shaa bamban...
*************************
  **********************
Sanadiyyar halaka junan su da su ka yi. Hakan ya sa garin ya yi tsit...ba ka jin motsin komai, sai koke-koken iyalan sarki Baqeer.
Bayan kwana uku, garin ya laafa. Sarauniya Samee ta hau kan karagar mulki,sabo da ba wanda ya isa ya ha na ta,a cewar ta, ita ke da karfin dakaru, duk abun da ta sasu,  shi su ke yi. Hawanta karagar ba wu ya ta dinga shinfida zalunci, da mugunta, ta re da kuma ka fa dokoki tsaurara a cikin mulkin ta.  Daga karshe kuma ta koori Sarauniya Ayra ta re da yaranta daga cikin masarautar, kuma da gargadin kar su kuskura su waiwayo wannan kasar.
Ha ka sarauniya Ayra, ta kwashe yaranta su ka lula birnin SIN ( EGYPT) Ba wai don ba ta iyawa da sarauniya samee ba ne, a'a kawai dai ta ba ta lokaci ne. kuma in har "muzuru na yawo shaho na yawo dole su hadu wata rana".  A birnin SIN kuwa, mahaifin ta ya karbe su hannu bibbiyu. A nan birnin SIN ta sa ka yaranta makaranta,a cewar ta ga ra su samu ilmi sosai, domin kwaato/karbo hakkokin su, ta re da kuma taimakawa al'ummar su.  Sabo da ta na da tabbacin da ace kasar su, su na da ilmi sosai da duk hakan bai fa ru ba. Shiyasa ta zaunar da ya'yanta  ta ce mu su ta na son su sa mu ilmi na addini da kuma na zamani,  sabo da ilmi bargo ne ga duk wanda ya lulluba da shi, ba ya tozarta . Sai ka ga shi ba kowa ba,amma matukar ya sami ilmi sai ya zama babba a cikin Al'umma....
******************************************
               *********************************
         Dai-dai wani katon get na ga an rubuta KAMBUN SARAUTA da manya baqi, shiga ciki na yi, a she Makaranta ce ta ya'yan sarakuna (aljannu) sarauniya Ayra ce bakin ta ba ya rufuwa sabo da farin cikinta, yaron ta ya ga ma makaranta! Burinta na gab da cika, amma za ta kara lokaci kadan kafin nan gimbiya Hoor ita ma ta gama karatun ta.
Akwana atashi asarar mai rai...ga shi Hoor har ta ga ma karatun ta. sun yi murna sosai. Bayan wa su yan kwanaki, ta sa aka fa ra koya mu su yaki ta re da dabarun ka re kan su....
DAN ALLAH KU YI HAKURI A MAIMAKON NA RUBUTA FU'AD SAI  NA RUBUTA FU'UD
DA FATAR ZA KU GYARA NGD
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA
     PLS
08144066758
YAR MUTAN ARGUNGU``` ❤️💙


.



```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
Marubuciyar...✍️
**Bayan wuya**
**Ashe ba so ba ne**
**Zumunta ko mugunta on typing...✍️
Writing-by Fatima Zara Alhassan ❤️
Fatima iman ibrahim ina godiya sosai❤️
SHAFI NA 6
      Bismillahir- rahmanir rahim
An koya mu su yakii sosai. Haka ta samu mahaifin ta, ta ce mishi nan da sati hudu ta na son zuwa kasar Farisa, ta re da yaran ta. Bai jaa zancen ba ya nuna ma ta amince warsa, ta re da ba ta kwarin guiwa, "idan su ka je, kar tabar Sarauniya Samee akan karaga, sabo da duk zuluncin da sarauniya samee ke yi, ana fada mi shi. Amma yanzu lokaci ya yi da za ki jee ma ta a makance,ma'ana duk wata hanya da za ta san da zuwan ku, zan rufe ta,sabo da ta saka matakan tsaro sosai a kasar ta. Ko kwaro ya bi ta gefen kasar ta sai ta sa ka an kashe shi... ballan ta na ke da tasan cewa ko bajima ko badade sai kin kai ma ta farmaki, sabo da haka je ki kira mini jikokina...? Bayan mun bayyana agaban kakan mu. Sai ya dauko kwarya, ya yi addu'o'i acikin, san nan ya ba ni ya ce, "karba kasha ka ba kanwar ka, wannan tsarine da yardar ubangiji, duk wani girman al'jani ko muninsa ko kuma tsafinsa, wallahi bai isa ya tsaya agaban jinina ba,matukar ya ce zai cutar da su, sai dai ya tsaya a gaban ku da alkhairi ba dai sharri ba. Dan haka ku tashi ku tafi, in-sha Allah ku ke da nasara! Amma ku sa ni, na hane ku da yin zalunci tun daga jinsin ku, har na bil'adama, Allah ya yi mu ku albarka!" Ameen Kakan mu, mun gode sosai da dawainiyar da kayi damu, Allah ya saka ma ka da alkhairi ya kuma kara ma ka lafiya. kuma in-sha Allah mu ma su biyayya ne akan umarnin ka, ma'assalam..
A hankali su ka koma farin hayaki,su bace bat! A kasar farisa kuwa, kwanan nan wasu irin mafalkai ta ke yi mai ban tsoro...wai an shigo masarautar ta an hallaka ta, am ma ta kisan gilla. Wannan abun na ta da hankalin ta ainun, ta kuma yi iyya binciken da za ta yi, akan gano dalilin wannan mafalkin amma ta ka sa ga ne komai akai!!! Hakan ya sa ta kara yawan dakaru ma su tsaron lafiyar ta. Wannan kenan....
Saukar mu kasar Farisa ke da wu ya, mu ka kutsa kai tsaye cikin masarautar. Duk yadda dakaru ke son tsayar damu, abu ya faskara. Dalili kuwa shi ne, da zarar sun nufo wajen mu da niyyar kai mana farmaki sai su jaa baya,haka mu ka dinga yi da su har mu ka isa cikin fada....

Sarauniya samee na ganin mu, ta mike tsaye cikin mugun firgici!!! Yau me zan ga ni, ni sarauniyar FARISa?! Me ku ka dawo yi a kasata?! Cikin tashin hankali ta ke kallon su, cikin kuma kaduwar hanta.
Ba ta tsinke da lamarin ba, sai da ta juya ta ga Yarima Fu'ad zaune akan karagar ta.
"Tashin hankali wan da ba a sa ma sa rana" Tabbas! mafarkin ta ya tabbata, amma wallahi sai dai su kashe ta ,ba za ta ba su mulki ba. Duk cikin zuciyar ta,ta ke wannan zance...
Ki samu wuri ki zauna, magana zamu da ke ta fahimta,amma fa idan kin bamu hadin kai. cewar yarima fu'ad,. cikin tsawa ta ce ," kai har ka isa ka zo gabana ka ce wai in zauna?! Waye kai kuma tashin yaushe da za kaban umarni, kuma kayi tunanin in bika, toh ko uwarka Ayra ba ta isa ba, balle yaron da aka haifa a ga ba na!!! Ke Samee... sa ka idanuwan ki cikin na wa, nine dai-dai yin ki, ba mahaifiya ta ba, dan haka umarni ne na ba ki, kuma dole ki bi...azuciye ta yi wurinsa, amma ga mamakin ta, ta ka sa hada ido da shi, sai ma wani shegen tsoron sa da ta ke ji. Toh me hakan ya ke nufi?!! Ta tambayi kan ta.
Murmushi Sarauniya Ayra ta yi, irin na ya'yan saraku na, san nan ta ce, "ai dama na fada miki, idan muzuru na yawo, shaho na yawo wata ran, za su hadu" yanzu kin yadda da magana ta?  Ta muzance sosai, ace kamar ta sarauniya samee,wai yau ita ake ciwa mutumci agaban dakarunta!!!. A yau ba sai gobe ba,za ki bar wannan karagar mulkin, za kuma ki bar wannan kasar gaba daya, kuma da sharadin duk ranar da kika dawo wallahi sai na sare kan ki, kuma bazan yi kaffara ba!! Na ba ki rabin saa'a ki yi nesa da kasar, komai kama da ke aka ce angani, toh kiyi kuka da kanki,. San nan sarauniya Ayra ta sa ke juyawa gefen dakaru, ta fitar da duk wadanda su ka bijirewa mijinta, ta sallame su``` ...











```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
Marubuciyar...✍️
**Bayan wuya**
**Ashe ba so ba ne**
**Zumunta ko mugunta

Please Login or Register in order to submit comment