Join Our WhatsApp Group

KHADEEJATU Complete Hausa Novel Document by KHADEEJATU


KHADEEJATU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22260KHADEEJATU

Reading Time: 1 Hours

Added On: 21, May 2023

Author: Khadija Adam Idris ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ????AINUWA ????RITER'S

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 132.6 kb

File Type: txt

Views: 832+

Download: 394+

Last download: 2 days ago

Description/Story: ✨✨✨✨✨✨✨✨An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨✨


*LABARI/RUBUTAWA**KHADIJA* *ADAM IDRIS*
( _Shalelen_ _kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN MAHAIFANA👩‍❤️‍👨*


*AND NOW*

✨✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abunda zai amfani Alummar musulmai.*Sadaukarwa*


Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu idris* Allah kara lafiya da nisan kwana
Amin.


_2nd January 2021_


1~2


Kano ta dabo tumbin giwa ko da mai kazo an fika gari mai tarin albarka tu mai dala da goron dutse.Unguwar dorayi wasu Yan Mata ne gudu biyu su na tafe su na hira dayar ta dubi yar uwarta ta ce “khadeejatu wallahi yanayin sanyi nan da karfin shi ya shigo wanna karan , muyi sauri muje mu yiwa Umma cefa nen nan, yau mu je islamiya da wuri.Wanda aka Kira da Khadeejatu ta dan harare ta tayi murmushi ta ce “Ai Hafsa ke kike makarar da mu a sanyin na a zane mu su ma malaman sam ba imani".Haka suka karasa gurin mai kayan miyar yana ganin su ya washe hakora ya ce “Yan biyu kune a tafe".Hafsa mutuniyar shi ta ce
“Malam Sabo kayan miya na dari biyu zaka ba mu"Malam Sabo ya ce “to h
Hafsatutu matar mai shayi” ya karasa cikin dariya.Hade rai ta yi Khadeejatu ta yi mumushi tana tafa hannu ta ce “Yau dai munji kan ku" ta kalli Hafsa ta sheke da dariya.Hafsa ta chuno baki gaba.Malam Sabo yayi dariya ya kalli Hafsa ya ce “Rabu da ita kinji bari in zuba maki "
Ya na gama zuba masu Hafsa ta ce “Malam sabo wannan yar Albasar zaka zuba Mana?"Malam sabo ya Kama ha'ba ya ce “Ai Hafsatu haka ma dan ku ne na kyauta ma ku ai albasa ta zama yar sarki"Khadeejatu ta ce “Allah dai ya kyauta" ta karba kayan miyar su ka tafi.Su na zuwa daidai kofar gidan su Khadeejatu, Khadeejatu ta sa dariya ta ce “Hafsatutu matar mai shayi" ta shige gida a guje.A zuciye hafsa ta ma ra mata baya Umma da ke wanke shinkafa taji garaf a banko kofa da sauri ta dago ta na dafe kirji.Da sauri khadeejatu ta banka kofar dakin Umma Hafsa ta bi ta.Wata sanyayyar Ajiyar zuciya Umma tayi ta ce “wallahi yaran nan sai ku sawa mutane ciwon zuciya kuna girma ko waccen ku ta yi 16 in a kauye ne da tuni an aurar daku kuma tsaff za ku zauna........."____________”Hajiya Zainab matar Dr Nuraddeen na ga Kira da sassafe na ce ko lafiya?" cewar Safiyya cikin damuwa Zainab ta kalleta ta ce “ba dole ba Safiyya kinsan matsala ta Nura ne duk ya wa ni chanja mun ko lallabani ba yayi nace ya samon yar aiki yaki
ni gani ma nake ko wanchar banza uwar nan ta sa ce take sa shi".Safiyya ta kalli Zainab ta ce “ A kan wannan ne duk kika tayar da hankalin ki ?"Zainab ta ce “ba dole in tada hankali na ba" da sauri Safiyya ta ce “kima kwantar da hankalinki ai muna da mafuta yadda har hanashi zuwa gurin uwarshi zaki iya"Mamaki dauke a fuskar Zainab ta ce “ta yaya za'ayi haka Safiyya? "Da murmushi dauke a fuskar ta ce “ta hanyar zuwa gurin boka mana"cewar Safiyya.Zare ido Zainab tayi ta ce “boka fa ki ka ce gaskiya ni bazan iya ".Safiyya ta hade rai ta ce “to wallahi nake fada ma ki kina zaune sai dai kiji ana gwuda uwar shi ta aura mashi wata matar kina nan zaune ni shiyasa sam bazan auri wanda uwarshi take raye ba kuma kiji ni da kyau karki sa ke kirana akan wata mstsalar ki" ta mike tare da daukar Jakarta.Ta mike zata futa ko mai Zainab ta yi tunani da sauri ta ruko mayafin Safiyya tana fadin “Ba za'ayi haka ba kawalli wallahi na amince"Juyowa Safiyya ta koma ta zauna murmushi tayi ta ce “ko kefa yanxu yaushe kike so muje ?"Cikin zumudi Zainab ta ce “ni ai ko yanzu ki ka ce muje a shirye na ke".


Safiyya ta ce “kin tabbata kuwa?"


Da sauri Zainab ta ce sosai Safiyya ta ce ”okay kina da kudi?"Zainab ta ce “ina dashi mana ko bani dashi ai na karba gurin honey ".Safiyya ta ce “To baki da matsala gobe kamar yanzu zanzo muje gurin bokan" hira suka cigaba da yi.


*WASHEGARI*


Wai ke Zainab meye haka ne ko sallah kin ki tashi kiyi yanzu zan futa office ba ki mun breakfast ba ?"“Tun bayan Auren mu kika wani chanja kai ka ce ba auren soyayya mukayi ba na kiyayyya ne".


Bude idon ta tayi ta kalleshi ta ce “kaga malam in zaka wuce gurin aikin ka da ya fi ma ka kuma sallar kai zan yiwa? da za ka ishe ni".


Briefcase dinshi ya dauka ya na fadin “Allah ya kyauta" ya sa kanshi ya fice .


Da harara ta rakashi taja bargo ta rufe fuskarta ta cigaba da baccinta.Shi ko Nura ya na tafe a hanya ya na mamakin Zainab da ta chanja halayyarta tun bayan aurensu da wata biyu ta sauya.*Da dadddare*


Nura ne ya kalli kanwarshi Maryam ya ce ”Maryam dan zubo mun abinci "Dagowa tayi ta kalle shi ta ce “to Yaya" kana ta nufi kitchen din.Sai da Mama ta ga ta shige kitchen din sannan ta mai da kallonta gurin Nura tsaff ta kare mashi kallon ta ce “Nura"Da sauri ya ce “Naam" ya na ajiye wayar hannunshi dan yadda yaji ta kira sunanshi yasan ba wasa.Gyara zama tayi ta ce “Wai Nura ina matarka ne da kullum sai kazo nan kaci abincin ita mai yasa bata dafawa ne ?ko meye kuma?


Shafa kanshi yayi ya sunkuyar da kanshi kana ya ce “Dama tace na nemo mata yar aiki nace ni banason yar aiki shine kuwa tace to ita ba baiwa ce ba da zata na wahalar gida ga girki" sai kuma yayi shiru....


Mama ta ringa jinjina maganganun a ranta ta ce “Ba matsala zanga ya za'ayi karka damu".Maryam ce ta karaso ta ajiye mashi abincin akan stool a gabashi ta ce “Yaya ga Abincin ".


Murmushi yayi ya shafa kanta ya ce “Nagode little sisi Allah nuna mun auren ki".


Da sauri ta rufe fuskarta tana dariya .


Murmushi yayi ya fara cin abincin sai da yayi nak sannan ya wuce gida.


___________


Yau ma asual bai yi breakfast ba haka zai wuce hospital gashi emergency ake nai man shi.


Garage ya nufa ya shiga motarshi ya murza mata key kana ya ba ta wuta mai gadi ya bude mashi gate ya fice.Ai ya na ficewa Zainab ta mike ta shiga wanka da sauri sauri ta shirya.Wayarta da kudade ta dauka ta sa a jaka ta yafa wani yalolon gyale.Ta na futowa falo sai ga Safiyya ta shigo kyalkyalewa da dariya Safiyya tayi ta ce “Uwar zumudi ba dai har kin shirya ba?"Zainab tayi dariya tana fadin “ba dole ba ke dai muje muyi sauri".


Ficewa su ka yi su ka shiga motarta mai gadi ya bude ma su su na hawa kan titi ta kunna masu kida wani kauye su ka nufa..............🖊️✍🏻
Kubiyo ni kuji ya zata kaya wannan salon da ban yake 🧚‍♀️💃


*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ........✍🏻✍🏻
Takuce har kullum *Addeejerh* ❤️

✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨*LABARI/RUBUTAWA**KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND* *NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .
Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.


3~4A wani guri su kai parking dan mota ba ta shiga gurin bokan.


Wani katon dutse suka nufa a matukar firgici Zainab ta kalli safiyya da ke kokarin hawa kan dutsen ta ce “kardai kice nan zamu hau?" tana maganar tana zazzare ido.Wata iriyar matsiyaciyar dariya Safiyya ta kyalkyale da kana ta ce “Ehh mana ai gidan bokan a can saman dutsen ya ke ".


A tsorace Zainab ta ce “Ni dai bazan iya hawa ba".


Safiyya ta ce “shikenan tunda bakya so sai mu koma ai".Da sauri Zainab ta ce “ A'a ina so yanzu ya zanyi"


Safiyya ta kalleta ta ce “haka zaki hau tunda kina so" ita taci gaba da danewa kamar yar biri.


Zainab dai ta na tsaye ta na tunanin ta ya zata hau wannnan tsiririn dutsen.


Safiyya ce ta kallota ta ce “wai ba zaki hawo ba ne? ki na bata mun lokaci"


Da kyar Zainab din ta kama dutsen ta fara hawa ko nisa ba ta yi ba sosai sai kafar ta daya ta ku sa zamewa a rude ta ce “Safiyya zan fa hansila" idanuwan ta duk sun cicciko.


Kyalkyalewa da dariya Safiyya tayi wanda ya kular da Zainab.


Ganin haka kuwa ta kulu tayi ta maza ta cigaba da tafiya amma yagololon mayafinta sai da ya fada.


Da kyar suka karasa su na isa Zainab ta dafe kirjinta sai haki ta ke yi .


Wani dan sumulmulen daki ne an rarrataye kawunan kwarangwal da tukwanen kasa dakin kewaye da jan kyalle.


da wata irin gigitacciyar murya aka ce “ku shigo da baya baya a cire takalma".


Ai jin wannan katuwar murya Zainab ta rukunkune Safiyya kamar za ta cire mata hakarkari.


Dariya Safiyya tayi aran ta ta ce “aikin banza"
shiga suka yi.


Wani yakunannen mutum ne da jan kaya a jikin shi da wata kwarya a gabanshi kansa a sunkuye .


Zama suka yi ita dai Zainab jikinta sai bari ya ke yi.


“Mai ke tafe da kune?". bokan ya tambaya cikin gardiyar muryarshi.


Safiyya ce ta kalli Zainab ta ce “ki mashi baya ni da kanki"


Cikin rawar baki Zainab ta ce “boka ina..so...ne ....a kark..a..to mun da hankalin mijina ko mai nayi kar ya tanka kuma ya koma kamar dan cikina wanda na haifeshi sai abunda nace mashi"


Hhhhhh bokan ya sheke da wata iriyar dariya da har saida Zainab taji hantar cikin ta ta kada Safiyya ko, ko a jikinta.


Haka bokan ya ringa sheka wata iriyar dariya kafin ya ce “ta kwana gidan sauki iya abun da kike so ayi akan shi kenan in ma ki naso a maida shi ko bandaki zai shiga sai ya tambaye ki" yana kwashewa da dariya.


Da sauri ta daga kanta ta ce “Ehh boka ayi hakan"


Hehehehehe yayi dariya ya dauko wata kwarya a ciki ya dauko wani kullin magani ya mikawa Zainab hannun ta na rawa ta karba ya sake miko mata wani kullin.


“Wannan na farkon a abu mai ruwa ruwa zaki zuba mashi ki tabbata ya sha dayan kuma a karkashin filon da yake kwanciya zaki barbada mai hhhhhhh sai kindawo nan boka mai cika aiki kenan".


“Ki tambayi kawarki kiji ya aiki na yake" cewar bokan


Safiyya ta ce “haka ya ke boka aikin ka kamar yankan wuka"


Zainab ta ce ”Nawa za'a bayar toh boka?"


Sai da yayi wasu surutai sannan ya ce “Aljanu sun ce a basu dubu 250 sannan in...


Read / Download KHADEEJATU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album