Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

SOYAYYAH CE book 1 Complete Hausa Novel Document by SOYAYYAH CE book 1


SOYAYYAH CE book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 9697



SOYAYYAH CE book 1

Reading Time: 0 Hours

Added On: 18, Apr 2024

Author: Abdul Alhaji Musa 10k ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : STRONG PEN WRITERS ASSO

Author Phone : 09077974042

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 58.14 kb

File Type: txt

Views: 341+

Download: 89+

Last download: 3 days ago

Description/Story:  *SOYAYYAH CE*©®2020
*MINI SERIES*
*✍STRONG PEN WRITERS ASSO.🖋🖊*
_aiki da nazari domin farin cikin makaranta(readers)_




*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIN*

MEENAH SERIES
RAEES AND NAJMAH
AWANNI CESA'IN
WAYE SILA

*AND NOW*

*🌹🌸SOYAYYAH CE🌸🌹*


*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Wattpad*
@Abdul10k
*WhatsApp no:*
@09077974042
*Facebook acc*
Abdul Alhaji musa
*YouTube chennal*
Rahama TV



*WANNAN LABARINE WACCE AKA KIRKIRA SO DONT U GUYZ SAY SOMETHING FLUSH*
_MINI SERIES MA'ANA GAJEREN LABARI SO KARKU ZATA LABARINE MAI TSAHO_
_WACCE TASAN KO WANDA YASAN BAZAIYI COMMENT BA DAN ALLAH KARYA KARAN TA_
*LOVE,ROMANCE,SWEETNESS,HAPPYNESS*



*BISMILLAHI DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI,ALLAH INA RAUKON YADDA NA SOMA LAHIYA NA GAMA LAHIYA*



https://www.facebook.com/groups/282175586024233/



*DEDICATED TO MY FANZ ONLY,LOVE YOU ALL*




*EPISODE. 1*




*Imran* *Imran*!!
Haka nake jiyo wata siririyar murya na ambatan sunana......
Yayin da na kasance kwance nake kan shinfuda ta.


Nayi zaton mafarkice amma daga misani sai na tabbatar da cewa wannan muryar daga duniyar tamu ta gaske ce bata mafarki ba......sabida muryan ta kara tsananta..


'Dago hannuna naiyi cikin sauri na dauko filo inda na danna kunnuwa na da ita,niya ta itace ta rage karan wannan kiran.

" *Imraan* wai wace iriyar baccine da kai tun dazu nake ta famar buga maka kofa,ko ka manta jiya kace nazo na tashe ka daga bacci ne..........koda shike bansan inda zaka ba,but kasani 8:30 yanzun......"
"Imraan!!.......Imraan!!"



Jiyo hakan danayi sai na tuno Cewar jiya na umurci kawata data zo ta tasheni da karfe 7:00 na safe....domin yau Monday shine ranata ta farko a university.......

Nanfa saina yunkura na nufi kofar danin nawa,budewa danayi saina tarar da kawartawa tsaye.
Wacce ta kasance makwabciyar mu,amma zumuncin data ginu tsakanin gidajen namu ta zarce ta makwàbtaka.

Sunan ta *Eysha* ta kuma kàsance itace kawata ta fari wacce mukà girma tare ....
Siririyace mai saukin kai ga kumà iyya magana da ladab,a kullum mukan iyya zaman hira har 12na dare,haka zalika takan iya zuwa gidan mu domin ta kwana........

Abin mamaki kuma shine idan nakai mata hira wata rana har bacci ta sace mu, na kuma kwana a dakin ta...hakan bata tabba zama fitina ga familin namu ba...
A kullum idan ummar ta ko abban ta suka ganmu tare sai suce damu "toh y'an kananan masoya kufa sani, idan kuka girmà àka bàku wannan labarin zàkukaryata.......
Kuma idan "Eysha" takai munzalin aure tare za'a aurar daku ga masoyin nata,domin ko kun zàmanto tamkar tif da taya.....






I'm 18 years old.......
Ance yabon kai jahilcin,amma yadda nake jin wasu na yabon kyaun nawan,sai naiyi zaton takai makura....

Santalelen saurayi nake,mai farin idanu da kuma kyaukkyawar d'igon baki na ido...
Gani da kakkaurar gira,da kuma mulmulallen lips....
Fari nake fes,sannan gani da shegiyar murmushi mai daukar hankalin....
Amma kash na kasance mai kunyar tsiya.....

Haka "Eysha" keyimin kirari a kullum,sannan ban taba amincewa ba har sai yau Dana tsaya kallon kaina a mirror......


Bayan na bude sa'in ne ta shigo tace dani....

"Imraan, wai inane zaka, naga tun jiya na tambaye ka kaki ka fadamini......gaka kuma da shegiyar minshari,tunfa 6:40 nake nan".
Sa'in da "Eysha"tazo nan a zancen ta sai na fashe da dariya, sannan na kalli cikin idanun ta nace da ita..

"Mai kike ci na baka na zuba.....aiko idan kika bi a sannu zaki naimo bakin zaren............"

" ah haba dai, har yaushe zan tsaya lalube,nafison naji Abu da d'imidiminsa..........."
Ansar da ta bani kenan niko,ko response babu na juya bàya na soma naiman burosh Dina....

Dauka nayi na rike a hannu sai "Eysha" ta sake cewa.

"Fadamini mana *Prince Imraan*whare are you planing to go,ko ka samo bugun zuciyar kace.....shine ka boye min".
Sa'in data zo nan a zancen ta sai na taka izuwa bayi na soma brush.....banko bata ansa ba"

Nanmah ta biyo ni har bayin ta tsaya kallona sannan kuma ta rike mini tawal......

Bayan na kammala brush sai nà baata ansàr cewa......

"your Highness abin bazata ce,so just be ready for it...."


"Okay, tunda kace hakan shi za'ayi......
.."

Nan muke sai ga umma tashigo da kofin shayi biyu.....Da kuma wainar kwai......
Riskemu tayi a "bedroom" yayin da nke kokarin sanya kayan...(sutura).

Sai tace " good morning,my dear son.........have your breakfast"
Ta furta cikin salon Burgewa.

Murmushi nayi sannan na nace da ita

"Morning dear mah......actually I can eat now cuz I'm late......"



"What!!,late.......okay .just ka kurbi ruwan d'umin ta rike maka ciki."
Umman tawa ce tayi wannan batu..yayin da take mika mini cup din.


Ansar kofin shayin nayi na rike a hannu na kuma taka izuwa bakin get inda suke biye dani.....
Sannan "Eysha"ta anshi dayar kofin...


"Mom uhm saina dawo" haka na furta cikin hanzari
Sannan kuma na mika Mata kofin...

"Eysha" ko tace dani
"Take care dear.........".
Dan gajeren murmushi nayi sannan nace da ita..ki kula da kanki kema......


Nan na fice daga gidan nahau "adaidaita" (keke napep)......nayi hanyar school din.


Sauka nayi cikin school din 8:50shep ida nasoma sauri.....sannan kuma rike nake da littattafai na a Hannu.....

Iso wani gini nayi inda na tambayi wasu yan mata biyu Cewar....

"Dan Allah friends *pure chemistry department* ......"

"Hayewa upstairs zakai xuwa thirt floor,sai kabi Dama...."
Haka _yan matan suka bani ansa cikin hadin baki..

Niko nai musu godiya na wuce,inda na karasa hold din da sauri.....
Wajen shiga ko nayi karo da wata santaleliyar yarinya.
Wacce take rike da kwalbar acid a hannu........

A yayin wannan karo kuwa dukkan takardu dake hannu na suka zube.
Itako hannun ta ya subuce kawai naji ruwan acid ya wiyan hanuna ..

Kwarma bagidajiyar ihu nayi,danko naji kamar yashe naman wajen wannan ruwan yayi.



Abinka da mai tausayi,itama ko ta zabga ihu,inda mutanen cikin ajin Suka foto cikin sauri zagamu sukayi....
Inda suka somamin fifita,itako ta naimi a kawo *emergency box*.


*30 MINUTE LATER*

zaune nake *rest bench*Ina kuma rike da waya ta a hannu,ina famar danne Danne......

Sai ga wannan yarinyar ta kawo mana *coffee* kofi biyu....
Daman tare muke a gurin amma ta tashi domin da naimo mana abinda zamu dan sarka a ciki.....

Zuwan ta tace dani..
"Yah hannun,da fatan ya daina radadi?".

"Ehmm banace a'a ba domin nadanji sauki.....".
Haka na nata ansa..


Sannan ta sake cewa.....
"Allah karo sauki......yasa kaffara ne."

"Amin"..

"Firstly I'm *Qudsiyyah*but idan sunan tai maka tsaho zaka iyya kirana "qudsy"
Haka ta furta yayin da ta mika mini nannu.....

Dago hannun nawa mai bandej na mika
Sannan nace da ita...

"Imraan....suna Nawa....Sabon dalubi a nan.

Dajiyo haka sai ta murmusa tace

"Be careful,karka sake gurje ciwon......"
Sannan ta sake da cewar
"Will you be my friend".



Nanfa na murmusa sannan nace
"alright no problem....

Duk wannan batun da mukayi hannun mu narike da juna....
Shiru mukayi sannan kuma babu wanda ya saki hannun dayan sa.

Karan gyaran murya na jiyo nan da nan sai muka sake Hannun.......
Dago kai nayi na dubi maishi


Nan na sake arba da wani sabon fuskar
Wacce a hannun sa littattafai nane baki daya......
nan yaja kujera daya ya zauna sannan ya jibge takardun gabanmu yace damu......

"It seems kun fahimci juna sosai,ah toh dai tunda bakuyi invite dina ba shine nazo da kaina...


Murmushi nayi sannan na tsunkwi daka,itako tace dashi...

"Oops aiko bamusan kana nan......But sorry".

Murmushi yayi sannan yace
"Ehmm never mind,ina ganin abokin namu na kunyar bako ko.......toh bari na gabatar da kaina..
sunana *Hussein*duk department daya muke,kunga KO zamuyi abotar mu cikin ruwan sanyi".

Dajin haka ko nayi murmushi sannan na dago Kai na kare musu kallo...

Sannan nace dashi

"I'm *Imraan*......"

Nan saina jiyo muryar *Qudsiyyah* nacewa

"*I'm qudsiyyah* nice to meet you guys...."
*we are now friends,kai I'm so happy*

*Nan fa dukkan mu muka murmusa*




Ahaka rayuwa ta,ta kasance a ranar farko na a university....
A gaskiya nayi farin ciki sosai domin *qudsy* da *_Hussein* sune friends dina bayan *Eysha*.
Dukda cewar yaune haduwaur mu sai mukai sharing numbers.



*4:00shep na dawo gida* bayan mun fito daga lectures...
Inda na shigo gidan cikin raha na kuma tadda abbana a falo yana cin abinci...
Shigata ya kirawo ni sannan yace Dani

"Dannan shine ka wuce dazu baka sanar dani ba.....

Kafin nace ub'ban sai na jiyo ummah ta bashi ansar cewa

"Aiko cikin rushing ya wuce,sai dama ya wuce na tuno cewar kanada *Ba'bir*....dako sai ka ajeshi yayin da zaka aikin.....".

Furta hakan tayi yayin da take kokarin zaunawa a,gefen mu.


"Oh Mom you don't have to worry...nayi manage a *adaidaita*"

Nanko abban nawa yace...

"Okay yayi kyau...ya makarantar take ya kaga wurin,da fatan babu Matsala"

"Oh babu matsala komi na tafiya daidai..
ansar Dana bashi kenan sai yace dani

"Ok wanke hannun ka muci abinci"......

Ansa masa nayi da toh Abba saina saka hannun nawa cikin ruwa nanfa umman tawa. ta hankalci hannun nawa taga an daure da bendej.

.

Nako ta zuro idanu ta Kira sunana cikin muryar tsoro.... ..

"Imraan...yana ga hannun ka da bandej?.....

Nako na basu labarin komi,babu abin da na boye.sannan na kuma basu labarin *sabbin abokanayen nawa
Nan tayi farin ciki da jin wannan batu sai tace dani.

"Okay next time,kayi taka tsantsan da *acid*
Danko bazan iyya ganin ka cikin mawiyacin hali ba.........
Zuciya ta zatayi bindiga....."

Niko na mayar mata da martani
..
"Oh mom,daina fadar haka. ..I will more careful next time.

Nan abba na yayi murmushi sannan yace da ni.
"Yah kamata kam kayi taka tsantsan da *acid da sauran kayakin lap masu cutarwa*".


"Okay dad...


Haka muka ci abinci sannan na yini yina chatting da *Hussein da kuma qudsy*
Domin duba WhatsApp dina danayi sai naga an sako ni...


Read / Download SOYAYYAH CE book 1

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album