Join Our WhatsApp Group

A BARI YA HUCE Complete Hausa Novel Document by A BARI YA HUCE


A BARI YA HUCE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 25105



A BARI YA HUCE

Reading Time: 2 Hours

Added On: 05, Dec 2023

Author: Sumayya Abdulkadir Takori ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07030137870

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 128.7 kb

File Type: txt

Views: 1302+

Download: 479+

Last download: 1 day ago

Description/Story:




FATAN ALHERI

Fatan ALHERIN littafin na sabon jaririn dana Haifa ne, AHMAD AL- KHAZRAJY.









TUKUICI
Tukuicin littafin na mai sunan Mamin mu ne, AMINAH SHEIKH AL-FATIH (Leena).









A BARI YA HUCE...

1










Littafin


SUMAYYAH ABDULKADIR takori88@yahoo.com
Hakkin Mallaka; Takori
Copy write; Takori


Shekarar Rubutu; 2012


GARGADI
Juya littafin ta kowacce hanya ko sake bugawa (reprinting) ba tare da izni ba abin tuhuma ne daga Lauya na Barrister Abdurrahman Yunusa ESK. idan kunne ya ji……!

GODIYA
Godiya ta mussamman ga aminiyata Haj. Zainab M. Ahmed Sultan Road, Kano. Banida abinda zan biyaki face addu’ar nan da kullum nake mana. Allah ya raya Mukhlis, Muhsin, Muslim, Munifa da auta Hanifa.


GORO
Goro ne ga Hadiza Umar Dogon-Daji (Mrs. Jelani Aliyu) Michigan, USA. Allah ya raya mana Amira, Mubarak da Asma’ul Husna.

KUNA RAINA
Hajiya Zulaiha Zubair (Zulai), Mrs. Tafida Ahmad-Khazrajy ya gode. Tareda ‘yar uwarki Haj. Zuwaira Ahmad Rufa’I (Mrs. Engineer Baffa Sayyadi) Marubuciyar littafin Sanadin Kaddara.

DOMIN KI
Littafin ba zai manta dake ba, da kuma dimbin kaunar da kike yiwa mai shi, Haj. Habiba Umar, Ireland, UK…out of sight.. is neber out of mind!


TUNA BAYA …….!
Wai Takori tace Tuna Baya Shine Roko;
Mariya Usman Sarki
Zuhra Amin Nasir Galadanchi
Nafisah Ahmad Muhammad
Sadiya Ahmad Muhammad
Allah ya taimaki malaman Galadanchi, Allah ya taimaki ZUBAIRIYYAH ISLAMIYYAH!

















ASSALAMU ALAIKUM
Masoyan TAKORI, sallama a gareku. Yaya gida, maigida, karatu da harkoki? Dafatan ALHERI, domin ALHERIN nake nufinmu dashi bakidaya, shiyasa nake yin rubutun.
Masu rubuto ‘tedt’ Takori bata (replying), masu bugo waya Takori bata dauka ba, masu rubuto sako ta ‘facebook inbod’ Takori bata bada amsa ba, da masu aiko ‘friendship rekuest’ Takori batayi ‘accepting’ ba.
Gabadaya sai in hada inyi muku jimillah, in baku hakuri in taushi zuciyarku, sabida al’amarin ne yafi karfi na, ya kuma shallake tunaninku. In kun duba karancin lokacin da ake fama dashi a yanzu zaku yi min uzri. Sannan rubutun ba sana’a ta bace. Har yanzu ni Daliba ce. Ga RAINO ga sauran al’amura da suka sha gabansa. Masu kiran waya kuma in ban dauka ba a zazzageni sai ince kada ku zargeni, tunda nace (tedt only). “Ai karya take bata da wani ‘hearing problem’ don kar a dameta ne kawai” wata kuma tace “kedai kawai ki fadi gaskiya, bakya daukar wayar da bata ‘yan uwanki, kawayenki da wadanda kika sani ba” da sauran su. Kalilan ne, kuma masu hankalin ke cewa “Allah ya yaye miki TAKORI”.

To masu yimin wannan addu’ar, nima ina yi muku addu’ar Allah ya biya muku bukatunku na ALHERI. Duk masoyana ina sane daku, koda kuwa ace sau daya ne muka taba gaisawa. Musamman Sokkotawa, ‘yan Gusau da Katsinawa. Wallahi duk ina sane daku, kuma ban mance da sunan kowa ba.
Ga masu cewa wai bani na rubuta littafin ALKAWARI BAYAN RAI ba, sabida yayi (short) kuma salon sa da tsarinsa ya banbanta dana sauran littattafan TAKORI, da yawama kai tsaye sun ce bai yi musu dadi ba, to sai ince “halin rubutun kenan”. Amma ni na rubuta shi. Saidai ba lallai ne kullum marubuci yayiwa makaranci yadda yake so ba. Yadda rubutun yazo masa haka yake rubuta shi. Ba tareda tunanin zai yiwa makaranci dadi ba ko a’ah?
Ga masu cewa sunan littafin bai dace da labarin ba, abinda nake nufi anan shine; Allah ya riga yayi ALKAWARIN Lanto zata auri Mu’azzam a BAYAN RAN Sageer.

Wassalamu alaikum
Maman Safah da Marwah ce…….!










A BARI YA HUCE...-1
G
urin-gawa karamin kauye ne mai tsohon tarihi da ya kunshi al'umma masu sana'o'i daban-daban, amma duka tushensu daya. Galiban malamai ne da manoma, kuma kauye ne da manyan malaman da a halin yanzun suka barwa duniya abin da ba za a mance da su ba suka fito. Gurin Gawa na nan cikin karamar hukumar Kumbotso, yankin Fanshekara ta jihar Kano. Karamin kauye ne, wanda ya samu tallafin gwamnati ta hanyar wutar lantarki, ruwan sha mai tsabta, da takin zamani, wanda ke taimaka musu kwarai wajen bunkasa harkar nomansu.

Akwai sanannen hadin kai tsakanin al'ummar garin mazansu da matansu. Sai dai kuma babu titi mai kyau a Gurin-Gawa. Idan mota ce zata shiga kauyen sai ta yi futuk da kura, mutanen cikinta sun gwaggwara kawunansu sabida rashin kyawun birjin.
Duk da haka wannan bai hana al'ummar cikinta jin dadin zamanta ba, motar haya ba ta shiga cikin kauyen, sai dai ta aje ka a titin ka hau achaba ko bayan akori-kurar Rake ta mutanen garin ka karasa ciki. Don haka da wuya ka ga mutanen birni na shiga kauyen, don a ganinsu ba su ga mai zasu tsinto cikin wannan kalataccen kauyen ba.
Samarin garin Gurin-Gawa kan fita cikin Fanshekara da wajenta domin neman kwabo, ta hanyar ga-ruwa, sayar da rake, dukanci, dako da sauransu. Don kalilan ne suka damu da makaranta wadda dama idan dai ta boko ce, to ba a zancenta cikin garin Gurin-Gawa. Makarantun allo da na Buzu su ne Allah Yai yawa da su a garin.

Malam Bedi, yana daya daga cikin dattawan garin Gurin Gawa, haifaffen nan ne iyayensa da kakanninsa. Sana'arsa shi ne noma, yana da gonar rake da gyada, sannan yana nome dankalin Hausa, makani da gurjiya.
Bedi da matarsa Hure, fulanin Gurin-Gawa ne na usul. Mutanen kwarai ne da duk Gurin Gawa ba wanda bai sansu ba, tare da yi musu kyakkyawar shaida. Babban dansu shi ne Habibu, wanda tun yana karami Malam Bedi ya dankawa kaninsa mai bi masa a haihuwa ya ke taya shi sana'ar fataucin goron da yake yi daga Shagamu zuwa Kano, wanda daga baya shi Habibu ya shiga makarantar horas da malamai (SAS) tun daga wancan lokacin kuwa ya koma Kano kwata-kwata. Shi da Gurin-Gawa sai dai yazo da yawo idan ya zo gaida mahaifansa wanda yakan dauki dogon lokaci bai yi hakan ba.
Su ma su Malam Habibu ba su wani damu da shi ba, don ba wata cikakkiyar shakuwa ce a tsakaninsu ba. Duk wani burinsu na duniya yana kan 'yar autarsu “MAIRO”, wadda ba su samu ba sai bayan shekaru sha takwas da haihuwar Habibu. Don haka idan ya zo a tura mai kujera ya zauna, ana lale da shi, idan bai zo ba ma falillahil hamdu.

Inna Hure ce duke tana faman firfita wutar iccenta, domin ta samu ta kammala abincin rana kamin Malam Bedi ya dawo daga gona. Idanunta sun yi jawur sai zuba suke, ga dukkan alamu irin azababben itacen nan ne Allah Ya hadata da shi. A gefe 'yar lelen ce zaune bisa tabarma tana dandasawa 'yar bebin karanta kwalliyar juma'a da wani tsalelen yankin yadin mamar-mamar da ta tsinto a shagon tela. Ta daga 'yar bebin tana cillawa tana cafewa tana wakarta cikin nishadi, ga dukkan alamu babu yarinyar da ke cikin farin ciki a gidansu a gaba dayan kauyen Gurin Gawa kamarta, sabida daurin gindin sangarta da cikakken gata da ta ke samu daga Innarta.

"Ke kam 'yar gata ce, Ta-Ummule.
Ni uwarki “MAIRO” na tsaya miki.
A taba ki a tabo bala'i,
A duke ki, in rama miki.
Innata ta tsaya min,
Ni kuma na tsaya miki........"

Sallamar Habibu ce ta katse ta daga wakar da ta ke rerawa 'yar bebinta, cikin zazzakar muryarta kamar gyare. Ta yi cilli da Ta-ummulen ta kwasa da gudu ta makalkale shi, tana cewa,

"Yaya Habibu oyoyo!"

Ya ce "Ke da Allah kazamar banza, cika ni, dubi bakinki damale-damale da busasshen koko, hanci duk busasshiyar majina, sannan kalli hannunki duk bakin tukunya, kin zo kin goge su duka a jikina. Wallahi duk sanda na doso garin nan cikin fargabar cakumon da zaki yi min da kazantarki nake, shashashar banza an girma ba a san an girma ba".
Ya rabata da jikinsa ta karfi, ita ko ko a jikinta, dariya ma ta ke abinta kamar ba da ita yake ba. Inna Hure ta cika fam, kiris ta ke jira ta sauke mishi kwandon bala'in da ke cike taf a bakinta, sabida wannan tijara da yake yiwa autarta.
A ganinta Habibu ya tsani Mairo ne kawai, don shi yana birni, ita tana kauye, duk da matsananciyar kaunar da Mairon ke masa. Babu ranar Allah da zata fito ta fadi, Mairo ba ta ambaci sunan Yaya Habibu ba. Shi kuma da zarar ya zo irin tarbar da yake yi mata ke nan, ita kuwa kamar dada tunzura ta yake ta yi masa oyoyon, da dukkan zuciyarta.

Ya matsa gaban Innar ya kai gwiwoyinsa kasa, ya ce
"Inna barkanku da gida, mun wuni lafiya?"
Ba ta juyo daga fifita wutarta ba, haka ba ta kalle shi ba, ta ce "Lafiya kalau". Cikin danne bacin ranta.
Ya yi shiru cikin zargin kansa. Ya san tabbas ya tabo Innar, don ta sha ce masa idan ba zai daina kyarar mata auta ba, to ya daina zuwa, babu dole.
Cikin kasada ya ce "Amma Inna ga wannan katuwar yarinyar ki zauna kina hura wuta, ita tana wakar 'yar bebi? Duk wani dan arziki kamarta ai yanzu ya dawo ne daga makaranta, yana haramar tafiya islamiyya, amma ban da wannan, ban da karare ba ta san komai ba, shi yasa duk wasu abubuwa na yara masu hankali, ba ta san shi ba............"
A fusace ta juyo ta zuba masa jajayen idanunta, ta ce "Kai saurara. Wai me ye gaminka da yarinyar nan ne? Me ta tare maka? In don oyoyon da ta ke yi maka ne ba ka so, zan hanata, amma wannan sababin da kake yi mata ya ishe ni. Ka zo gidan su ka uzzireta babu gaira babu sabar? Ba ta zuwa makarantar, idan kai ka haife ta sai ka dauketa ka kai ta".
Ya sunkuyar da kai ya ce, "Allah Ya ba ku hakuri Inna, Inna Allah Ya huci zuciyarku".
Ta ja tsaki, "Tsuuuu!" Ta ci gaba da aikinta tana ta sababi, shi kuma bai kara tofawa ba, bai kuma tashi daga durkuson shi ba. Malam Bedi ya yi sallama ya shigo, rataye da fartanyarsa da alama a gajiye ya ke likis, sai gumi ke disa daga wuya da goshinsa. Yana ganin Habibu sai ya fadada far'arsa, amma jin Inna Hure na ta sababi sai ya maida fuskarsa ya dinke. Ya dade yana sauraronta ba ta san ma ya shigo ba, tana ta fadan idan Habibu ba zai daina tsangwamar mata Mairo ba, to ya daina zuwa, don ba ita ta kirawo shi ba.
Malam Bedi ya yi gyaran murya, sai a nan tasan da tsayuwarsa. Ta ce "Ai gara da ka zo, dama binka zan yi yanzun, ka ja wa yaron nan kunne ya sakar wa diyata mara ta yi fitsari, tunda ba a gidansu ta ke zaune ba, balle ya ji kunya don an ce kanwarsa ce".

Malam Bedi ya ce, "Anya Hure? Kina kyautawa abin da kike yi wa Habibu? Ina laifinsa don ya zo gaishe ki? Wannan yarinya da kike ta tada jijiyar wuya akan an gaya mata gaskiya, wane ne majibincin al'amarin ta nan gaba a bayan mu? Wannan din dai da kike cewa ya fita harkarta shi ne ba wani ba. To idan ya fita harkar tata ranar da babu mu, wane ne zai shiga?
Shin ma me ya yi mata da zafi? Don kurum ya ce ta dinga wanka? To ki yi hakuri, Habibu ya daina cewa 'yar ki ta yi wanka, don Allah ta shekara ba ta yi ba. Kai taso mu tafi masallaci kar mu rasa jam'i".
Ai jin haka ta yi daki da gudu ta yayibo mayafinta da takalmin robarta, a gujen ta sake fitowa, "Yaya Habibu ni ma zani masallacin, dama tun jiya ban yi sallah ba".
Wani takaici ne ya sake kama shi, ya hadiye ya ce, "To mu je, amma sai ki tsaya a wajen masallacin daga gindin bishiya kina bin jam'in, don mata ba sa zuwa masallacin maza".
Ta ce "To idan mun fito zaka rakani mu je mu tsinko wa Inna tsamiyar kunu? Dama Rabe shi yake dora ni, kai kuwa ka ma fishi tsawo".
Ya kama baki, "Yanzu Mairo bishiyar tsamiya kike hawa?"
Cikin son ta burge shi, da alfaharin hakan sosai a kwayar idonta, ta ce
"Mu hau tsamiya mu sauko, mu hau magarya, mu hau dinya, mu tsallaka goba. Rannan Lanto ta fado tim! Ta karya kashin baya, ni kuwa idan na makale a jikin reshen bishiya kamar 'yar Birrai nake. Bana fadowa, sai dai in ciko bujena da goba da tsamiya........."
Ya yi gaba ya rabu da ita don takaicinta kamar ya amayo zuciyarsa, amma sai ya yi tunanin to ita me ye laifinta? Innarta ce ta daure mata gindi.

Habibu saurayi ne dan kimanin shekaru ashirin da biyar. Ya kammala kwalejin horas da malamai ta Kano, wato (SAS), yana jiran sakamako ne ya wuce babbar makaranta, kodayake ma abin da ya kawo shi Gurin-Gawa kenan yanzun, wanda yake son su tattauna da mahaifinsa.

Alhaji Abbas Mai goro kanin Malam Bedi ne ciki daya, uwa daya uba daya, shi ke rike da Habibu da hidimar karatunshi, ko da yake morar juna suke tunda kuwa duk wahalar kasuwancinsa na goro, a wuyan Habibun ta ke, wadda ya ke gudanarwa idan ya dawo daga makaranta da ranakun karshen mako.
Suna zaune a unguwar Yakasai a cikin birnin Kano. Yana da matan aure biyu da 'ya'ya bila adadin maza da mata. Saidai ‘ya’yanshi kanana ne da ake haifa akan idon Habibu. Cikinsu duka babu mai shekaru goma. Babbar diyarshi Ladidi sa’ar mairo ce. Don haka Habibu tamkar wani jigo ne ga iyalin Alh. Abbas wanda duk suke kauna sabida zumuncinsa da rikon amana.
A rayuwar Alh. Abbas bai taba ganin yaro mai kwazon neman na kai da amana irin Habibu ba. Tunda ya ke tare da shi, kwandala wannan bata taba bata cikin lissafinsa ba, kimanin shekaru ashirin ke nan. Watau tun Habibun yana dan shekara biyar. Wannan ne dalilin da ya sa ya maida Habibu dan cikinsa ba Dan dan uwansa ba.
Taimako dai-dai gwargwado Alh. Abbas na yi ma yayan shi Malam Bedi, kamar ta samar mai ingantaccen takin zamani, da taimaka mai da motocin noma a yayin girbi, wadanda yake dauko masa haya daga KNARDA.
Bayan wannan sallah da azumi shi ne sutturarsu, haka ta fannin abinci lokacin azumi, tun daga kan sukari, lipton, madara, da su taliya ba abin da ba ya taso Habibu ya kawo musu, sai dai idan suna nomansa a nan Gurin-Gawa.
Zumunci ne mai karfi a tsakaninsu, wanda iyayensu suka dora su a kai, har gida Alh. Abbas ya sayawa Mal. Bedi a Yakasai ya ce ya dawo su zauna tare, inda shi kuma ya ce shi da rabuwa da Gurin-Gawa sai dai mutuwarsa. Ko ita ba ya fatan a fitar da gawarsa daga Gurin-Gawa, su je can su tsinci abin da suke tsinta a birnin, shi kam a gareshi kwanciyar hankali shi ne komai.

To amma wannan zumunci na mazan ne banda matan. Babu shiri ko kadan tsakanin Inna Hure da matan Alh. Abbas wato Habiba da Hajara. Tun sanda daya daga cikinsu ta taba cewa a bata Mairo ta dinga taimaka mata hidimar ‘ya’yanta ta kulla gaba da su. Ta ce kuma wadda duk ta kara tako mata gida, Allah Ya isa. Ta rasa dalilin da 'yar tata...


Read / Download A BARI YA HUCE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

4 Comments On A BARI YA HUCE
avatar
fatimah-1

5 months ago

Reply

Pls book 2

avatar
shuraih99

5 months ago

Reply

Replying to fatimah-1

Tuntubi nambar nan 07030137870

avatar
hajara-muhammad

5 months ago

Reply

An interesting Novel

avatar
hajara-muhammad

5 months ago

Reply

An interesting Novel

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album