Join Our WhatsApp Group

MAIMOON Complete Hausa Novel Document by MAIMOON


MAIMOON

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 263219



MAIMOON

Reading Time: 21 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Maman Mama ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.29 mb

File Type: txt

Views: 1354+

Download: 1804+

Last download: 18 minutes ago

Description/Story: Compiled By Umar Dalha Funtua
MAIMOON
By
Maman Maama

Bismillahir Rahmanir Rahim


Episode One : The Beginning of the Beginning

Shin ta ina zan fara ne, in fara ta haduwa ta da Ibrahim ne ko kuma ta haduwa ta da Sultan? Ko kuma in fara da baku tarihi na ni kaina?
Sunana Maimuna Muhammad Dikko. An haifeni kuma na tashi garin Abuja, Nigeria. Mahaifina Alhaji Muhammad Dikko bafulatanin garin 'yalleman ne dake jahar Jigawa. Garin 'yalleman garin Fulani ne kyawawan gaske wadanda kuma Allah yayi musu arziki sosai har suka watsu a duk fadin Nigeria, musamman garin Lagos da port hercourt tunda yawancin arzikin su na chanjin kudi ne. Mahaifina bai bi family tradition ba saboda shi ya kasance dan boko ne. Yayi primary school dinsa a nan garin 'yalleman tamkar sauran 'yan uwansa amma saboda hazakarsa sai head master dinsu ya bawa mahaifinsa Alh Lawan Dikko shawarar in dai da hali gwara a tura shi kasar waje Dan ya fi samun karatu mai kyau.
Da yake kakan mu mai hali ne tun a wancan lokacin, sai ya tattara makuden kudade ya dauko yaro ya tafi dashi Lagos, da taimakon 'yan uwansu da suke can aka samar wa Muhammad biza zuwa England inda a can ne aka samar masa admission a makarantar Gifted International College inda ya fara karatunsa na secondary school.Duk bayan shekara ake basu hutun session, Muhammad yakan zo Nigeria ya ga iyayensa da 'yanuwansa ya koma, shi kuma Alh Lawan duk sanda Muhammad zai koma sai ya hada kudade masu yawa ya bashi saboda harkar registration da kuma bukatunsa na yau da kullum. Mahaifiyar Muhammad ma Hajiya Adama ba'a barta a baya ba domin tana iya kacin kokarinta dan har shanun ta na gado take sawa a sayar mata a boye bada sanin mai gidanta ba ta tattara kudi ta bawa Muhammad.
Kwanci tashi har Allah yasa ya gama sec sch dinsa kuma a take ya samu scholarship na karatu a Oxford University inda ya karanci business administration saboda burinsa na ganin ya gama karatu ya dawo gida yana taimakawa mahaifinsa a harkar kasuwancinsa. Daga lokacin ne ya gayawa mahaifansa cewa babu zancen biyan kudin makaranta kuma tunda yanzu he is on scholarship, amma duk da haka Alh Lawan yakan aika masa da kudade dan ya biya bukatunsa. A lokacin da ya gama first degree dinsa ne ya dawo gida da niyyar cika burinsa na karbar garkar business din mahaifinsa amma hakan bai samu ba saboda rigimar data barke a familyn su inda kishiyar mamansa wacce ake kira da Hajja tayi tsalle ta dire tace sam ba zata sabu ba bindiga a ruwa. A cewar ta duk wahalar da aka sha da makudan kudaden da aka kashe akan karatunsa sannan ya dawo kuma yace zai karbi dukiyar gida? Ta kara da cewa" inace cewa a kayi shi mai kwakwalwa ne ba zai yi kasuwanci ba karatu zai yi, sai da aka gama kashe kudi a karatun nasa sannan kuma zai zo yace zai yi kasuwancin to ba'a isa ba wallahi, suma sauran yaran gidan ai 'ya'yane".
Da wannan Muhammad ya tattara ya koma England ya dora karatun masters dinsa, yana gamawa ya wuce pH D. Bayan ya gama ne kuma ya karbi aikin lecturing a makarantar. Shekarunsa biyar yana lecturing a Oxford aka bashi award na professorship. A shekarar ne kuma mahaifansa suka dage akan lallai ya dawo Nigeria yayi settling down kaman sauran 'yan uwansa. Saboda gogewarsa a harkar ilimin kasuwanci da mu'amala da kasashen waje yasa yana dawowa Nigeria government din wancan lokacin ta bashi mukamin ambassador. Kasar da aka fara turashi itace makociyar mu, Niger.

Wannan kenan;
Mahaifiyata Hajiya Fatima wadda ake kira da Bintou, buzuwa ce ta asali, mutuniyar kasar Niger ce. Mahaifinta ya rasu run tana yarinya kuma dama it's kadai Allah ya bawa mahaifanta. Mahaifiyarta wacce sunanta aka saka min (Maimoon) ita ce ke kula da ita da karatunta har ta kammala sec sch dinta. Anan suka fara chuku chukun turo ta Nigeria dan tayi jamia anan amma saboda rashin hanya da rashin abun hannu sai abun ya gagara. A nan ne Allah ya hada su da mahaifina lokacin yana matsayin ambassador na Nigeria a Niger. Farko tausayinta ya fara ji da sha'awar yadda take da son karatu, daga baya kuma sai soyayya ta fara shiga tsakanin su duk ya cewa ya girme mata sosai. Dama kuma a lokacin Inna (haj. Adama) ta takura masa akan maganar aure dan haka bai samu matsala ba akayi aure ya taho da ita Nigeria ya ajiye ta a gidanmu dake Abuja unguwar Aso drive inda har yau anan muke da zama.


Episode Two: Meet my Family

Gidan mu katon gida ne saboda sanda daddy ya gina shi yayi niyyar dauko iyayensa ya dawo dasu Abuja amma Baffa (Alh Lawan) yace sam shi bazai bar 'yalleman ba, wannan ya saka daddy ya tsantsara musu gida a can wanda duk da kudin da 'yan garin suke ji dashi sai da gidan ya zama abin kallo. Sannan ya kawo ma'aikata ya zuba musu tundaga kan masu shara har zuwa kuku. Saboda yace lokaci yayi suma da zasu huta, kuma duk abinda yayi inna sai yayi wa Hajja. Ai kuwa suna hutawar dan babu abinda suke yi illa su ci su koshi su kwanta, kuma duk shekara sai sunje aikin hajji, sannan al'adar daddy ce duk sanda aka turashi wata kasa a matsayin ambassador sai ya debe mu munje munyi wata daya har su Baffa da Inna saboda yana so mu samu wayewa irin ta zamani amma yace ba zamu rayu a can ba saboda tarbiyya.
Mu biyar Allah ya bawa mahaifanmu, uku maza; ya Lawan, ya Habeeb sai Faruk, biyu mata; Hafsat da Ni. Ya Lawan ne babba sai ya Habeeb, sai Hafsat sannan Ni sai dan autan mu Faruk. Da yake mommy kwanika tayi sai ya zama babu tazara sosai a tsakanin mu, dukkan mu a shekaru bakwai ta haifemu sai kuma haihuwar ta tsaya mata, daddy kuma yace mun ishe shi fatan shi Allah yayi mana albarka. Zo gidan mu kaga kyau, saboda mix ne aka samu na Fulani da Buzaye, dan haka in ka ganmu sai ka kasa tantance wanne kabila ne mu, tundaga ma zan mu har matan mu haka muke dan sauda yawa inna takan aiko mana da rubutu tace maganin baki.
Ni maimunatu wadda ake kira da maimoon kamar yadda ake kiran wacce aka saka min sunanta wato maternal grandmother dina, nice ta hudu a gidan mu, nice kuma auta a mata. Fara ce ni tas, fatata mai sheki silkin Fulani da Buzaye, ina da tsaho amma ba sosai ba, fuskata oval shape ce mai dauke da dara-daran idanu kwantattu masu yalwataccen eye lashes, girata kamar an zana ki min ita. Hancina dai-dai misali, lips dina sirara masu kalar pink mai haske, gashin kaina mai cikane kuma mai tsaho, Wanda yazo har kan kafadu na. Ina da dimples a both chicks dina masu lotsawa koda magana nakeyi ballantana kuma ace nayi murmushi.
A gidan mu muna magana da daddy n mu da fulfulde, mommy da buzanci, sannan a tsakanin mu muna magana da English, a school ma English dinne dan haka sai kuma tashi babu Hausa sosai sai dai muji a gurin neighbours ko kuma in munyi 'yan aiki hausawa.
Duk a cikin 'yan'uwana na fisu surutu dan ya Walid parrot yake ce min tun ina yarinya, da yake shi ba mai son magana bane, kullum sai yayi ta korata yana cemin parrot, ni kuwa duk abinda na gani sai na tambaya, in ba'a bani amsa bama in yi ta tambayar har sai an bani amsa sai in sake tambayar wani abun daban. Tun sanda na shiga kindergarten daddy ya fahimci duk cikin 'ya'yansa nafi daukan kwakwalwarsa duk da suma sauran ba baya bane wajen karatu. Tun daga lokacin sai yake biyemin inyi tayi tambayoyi yana amsamin har ya zamanto mun shaku sosai fiye da yadda muka shaku da mommy. Mommy n mu wacce a yanzu lawyer ce takance ko ita zan gada ne in zama lawyer saboda yawan tambayoyi na.
Ina shiga basic school na zama tauraruwa, ga kyau, ga kokari, ga surutu mai shiga rai. Sai ya zama kowa yana ji dani a school din. Bani da fada sam- sam, kuma ina da tsoro, ko juniors dina nayi wa wani abu by mistake sai in basu hakuri saboda ina bala'in lallaba jikina. A basic school na samu nickname din MOON saboda shape din fuskata da bright dimpled smile dina, ga kuma yanayin sunana MAIMOON. Wasa wasa sunana har ya fara bata in ba'a register din makaranta ba. Moon kowa yake kira na dashi.

Kasancewar mommy n mu ita kadai ce a gurin mahaifiyarta (daada) yasa ta dauko ta ta dawo da ita Nigeria cikin gidan mu, akayi mata part dinta a kusa da part din su inna, mu kuma sai ya zamanto bamu da gurin hira sai gurinta tunda Allah bai bata haihuwa da yawa ba sai kuma ya dora mata son mu. Kullum tana cikin kula damu, kunshi da kitso a kan mu ni da Hafsat baya tsufa sai an sake wani, duk da muna da gashi amma kullum kanmu a kitse yake ganin sha'awa.


Episode Three: Loved by All

Shekara daya Hafsat ta bani don haka aji daya ta fini da shi amma ka ganmu sa ka dauka ta bani shekaru da masu yawa saboda ni Allah yayi min karamin jiki, babu tsaho babu kiba sai dan karan surutu, ita kuma Hafsat bata da magana sosai amma akwai sa ido da bin kwakwkwafi, don haka duk abinda nayi tana gani na kuma muna zuwa gida zata gayawa mommy ko daada, inda ita kuma mommy zata hauni da fada, da yake mommy n mu tana da zafi, wannan shi yake kawo yawan sabani a tsakani na da Hafsat. Babban aboki na shine ya Habeeb wanda surutun mu da son karatun mu yazo daya dashi, kullum in mun dawo daga school ina dakinsa, idan an bamu homework shi yake koyamin, shi yake kawomin novels wani lokacin ma in kwanta a cinyarsa yana karanta min. Faruk kuwa dan auta kullum yana gurin daada dan a can ma dakinsa yake in ka ganshi a part din mu to daddy ne yazo gari.
Ina basic 4 Hafsat ta na 5 muka zana common entrance a tare kuma duk mukaci. Babu yadda mommy ba tayi ba akan daddy ya fita damu waje muyi karatu yaki, yace tarbiya tana da wahala a kasashen waje ko da kuwa kasashen larabawa ne, musamman tarbiyyar 'ya'ya mata. Yayi believing cewa makarantun kasarmu a good enough.
Ba tare da bata lokaci ba aka sakamu a secondary school tare da Hafsat, wannan ba karamin bata ma Hafsat rai yayi ba dan ranar har kuka tayi su daddy na yi mata dariya wai zatayi set daya da kanwarta. Ni kuwa sai na bata hakuri na yi mata alkhawarin idan anzo promotional exam zan ki yin kokari yadda za'ayi mini repeating ita kuma ta wuce. Mommy ba karamin takaicin tafiyar mu tayi ba musamman ma da yake boarding school ce, ana gone zamu tafi na ganta a kitchen tana kuka tana soya mana miyar tankwa, anan na tsareta da tambayoyi taki kulani balle ta bani amsa sai daga bata ta jawoni ta rungume tana ci gaba da kukan ta.
Ranar tafiyar mu kuwa mommy cewa tayi ba zata rakamu ba amma da muna zo tafiya da kyar daddy da daada suka banbare mu daga jikinta dan cewa tayi mun fasa karatun, Daddy kuwa sai dariya yake yi mata, ni kuwa zuciya ta fes ina ta murna abinda. A lokacin shekarata goma amma in ka ganni zakayi tunanin banfi shekara bakwai ba.
Ana kaimu makaranta akayi admitting din mu, Daddy ya roki principal din mu cewa ta bamu daki daya ni da Hafsat saboda yana son Hafsat ta rinka kula dani. Haka kuwa akayi, aka bamu daki daya, gado daya, ni ina sama ita tana kasa, class din mu ma daya, seat dina yana gaban nata. Amma muna zuwa class Hafsat ta chanja seat ta koma can baya wai dan kada a ganmu a tare a gane ni kanwar tace.Amman duk da haka duk teacher din da ya shigo in ya ganni a gaba in yaje bays kuma yaga Hafsat sai ya tambaye ta "is she your sister" ya nuno ni, ita kuwa Hafsat sai bakin ciki ya kamata. Daga baya wai ta tsiri saka nikab tana rufe fuskarta dan kar aga kamannin mu.

A makarantar mu muna da masu yi mana komai tun daga kan shara, wanki, guga, wankin toilet da sauran su. Mu dai bamu kawai shine muyi karatu. Ai kuwa Moon an samu abinyi, nan na zage na kama karatu baji ba gani, kullum ina library sai dai in fito inyi sallah in ci abinci in koma. Da daddare kuma bana karatu sai bacci, saboda ni din gwanar bacci ce, tun inayin sallahr isha'i zan kwanta har sai assuba zan tashi inyi sallah. Daga nan sai mu tafi islamiyya wacce mukeyi daga assuba zuwa 7. Sannan muzo muyi wanka muyi breakfast a dinning hall sai mu wuce class sai 10:30 mu fito break a kawo mana snacks da drinks, wani lokacin kuma farfesu ba kifi ko naman rago da bread mu ci mu koma class. Sai 1:30 muke tashi daga class mu je mosque muyi sallah sai mu shuga dinning hall muyi lunch sannan mu wuce hostel. Daga nan sai inyi wanna in saka evening wears dina in koma class area in shiga library bana fitowa sai 6:00 sannan zan koma hostel in yi magrib, daga nan zan saka Hafsat a gaba da surutu tare da sauran 'yan dakinmu. Sau da yawa inna dameta sai ta saka ear piece a kunnen ta ta rabu dani, amma haka bazai hana ni yin magana taba. Ban damu ko tana jina ko bata jina ba.
Hafsat duk ta rame saboda ita 'Yar hutu ce gaskiya. Kuma da gaske tana missing gida, kullum bata con abinci sai race babu dadi, ni kuwa sai in hada da nata da nawa in cinye babu abinda ya dame ni, as long as akwai books a library to bani da matsala.
Duk karshen wata mommy da daddy sai sunzo mana, in ya na gari, ranar visiting day su kawo mana kayan sosai drinks, chocolates, biscuits amma banda kayan abinci kuma banda kudi, haka rule din makarantar yake. Mommy tana damuwa idan taga yadda Hafsat ta rame, in ta tambayeta dalili sai ta saka mata kuka tace ita gida zata tafi, ni kuwa sai inyi ta kallon ta ina mamakin wai ita menene matsalar ta, saboda ni dadi make ji tamkar an saka ni a aljanna. Daddy ya lura da yadda nake jin dadin school kuma ya bani kwarin gwuiwa tare da bani study tips yadda zan fi gane karatu sosai. Sai ya zama na da...


Read / Download MAIMOON

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album