Join Our WhatsApp Group

TSIRA DA HALAKA 1 and 2 Complete Hausa Novel Document by TSIRA DA HALAKA 1 and 2


TSIRA DA HALAKA 1 and 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 31875



TSIRA DA HALAKA 1 and 2

Reading Time: 2 Hours

Added On: 21, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 176.34 kb

File Type: txt

Views: 1490+

Download: 564+

Last download: 2 days ago

Description/Story: An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__


TSIRA DA HALAKA!!!
Littafi Na Daya.
Part Â
A wani zamani can baya mai tsawo daya shude a
yankin kasashen bakaken fata,anyi wata kasa
mai
suna Hirtoliya.Kasar Hirtoliya tana bangaren kudu
ne kuma ta kunshi manyan birane a karkashinta
guda talatin da uku wadanda dukkaninsu a
karkashin sarki guda daya suke wanda ake kira
da
suna Garzub dan Inkal.Sarki Garzub ya kasance
sadauki kuma gagarumin MAYAKI sannan
gwarzon
matsafi wanda ya zama GAGARABADAU a
nahiyar
da yake gaba daya,kuma DODON MAZA abin
tsoro.Ba komai ne yasa sauran kasashen dake
makwabtaka da sarki Garzub suke matukar
tsoronsa ba face tsananin karfin
mayakansa,yawansu da kuma sa'arsu.Ance
tunda
sarki Garzub ya hau KARAGAR MULKI tsawon
shekaru arba'in daidai ba'a taba cinsa da yaki ba
kuma a duk tsawon shekara guda yakan fita yaki
kamar sau goma.Duk yakin daya fita sai ya sami
nasara sai dai aga ya dawo gida da dimbin
ganima
da bayi masu yawan gaske.Bisa wannan dalili ne
sarki Garzub ya tara dukiya mai yawan
gaske.Mutanen birnin Hirtoliya suna jin dadin
mulkin Garzub musamman yan uwansa
sarakai,attajirai da matsafa,amma su talakawa a
bangarensu ba yabo ba fallasa domin ba'a
kyautata musu yadda ya kamata kuma ba'a
tsangama musu face wadanda suka kiyin biyayya
ga sarki ko kuma suka karya daya daga cikin
tsaurarn dokokinsa guda uku.Doka ta farko itace
dole a duk shekara kowanne talaka ko mai arziki
ya biya haraji na buhun abinci guda biyu ga
sarki.Wannan doka akan kowa take komai
matsayinka komai kaskancinka.Doka ta biyu
itace
ba'a yarda wanda bai shafi sarauta ko kuma bai
samu izini ba ya shiga gidan sarautar garin koda
kuwa mazauna cikin gidan ne suka gayyace shi
dole saida sanin sarki.Doka ta uku kuwa itace
ba'a
yarda mutum yayi wani addini ba daban face
addinin bautar wani gunki mai suna Larruta.Idan
har aka kama mutum yana wani addini daban
HUKUNCIN KISA ne a kansa kawai.Sarki Garzub
yana da wani 'da guda daya kyakkyawan saurayi
kuma matashi dan shekara ashirin da uku mai
suna Uzaima.Uzaima ya kasance sadauki kamar
mahaifinsa sannan GWARZON JARUMI ne a filin
daga mai TARWATSA MAZA.Saidai halayensa
sunsha bamban dana mahaifinsa domin shi ko
kadan bai damu da dukiya ba kamar yadda ko
yaushe mahaifinsa ke kokarin tarata sannan ya
kasance mai tausayi da adalci don haka yana
adawa da dokokin da sarki ya kafa guda
uku.Musamman wannan doka ta baiwa sarki
buhun
abinci guda biyu a duk shekara.Sau tari idan
yarima Uzaima yaga talakan da bazai iya biyan
harajin ba sai yaje har gidansa a sirrance ya
bashi
domin yakai fada.Saboda duk talakan da aka
kama
da laifin rashin kai wannan haraji tofa sai yayi
shekara uku a kurkuku.Ita kuwa wannan doka ta
hana kowa shiga gidan sarautar ba karamin ciwa
Uzaima tuwo a kwarya take ba saboda yana
matukar son ya rinka shigowa da abokansa cikin
gidan sarautar suna debe masa kewa amma babu
hali.Shi dai Yarima Uzaima ya kasance mutum
mai
son mutane kuma wanda bashi da girman kai ko
kadan,domin bai dauki kansa komai ba.Ga wanda
bai sanshi ba sai yayi zaton cewa shi ba dan
sarki
bane domin idan yasa kansa sai kaga yana taya
mutane aikin wahala kuma duk inda yaga ana
zalunci tofa sai ya hana.Yarima Uzaima yana da
wani aboki mai suna Kaizur wanda ya zamo
amininsa,kuma sun shaku ainun domin a kullum
sai Yarima Uzaima ya ziyarci gidansu Kaizur
kuma
idan yaje tun safe baya tafiya gida sai yamma
tayi.Mahaifin Kaizur ya rasu tun baifi shekara
goma
sha biyar ba,sai mahaifiyarsa wacce ake kira da
Siyala wacce ta kasance makauniya yar shekaru
hamsin da daya sai kuma kanin Kaizur wani dan
shekara bakwai mai suna Hidal.A kullum idan
Uzaima yazo gidan su Kaizur sai ya tahowa da
Hidal kyautar wani abu,Bisa wannan dalili ne
Hidal
ma ya shaku da Uzaima yayi sabo dashi ainun
har
ya zamana cewa shakuwar ma sau tari idan suka
zo zasu rabu sai Hidal yayita kuka.Bisa wannan
dalili ne yasa Yarima Uzaima ya fara kwana a
gidan su Kaizur.Lokacin da Sarki Garzub ya fara
fahimtar cewa Yarima ya fara kwana a waje sai
ya
kafa masa doka mai tsauri akan hakan ya
zamana
cewa dole ne ya kasance kullum a gida da zarar
Magriba tayi.Al'amarin daya jefa Uzaima cikin
tsananin damuwa kenan,gashi bashi da ikon ya
shiga da Hidal izuwa cikin gidan sarautar don
kada
ya janyo masa HUKUNCIN KISA.Haka dai ya
lallami
Hidal akan yayi hakuri akwai lokacin da zaizo ya
zamana cewa babu abinda zai rabasu face
Mutuwa.Ganin yadda ra'ayin yarima Uzaima ya
zama daban dana mahaifinsa sai mahaifinsa
nasa
yayi watsi da al'amuransa ya zuba masa ido
kawai
duk da cewa yana matukar kaunarsa a
matsayinsa
na dansa guda daya jal a duniya.Ko kadan
karkokin sarauta bai dami yarima Uzaima ba bare
kuma wani abin duniya.Yarima Uzaima bai taba
ganin wata budurwa data burgeshi ba bare ya
nuna
yana SONta.Saida sarki Garzub yasa aka zo da
yan
mata goma sha biyu 'ya'yan manyan sarakai na
nahiyar wadanda suka kasance kyawawan gaske
ana gabatar dasu ga Yarima Uzaima domin ya
zabi
wacce zai aura amma sai yace gaba dayansu
babu
wadda tayi masa.Al'amarin daya fusata sarki
Garzub kenan saboda Uzaima ya bashi kunya a
wajen wadannan sarakuna.Cikin fushi sarki
Garzub
ya dakawa Yarima Uzaima tsawa yace yakai
dana
idan har kana da wata matsala ne ta rashin lafiya
to ka gaggauta sanar damu domin mu nemo
maka
magani.Ka sani cewa yan matan da muka kawo
maka babu kamarsu a wannan nahiya gaba daya
kuma ba zaka taba samun mai kyau irin naus
ba.Sa'adda Yarima Uzaima yaji wannan batu sai
ya
durkusa bisa guiwoyinsa a gaban sarki Garzub
sannan ya dubeshi cikin girmamawa yace yakai
Abbana ka gafarceni,hakika na san na bata maka
rai,amma ina
Son ka sani cewa ba don komai naki daya daga
cikin wadannan yan mata ba sai domin nasan
cewa zasu aureni ne saboda matsayina ko kuma
saboda shakkarka.Ni kuwa nafi son na auri
wacce
take yi mini SO na gaskiya ba don komai ba
kamar yadda ka bani labarin yadda ka hadu da
mahaifiyata harka aureta.Koda Sarki Garzub yaji
wannan batu sai jikinsa yayi sanyi,ya sunkui da
kansa kas ya kasa cewa komai.A wannan lokaci
fada a cike take makil da jama'a,kawai sai akaga
idanun sarki sun kada sunyi jawur.Nan take ya
juya ya shige izuwa cikin GIDAN
SARAUTAR.Al'amarin daya janyo fadar ta watse
kenan gaba daya kowa ya kama gabansa.Dalilin
wannan abu daya faru sai da sarki ya kwana uku
bai zauna a fada.Al'amarin daya DUGUNZUMA
hankalin gaba dayansu suka kai masa ziyara gida
don zatonsu ko sarki bashi da lafiya ne,saboda a
saninsu a tsawon shekaru arba'in da hawa
karagar
mulkinsa bai taba fashin zamab fada ba.Lokacin
da yan majalisar suka iso wajen sarki domin su
dubashi sai ya aiko a gaya musu cewa shifa
lafiyarsa kalau kuma ba zasu sami damar
ganinsa
ba yanzu sai ya nemesu da kansa.Koda jin
wannan batu sai hankalin yan majalisar ya kara
dugunzuma fiye da koyaushe.Cikin sanyin jiki da
matukar damuwa suka juya suka fice daga cikin
gidan sarautar."Abinda basu sani ba shine a duk
sa'adda sarki ya tuno da matarsa marigayiya
wato
mahaifiyar yarima Uzaima sai yaji ya tsani komai
da kowa a duniya.Babu abinda yake so sama
daya
killace kansa yayi ta kuka da begenta Yana
tunano
abubuwan da suka faru a baya shekaru ashirin da
biyar da suka gabata.Wata rana sarki Garzub na
zaune a fadarsa jama'a sun kewayeshi ana
tafiyar
da harkokin mulki sai ga wadansu bakin mayaka
sunzo daga wana kasa da ake kira Farzuba.Kai
tsaye mayakan suka shigo cikin fada suka iso
har
gaban Karagar sarki suka zube cikin girmamawa
suka kwashi gaisuwa sannan daya daga cikinsu
ya
dago kai ya dubi sarki Garzub yace yakai wannan
gwarzon sarakuna kayi sani cewa mu manzanni
ne
daga sarki Kurazu na birnin Farzuba.kuma munzo
ne domin mu isar da sako.Sarkinmu yace mu
gaya
maka cewa ka zauna cikin shirin yaki domin
yanzu
haka akwai wata runduna ta mayaka jinsin
larabawa da suka sauka a gabar tekun
kasarmu.Adadinsu ya kai MILIYAN ARBA'IN.Ba
komai ne ya kawosu wannan nahiya tamu ba sai
FARAUTAR BAYI da diban albarkatun kasa.Sarki
Kurazu ya baiwa wadannan mayaka hadin kai
sun
kwashi bayi masu yawa gami da dukiya mai
yawa
a cikin birninmu,kuma suna nan suna shawarar
su
karaso nan kasarka.Sarkinmu yace shi kam ya
san
ba zai iya ji da wadannan larabawa ba shi yasa
ya
basu hadin kai kuma yana mai baka shawara
akan
ka basu hadin kai in ba haka ba zasu shafe
kasarka su kashe dukkan mayakanka su kwashe
arzikinku suyi tafiyarsu.Hatta addininka daka
gada
a wajen iyaye da kakanni sai ya gushe daga
doron
kasa....Kafin wannan mai jawabi ya gama rufe
bakinsa tuni sarki Garzub ya zare takobinsa cikin
ZAFIN NAMA ya fille masa kai.Kan yayi tsalle ya
fadi can gefe daya,jini yai tsartuwa ya bata
fuskokin ragowar yan uwan nasa.Hakan ne yasa
suka firgita ainun jikinsu ya kama kyarma.Kawai
sai Sarki Garzub ya bushe da dariya lokaci guda
kuma ya hade fuska ya dubi ragowar manzannin
a
fusace yace ku kuma ku koma ku gayawa
sarkinku
cewa ni bazan bada hadin kai ga wadannan
larabawa ba kuma ba zanyi zaman jiran isowarsu
kasata ba gani nan tafe da kaina zan taresu ko
Ni
ko ko su!(Hmm Kunji Gwarzon Namiji).Ku
gayawa
sarkinku cewa shine ya cucemu daya basu dama
sukayi abinda suke so a cikin kasarsa shi yasa
suke tunanin zasu iya karasowa nan kasar su
dasa
wawaso.Ku bace min da gani!Koda gama fadin
haka sai manzannin sukayi sauri suka fice daga
cikin fadar jikinsu na bari.Take dakaru suka dauki
gawar wannan manzon aka goge inda jini ya
bata.Shi kuwa sarki Garzub sai ya dubi sarkin
yakinsa wanda ake kira da suna Zamud yace
dashi
maza kaje ka shirya yaki da dakaru Miliyan
Talatin.Zamud ya risina yace an gama ya
shugabana.Nan take Sarkin Yaki Zamud ya juya
ya
fice da gudu.Gaba daya wannan rana babu
abinda
ya gudana a birnin Hirtoliya face shirye shiryen
yaki.Nanfa aka rinka fito da MAKAMAI kala kala
masu bukatar washi aka wasasu,wadanda suka
lalace akayi watsi dasu aka shiga kera
sababbi.Haka kuma aka shiga tanadin Guzuri.Tun
safe aka fara wannan shiri amma ba'a
kammalashi
ba saida dare ya raba.Bayan an gama shiri ne kaf
sarki yasa aka kirawo Zamud yace dashi abinda
nake so dakai shine kada a tafi da mace wannan
yaki ko guda daya.Koda jin haka sai Zamud ya
cika da tsananin mamaki ya dubi Sarki Garzub
yace ya shugabana ka sani cewa tafiyar da
zamuyi
daga nan zuwa birnin Farzuba ta kwana ashirin
da
tare ce,anya kuwa dakarunmu zasu iya hakurin
rashin mata har tsawon wadannan kwanaki?Ka
sani
cewa basu taba fuskantar irin wannan matsala
ba.Cikin Fushi Garzub ya dakawa Zamud tsawa
yace umarni nake baka ba shawarar ka nake
nema
ba.Kuma ka sanar da su wanda duk yayi jima'i
da
wata macen akan hanya ko yayi fyade hukuncin
kisa ne a kansa.Ka sani cewa wannan umarni ne
daga abin dogaronmu mai girma Larruta.Koda jin
haka sai sarkin yaki Zamud ya sake risina yace
sakonka ya isa ga dakaru.Kawai sai ya mike
tsaye
ya juya ya fice daga cikin fadar.Kashe gari da
sassafe dakaru Miliyan talatin suka taru a kofar
gidan sarautar bisa dawakansu cikin shigar yaki
dauke da MUGGAN MAKAMAN YAKI.Idan mutum
yaga yawan wadannan dakaru dole ne ya firgice
yayi tsammanin cewa YAKIN DUNIYA
za'ayi.Bayan
kowa ya hallara sai sarki Garzub ya fito daga
cikin
gidan sarautarsa shi kadai bisa wani farin
ingarman
doki cikin gagarumar shigar yaki mai matukar
kwarjin
da ban tsoro irin wacce ba'a taba ganin yayi
irinta
ba.Sarki Garzub bai taba sanya sulken karfe a
jikinsa ba a duk sa'adda za'a fita yaki amma a
wannan karon sai akaga gaba dayan rigarsa da
wandonsa na karfe ne kanse ne kawai bai rufe ba
da hular karfe.A bayansa ya rataya wata
zabgegiyar takobi wacce asalinta ta mahaifinsa
ce.A kuibin cinyoyinsa na dama da hagu kuwa
wadansu siraran takubba ne guda biyu.Da ganin
sarki Garzub a cikin wannan shiga sai gaba
dayan
dakarun suka sha jinin jikinsu domin dun san
cewa lallai yakin dake gabansu ya wuce gaban
tunaninsu.Nan take dukkaninsu sukaji tsoro ya
darsu a cikin zuciyarsu.A wannan lokaci gaba
dayan mutanen birnin sun taru a gefe daya maza
da mata,yara da manya,da yawa daga cikin
iyalan
dakarun da zasu fita wannan yaki suna kuka
domin
basu da tabbacin za'a sake saduwa.Lokacin da
sarki Garzub ya iso gaban dakarun yaki sai ya
kallesu tun daga kan na farko dake tsaye a
hannun
hagu izuwa kan na karshe dake hannun dama
sannan ya dubi na tsakiyarsu ya hanga izuwa
can
baya inda baya iya hango na karshe.Kawai sai
yayi
murmushi ya sake duban Zamud yace yakai
sarkin
yaki kayi sani cewa wannan yaki da zamu fita
yaki
ne na tarihi wanda har abada baza'a taba
mancewa dashi ba.Yaki ne na tsanani wanda
bamu taba yin kamarsa ba kuma abu ne
mayuwaci
idan zamu sake yin irinsa nan gaba.Ka sani cewa
lokacin dana tambayi mai girma Larratu ya sanar
dani yadda karshen wannan yaki zai kasance,sai
yayi shiru baice dani komai ba har izuwa lokaci
mai dan tsawo.Daga can sai naji muryarsa ta
kama
rawa kamar kuka yace yakai sarkin sarakuna kayi
sani cewa a wannan yaki naga cewa za'a rasa
miliyoyin rayuka a kowanne bangare amma ni
kaina na kasa gano abinda zai faru a karshe
saboda ABOKAN GABAR taku sun shirya kafin su
fito.Duk abinda muke takama dashi suma suna
dashi,saboda haka komai zai iya faruwa a
wannan
yaki ko dai ku sani nasara ko su su samu.Abinda
nake so dakai shine ka karkafi jama'arka da
kwarin
guiwa,kayi sani cewa KARAYAR ZUCIYA tun a
fari
tana janyo rashin nasara.Sa'adda sarki Garzub
yazo nan a zancensa sai yayi ajiyar zuciya
sannan
ya dubi gidan sarautarsa.Nan take idanunsa suka
ciko da kwalla ya koma gefe daya ya sunkui da
kansa kasa.Cikin matukar damuwa sarkin yaki
Zamud ya taho gareshi ya tsaida dokinsa daf da
nasa suka dubi juna sannan yace ya shugabana
lafiya kuwa naji kayi shiru baka yiwa dakarunka
bayanin komai ba?Dajin wannan tambaya sai
sarki
garzub yayi ajiyar zuciya sannan yace yakai
Zamud
kayi sani cewa ba komai bane yasa na kasa yin
bayanin komai ba face tunowa da wasiyar da
mahaifina yayi mini kafin yabar duniya.Wasiyar
kuwa da ita ya mutu a bakinsa yana mai
cewa"Ya
kai dana gashi har ajalina zai riskeni baka yi aure
ba bare naga jikana,saboda kawai har yanzu
baka
sami bacen data burgeka ba.Ina mai rokonka da
lallai ka nemi mace ka aura don ka sami magaji
kafin kaina naka ajalin ya riske ka.Ina son kayi
mini wannan alkawari yanzu take domin na mutu
da farin cikin hakan.Sa'adda mahaifina yazo nan
a
zancensa saina rungumeshi kuma na fashe da
kuka ina mai cewa yakai...


Read / Download TSIRA DA HALAKA 1 and 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On TSIRA DA HALAKA 1 and 2
avatar
hafeez-dalhatu

2 months ago

Reply

Godiya

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album