Join Our WhatsApp Group

AMINATU Complete Hausa Novel Document by AMINATU


AMINATU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 11981



AMINATU

Reading Time: 0 Hours

Added On: 01, Sep 2023

Author: Mrs Kamal ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 810 669 8241

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 67.09 kb

File Type: txt

Views: 790+

Download: 150+

Last download: 6 days ago

Description/Story: AMINATU
Na Humaida mrs Kamal
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook Publish by www.hausaebooks.cf

[08/01 5:31 pm] +234 810 669 8241: [9/24, 3:12 PM] Mrs kamal: [9/24, 3:12 PM]
Mrs kamal: _1_
*A'minatu*
Gudu tak'e ba tsayawa! tana haki amma idan ta waiga sai ta k'ara rugawa da
gudu har takai titi ba tare da ta sani ba.
sak'a kai kawai tayi ji tayi kauuu mota ya kad'e ta innalillahi wa inna
ilaihi rajiun shine Kalmar da da`n saurayin yak'e fada! ya dauk'e ta yasa cikin
mota yaja zuwa asibitin mallam aminu Kano suna zuwa aka shiga da ita!
hannun
sa yasa
yaga bata ko numfashi nan da nan ya k'ara rikicewa, Dr pls save her
life karka bari ta mutu wlh bansan taba.
Ya shiga tashin hankali sosai sai addu'a yake Allah yasa karta mutu, bayan an
shigar da ita Dr yafara dubata ciikin ikon Allah ya samu tafara numfashi yayi
hamdala.
Ya barwa wata kyakkyawar Norse ta cigaba da duba ta shi kuma ya fito, d'an
saurayin na ganin shi ya rugo da gudu xuwa wajen shi, Dr marwan yajikin nata?
" biyo ni office Suna shiga Dr marwan yace have a site! ka kwantar da
hankalin ka fu'ad zata samu sauki cikin yardar Allah sai dai ta bugu Dan haka
tana bukatar Hutu kaje gida ka dauko Wanda zai dinga kulawa da ita.
" ok Amma Dr Dan Allah ka taimaka min ka kulamin da ita yanxu zan dawo.
Tun kafin Dr marwan yayi magana ya bude kofa ya fice yaja otar da gudu zai
tsaga kasa SBD gudu waiyooo ni fu'ad yazanyi da raina shin wazan dauko ya duba
baiwar Allah nan? tunani ya masa yawa kansa ya cushe ya tsaya agefen titi yana
xubda hawaye SBD tausayin kansa daya kamashi! wayar da tayi Ringing shiya dawo
dashi daga duniyar tunani a hankali ya dauki wayar amma yakasa furta kalma
daya!
What??? Subhanallah meya same shi na shiga uku ne fuad ya zanyi da raina ya
Allah ka kawo min dakarfi ya bugi sitiyarin motar!
Wani zazzafan hawaye na bin kwancin sa .
Taku
*Humaida (Mrs kamal)*✍🏼
[9/24, 3:12 PM] Mrs kamal: _2_
*A'minatu*
Yasa hannu yana sharewa shikan shi yasan yazama abin tausayi yasa hannu ya
kunna motar ya fara tafiya ahankali har ya isa wani katafaren gida
Mai dauke da kayan alatu na zamani horn yayi maigadi yazo ya bude masa gate yana
shiga ya bude mota dasauri ko rufewa baiyi ba yashiga cikin gidan yana ya kiran
phatty! Phatty! tana saida ya karaso cikin falon ya ganta kwance tana tauna
cwigam.
Phatty, bakiji ina kiranki ba, haba fu'ad kai kasan banason haniya ko ihu
amma meyasa kakemin, kiyi hakuri kuskure ne, dama....dakata banason complain
indai abinci ne kai kasan bani da lokacin dafawa, ta juya ta ka'ra gishin gida'
ya mik'e jiki a sanyaye har yakai bakin kofa ya sake juya yana kallon ta cikin
sanyin murya yace phatty I need ur help kizo ki taimaka min nayi accident a
hanya yana hawaye yana mata magana.
Sai a lokacin tad'aga ido ta kalle shi cikin k',asaita tace ayya sannu ko jeka
watsa ruwa ajikin ka zakaji dadi.
Nooo phatty na kad`e wata yarinya yanxu haka tana asibiti inason ki taimake ni

kije ki zauna da ita pls
Arazane ta juya cikin zafi take magana kaikasan bazan iya ba banason haniya kaje
ka roki inna balaraba nasan zataje Dan tanada tausayi amma nibada ciwo ba na
zauna a asibiti.
Taku
*Humaida (Mrs kamal)*
[9/25, 6:34 PM] Mrs kamal: _3-6_
*A'minatu*
Phatty! Me yasa kike min haka I'm not ur husband, a yanxu umarni nake baki ba
Neman shawara ba idan har baki zo mun tafi asibiti kin kula da baiwar Allah nan
ba kada nadawo NASA meki a gidannan.
Abakin auren ki fu'ad ni zaka gayawa Abakin aure na ai kasan nida kai mutu
karaba muje zanyi amma da sharadi idan zaka biyani zanyi idan kuma baza ka biya
ba, ba inda zani, yi hakuri muje zan biya hijabin tasa suka wuce asibiti tana
shiga saida gaban ta ya fadi ganin yarinya kyakkyawa akwance Wanda shekarun ta
bazai wuce 18 years ba ta matsa kusa da ita tace sannu baiwar Allah.
Da kai ta amsa mata yanxu ya kikeji ajikin ki ahankali ta bude baki tace dasauki
saidai ina tunanin halinda nabar Ummi na, nasan yanxu tadamu tasan halin da
nake ciki Dan Allah ki taimaka min.
Wani irin taimako zan miki baiwar Allah? Inason kije ki fadawa Umma ta abinda
yafaru dani,
Keee

dalla dakata niba surutu nazo kimin ba .

Karki damu zan kibari ki kara jin sauki saiki min kwatancen gidan naku
musu bayanin komai.

zanje na

Ngd sosai amma ya sunanka meya sa kike tambayan sunan sa kedai ki warke ki
k'ara gaba banason shishhgi .
Phatty why?why?? Meya sa baki da hakuri
Hmmm fu'ad na kasan ina sonka yazama dole nayi kishi da kai Dana zauna da
kishiya gwara nayi yawo tsirara,
Haba Anty meyasa zakice haka ai kishiya abin sone ko uncle hmm nikam ya sunan
ki? Sunana Amina amma ana kirana da meenat ko ummu ammara.
Fu'ad meye naka

na tambayar ta katafi mana ka barmu nizan kula da'ita.

Zan tafi baizama lallai nadawo ba kisani jin tsoron Allah shine abinda nake
fad'a miki kullum kizama mace tagari a duk inada kika tsinci kanki Dan Allah ki
rikemin amana banda Tara k'awaye a gida my phatty yau zan barki baizama lallai
na dawo ba.
Uncle ina

zaka? Ina ruwanki da inda zashi .

Taku
*Humaida(Mrs kamal)*
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: _12-14_
*A'MINATU*
Tunda Allah ya hada su , suke son junan su musamman maryam Wanda komai
zatayi Abba na yana ranta Sam batason Bacin ransa ko kadan , dakyar mahaifin
ta ya yarda ta auri Yahuza sunyi aure cikin so da kaunar juna.....

Suna matukar kulawa da junan su basa

son abinda zai tabi dayan

su......

Bayan auren su da shekaru biyu aka samu cikina murna wajan iyaye na da
kakan Nina bazai misaltu ba, dukkan kulawar su ya koma kan mahaifiya ta basa
son bacin ranta Wannan kulawar da ake bata dayawa shi yayi sanadiyyar dasa
kiyayyar ta a zuciya inna Zainabu ta tsane ta gashi dai ba gari daya suke ba
amma inna Zainabu ta matsa saidai su dawo kano da zama Abba na baiso haka ba
amma yazama dole yayiwa iyayen sa biyayya......
Tunda suka koma kano da zama mahaifiya ta, tayi ban kwana da farin
ciki. .....
In kinga tayi murmushi to da mijin tane inkinga kwallan ta to tabbas da inna
Zainabu ne, Watarana suna zsune sukaji sallama suka amsa yaro ya shigo yace wai
ana sallama da *maryam Rano* abin ya bata mamaki tana mik'ewa inna Zainabu ta
mike tana tafiya ta ingijeta gefe ina zaki?, *shan shani I mai kafar yawoo*
dalla matsa kibani guri na wuce...
Haka ta matsa mata tunda inna Zainabu ta fita bata dawo da wuri ba bayan ta
dawo take CE Mata wai Sagir yana gaisheta da murnan ta tashi tana cewa INA
shike? Allah sarki Yaya sagir....
Hhhhh gwanda ma ki koma ki zauna SBD yariga ya tafi ga abinda yace nabaki
nima na figi tawa rabon kuma inason kisani daga yau nima nazama matar yayanki
sagir saiki hadiyi yawu ki mutu .....
Tunda taji wannan maganar Cikin ta yafara murd'awa da karfi ta kwalawa inna
Balaraba kira tazo ta shigar da'ita d'aki cikin yan mintoci ta haihu...
Murna kam anyishi Dan harda mutanin Nasarawa sunzo duk Tsanar da inna Zainabu
kewa Umma ta baihana ta nuna tana matukar sona ba....
Ta shaku sosai sa yaya sagir soyayya mai karfi sukeyi a tsakanin su amma duk
da haka bata kaunar wani Dan uwan Umma ta yazo wajan ta...
Taku
*(Mrs kamal*)
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: _6-9_
*A'MINATU*
Pls don't go! Ka tsaya tare dani I need ur care, meenat kada kidamu nafasa
tafiya har sai kinsamu lafiya na maidake gaban iyayen ki daga wajan zan wuce.
Ngd Allah yasa maka da Alkhairi,
Fu'ad meyasa zaka fasa bayan kayi niyya
Karka damu zan kula da'ita har ta warke dakaina zan mayar
ta.

da ita gaban iyayen

INA xuwa Dr marwan yana kirana, fitar shi da kadan yadawo tare da paper a hannu
ya kalli meenat yace yan mata lafiya ya samu ko? Kwarai kuwa saidai nakara
godewa Allah .
Yanxu Ku had'a kayan Ku gida zamu gida sai kiyi wanka ki huta kibamu

labarinki.

Hmmm labarina? Ayya dama kabar shi dayafi Dan banason tunawa,
Bayan sun gama had'a kayan su suka shiga mota yaja zuwa gida.
My phatty naji bakice komai ba tunda nafara magana me kakeso nace bayan ka
wulakan tani agaban agola, Wacece agolar? *A'minatu* na Sam ba agola bane kada
nakara ji kin kirata da wannan sunan Dan bashi akayan ka mata ba.
Suna isa phatty ta ban kad'e kofa da karfi ta fita tana wani irin huci. Ya juya

ya kalli meenat yace kada kidamu kinji haka take zata warware, yafita ya bude
mata motar itama ta fitooo direct gefen sa ya wuce da'ita yanuna mata toilet
yashiga ta watsa ruwa ya dauko kayan phatty yabata tasa ta gabatar da sallolin
ta.
Yana zaune a falo ya kifa kansa yaji sallamar ta yad'ago ahankali ya zuba
mata jajayen idon shi dasu ka kumbura saida ta tsoro ta ganin irin kallon da
yake mata.
Ahankali takarasa tazauna suka fuskanci juna
magana,

cikin San sayar murya tafara

" Uncle fu'ad shin zan iya sanin *Labarinka* SBD na lura kana cikin damuwa Dan
Allah kafadamin ko da taimakon da zan iya maka.....
*TAKU*
*HUMAIDA*✍🏼(Mrs Kamal,)
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: _10-12_
*A'MINATU*
*farkon labarin na!*
sunan k'aka na malam musa ba fulata nin gombe , amma ya dawo Kano da zama
anan ya had'u da mahaifiyar baba na inna *Balaraba* sanidiyyar wani mako
cinsu , basu taba ganin juna ba har aka daura aure....
Amma inna Balaraba bata tab'a nunawa iyayen k'in wannan had'in auren ba
koda a fuska ,Mahaifin inna Balaraba shi yane mawa malam musa aikin yi,na sayar
da zannuwa a *kwantin kwari*bashida da matsala mutum ne mai
rikon amana ga
ibada...
Tunda malam musa ya auri inna Balaraba basu tab'a fad'a ba har Allah yasa
tasamu juna biyu murna wajan sa bazai misaltu ba, haka iyayen ta, lokacin da
ciki yakai 9months ta haifo d'anta kyakkkawa kamar baban sa...
Ranar suna yaci sunan mahaifin ta *Yahuza* basu canza masa suna ba saidai
inna Balaraba bata kiranshi da sunan saidai tace masa d'an juma...
Bayan shekaru biyar tasake haihuwar mace akasa mata suna *Zainab* sun taso
cikin tarbiya da girmama juna Iyayen su sun basu ilimin Arabic sosai....
Mahaifina Na da shek'ara a shirin yabar garin kano zuwa *Nasarawa state*
wajan abokin baban sa anan yasamu ya ci gaba da karatun sa....
Inna Zainabu Nada shekaru 16 aka aurar da In takaice miki mahaifina yasamu
karatu sosai kuma Allah ya hadashi da wata baiwar Allah mai suna Maryam Rano
mahaifin ta hamshakin mai kudi ne...
Taku
*MRS KAMAL*
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: *16-18*
*A'MINATU*
Hakane my son I know! Umma ta wacece a falon ki? Hmm kajimin shu'umin yaro
phatty cefa bakaga kamar kawun ka ba..
Hmm lallai girman mata ba wuya Sam phay ta girma haka shine kota gaishe ni
kila itama bata gane ka bane...
Ni zan tafi idan kashirya ka same mu a big parlour , OK *A habbak'i* ya UMMI!
*A habbak'a* ya ~fu'adul huffaz~tana fadan haka ta fita bayan nagama na fito ina

xuwa nasake cin karo da phatty saida naji gabana ya fadi SBD yanda naga yarinya
kara shiga raina tayi tabbas nasan zan daukowa kaina dutsen dala ba gammu..
A haka NA zauna
kowa ya watse aka
fu'ad, thank u my
Hmmm nifa bancika

muka gaisa dasu Abba harda phattyn bayan mun gama cin abinci
barmu mu biyu tadago ido ta kalle ni tace welcome back Yaya
sst how is ur study? i hope everything is moving smoothly!
son yawan magana ba kawai ka ware zanyi bak`i...

Meenat a taikace Ashe phatty samarin tane zasu zo a gsky tun daga wannan
ranar naji na tsane ta har zuciya na SBD phatty ta dauko rayuwar ya hudawa
sosai gashi ba Wanda ya isa ya Gaya mata magana taji...
Kwatsam muna zaune aka kira family meeting muka hadu dukkan mu bayan kowa ya
zauna aka fara bude taro da addu'a Baffa yafara nasiha bayan yagama inna
Balaraba ta amsa saiji nayi tace idan mai duka ya kaimu watan gobe wato watan
azumin tsoffi da kwana 11 zamu aurar da yaran nan su biyu da sauri phatty ta
da'go kai tana tambayar inna Balaraba...
Waye mijin nawa?, kibari idan Allah ya kaimu ranar zaki Sani Mara kunyar
kawai....
Bayan mun tashi daga wajan meeting na koma gida na dinga tunanin dawa za
had`ani aure da wannan tunanin na kwana....
Washegari Umma ta, tashigo d`akina tace fu'ad nazo nan ne Dan gargadeka akan
batun auren ka duk matar da aka baka ka karb`a hannu bibbiyu da addu'ar samun
zaman lfy mai d`orewa ka mana biyayya insha Allah rayuwar ka bazaka tabe ba....
My son promise me, Umma ta na mika mata hannu tace promise? Nace promise
lovely mom..

my

Yauwa my son may God bless u Amin....
Tun nadawo sau daya naje gidan su inna Zainabu ina zuwa tamin zagin
wulakanci na fita tun daga wannan ranar ban sake xuwa ba....
Da ranar aure ya xagayo aka dauramin aure da.....
*urs*
Humaida (Mrs kamal)
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: *18-20*
*A'MINATU*
Aka dauramin aure da phatty tabbas banyi farin cikin haka ba amma idan natuna
yadda girman yiwa iyaye biyayya yake sai nayi murmushi nayi addu'a samun
kwanciyar hankali tare da zaman lfy mai dorewa.....
"Bayan 'yan biki sun kawo amarya kowa ya watse sai ita kada'i, ko kawayen ta
ba'a barsuba ina zaune nida abokai na phatty ta kirani tacemin anbarta ita
kadai a gida kuma tsoro take ji...
Na tashi muka tafi abakin k`ofa nace wa abokaina su koma abinsu ngd haka kuwa
akayi.....
Nashiga da farin cikina ina zuwa na shiga d'akin
nayi mata sallama ta amsamin acikin k'oto...

da na tabbatar phatty na ciki

" d'aga idon da zanyi dasauri na sauke su k'asa sanidiyyar abin da idona yagani
Wanda bai tab'a ganin irin shiba hankali na ya gushe bansan lokacin da ledar
hannu na ya fad'i ba dasauri na tinkari wajan da phatty take na rik'e Mata hannu
nace...
Phatty na meye haka "why ar u crying waya tabamin ke?"

Bakowa kawai dai banason rabuwa da inna tane shiyasa
Hmmm 'yan Matan inna yi hakuri kinji taso muje muyi alwala muyi sallah....
Waiyo Yaya fu'ad cikina ciki kuma bude min nagani don't worry dear yadaina "noo
phatty pls open it let me see ",
Hhhhh nace maka I can't.
Saifa kin budemin na dubaki kar wani Abu yasameki,
Hmmm *Meenat*bazan iya gaya miki sauran ba *sirrine* amma ataikace phatty bata
bari ko nafila munyi ba tunda wani Abu yashiga tsakani na da'ita shi kenan
narasa gane kaina banajin maganar kowa saina ta Dana inna Zainabu 😭😭...
Bana xuwa gun Umma ta abin yana cimin rai narasa dalilin haka in takaice
miki phatty bata bani kulawa Sam ,SBD tunda mukayi aure ko b'atan wata bata
tab'a yiba....
Bansan ta inda Zan bullowa lamarin ba, yanxu haka kiran da akamin
sukayi Allah yayiwa Abbana rasuwa .....

cemin

*meenat* zantafi bazan dawo ba zan gudu nagaji da bak`in hali irin na ta Gashi
natsani xuwa garin mu idan ba phatty ce tacemin natafi ba,pls meenat ki
rok`amin ita ta barni Dan Allah...
Basai ta rok`eni ba katashi katafi zan kula da'ita kafin ka dawo ko kuma na
maidata village dinsu kada kamin musu Yaya fu'ad kasan ban da mutunci zan iya
komai akan ka....
Ke kuma idan zaki cire rai gwanda ki cire kallon kitse kikewa rogo, kada
kiyi wasan auren min miji, *Mijin phatty* dagani sai makara gwanda kije kiyi ta
tallan nono dagan nan kila kyasamu mashin shini inafatan kingane....
My phatty kinsan cewa ni mijin mace d`aya ne daga ita bak`ari Dan haka ki
kwantar da hankalin ki kamar kina jirgin sama mai ya k`are yanxu zan maida
meenat gidan su daganan zan wuce...
Urs
*(Mrs Kamal)*
[08/01 5:32 pm] +234 810 669 8241: *20-22*
*A'MINATU*
"Zancen kake so wai ance da gauro ya iyali.
Haba sweety na...


Read / Download AMINATU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album