Join Our WhatsApp Group

MASARAUTAR MU Complete Hausa Novel Document by MASARAUTAR MU


MASARAUTAR MU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

DOWNLOAD

Uploaded by @Taskar

Total Words: 53357



MASARAUTAR MU

Reading Time: 4 Hours

Added On: 08, May 2023

Author: Sumayya Abdulkadir Takori ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07030137970

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 274.8 kb

File Type: txt

Views: 9011+

Download: 4684+

Last download: 21 hours ago

DOWNLOAD
Description/Story:
MASARAUTAR MU!







Littafin









SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com



SADAUKARWA
Ga Bilkisu Askira, (Billie Askira), Maiduguri, sabida gudummuwar ki yayin rubuta wannan littafi.

JINJINA
Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah.

GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali.


SHIMFIDA
Rana ta tasamma faduwa, misalin karfe biyar na yamma. Lahadi ce, wadda ta kasance ranar kasuwar kauyen. Tsanyawa, karamar hukuma ce a cikin birnin Kano. A dai-dai wannan lokacin kasuwar garin ta fara watsewa, kowa na kokarin komawa gida cikin iyalin sa domin lokacin magariba ta kawo kai. Malam Hashimu, daya daga cikin dattijan garin Tsanyawa, dattijo ne mai kamala dan kimanin shekaru sittin da biyar, ya baro kasuwar akan keken sa, wani tsohon keke wanda da kyar tayoyin sa ke juyawa sabida tsatsa da tsufa. A hankali yake tafe a gefen hanya kikiki-kikiki....bayan keken sa dauke da tsarabar kasuwa ta kayan miya (kayan gwari) wadanda yake sayarwa da tsarabar yalo, dafaffen rogo da rake dasu agwaluma cike taf a katuwar leda.

Tun daga bayan darnin gidan sa ya ke jiyo tashin kukan diyar sa SA'ADE. Zuciyar sa ta tsinke...kamar koyaushe ya ji kukan yarinyar tasa. Ya kara gudun keken sa ya iso gida jikin sa yana rawa, da hanzari ya jinginar dashi a jikin jinka ba tare da ya bi ta kan ledar tsarabar sa ba, ya fada gidan da dan banzan sauri, babbar rigar sa tana harde shi saura kadan ya fadi, da kyar ya samu ya dafa katangar dakin sa ya shigo gidan kamar an jefo shi.
Abinda ya zata shi ya gani, wato mai dakin sa ce Inna Laure ke jibgar Sa'ade, da wani murtukeken iccen darbejiya tun karfin ta, yarinyar tana ta ihu da neman taimako kamar kullum. Hannu ya mika ya daga yarinyar wadda ke kuka kamar ranta zai fita tana fadin.....
"Baba ka cece ni Inna zata kashe ni....". Inna Laure ta yarda iccen tana masifa tana fadin.
"Gobe ki sake dawo min da sauran gasara baki sayar ba, ki ga yadda zanyi da ke a gidan nan. Haka kawai ki dinga jaza min asara, ai ba uban naki ya bani jarin ba, in baza ki yi min talla ba, to ya dauke ki ya yi miki aure. Ba zan zauna ina ciyar daku ga banza ba, kartin banza kartin wofi da basu san komai ba sai ci da juyewa a masai, dole ki fita ki nemo min tunda kun zame min jaraba daga ke har sullutun uban naki da bai ko iya ciyar da gidan sa".
Malam Hashimu bai ce komi ba, amma ba kalmar data fi bakanta mai rai cikin maganganun ta irin "sullutu", ya tada yarinyar ya kama hannun ta suka nufi dakin sa. Har zuwa lokacin Sa'ade kuka take yi jikin ta yayi birdin-birdin yana ta rawa.
A gefen wata tsohuwar kujera kwalli daya da ke dakin mahaifin nata ta zauna, ta takure jikin ta tana sheshsheka hadi da hadiyar zuciya.
Malam Hashimu ya ce "bar kukan ki gaya min kin ci abinci?"
Sa'ade ta girgiza kai hawaye na sakko mata. "Baba tun kokon safe, ban kara cin komai ba".
Tashi yayi ya koma inda ya jingine kekensa ya dauko kullin ledar da ya dawo da ita, ya dawo ya zauna a gaban 'yar tasa. Kwancewa yayi ya fiddo daurin awara mai zafi a cikin leda ya tura mata gaban ta ya ce "maza cinye".
Sa'ade ta shiga tunkuda awara a bakinta hannu baka hannu kwarya, daidai lokacin aka bankado labulen dakin aka shigo.
Laure tasa hannu ta dauke kullin awarar gabadaya tana fadin "eh lallai! Gata mugun abu, in baki dambu ki ci ki koshi, ki cewa ubanki ban baki abinci ba ko? To daga ke har shi kun yi kadan ku nuna min iyakata a gidan nan, idan bazaki ci abinda na dafa da kaina ba, sai dai ki kwana da yunwar ki". Ta fice kamar kububuwa tana maganganu da fadace-fadace kamar sabon kamu.
Malam Hashimu ya sunkuyar da kai, Allah kadai ya san abinda ya ke tunani, zuwa can ya dago ya ce
"Sa'ade!"
Cike da haushin baban nata wanda ba ya iya tabuka komai a gidan sa, Laure ta gama raina shi sabida sanyin halin sa. Sa'ade ta daga kai ta sauke manyan idanun ta akan mahaifin ta. Ya ce "me yasa data baki dambun baki ci ba?" Ta bude baki cikin murya ta wanda ya ci kuka ya koshi ta ce "Baba ni bata bani ba, babu dambun data bani, bana gidan ma, tun safe ta dora min tallan gasara. Ni kuma sai na tafi makarantar su Hanne na tsaya a bakin taga ina jin yadda ake koya musu karatu, sai da aka tashe su na tafi tallan gasarar, kuma har yamma tayi ban sayar gabadaya ba, na dawo mata da saura shine take duka na".
Girgiza kai yayi ya ce "ki yi ta hakuri kin ji Sa'ade? Watarana sai labari. Insha Allahu sai Laure ta amfana da ke watarana, ina raye ko bana raye kullum ina gaya mata wannan. Ni Allah bai dora min iya fada da masifa ba, bana son su, ban kuma iya su ba. Shi yasa na barta da halin ta. Ki cigaba da yi mata biyayya, ita din duk yadda take uwa ce a gare ki. Da dadi ba dadi ta rike ki har kika kawo munzalin da kike yau. Shi yasa nake kauda kai akan duk muzgunawar data ke miki kada ta ce don ba ita ta haife ki ba........".
Sa'ade ta katse Baban ta da sauri da tambayar data dade tana cin ta a zuci.
"To Baba ni wacece uwata? A ina take? Ka ce tana raye, amma meyasa ban taba ganin ta ba ko a hoto?"
Fuskar Malam Hashimu nan da nan ta tattare ta koma kamar jikakken tsumma, ba ya son tuno ta.....ba ya son tuno duk abinda zai tuna masa da ita...... ta bar masa tabon da har abada bazai taba bacewa daga zuciyar sa ba! Ba kuma zai taba gayawa Sa'ade inda take ba har sai ita din ta nemeta da kanta, wanda ya san mawuyaci ne tayi hakan; a matsayin da take kai a yanzu, da kuma shi data gujewa. Da Sa'aden data haifa bada son ran ta ba! Ya riga yayi amanna da cewa....... ko bajima ko ba dade zata nemi Sa'ade, a lokacin da zai nuna mata shine ubanta duk talaucin sa. Mulkin ta bai yi isar da zai kwatar mata 'yar ta daga hannun sa ba.
Idanun sa suka kada suka yi jazur da ya tuno kiyayyar uwar ta gare shi, mummunar kiyayyar da ko a hikaya bai taba jin irin ta ba, ba don komai ba sai don shi talaka ne? Idan yayi la'akari da inda take aure ta kuma yi zaman ta yanzu? Daga ita sai shi, sai Ubangijin ta suka san dalilin kiyayyar ta gare shi. Murya a sanyaye ya ce.
"Ga Yalo da dafaffen rogo yi maza ki ci ki debi ruwa a randa ki sha, ni zan je na yi alwallah". Ya fada yana mai kaucewa kaifin manyan idon Sa'ade, wadanda a lokuta da dama suke firgita shi ya ganta ta rikide ta koma masa kamar BILKISU!
Sa'ade bata dauke idanun nata daga kansa ba har ya bar dakin, sannan ta ci dafaffen rogon ta koshi, bayan ta ture yalon gefe, ba ra'ayin ta bane. Ta kora da ruwan randar baban dake gefe mai sanyi da gardi. Ta mike ta fito tana leken Inna Laure a madafi, da ta ga hankalin ta ya dauku ga tukin tuwon data ke yi sai ta kwashi takalmanta a hannu ta danna a guje ta fice daga gidan.

Gida biyar ne a tsakanin gidan su da wanda ta shiga, ta maqe murya tana fadin "Hanne tana nan? Ta zo inji Iliyasu!" Hanne wadda ke alwala a gindin rijiya tayi murmushi ba tare da ta juyo ba ta ce "Sa'aden Baba, Sa'aden Hanne, Naziru na kira a dandali!". Suka kwashe da dariya a tare. Sannan Sa'ade ta shigo tana fadin "ai ban baki labari ba, jiya da ya zo waje na Inna Laure ta dage sai na fita, ina zuwa mun fara gaisawa ya saki wata tusa kamar mushen jaki, don wari ba shiri na gudu gida, gara mun dukan Inna akan tusar Naziru. Kuma lazim ne kullum ya zo sai ya yi ta.
Ni me yayi min zafi da Naziru? Ga saurin tusa sannan ga shegen surutu". Hanne sai dariya take yi harda hawaye.
"Inna Laure ke son sa sabida yana kawo mata dankalin da yake sayarwa kuma yana bata 'yar murtala idan ya zo". Innar Hanne ta fito daga bayan gida rike da buta da alama alwala zata yi, duk abinda suke fadi tana jin su, a ranta amincin su yana bata sha'awa, ta ce
"Ho! Sa'aden Hanne, ba'a fita da manghariba fa, na hana ki amma bakya ji, zo ga abinci na ajiye miki na san ba ki ci ba" Sa'ade ta tsugunna ta gaida Innar Hanne, ta wuce madafi kanta tsaye don ta dauki abincin data ce ta dauka. Kusan kullum sai Innar Hanne ta ajiye mata abinci.

Sai da suka yi sallah sannan suka ci abincin ita da Hanne a kwano guda, suna ci suna hirar samarin su suna kwasar dariya, Hanne ta roki Innar ta zata raka Sa'ade gida kada Inna Laure ta doke ta.
Har dakin Inna Laure Hanne ta raka Sa'ade, wadda ke rabe-rabe a jikin bango irin na wanda ya san yayi laifi, da Hanne ta fita ji tayi kamar ta bita a guje. Hanne na bada baya Inna Laure ta shaqo Sa'ade ta makure ta a jikin bango ta ce.
"Shine don kar ki kwashe min tuwo kika faki ido na kika tafi gantali ko? To kin yiwa kwanon tuwon ki, ko loma daya bazan baki ba, ki kwana da yunwar ki, 'yar banza mai mugun hali irin na uwar ta".
Sa'ade dai bata tanka ba, don inda sabo ta saba ji a bakin Inna Laure uwartamai mugun hali ce. Kuma dai a koshe take, don haka bata damu ba data ce bazata ci tuwon dare ba.
******
Washegari ma da Inna Laure ta dora mata gasara maimakon tabi gida-gida kamar yadda ta ke yi sai ta karkata hanya ta tafi makarantar su Hanne, yau ma a bakin taga ta tsaya daidai saitin da Hanne ta ke farantin gasarar ta yasar da shi a gefe. Malamin yana cikin bada darasi ya hangota tana leke. Zagayowa yayi ba da sanin ta ba sai ganinsa tayi a bayan ta, ta zabura zata gudu ya tare hanya.
"Shiga aji ki zauna, zan sa Dagaci ya yiwa baban ki magana, kullum ina ganin ki kina leken kawayen ki, wanda ke nuna kina sha'awar karatun da muke yi".
Bakin Sa'ade ya ki rufuwa don dadi, sai dai ta sani Inna Laure bazata taba bari ba, shi kuwa Baba sai abinda tace sabida tsoron masifar ta. Hankalin ta ya dauku ga abinda ake koya musu A BA CA DA Ee FA GA HA.....! Sa'ade ta bude murya tafi kowa yi... abinda ya dauki hankalin malamin a kanta ya gane da gaske take son karatun.
Don haka kamar yadda yayi alkawari har kasuwa ya bi Malam Hashimu bayan sun tashi, cikin nutsuwa ya neme shi ya bar Sa'ade ta dinga zuwa makaranta a daina dora mata talla. Malam Hashimu yayi shiru, daga bisani ya ce a sanyaye,
"uwar rikon ta bata so, kada ka sa ni a tashin hankali ina zama na lafiya".

Sa'ade data zo washegari malam yace tayi zamanta, ana tashi yaje ya gayawa Dagachin Tsanyawa, shi kuma ya tura aka kira masa Malam Hashimu da Laure, a gabanta ya ce yayi umarni ga Malam Hashimu ya saka 'yar sa a makaranta a daina dora mata talla lokacin zuwa makaranta, idan kuma sun ki to su tattara su bar Tsanyawa dama dukkan su ba haifaffun garin bane, gara Laure wadda ta zo da ita Tsanyawa daga kauyen Kiyawa 'yar asalin garin ce. Shi kuwa Malam Hashimu Dagaci ya ce har gobe bai san daga ina ya zo ba.

Mafari kenan da Sa'ade ta samu 'yancin zuwa makarantar boko har da ta allo, wannan bai hana Laure cigaba da dora mata talla ba a duk lokacin da ta dawo. Tana aiki tana mita tana tsinewa Dagacin Tsanyawa. A wannan lokacin ne makerin budurci ya soma kera Sa'ade, ta fara kirgan dangi har da jinin al'ada a shekarun ta goma sha biyu kacal.
Hanne ce ta koya mata kunzugu, da wankan sallah da tuni Innar ta ta koya mata don ta riga Sa'ade farawa.
Manema suka yiwa Sa'ade Caaaa! Manya da yara. Kai ka ce wata budurwar kirki ce, bayan Naziru mai dankali harda dan Dagachi dake karatu a birni, da wani Alhaji Talle mai mata uku amma yana da sukuni sosai. Kyawun fuskar ta shine abinda ya ke fara jan hankalin maza a kanta, wani irin sassanyan kyau ne da ita na mutanen wani yanki daga BORNO da ake yiwa laqabi da shuwa-arab wanda ake rasa gane daga inda ta samo shi don kwata-kwata bata yi kama da mahaifin ta ba, wanda yake baki, tittirna, mai gajeren hanci.
Mutane da yawa a garin na fadin Sa'ade ba 'yar sa bace, tsintota yayi, don babu wanda ya san shi da uwar ta, kawai an wayi gari ne an ganshi a garin tare da yarinyar 'yar shekaru uku yana rainon ta. Daga baya ya nemi auren Laure, ba bata lokaci aka bashi ba tareda binciken asalin sa ba don ta buwayi marikanta kuma ta rasa mijin aure duk fadin kauyen.

A tsakankanin wannan lokacin ciwon da aka rasa gane kansa ya kama Malam...


Read / Download MASARAUTAR MU

DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

DOWNLOAD
1 Comments On MASARAUTAR MU
avatar
zainabaliyu

7 months ago

Reply

I really appreciate masarautar mu, thank you

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album