Join Our WhatsApp Group

UNCLE DATTI JIKINA YA KE SO Complete Hausa Novel Document by UNCLE DATTI JIKINA YA KE SO


UNCLE DATTI JIKINA YA KE SO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 80772



UNCLE DATTI JIKINA YA KE SO

Reading Time: 6 Hours

Added On: 15, Sep 2023

Author: Eddatou ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : *????SHINNING STARS WRITER'S ASSOCIATION*

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 440.46 kb

File Type: txt

Views: 792+

Download: 494+

Last download: 3 days ago

Description/Story: *💫SHINNING STARS WRITER'S ASSOCIATION*

'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
                  JIKINA YAKE SO!
©
*eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*

*GARGADI:* '''Ban yarda a sauya min labari, editing ko cutting page daga cikin littafina ba tare da izinina ba dan haka a kiyaye.'''

*HASKE:*''' Kirkirarren labari ne wanda ban yi shi dan komai ba sai dan na tunasar da mu wasu muhimman abubuwa dangane da rayuwar mu ta hau da kullum.'''

Page 1-2

*************************⬇**********************
************* Top Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.thn.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > tophausanovels@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Top Hausa Novels

Twitter: Top Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/tophausanovels

Telegram Group: https://t.me/tophausa


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na TOP HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Top Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Yarinya ce y'ar kimmata shekara tara taci ado cikin English wear na gown an tufke mata kai da baby pink d'in ribbon mai kyau.
Ba wata fara bace cen amma ba laifi kakkyawa ce son kowa kin Wanda ya rasa, tana da dimple a kummatun ta da suke lotsawa a duk sanda take murmushi ko dariya hakan ba karamin kawata fuskan ta yake yi ba.
" Aunty aina!!!! Aunty aina ki bani chocolates d'in da uncle datti ya sayo min", ta fad'a a lokacin da take nufar parlorn da mugun guru saboda har ga Allah tana mugun son chocolates hakan ya sa a kullum tazo gidan sai ta saka uncle Datti ya saya mata.
" Allah Khadija ba zan bayar ba, wai shin ba na hana ki shan zaki ba? ko zo kike yayi miki illah ne? ta fad'a a takaice tare da d'an had'e rai".
"Eeeyyaaaa aunty na yi hakuri ki ban, yau d'aya kawai ki ban nashi daga yau ban k'arawa.
" Hmmmmm nana kenan ke yarinya ce ba za ki fahimci illan shan zak'i ma mace ba but tunda kin ce haka mik'a min eye glass d'ina na saka sai muje na d'auko miki", domin Rana mugun fama da chronic ciwon ido bata gani sai da glass medicated, idan babu wuri duhu baka kirin yake koma mata hatta tafukan hannayen ta ma.
Kamar dama jira take yi ta d'au glass d'in a kan glass table ta mik'a mata ta karb'a ta kafa daga nan ta jawo hannun k'anwar ta suka shige d'aki tace ta tsaya a waje dan kar taga mab'oyan.
Guda d'aya ta fito dashi ta mik'a mata ungo wannan tafi kar ki kuma damuna.
Maimakon ta k'arb'a ta turo baki ta tare da sakin kukan shagwab'a wai ita baza ta k'arb'a ba sai an kara mata.
Jin kukan nata yayi yawa uncle Datti ya fito ranshi a b'ace, shi dai bai san me ya saka saffffff baya k'aunar b'acin ran baby angel ba balle kukan ta, a duk ran da ta saki kukan rigima bai da tsukuni a zuciyan shi har sai ya biya mata bukatunta tayi shiru.
So tari idan yana rawar k'afa a kan Nana Aunty Aina har mamaki take wai shin tsakanin ita da Nana was yake aure? Me yasa baya tarairayanta kamar yanda yake yi mata? ko dai Uncle Datti son Nana yake, duk wannan tunanin su suke mata yawo a kwakwalwar ta ba tare da ta samo amsar su ba.

Gani tayi ya nufo wurin Nana ba duk ya gigice ya susuce kamar wani wawa yana lallashin ta" shiru, yi shiru my angel fad'a min me ke damun ki, wa ya tab'o min ke", ya jero mata tambayoyi a tare.
Baki wangalau aunty Aina ta bud'e tana kallon shi da mugun mamaki, abunda ya dad'a bata mamaki ji tayi Nana ta kuma rushewa da kuka har tana shid'ewa ala dole ita tayi fushi shi kam sai ma gabaki daya ya fita a hayyacin shi ya rasa ina zai saka kanshi yaji dad'i.
Zumb'uro baki tayi cikin shagwab'ar ta tace "Uncle chocolate zan sha, aunty Aina tak'i ta k'ara min", ta fad'a cikin kuka tana langab'e kai.
" To to to yi shiru zo muje na saya miki, fita suka yi daga gidan shi da Nana suka bar Aina a tsaye jigum kamar gawa tana mamakin Datti.
Da taga abun ba mai k'arewa bane ta fad'a kitchen ta dafa had'add'iyar shinkafa jelof wanda yaji kayan had'i, ga wani uban k'amshi da ya gama gauraye kitchen d'in, tana gamawa ta fad'a d'aki ta rage kayan jikin ta kana ta fad'a bathroom. Tana gamawa ta fito ta shirya tsaffff cikin leshi mai ruwan toka d'inkin riga da zani. Kallo d'aya zaka yi mata ka san cewa ta had'u ba k'arya domin kyaun ba daga kayan jikin ta bane daga itan ce, cuz she is a kind of beautiful.
Parlour ta koma ta zauna shiru- shiru babu su babu alamar su har aka fara k'iran sallar Magrib, tayi alwala ta gabatar da sallar ta, tana idar da sallar kenan sai taji sallamar Datti a d'akin ta, ta amsa tare da juyowa sai ganin Aina tayi da kaya niki-niki a laida ta tare ta da ido tana kallon ta".
"Heeeee madam wannan kallon na mene ne?, Datti ya fad'a yana tapping d'inta da hannu."
Ta d'an had'e rai tana kallon shi haba dear d'ina for how long zan fad'a maka cewa ka rage saya wa yarinyar nan kayan zak'i? You now it ba sai na fad'a maka dalilina ba sanin kanka ne cewa akwai mai ciwon Suger a family d'in mu and ance ana gadon ciwon ko ka manta ne".
Come on wife......., ya fad'a tare da jan maganar, i know ina sane ban manta ba sanin kanki ne nima ba zan so abunda zai cutar da ita, ciwon suger bata kama yara under ages da zarar mutum ya doshi shekaru 40 a lokacin ne aka bata shawara da ta dinga kiyayewa."
Amma duk da haka ka rage, kana shagwab'a yarinyar nan da yawa.
Murmushi yayi mata yana cewa" duk abun da nayi wa Nana ban fad'i ba jinin mu ce ita".
Ganin yanda ta had'e rai ya san ya tab'o mutuniyar hakan yasa yace wa Nana ta je d'aki ta jira su, hakan kuwa aka yi bayan fitan ta ya rungumo abar shi zuwa jikin shi ya hau lallab'a da kalan soyayya har sai da ya tabbatar ta sauko.
Kasancewar shi ma'aikacin gomnati hakan yasa washe gari da safe ya shirya ya tafi Office dan akwai wani aiki a gaban shi da yake so ya kammala. Kwararren likitane asubitin Plateau Hoptil da ke garin jos, yana isowa ya tarar an kawo musu patient da za'ayi mata surgery breast d'inta wacce bayan gwaji aka tabbatar da tana d'auke da breast fibro domain", haka suka shigar da patient d'in suka hau yi mata aiki, tun shigowan shi surgery room d'in sai wajen k'arfe uku kafin nan ya samo ya huta cuz aikin yau ba sauk'i mutane sunyi musu yawa".
Bayan ya fito ne ya soma nema number d'in Aina a waya cikin sa'a ringing d'aya ta d'aga tare da yi sallama ya amsa mata".
"Wife kin ji wajena shiru ko?
" ummmm", ta amsa tana mai dad'a manna wayan a kunnen ta".
" Baby angle d'ina fa it has been long to hear from her".
"Tana room d'in ta she is busy playing with her teddy", hmmmm wait kitso take mata".
" Dariya mai sauti yayi kafin yace" baby angel kenan sarkin rigima any ways nima yanzun nan na kammala aikina yanzu ma haka gida na nufa, me zan taho muku da shi?"
"Komai muna da shi my man domin kuwa baka rage mu da komai ba".
Tsintar kanshi yayi da jin dad'in maganar ta, Aina mace mai tattausan lafazi, ta san k'almar da zata yi amfani da shi dan ta faranta mishi.
Bayan sunyi sallama ya kashe way an shi daga nan ya shige mota bai zame ko ina ba sai family house d'in su ya tarar da kakar shi Hajiya Rahane wacce suke k'ira da tsohuwa tana kallo a talabijin tana yi tana karkad'a kai".
Sallama yayi mata bata ji ba har ya zauna bata san da ma ya shigowa ba, tsinkayo muryar shi tayi yana cewa" tsohuwa kallo ake yi ne nake ta sallama baki ji ba?
Ta juyo a hankali tana kallon shi d'auke da murmushi a fuskanta" ai film d'in ne tayi dad'i da yawa, Allah idan ina kallo mai dad'i har ban so na daina".
" Dariya yayi, ya mik'e ya d'auki goran ruwan faro ya b'alle murfin ya kafa a bakin ya hau sha, tsohuwa kan ci gaba da kallon nata tayi cikin shauk'i tana murmushi. Sai da ya sha iya shan shi kafin ya cire goran a baki ya maida muffin ya rufe yana cewa" affff ashe ma bamu gaisa ba, ya gaishe ta ta amma ba tare da ta d'auke idanuwan ta akan TVn ba".
Da yake daffffff take da ta gama kallon haka shima ya zauna jiran ta amma shi ba kallon yake ba, fito da waya ya shiga gallery yana watching hoton baby angel.
Bayan ta kammala ne ta tattara dukkan hankalin tace" Abubukar", ya d'ago da sauri yana kallon ta da mamaki ji yayi ta k'ira sunan shi gasau babu sakayawa.
" Ya baka taho min da y'ar jikalle na ba,? Tana nan sai rigima take yi kin san halin Nana".
"Y'ar neman nan ba ta samu kana biye ta ba dolle yayi, ni dai ban san ranar da zata yi hankali ba".
" Tsohuwa kenan, dai-dai da rana d'aya bana k'aunar b'acin ran Nana shi yasa nake biye ma fitinar ta".
Haka dai suke ta hira kusan rabin hiran akan Nana ya kare, bai wani dad'e ba yayi sallama da ita ya nufi b'angaren mum d'in shi ya gaida ta kafin nan ya shige sauran sauran b'angarorin ya gaishe su daga nan kuma ya nufi gida a ranshi yana jin tsananin kewan Nana na kama shi.

eedatou muje zuwa..............

*💫SHINNING STARS WRITER'S ASSOCIATION*

'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
               JIKINA YAKE SO!
©
*eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*

Page 3 and 4

Ba shi ya iso gida ba sai wajen karfe takwas da rabi na dare cuz of go slow din da yaci karo dashi a hanya.
Ko da ya iso ya tarar Nana a kan kujerar three seaters tana sharar barci sanye take da riga da gajeriyar wando wanda bai gama rude kanta ba, tsayawa yayi for some few seconds yana kallon ta murmushi ne ya d'an sub'uce mishi" lallai Nana sarkin kiriniya ji yanda take ta sharara barcin ta hankali kwance", bin kayan jikin ta yayi da kallon sai yaga ta bala'in yi mishi kyau domin kuwa shekarun Nana bai hana bayyana kyaun surar ta ba, yanda jikin ta ya murje yayi b'ulb'ul zaka d'auka kamar ta yaran larabawa d'innan ne. Tsintar kanshi yayi da nufar wajen ta ya tsugunna dafff kunnen ta ya hura mata iskaaaa", cikin barcin ta taji, ta d'an yi mik'a kamar zata rashi sai ta gyara kwanciya ta koma ta kwanta.
" Cije libs d'in shi yayi a hankali ya kuma kafe ta da ido, komai na Nana daban ne tana da kyau da kan diri, a hankali ya sa hannu biyu ya kinkime ta ya soma tafiya da ita, yayin da ya maida jakan shi da ya shigo da ita d'aya hannun nashi.
D'akin shi ya nufa ya dire ta a kan bed d'in shi kana ya lek'a d'akin Aina ya tarar da ita kan Sallaya ta idar da sallah kenan tana lazimi.
Zama yayi a kan tafkeken bed d'in ta ya jawo pillow ya kishingid'a yana jiran ta har ta idar ta ninke sallayar ta ajiye tare da zare hijabinta shima ta tana ninkewa lokaci guda tai murmushi tana kallon Datti" barka da dawowa mijina", da murya mai zakin gaske ta fad'a.
Amsa mata yayi shima cikin murmushi kana ya d'an turbune fuska da tsigar wasa yace" shine kika bar min baby angel d'ina a parlour ita kad'ai ko? Wife mun kusa mu bata fa",.
Ohhhhh damn it!!!!!!!!, na manta Nana batayi sallah ba take barci sai yanzu na tuno ma, mai baby angel tare muke da ita nima sallah ne ya shigo dani amma bari na tada ta".
Kafin ya bud'e baki yayi magana tuni tayi hanyar parlour ko da ta iso bata tarar da kowa ba ta lek'e bayan kujera nan ma babu ita babu alamar ta, nan idanuwan ta suka cicciko kamar zata yi kuka? Ina Nana ta yi da daren nan ita da ta barta tana barci? Tsoro ne ya d'an kamata a lokacin da wani tunani ya fad'o mata ta safe kirji tare da waro ido waje" na shiga uku kar dai shigowa gidan nan akayi aka tafi da Nana"?
Kuka ta fashe da shi da gudu tayi d'akin ta ta tarar da Datti a inda ta barshi yana ganin yanayin da ta shigo a firgice yace lafiya kika shigo haka? Me ya faru? Banda kuka babu abunda take yi da kyau ta iya bud'e baki tace" banga Nana ba?"
"Kamar yaya baki ga Nana ba? Ya jefa mata tambaya fuskar shi na bayyana mamaki.
Wallahi na duba kafff parlourn nan babu Nana babu alamar ta, nafi kyautata zaton satota akayi".
Sai yanzu ya fahimci inda ta dosa bai san sanda dariya ya subuce mishi ba har sai da ya kular da ita tace" wato baka damu da b'atan baby angel d'in da kake ikirarin taka ce ba shine ma na zama abin dariya?, ta kuma rushewa da kuka tana tunanin halin da y'ar k'anwar take ciki".
Ganin abun nata dad'a k'aruwa yake yi gashi ko kad'an bai son jin kukan mace balle na wacce take da muhimmaci a rayuwar shi, wacce babu abunda zai iya saka mata da shi sai addu'a domin irin guduwar da ta bayar a rayuwar shi, ba shiri ya had'iye dariyar shi, cikin rad'a yace" yi shiru daina kukan haka matata idan ba su kike ki saka nima na taya ki ba, guess what? baby angel na d'akina tana barci.
Kuka mai d'auke da hawaye ne ya makale mata lokaci guda tace" Dan Allah? da gaske? ya d'aga mata kai alamar "eehh"
Zolayar ta yayi yana cewa" Ashe Ainata ma ta damu da baby angel d'ina amma tafi ganin ganin ina son baby angel fiye da kowa.
Kin san dalilin da yasa nake son Nana?
Ta girgiza mishi kai tare da yin kasa da kan ta tana murmushi kasa-kasa, " sabo da wife d'ina tana sonta bayan haka jinin mu ce ma'ana soyayyar Nana a jinin mu yake".
A tare suka kwashe da dariya daga nan suka d'unguma parlour ta...


Read / Download UNCLE DATTI JIKINA YA KE SO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album