Join Our WhatsApp Group

TAUFEEK Complete Hausa Novel Document by TAUFEEK


TAUFEEK

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 108758



TAUFEEK

Reading Time: 9 Hours

Added On: 29, Sep 2023

Author: Hafsat A Garkuwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : AL'UMMA WRITER'S ASSO

Author Phone : 08132761212

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 548.16 kb

File Type: txt

Views: 842+

Download: 634+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: *TAUFEEƘ*

       NA
*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

*AL'UMMA WRITER'S ASSO...*✍🏻

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

'''Alhamdulillah!Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah nagode maka da ka bani ikon dawowa a karo na barkatai, Allah ka bani ikon rubuta abunda Al'umma zasu amfana dashi, ka tsare alƙalamina da rubuta sharri, Real fan's gani na sake dawowa ƙaunar da kuke nunawa book ɗina ne yasa na dawo muku tare da zazzafan littafi wanda ke ɗauke da darusa da dama, dafatan zakuci gaba da bani haɗin kai domin da bazarku nake takawa, kar na cika ku da surutu ku dai mu haɗu cikin labarin mai taken''' *TAUFEEƘ* '''wanda yazo muku da sabon salo.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🚴🏻‍♀️'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💞 Sa'eedina matuƙar gdy a gareka da gudummawar da kake bani tare da ƙarfafamin gwiwa Rabbi ya tsare min kai a duk inda kake, ya ƙara maka lafiya da nisan kwana amin ya rabbil izzati.🤲🏻'''

*Episode 01*

'''Kaduna'''

*Millonium city* anguwa ce wacce ta tara manyan attajirai masu faɗa aji a cikin Kaduna, tare da rantsartsun gida tamkar wanda aka dasasu saboda yadda tsarin gidajen anguwar yake kai kace kawai tsirowa sukayi, haka gidan *Alhaji Nasir Adam Salwa* yake shima, da sauri na ƙarasa ganin kaf anguwar gidansa yafi na kowa haɗuwa ina saka kaina kiɗa na faraji yana tashi, na babban mawaƙin nam *Justin bieber* cikin waƙarsa mai taken *Let me love you* sosai kiɗan yake tashi kai kace gidan disko ne, filin gidan na shigo wanda suke ƙayace da Flower masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali gefe guda kuwa babban compound ne mai cike da rantsartsun motoci masu matuƙar tsada da kyau guda 12 ga fili nam wanda zai iya ɗaukar fiye da 10 tsakiyan gidan zagaye yake da wasu flowers masu fidda wuta da dare ga wani ɗan rami dake fidda ruwa fari sal, abun gwanin birgewa, kamar daga sama naji wani mutum na cewa "wlh yaran nam sam basu da ta ido ku zauna ku ƙurewa mutane sauti kamar wanda kuke gidan disko. kallon inda naji maganar nayi wasu ƴan matasa ne su biyar suna zaune a wata ƴar runfar shaƙatawa amma kana kallonsu kasan masu aiki ne ɗaya ne ɗan dattijo sosai a cikinsu duk da manya ne amma ɗayan ya girmesu, dariya suka saka jin abun da Ali yace, na kusa dashi ne yace "kai dai ka bari Ali wlh lamarin Yaran yana bani haushi. Ɗan dattijon ne yace "ai ba ku kaɗai ba wlh shiyasa bana so Yallaɓai *TAUFEEƘ* ya bar gidan nam dan da yana nam sai dai kaji ƙira'a yana tashi duk da shima yana sa kiɗam amma ba irin na mahaukatan nam ba na su marigayi Shata yake sakawa duk da yana ɗan saka nasu Adamu zango.
Gaba ɗaya suka sa dariya Garba yace "Baba zancenka haka yake wlh amma kaga su *Nazmar,* *Jawaad,* *Nabeeha* sam basa ji kamar masu kunnen ƙashi in har Yallaɓai *TAUFEEƘ* baya nam to sufa sallarsu ce shiyasa nake addu'a Allah ya dawo da yallaɓan mu lfy, gaba ɗaya suka amsa da "Amin ya rabbi.
Sallau ne yace "ai baku san wani abu ba kunga wannam ɗan chakurkurin Yaron? mai sunan larabawa *Ka'aaf* ko? to wlh shima ya shiga cikinsu dan ko jiya da Mai gida ya aikeni a tsakiyansu na tsince shi yana ta tiƙar rawa. gaba ɗaya suka bushe da dariya Sani harda riƙe ciki dan kaf cikinsu ya fisu iya dariyar mugunta.😹
Wajen na barsu suna ta tsaigumin su dan nima sai da na dara dan yanayin yadda suke maganar dole ya baka dariya, nufar cikin gidan nayi wata ƙofa ce ta glass da glass gabana sai da ya faɗi ganin ina hango kaina a ciki, ƙarasa wa nayi a hankali na danna wani rame wajen handle ɗin kawai sai naga ƙofar ta buɗe wani irin sanyayan iska tare da ƙamshi naji ya bugi hanci na takawa na farayi a hankali na nufi cikin katafaren falon, Ji nayi ƙafata ta nitse a cikin wani abu mai matuƙar laushi da taushi da sauri na kalli wajen domin naji yadda ƙafata ke lumewa ba tare da nasan inda take shiga ba, wani jahilin carpet na gani mai matuƙar ɗaukar hankali ɗan madaidaici ne jikinsa ko bayan kuliya albarka tsabar laushi, ban tsinke da lamarin ba saida naga yadda tsarin falon yake, Babban falo ne sosai wanda yake Ƙayate da kayan more rayuwa masu ɗaukar hankali tsayawa faɗa muku yadda fallon yake ma ɓata lokaci ne, gefen da nake jiyo sautin ƙiɗa na kalla, masha Allah na furta domin ganin wasu wanda nake tunanin sune su *Nazmar* maza ne guda biyu sai kuma mace ɗaya wacce baza ta wuce 19 year's ba sanye take da riga iya gwiwa Pink colour wacce taɗan kamata tana da manyan na fulani wanda suke a tsaye ƙyam kamar zasu faɗo ƙasa, sanye take da wando fari sol wanda ya matuƙar matseta da kaɗan ya wuce gwiwarta doguwace amma ba sosai ba sai dai farace sol, ƙafarta sanye yake da takalmi mai tsine mai igiyoyi pink colour kayinta ba kwali sai uban tilin gashi da ya zubo mata har gadon bayanta baƙiƙƙirin a tsefe fuskarta ƴar madaidaiciya ce mai ɗauke da manyan idanu wanda yake cike da gashin ido giranta ba a cike take ba, dogon hancinta ɗauke yake da ɗan ƙaramn bakinta kallan pink sai motsi yake da alamar waƙar take bi, a duk motsinta dimple ɗinta sai sun lotsa rawa take cike da burgewa duk wani sassa na jikinta motsawa yake duk da batayi kwalliya ba amma *Nabeeha* ƙarshe ce wajen kyau dole duk namiji mai jini a jika in dai ya kalleta sai yaji wani sauyi a cikin jikinsa lokaci ɗaya zata tafi da imaninsa.

Mazan kuwa da baza su wuce 26 year's ba kansu ɗaya kana kallonsu zaka fahimci ƴan biyu ne saboda tsantsar kamar da sukeyi da juna, sanye suke da t shirt ash colour da wando baƙi iya gwiwa kansu cike yake da gashi irin na fulani fuskarsu ɗauke take da siraran idanu masu ɗaukar hankali ƙafansu sanye take cikin takalmi sauciki shima ash dole in ka kallesu sai sun burgeka dan iya kyau *Nazmar* da *Jawaad* suna dashi wani kyakyawan yaro na gani a ƙasansu wanda bazai wuce 4 year's ba sanye yake da kaya sak kallan nasu Nazmar komai iri ɗaya ne yaron kyakykyawa ne sosai mai fara'a shima kamar su ɗaya dasu Jawaad sai dai har shi ya fisu kyawu *Ka'aaf* kenam shalelen gidam.

Rawa suke cike da ƙwarewa sosai suke bin waƙar da yadda rawan waƙar take, kamar daga sama naji ance "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Nabeeha! mai kike haka? ta faɗa cikin tsawa dan tasan in ba tsawar tayi ba baza sujita ba,kallonta nayi daga sama har ƙasa babbar matace wacce daula tabi jikinta dan in ba ka sani ba baza kace shekarunta sunkai 50 ba saboda jikinta sam bai nuna haka ba ƴar gajeriya ce amma ba sosai ba ba fara bace sosai sai dai Allah ya mata kyau kana kallonta za kaga tsantsar kamar da suke dasu Jawaad sanye take da rantsatstsan leshi mai matuƙar tsada da kyau baƙi mai ratsin golden, tasha ɗauri sarƙarta ta gwal sai sheƙi take har awarwaron hannunta ta gwal ce ƙafarta sanye take da flat ɗin takalmi golden babban mayafi ta yane kanta dashi shima golden colour sai baza fitinannam ƙamshi take kana kallonta kasan daga anguwa ta dawo domin yanayinta akwai gajiya.
Nabeeha jin muryar tayi kamar daga sama da sauri ta jiyo ta nufota cike da shagwaɓa tana zuwa ta faɗa jikinta cikin shagwaɓarta wanda yabi jikinta tace "Allah sarki my sweeti na wannam ƙiran ai sai ki kashewa shalelenki dodon kunne. ta ƙarasa tana rungumeta tare da shigewa jikinta.
Murmushi dattijuwar tayi tace "wlh Nabeeha in kika yi wasa sai na haɗaki da *Taufeeq* ya chaskalamin ke tunda na fahimci bakya jin maganata.
Ƙara shigewa jikinta tayi tace "ni dai pls ki daina min maganar wannam Ya Taufeeƙ ɗin dan ni ban san waye ba, ta faɗa a sangarce tare da murguɗa baki. "Oh haka kikace ma wlh ko kamar a kunnensa ni maza ɗagani na ƙarasa na gaji sosai wlh. ta faɗa tana tureta daga jikinta ta nufi cikin fallon. Nazmar ne ya kashe ƙiɗan suka nufo cikin falon suna oyoyoo my sweetie!!! zaunawa su Nabeeha sukayi a manyan kujerun dake falon ta kwanta a kan cinyarta ita ko sai shafe kanta take suna dariya jin tahowan su Nazmar, suna zuwa suka rungumeta suna sake cewa oyoyoo Sweetien mu sannunki da dawowa i miss u wlh suka faɗa a tare harda Ka'aaf da ya ɗale cinyarta dan sun koya masa komai shima, mamaki ne ya kamani jin sunan da suke ƙiran mahaifiyar tasu wai Sweetie abun gwanin burgewa.😄

Kamar daga sama sukaji ana "kai! kai!! kai!!! mai kuke shirin yi haka? karya min Matar kuke so kuyi? wlh kar na iso na sameku dan zanyi mogun saɓa muku banson sangarci wollah. wani ɗan dattijo ne mai matuƙar kyan gaske wanda zai kai 62 a duniya amma jin daɗi ya ɓoye hakam sanye yake da wata ɗanyan shadda fara sol wanda tasha aiki daga gani shine mahaifinsu miji ga Sweetie,gaba ɗaya suka kallo inda yake cike da fara'a bakinsu a haɗe sukace "haba Papa ai Sweetie tamuce ta amana babu rabuwa a tsakanin mu. suka faɗa cike da zolaya Papa yana ƙarasowa ya jawota jikinsa yace "dole ko zaku rabu dan jakar ubanku, maza Queen mu haura sama dan nasan kin gaji sosai amma suna so su ƙara gajiyarmin dake, ya faɗa yana shigar da ita jikinsa, ba ruwansa da ƴaƴansa da suke kewaye dashi, Sweetie dai duk kunya ya ishe ta ganin shi ko a jikinsa ne yasa ta ɗan basar dan inda sabo ta saba, su Nabeeha ne cike da wasa bakinsu a haɗe sukace "gaskiya ana bawa luv haƙƙinsa anam wajen. Papa da ya riƙe Sweetie suka fara haurawa sama yace "kwaji dashi dai wlh dan ni nayi nam da Queen ɗita haka kawai baza ku nakasamin ita ba. a haka suka haura wani ɗaki suka shiga wanda ya ƙayatu da kayan more rayuwa suna shiga ta janye jikinta cike da kunya tace "wlh Papa'n yara kana kunyatar dani gaban yaran nam kasani sarai yanzu fa mun girki amma abubuwa kake min kamar ba gobe. ta faɗa cike da shagwaɓa, dariya yayi yace "Allah in dai nine sai dai nayi ta baki kunyar kawai kawai bazanyi luv ba dan na tara yara bazai yiwu ba in kuma bakya so sai dai na ƙaro miki amarya wacce zata na biyeni muna shan luv abunmu. ya faɗa cike da zolaya dan yasan abin da tafi tsana kenam duk duniya shima ya faɗa ne kawai amma ko da wasa bazai fara ba.
Kallon sweetie yayi yaga gaba ɗaya annurin fuskarta ya ɗauko kuma sarai yasan dalili dan a rayuwarta babu abun da ta tsana irin maganar kishi ji take kamar zuciyarta zata buga matuƙar aka kawo mata zancen kishi, da sauri ya jawota jikinsa tare da ɗaura hannunsa a kan fuskarta...

★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★

Kuka take sosai kamar ranta zai fita ta saka gawawwakin iyayenta gaba wanda aka musu kisan wulaƙanci, sosai take kuka tare da cewa "Abba dan Allah karku tafi ku barni wajen ƴan uwanku wlh daga ni har ku ba son ku suke ba, kuyiwa Allah ku tashi karku tafi ku barni kuzo mu tafi tare daku wlh barina a duniyar nam tamkar barina a cikin rijiya ne mai cike da zakuna da macije... wani kuka ta kuma fashewa dashi mai matuƙar ban tausayi, wasu mutane ne suka shigo falon fuskarsu babu wata walwala suna zuwa gabanta suka tsaya ɗaya daga cikin su ne ya ɗaga hannu ya wanketa da wani irin gigitaccen mari har sau biyu, cikin kakkausar murya yace "wlh wannan furucin da kike sai kinyi dana sanin yinsa dan kin samu kina da dangin mahaifi kamar mu marassa manta alheri shine kika wannam zancen banzan to wlh zaki yabawa aya zaƙinta sai kinyi dana sanin furucin da kikayi shegiyar yarinya mai suffar kafirai, ƙafarsa ya ɗaga ya sauƙe mata...'''(Ya kuka ji labarin? sai dai kuma fan's banyi alƙawarin typing kulluma ba matuƙar kuna comment yadda ya kamata to zanyi ƙoƙari ina baku update rashin comment ɗinku shi zaisa ku jini shiruuuu😹comment ɗinku shi zai nuna min yadda book ɗin ya karɓu a gareku.)'''
08132761212

*ONE LOVE*💕🤞🏻

*TAUFEEƘ*

  NA

*HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Wattpad='''
*MUM SEEYAMA*

'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

'''Bismillahir rahmanir rahim'''

*DEDICATED TO*
'''My Soul Musa💋 Sa'eed.'''

*Episode 02*

*…* Sosai Papa yake faɗa mata kalamai masu matuƙar sanyaya zuciya, har ya samu ta sauƙo suka lula duniyar su ta masoya, domin Papa gogagge ne wajen iya tarairaya da iya sarrafa mace, duk iya war mutum Papa gaba yake dashi, hakan yasa Sweetie take ƙara jin ƙaunar sa a cikin zuciyarta.

'''(A nam zan ɗan ja hankalin maza kafin na iso fannin mata, mace tana matuƙar son iya tarairaya da riritawa musamman wajen sex tana so ayi mata wasanni sosai saboda hakan shi zai ƙara mata ƙaimi wajen taimaka maka, sannam ke ma ba wai zama za kiyi kamar wanda zaki ɗauk hoto ba dole zaki taimaka masa wajen tayasa ziyarar da zayaje😉 hakan shi zai ,№2ƙara muku so da ƙauna tare da shaƙuwa me ƙarfi  yaji fa in fa bake ɗin nam ba sai rijiya lol.'''🤣)

  Su Jawaad suna zaune sai bawa Nabeeha labarin su Papa da Sweetie suke irin soyayyar da suke bugawa tun suna yara kasan cewar ita bata jima da zuwa gidan ba domin ita ƴar ƙanwar Papa ce da yake London Allah yayi masa rasuwa shi da mahaifiyarta saka makon haɗari da suka yi, hakan yasa Papa ya dawo da ita gabansa domin su uku kawai iyayensu suka haifa daga Babar Yayar su Aunty Sa'a sai shi sai ƙaninsa mahaifin Nabeeha, duk da Aunty Sa'a taso ta karɓeta ganin ita ce mai yara mata kamar Nabeeha har su uku sai kuma babban ɗanta guda ɗaya shine namiji, amma fir Papa yaƙi hakan yasa dole ta haƙura ta bar masa dan gudun kar zumuncin su ya ɓaci, dan Papa yana da matuƙar ɗaukan zafi zuciya ne dashi kamar me, amma kuma mutum ne me sauƙin kai da barkwanci, yaran Papa huɗu Taufeeq shine babba wanda yanzu haka yana ƙasar Istanbul shugaban ƙasa ya turasa ya wakilcesa taro, Minister ne shi duk da ƙarancin shekarun sa 32 year's babban miskili ne na bugawa a jarida, baya son shashanci baya ɗaukan ƙazanta da rainin hankali, ɗan gaye ne sosai yana son mutum me ganin girman na gaba dashi, da wuya kaga dariyarsa sai dai duk randa kaga dariyas sa baza ka taɓa marmarin ya daina ba, duk da haka fuskarsa ba yabo ba fallasa, tun yana yaro yake son harkar siyasa domin shi ya tashi yaga mahaifinsa yake yi, hakan yasa bai sha wahala ba wajen zama minister, duk da dama ya chanchanta...


Read / Download TAUFEEK

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album