Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

GIDAN BATURE Complete Hausa Novel Document by GIDAN BATURE


GIDAN BATURE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 48741



GIDAN BATURE

Reading Time: 4 Hours

Added On: 20, Aug 2023

Author: Ummu Subay'a ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 280.11 kb

File Type: txt

Views: 2211+

Download: 2172+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story & Family Saga)

Ummu Subay'a

dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)

Wattpad UmmuSubaya

Ina mai bawa SOYAYYA CE fans hakurin rashin ci gaba da banyiba a dalilai na tsaro

Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE

0⃣1⃣

"MA'U MA'U MA'U pls xo kiban littafina ai bani na hanaki yin assignment dinba, kuma ai kinsan ina baki ki copy idan har ba'a mana gargadin kada a kawo iri dayaba"
Wata yarinya ce da baxata wuce shekara 15 ba takebin wadda ta kira da MA'U itama baxata wuce 15 years dinba, tanata mata magiya


Amma ko a jikin Ma'u sai tafiarta take kamar ba da ita akeyiba hadda guntun dariarta

Palon Amminta ta nufa kai tsaye anan ta taradda Anty Jidda tana bawa diyarta Amal nono, tunda taga Ma'u ta shigo da sauri tasan akwai magana

" wa kuma kika tabo Anty Masifa" bata gama rufe bakinta ba Sukrah ta shigo kamar xatayi kuka

Murmushi Anty Jidda tayi tace

"Nasan xa'a Rina ai, Shukrah me tayi miki?"

Hawayena suka fara ambaliya a fuskar Shukrah

"Assignment nawa ta kwace wai xata kwafe kuma.tacewa Uncle namu nice na kwafe nata baicin kuma yace bayason copy copy"

Kallon bbu wasa Anty Jidda tama Ma'u wadda take tsaye ta kama kumkuminta kamar wata babbar mata

" maxa bata littafinta"

Bani Ma'u ta tura tace

" wlh baxan bataba don ban yiba kuma ban iyaba, da a dake ni daya gwara an dakemu mu biyu"

" xaki bata ko sai na tashi na babbalaki a wajen"

Ganin sarai Anty Jidda xata aikata abunda tace don tasan ba'a kawo mata wargi yasa ta fara kwadawa Amminta kira

Ai kuwa bbu bata lokaci sai ga Ammi ta bayyano

" keda wayene? Sam ba'a barin kuruwarki ya huta sai an dinga daga miki hankali"

Ssai Anty Jidda ta bata rai tasan sarai yanxu Ammi xata goyi bayan Ma'u

"Wlh Ammi kekike goyawa Ma'u baya take duk fitsarar dake, har ta isa na bata umarnin tace baxatayi ba, wlh kada kiga idon Ammi idan bakiyi maxa ki bata littafinta ba bbu Uban da xai hanani farfasa miki jiki da duka"

" uwar ubankine xata hanaki fasa mata jiki da duka kinji ko nace ni nan Asma'u uwar Ahmad ubanki ni xan hanaki fasa mata jiki da duka, littafi kuma baxata bayarba, ke kuma munafuka kinyi fuska kamar wata munina kina jira a amsa miki littafinki to baxata bayarba maxa bacemin daga part

Da gudu Shukrah ta fice tana kuka mai ban tausayi don ta tabbatar littafinta ya tafi kenan forever

A balcony Shukrah taci karo da Zahra, har xata wuceta Zahra ta kamo ta

" keda waye? Waya dakeki"

Cikin kuka Shukrah ta mayarwa Zahra abunda ya faru, ssai ran Zahra ya baci kama Shukrah tayi suka koma Palon Ammi

Nan ma sun sami Jidda nata mitan abunda Ammi tayi

Saura kiris fitsari ya kufce a marar Ma'u ganin Zahra Dodonta, bbu shiri ta koma bayan Ammi

Ita kanta Ammi tasha jinin jikinta ganin Zahra don tasan bbu abunda xai hanata karbar littafin

" to algumguma kinje kin dauko Anty fitsara taxo karba miki, to bari kiji ko uban Zahra'un kika kawo baxa'a bada littafinba"

Inji Ammi tana kara kare Ma'u dake bayanta

Ganin.tsayawa magana ma bata lokaci ne yasa Zahra nufo bayan Ammi gadan gadan don amsar littafin

Cikin karfin hali Ma'u tayi hanxari ta raba littafin gida uku ta xubar a kasa ta juya ta nufi bedroom na Ammi kamar walkiya ta shige ta rufe kofar hadda sa ki don sam bata gigin barin kofar Ammi baki saboda rana irin wannan

Marayan kuka Shukrah ta saka ta fice tabar falon gwanin ban tausayi

Takaicine yasa Jidda sabar diyarta a kafada itama ta fice

Zahra kam tsayawa tayi kamar mutum mutumi don tsabar bakin ciki, dakyar itama ta ja kafarta ta fice daga falon xuciarta na tafasa

Ita kanta Ammi jikinta yayi sanyi kujera ta samu ta xauna tana kuma godia ga Allah dayasa hakan ya faru BATURE baya gari da yau na lahira sai yafi Ma'u jin dadi

"Assalamu Alaikum"

Kamar daga sama Ammi taji Muryan BATURE ya rangada Sallama

A firgice ta juyo tana kallon bakin.kofar falon don.tabbatarda abunda kunnenta ya ji

Ba karamin raxana tayiba dataga BATURE tsaye a bakin kofar falon yana jiran amsa sallamarta

Adan kidime ta amsa tace

" jabbama Gorko amm"

Cikin takunsa na katsaita ya shigo cikin falon yana karantar yanayinta, daria ma ta basa don sarai yasan meya wakana

A bakin kofa sukaci karo da Zahra ta sanardashi abinda ya wakana

Amma ya batsar kamar baisan komai ba, xama yayi kusa da ita

" saukar yaushe BATURE"

Wayarshi ya fito dashi daga aljihun gabar rigarsa ya hau latsawa kan yace

" saukar safe, bandai shigo cikin gida bane ina can company tareda Balarabe"

Murmushi Ammi tayi tace" wato kace nina fara tokali dakai a gidan nan kenan"

Ssai ta kara bashi daria wai a nata xata buga cikinsa kenan

Kamar baxai amsaba yace " eh dake na fara haduwa"

Dadi ssai Ammi taji tana ganin yau Ma'unta ta kubuta daga ukubar BATURE sai kuma gobe wani lamarin ya bullo

Gyara xamanta tayi tace" in kawo maka furane"

Murmushi yayi a xuciarshi yace

" kin kama kanki da kanki "

A xahiri kuma yace

" yanxu kam bana jin yunwa amma kan na kwanta xanso nasha"

Mikewa yayi ya gyara wuyar rigarsa
" xan.shiga cikin gida na gaida su Umma, Ma'u ta dau furar ta kaimin part na tasa a fridge"

Bai jira cewar Ammi ba yasa kai ya fice yana murmushin mugunta

Sanin tsananin wayon Ma'u ne yasashi wucewa part din Ummi duk da bai jima da barin part dinba



Koda Ammi ta fadawa Ma'u sakon BATURE kuka tasa

" wlh Ammi an fada mishine shi yasa yace na kai mishi Allah bani kaiwa"

Rarrashinta Ammi ta shigayi
" bbu wadda ya fadamishi ai da an fada mishi xuwa xaiyi ya balla kofar ya dakaki yau ya fara balla kofarne"

Baki Ma'u ta tura don ita har yanxu bata amince da BATURE bai san da abunda ya faru ba

" to ki kai masa da kanki mana ai baxai gane ke kika kaiba tunda baya dakin"

Da mamaki Ammi take kallon Ma'u tace

"Kinci ubanki ja'ira wato fitsarar taki takai a aikeki ki aikeni"

Kara tura baki Ma'u tayi tace

"To to basai ki bawa matarsa takai masaba"

Mikewa Ammi tayi tace

" kinga rabani fa bala'in BATURE ki mike ki dau furar nan ki kai masa, ko idan ya shigo ya Tara miki jini da majina bbu ruwana"

Bbu yadda Ma'u ta iya taje ta dau furan tana mita

"Shi Ya BATURE kam ubankune da yakeyin duk abunda yaso bbu mai taka mishi birki kodon yaci sunan kakanmune? Ai cin suna ba cin girman mai sunan bane, gani nida naci sunan Ammi amma Sam bbu mai daga min kafa komai nayi sai an takamin burki"

Murmushi tayi

" koda shike nima ina kwatar yancina don bbu mai cemin kule bance ass ba"

Kamar yadda BATURE ya hasaso haka kuwa ya faru sanda Ma'u tabi part nasu Ummi ta leka don tabbatar da BATURE na wajen

Ai kuwa ddi taji data ganshi tare da Zahrarsa suna soyewa a falon Ummi, kwafa tayi ta wuce part dinsa tana cewa

" mutane sai karuwanci ido da ido ko kunyar manya ma basaji, ji inda ta kwanta a jikinsa kamar suna palonsu, suyi su koma inda suka fito ma na sheke ayata bbu kasalanda"


Janye Zahra yayi daga jikinshi ya manna mata peck a check dinta yace

" Habibty bari inje kada ka kufce min kin santa kamar walkiya take"

Daria Zahra tasa tace"

Ok Baby idan kungama dramar Ku ta tom and jerryn sai na kirani don baxan iya tsayawa Ku cikamin ciki da daria ba na kasa nuna maka yadda nayi missing dinka"

Hararar wasa ya watsa mata

" ji kamar xatayi wani abun kirki, yau dai ki shirya 7 hours service na jiranki"

Murmushi kawai tayi shi kuma ya fice son matarsa na kara shiga jikinsa

Cikin hanxari Ma'u ta shiga falon BATURE ta bude fridge taxa Furan data kawo ta juya da Saudi xata fita kawai sai taga kofa a karkabe

A raxane ta fara kewaye falon da kallon, karaf idonta ya sauka akan BATURE
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download GIDAN BATURE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album