Join Our WhatsApp Group

BARRISTER SHURAIM BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by BARRISTER SHURAIM BOOK 1


BARRISTER SHURAIM BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33056



BARRISTER SHURAIM BOOK 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 27, Jun 2023

Author: Had Seeyamah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Manazarta Writer's Association

Author Phone : +234 701 032 5010

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 187.23 kb

File Type: txt

Views: 1276+

Download: 389+

Last download: 6 days ago

Description/Story:  2023



🧑‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*


*HAD SEEYAEMAH🌺*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*



_FREE BOOK_


*ina gode wa Allah daya Bani ikon rubuto muku wannan Labari mai suna barrister shuraim*
*Ina godiya ga Allah daya bani ikon rubuta wannan labari ubangiji Allah kasa nafarashi lafiya nakuma gama shi lafiya abinda zanfad'a daidai Allah sa ayi amfani da shi kuskure kuma akasi aka samu sai ay watsi dashi*

*ina jin jinawa marubuta kamar su Aunty binta abale ,aunty jamila jamee ummu mahir marubuciyar iyar makaho,shamsiyya manga marubuciyar fansar fatalwa,mujahida matar malam ammyn kausar ita kan nasan kunsan,littafanta daga ciki akwai so! tare da fatima habib* *marubuciyar sarkin ado sai ku garzaya ku karanta kar a baku labari ubangiji Allah k'ara basira* *(Ameen) tare da sauran marubuta*
*na saudaukar da wannan littafin ga al,umman garin Azare .*
Tsokaci
Banyarda wani ko wata su chanja min littafi ba .
In an samu kamanceceniyar labari akasi akasu .

___________________

*Bismillahirrahmanirrahim*


*PAGE 01*


Kowa cikin farin ciki nake ganinsa a wannan time ɗin da ɗalibai suke murna sun samu sakamako mai kyau akasin wasu da suka fito da C.o, Amma Alhamdulillahi kowa ya samu result mai kyau Dr Najeeb Na gani a cikin mutane suna ta musabaha.

"Ina Abokinka Barrister Shuraim."? wani abokinsu ya tambayi Dr Najeeb."Oh na manta ɗazun na baroshi a garden." suka garzaya i zuwa garden ɗin Sai suka same shi ya fada tinani mai nisa suna magana baya jinsu daga karshe Najeeb yace..."Yadai Barrister what wrong with you."? Saurin kallon su yayi domin bai ma san sun iso wajen ba sannan yace."Ba komai ya ke damuna ba a yanzu illa Abu uku, Na farko daga school ɗinnan bansan ina zanje ba,na biyu yarinyar da nake yawan mafarkinta tana buƙk'atar taimako daga gareni,na uku a ina iyayena suke."?

Numfashi Najeeb ya furzar da numfashi mai zafi a bakinshi yace."Calm down Abokina in shà Allah matsalar ka ta farko karka damu zaka zauna a gidanmu, yariyar nan kuma Zamu ganta in shà Allah, Karfa ka manta yanzu kai barrister ne su Abba da Ummi kuma Zamu nemosu Amma dai yanzu tashi muje muyi wanka mu shirya around 9:00 pm Zamu bar kasar London zuwa ƙasar mu ta gado Nigeria".

Tashi sukayi yayi ban kwana da abokan su na London, Egypt da India.
Sun nufi gidan da suka sauka suka shiga wanka, barrister Shuraim shi ya Fara fitowa, dogo ne amma ba can ba yana da faffaɗan ƙirji kuma shi ba irin ramammun maza bane yana da gashi a kwance akansa luf sai kace na fulani, yana da saje siriri ga manyan idanuwa haɗe da dogon hanci bakinsa kuwa irin Wanda Mata suke cema lips kiss for any time gashi fari kyakykyawa son ko wacce macce kin wacce tarasa hmmmmm! idan zan tsaya faɗa muku kyan da gayennan yayi sai mu kwana anan bamu Gamaba.


Da tawul naga yafito yana goge gashinsa bai tsaya a ko ina ba sai gaban mirror dake manne jikin dakinsu. mayuka yasoma shafawa sai kace wani mace daga bisani ya ɗauki cumb domin gyara gashinsa wani dogon wando yasa, ya ɗauko baki hade da farar t-sheet ya saka ya ɗauko hular Sanyi baka yasa haɗe da cover shoe, turare ya fesa ajikinsa mai sanyin ƙamshi, Yayi kama da sharukhan d'an india amma yafi sharukhan tsawo...Najeeb ne ya buɗe toilet yana ce musu time zai ƙk'uremana .

*NIGERIA*

Y'an makaranta ne suka tashi a garin Kaduna ƴayan Mata huɗu ne naga ukun sun ɗau hanya ɗaya suna cewa.."Amal sai mun haɗu gobe wajen final exam."


Murmushi wanda suka kira da suna Amal tayi tana cewa ." Allah ya kaimu lafiya."... Tafiya take a slowly tana tunanin mai zata tarar agidan su ko an ɗaura abinci ko ba a ɗaura ba? tana tsaka da tunanin taji an Shaƙa Mata wani Abu a hanci daganan bata sake sanin inda take ba, a k'atuwar jeep mai tinted a ka jefata gudu suketa tsalalawa Kamar zasu tashi Sama.

*LONDON*

Dr Najeeb ne yagama shirinsa sun fito zasu nufi airport domin komawa Nigeria sai kawai mukaji ringing na wayar Dr dauka yayi yana cewa.."Hello My Mom gamunan zuwa airport muna hanya Momy a dafamana Abun dadi." Momy tace ."My Boy karka damu ina ɗana Shuraim."? Dan kallon Shuraim yayi yana cewa.." Gashinan yana jinki Momy."


Dan murmushi Shuraim yayi yana karɓa wayar daga hannun Najeeb cikin sweet voice nasa ya ce."Hello Momy good morning."

"Morning my son I hope kuna lafiya me za a dafamuku."?
Yace."Momy mu komaima Zamu ci."

tace."A'a banason haka My Son kaima ɗana ne" yace "Momy a mana girkin gargajiya mun Daɗe bamu ciba". "ok bye my Son sai kun iso" ending call ɗin su ka yi sannan ya juya ya dubi abokin shi Najeeb
Barrister Shuraim yafara cewa." dama Momy ta sanni abokina kaji yadda takemin.?


★★★


Amal ce ta farka da ga doguwar sumar da tayi a lokacin ta ganta a kulle an d'aure hannunta da k'afarta ga yunwa na damunta, sai wani mai kama da samudawa yazo yace mata."mai kike so asayo maki."?ko kallansa ba taiba, seya juya ya yabar d'akin da take ya nufi restaurant domin yi mata take away had'e da sayo mata ice cream and chocolate ya dawo ya kawo Mata amma tak'i ci fita yayi ransa ab'ace ya k'ira madam Yace.."akwai ma tsala yarinyar nan takicin komai fa."


Madam tace.."what."!?a tsorace tayi tambayar ta cigaba da cewa." kana nufin nayi asarar kud'ina kaga kasa maganin bacci aciki kasan yadda za a yi yarinyar nan taci, tayi bacci saboda intayi baccinne Zan samu damar yin aikina yadda nake so, inason kaita ai katau garin Azare gidan babban Alhaji, kuma kasan iyayenta basu da k'arfi amma bazasu bar y'arsu ta tafi ai katau ba sai karatu, zan sami kud'i mai tsoka a tafiyar nan da zatayi daga bisani mu K'ira iyayenta muce anyi kidnapping nata muna son million 30,kaga bata yadda za ayi su samo kud'in daga nan target d'ina na biyu zan fad'ama Yadda za kaya.


★★★


Acan Abuja kuma sunyi manyan bak'i wato mutanen London sun iso k'asar su Nigeria Barrister Shuraim ne ya fara sauk'owa a step by step na jirgin, hannunsa bisa aljihunsa sai murmushi yake duk da miskilinsa amma yau yana cikin farin ciki dawowarsa gida, Dr Najeeb ne ya sauko suka nufi motar Khalifa da Abdullah sun zo d'aukarsu i zuwa gida.


Akwai shak'uwa tsakaninsu suna tafiya a hanya twice suke cewa."Yaya kaga yadda kayi kyau kuwa kamar bakai ba amma gaskiya nima zan cewa Dady ya fita dani waje."..Barrister Shuraim ne yace"annena kuyi zaman ku a k 'asarku Nigeria kuyi karatunku zai fi muku alkhairi." Bayan sun iso gida suna hirarsu gwanin sha'awa horn sukayi gate man yazo ya bud'e gate yace..."Aa Najeeb Bokan turai sannun Ku da dawowa a gaskiya inda a hanya na ganka bazan gane ka ba."


Barrister shuraim ne yafito cikin tak'ama kamar d'an gida, gaisawa sukayi suka wuce ciki.
Da momy suka fara cin karo tace..."wooow you are welcome yarana." hugging din mom sukayi suka wuce ciki Najeeb yace.."Momy Dady yana gida."? tace."yana sama yanzu zai sakko."


Sega Dady yana sau k'owa Daga bene, shuraim da Najeeb sukaje suka durk'usa suka gaidashi sukai godiya, Dady yace.." barka Yaranah ya karatu,
yanzu dai karatu kun gama shi to Allah muku albarka, kuje kuje Ku watsa ruwa sai Ku fito kuci abinci." suka tashi sukayi sama suka tafi side din su Najeeb d'akinsa suka shiga komai an gyrashi tsaf tsaf shape shape suka shiga wanka suka Sako k'ananun kaya su ka nufo parlourn dining suka nufa, Momy ce dakanta yau tace zatayi service dinsu. Dady yace" hmmmmm Hajiya kina sakalta yarannan fa, amna Auta bakya Mata haka." dariya tayi tace." na jima ban gansu bane." shuraim yai tagumi ya fad'a tunani.

A garin Kaduna madam ce tasa wannan mai kamar samudawan ya K'ira Baban Amal a waya Yace.."hello Alhaji munyi kidnapping y'arka Amal muna buk'atar 30 million mun barka lafiya zuwa anjima Zamu sake K'ira." kit yakashe wayar

A garin abuja kuma Dady ne yace.."shuraim meke damunka."yace" bakomai." Dady yace.."Aa akwai sai dai idan baka d'aukemu amatsayin iyayenka bane." shuraim yace."Aa Dady ba haka bane." Dady yace."to ina parlourn sama inkun Gama cin abincin kuzo Ku sa meni ina son magana daku." Dady har mu inji Khalifa da Abdullah."..."Aa Banda Ku."fushi sukayi .

A garin Kaduna baban Amal ne yake rafka salati "innalillalahi wa inna ilaihirra ji un."maman Amal ce tace..."meke faruwa Alhaji."!?zaman yan bori yayi yanzun nan aka kirani anyi kidnapping din Y'armu Amal." Ai salati umma ta rafka ta sanarwa ubangiji tace..."a ina."!? yace.."Ai ba shi ne Abun tambaya ba yanzu million 30 suke nema nida ko million 1 ban t'aba gani ba a rayuwata nashiga uku." Umma ta fashe da kuka tana salati tace.."yanzu ya za'ayi." Abba ne yace." Bari na K'ira k'anina na sanarmai." abban amal yace.."kiyi hakuri kibar kuka adduah zamu farayi."

Sukuma su Shuraim sun gama cin abinci sun tafi gun Dady Zama su kayi, Daddy yace."Najeeb naji komai daka fa d'amin dan gane da abokinka amma

Danjin yadda zata kaya Nagode , tofa anayinta to Allah sa Dady yabar barrister shuraim ya zauna agidan.
Inkunga kuskure acikin wannan d'an labarin nawa dan Allah ina mai r'okonku da Ku sanar dani ni kuma zan gyara Abun da Bai dace ba 💖💖💖💖💖💖


_ina mai mana ta'a ziyyar babban rashi da mukayi a garin Azare na malam kabiru ahmad(jazzy) ubangiji Allah kamasa rahama ka gafartamasa mukuma kabamu juriya da hak'uri na rashin babban malami da mukayi a garin Azare 😭😭😭😭😭😭In tamu tazo Allah sa mucika da imani mu mutu muna musulmai (Ameen)_



Rubutawa da tsarawa📝
*HAD SEEYAEMAH🌺*

Al k'alami yafi takobi inji ni siyamah

share
comments👏🏼

my watsapp number
08137873838*🧑‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*


*🧑‍⚖️BARRISTER SHURAIM🧑‍⚖️*

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*HAD SEEYAEMAH🌺*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*


_FREE BOOK_

*PAGE 2*

daddy d'in
najeeb ya tambayi shuraim yace"/ yanzu shuraim asali kai d'an wani gari ne? Barrister shuraim ne ya sun kuyar da kansa yace ", Asalin labari na shine sunana shuraim Muhammad Al ameen i yayena mu biyu su ka haifa nida k'anwata asiya, tsa kanina da asiya akwai shekara 7 saboda mahaifiyata sai da tajima kafin ta haihu abbanah da ummi nah sun Bani tarbiya irin wacce ya dace iyaye suba y'ay'ansu, alhamdulillah nayi ilimin addini da kuma na zamani bawai ina al fahari bane, ni kaina nasan ina da k'ok'ari tun ina d'an shekara 15 a duniya na sauk'e alk'ur ani,
i yayena suna ji dani sosai , a lokacin da mahaifiyata ta haifi asiya mahaifina yayi k'udi saboda kasuwanci yake yi a lokacinne abokanan kasuwancinsa basa son cigabansa , mahaifina yana hak'uri ko yaushe ya ce kowa rabonsa zai samu muna zaune a garin borno state wato garin Maiduguri asalin mahaifina dan garin Azare ne kasuwancine yakai shi Maiduguri agarin adamawa ya auri mahaifiyata.

Alokacin danake ss2 a karatu mahaifina yake zuwa dani kasuwa anan ne na fahimci mahaifina ya na da hak'uri sosai domin a bokanan kasuwanci nsa suna cutar dashi so sai tun daga wannan lokacin nasa araina, na fasa kasuwanci lawyer zan Zama domin nakare Al ummar mu wato talakawa .
dalilin dayasa ni yin haka ,dady! mahaifiyata ,kamar yadda na fad'a ma abaya y'ar adamawa yola state ce mahaifinta babban attajiri ne a garin adamawa a dalilin zuwan mahaifina ne man auran mahaifiyata, babanta ,bai yadda ba y'arsa yarima zata aura shine ta biyo mahaifina tagudu sukazo maiduguri aka d'aura musu aure a wajen malam dake garin maiduguri ,labarin auren iyayena kenan, shi yasa nake son zama lauya domin na taimaki mahaifiyata ta dawo ga iyayenta ,sai kuma yanzu haka na rasa i yayena na wani lokaci 😭 amma insha allahu dady zanyi k'ok'ari na nemo i yayena a halin yanzu da ga nan sai in had'a mahaifiyata , da nata iyayen ,ina kuma son tai makon talakawa, saboda irin abinda masu kud'i suke ma talakawa in sun kawo k'ara , dady
Tun daganan na dage da karatu na daina zuwa kasuwa ko yau she sai dai time to time, a ranar Dana gama secondary na fito da 9 credit mahaifina ya jidadi sosai har yasamin mota, da Samsung galaxy ,yakuma min alk'awarin zuwa kowacce k'asa domin yin karatu a time d'in nazab'i k'asar Egypt, domin nayi karatuna na law acan , mahaifina ya sau min komai nasa, to nikuma dake Bani da a bokai da yawa saboda ni ba maison raini bane,

mahaifiyata har kuka Tasha yi akan mahaifina ya daina ban k'udi amma kash mahaifina shi Bai d'au hakan a ma tsayin komai ba nima a lokacin gani nake bak'in ciki take min amma kuma duk wannan kud'in in dady ya bani Sadaka nake zuwa nara ba shi yasa kullum Allah yake K'ara daukaka abbanah .

Ranar da bazan tab 'a mantawa da ita ba a rayuwata itace a ranar da naje mall yin shopping aka kirani daga school, ana nemana ina zuwa naga abin farin ciki ne gomnati tad'auki nauyin karatun wasu daga cikin school d'inmu alhmdlh nima hardani aciki a lokacin ina murna nakoma gida domin sanarwa iyayena! aka tayani murna , abbana har party ya had'a mana, ran dazan tafi suka rakoni har filin jirgi dake kano,Na tafi harda kuka na,
Bayan kwana na uku a london se wani abokina ya turan video ta whatsapp, ina bud'ewa naga gidanmu gobara takama sai ci yake yi Yakama yanata ci da wuta a lokacin nace abbanah! ,ummi!! nah,my little asiya !!!, banga a lamar da mutum a gidan ba mutane suna ta k'ok'arin kashe wutar amma kamar K'ara Mata fetur Ake bansan lokacin da na fad'i sumamme ba. Dan a tunanina mafarki nake Ashe bahakabane,...


Read / Download BARRISTER SHURAIM BOOK 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album