Join Our WhatsApp Group

MATAR MALAM Complete Hausa Novel Document by MATAR MALAM


MATAR MALAM

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 96173



MATAR MALAM

Reading Time: 8 Hours

Added On: 21, Jul 2023

Author: Mai Dambu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ????RILLIANT WRITERS ASSO????*

Author Phone : 08130269641

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 548.18 kb

File Type: txt

Views: 2099+

Download: 1027+

Last download: 3 days ago

Description/Story: MATAR MALAM
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
                         🌺🌺👳

    *Bismillahi Rahamanin Raheem*

        *Written by*
             Mrs Fulani🐄
        
🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }




  *.......1*

        Hannuna ɗaya rike yake da wayata yayinda ɗaya hannun ke rike da jakar makarantata, cikin kwanciyar hankali nake taku cikin isa da gadara, dai dai majalasin Imam Usman nazo wuccewa, karatu suke shi da ɗalibansa ina wuccewa ne amma har najiyo tambayar da ɓarawon kajin unguwarmu ya jefa masa, na cewa..
  "Allah ya gafarta, meye laifin yan matan da suka zaɓi lalacewa akan aure, zaka gansu kullum cikin shigar kayan banza da siffa marasa kyau." Ɗagowa sauran sukayi suna kallona, abinda ya tabbatar min kenan dani suke,

       Shi kuwa Imam Umar zuciyarshi ɗaya ya fara da cewa.
"Manzon Allah (S.A.W) yace akwai wasu mata amma yan uwane, sazu saka kaya amma zai bayanar da suran jikinsu, inda basun tuba ba, toh wuta ya tabbata a garesui, Allah ya kiyayyemu, sannan iyayensu suna da laifi suma, kamata yayi su nime mutumin kirki subada yaransu gudun karsu lalace."  Bayani sosai yayi musu, wanda ban karasa ji banayi wuccewata dan basu gabana,

              Da sallama na shiga cikin gidanmu, da matar Babana muka haɗu girgiza kai tayi cike da bakin ciki tace,
"Naiha Allah ya shiryaki, shirin addinin Islama.Kuma wallahi idan baki cire wannan kayan jikinki ba sai na ɓallaki, shasha kawai"

         cikin kunkuni na wucce tare da cewa" ba zan cir..." Haɗa ido mukayi da Yaya Ishaq dodon gidanmu kenan, simsim na shige ɗakinmu na yan mata.
           Girgiza kai yayi cikin ɓacin rai ya fito gurin Matar babanmu yace.
"Innaji daga yau Naiha baxata kuma zuwa gidan Annah ba, dan duk wani shaiɗanci acan take ɗaukowa, ɗabi'ar yaran gidan duk ta kwashe dubi irin shigar jikinta don Allah, har kunya nake ace kanwatace ita, ko Ramla da Hajra da Zubaida basu wannan haukar kaman ita, kuma banga laifinta ba, tunda Annah ke saya mata kayan ba wata ba, zanyi maganin abun."

         "Yarinya ce sosai aiko su Ramla da kake zancanka akansu sun ɗan girmemata, kaga kenan har yanxun hankali bai gama wadatarta ba, Allah ya shirya mana ita" inji Innaji.

             D'aga labulen ɗakin yayi ya banka min harara kafin yace.
"Uban me kike a ɗakin da bazaki islamiya ba."

        Mikewa nayi cikin taurin kai da rashin kunya, irin na tashen balaga, domin jin kaina nake dai-dai dakowa, kayan isalamiyata nasaka sannan fito ɗauke da jakata ina fitowa banganshi ba sai jin sakonshi nayi a tsakiyar kaina, ihu nasaka ins yarfe hannuna, yace.
"Wucce saura naganki a gurinsu Baby kintsaya,"

      ina zubda kwalla ina kuka rike da kaina, har na kusan isowa majalasin suna nan tare da ɗaliban basu tashi ba, can gefensu kaɗan ɓarawon kajine naji yace.
"Allah kashirye mu, ace mutun ya zaɓi duniya fiye da lahiranshi makarantarma sai an haɗa da duka, kafin aje."

     Raina ne yakara ɓaci cikin hasala nace.
"Dan kutu...Abukazan kazanka bazan je ba inkai kake da wuta da aljanna karka bani da du... jaki ɓarawon kaji kawai yaushe har kasan Allah da zaka min wa'azi na ɗauka waw..."

    "Ya isa haka, Allah ya shiryeki shiriyar Addinin musulunci, wucce ki bar nan." juyawa nayi ahasale naga waye yayi min katsaladan a cikin maganata da ɓarawon kaji. Ina juyawa naga imam Usman, cike da tsiwa nace.

"Toh kaja masa kunne kar yasake shiga shirgina dan zanci ubanshi,"

         girgiza kai yayi cike da al'ajabi, yanda nake kallon kwarya idanunshi nake kafta rashin *M* gyaɗa kai yayi cikin sanyin murya yace.
"Shikenan bazai sake ba balle kisamu damar zaginshi amma ki daina zagi babu kyau, yana zubda mutunci."

           Tafiya nayi tare da ɗaga kafaɗata, rakani yayi da idanunshi, sannan ya maidasu kan Nura, komawa yayi gurin zamanshi ya zauna sannan yace.
"Nura babu ruwanka da yarinyar can dan nalura bata shiga shirgin kowa toh don Allah kodan ka tsira da mutuncika ai sai ka, daina tanka maka, tunda kaga yanzun tana matakin jin ita wata ce, toh karka sake,"

                Gyada kanshi yayi, nan suka cigaba da karatunsu.

         °°••^^ ΔΔΔΔ^^••°°

     Ni kuwa dana isa makaranta na makara ina shiga ana Amir ɗin makarantarmu shi ke taran lati, kallonsu nayi na ajiye agefe sannan nasa kaina wucce, finciko hijabina yayi dan dole na dawo, cike da ɓacin rai yace min.
"Miko hannuninki malama.,"
           Murmushi nayi sannan namika masa, sai da yagama tsulla min bulala biyar ko ɗigon hawaye babu a cikin idanuna, har zan wucce Malamin Sira yace min.
"Dawo nan ki cire  wannan farcen arnan da kikasa, karamar mara kunya."

         Koɗar banji ba na juya nakalleshi sannan nace.
"Hmm malam Yahaya bazan cire ba sai dai nadaina zuwa makarantar,"

                 Cike da mamaki, malam yahaya kalleni daman duk cikin malamai yafi zafi, toh ido da ido nace bazan cire ba, karɓan bulalar hannun Amir yayi yazo har gabana yace.
"Kika ce bazaki cire ba, ko?"

          Sam babu tsoro a tare dani na gyaɗa masa kaina, zuga min bulalan yayi, sai da na botsare, cike da rashin kunya nace.
"Allah zai saka min,"

        Bai fasa ba, sai da yayi min mugun duka, dakyar Malamai suka kwace ni, ina mikewa nace.
"Wallahi zaka biya abinda kayi, zaka san kataɓani, sai nanuna maka iyakarka, kazami kawai."

     Ina gama faɗin haka najuya nabar makarantar, ban tsaya ko ina ba, sai gidan Kakanina, tundaga bakin gater nake fasa ihu, hannuwana akaina, ina cewa wayyo Allah zasu kasheni.

          kakata Annah tare da Alhaji Ubale yayan Mamata, suka fiti suna tambayar dalilin da nake kuka nan nafaɗa musu abinda ya faru, dani ba tare da ɓata lokaci Alh ubale yasakani a mota sai makarqntar, yana isa ya shige har ofis ɗin Shugaban makarantar, nan yasamu anawa malam yahaya faɗa, akan dukar da yakewa ɗalibai, shugaban makaranta nagamawa kawuna shima ya ɗaura nashi inda yayi masa barazanar matukar baifita har kana ba, zaisa a ɗaureshi. Hakuri sukayi tabadawa, har muka bar ofis ɗin class ɗinmu ya kaini, nan yayi tabani hakuri, sannan ya koma gida, zama nayi cikin gadara kafana ɗaya akan ɗaya, ina kallon kowa cikin isa da jin kai.

             Har aka tashi babu wanda ya shiga harkata, Ramla da Zubaida kuwa rankwashina sukayi ransu a ɓace da abinda na aikata wanda nake ji a raina ko kaɗan banyi kuskure ba.

                   Koda muka isa gida ɗakinmu muka wucce inda ni nacire kayana, na fada ban ɗaki nayi wanka sannan nafito, hmmmmm

        Zaku sha mamaki idan kuka ga irin wanka danayi naci uban ado, kaman me zuwa gasar kyau, badan kowa nayi wannan wankan ba sai dan zuwan saurayina, wanda muke haɗuwa dashi a bayan gidan Imam Usman, nan nake zuwa musha hiranmu.

                     Ina gamawa najera filo kaman kullum nafita daga gidan dukda an shiga masalaci sallar magirb, nan nabita bayan gidanmu na isa gurin bai zo ba, gidansu baby nashiga, ina gidan har akai sallar isha, sai ga wani yaro ya shigo, wannan ana kiran baby ina jin haka nayi waje shine, dake ta gurin babu mutane ina ganinshi na falla da gudu, buɗe hannunwanshi yayi na shiga ciki, shi kuma ya rungume ni, tsam a jikinshi,  sunkuyo da fuskarshi yayi sitin kunnena yace.
"Babylove, muje masaukina mana," a tsorace na ɗago kai nace masa.
" Kayi hakuri idan akaga bana nan, kusan kashe ni, za'ayi"

                jan hannuna yayi muka karasa bayan gidan Imam Usman, nan ya zauna akan wani dutse nikuma na zauna akan cinyarshi, muka cigaba da hira, can hiranmu damuke wanda kusan Ashow yafini zakalkalewa, gurin faɗar manyan magana, ashe a dai-dai window imam muku wannan maganar dan har wani magana nayi dan nanunawa Ashow nima yar garice nayi, aikuwa, jin abinda na faɗa Ashow ya shiga kiss ɗina ta ko ina, shi kuma Imam jin abinda muke yasa ya, fito daga gidan yazo koranmu,, da wani katon toucinsa, yana haskamu kuwa, sai akan fuskana,......


       

        *Matar Usman*💕
[4/26, 18:34] Me Dambu: 🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }


🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳

*Writtern*
By
Mrs Fulani🐄

*:~2*

Mamaki da al'ajabina ya kusan kadashi kasa, sauka nayi akan cinyar Ashow, dan wani irin kunyar Imam Usman ne ya rufeni, daga can yace min.
"Zoki wucce gidan."

Dukda muryanshi a sanyayye yake bai hanani fahimtar ɓacin ranshi ba, jikina bakwari nawucce, komawa yayi gurin Ashow ya kalleshi cikin ɓacin rai yace.
"Kaman yanda ka lalata Y'ar wani, Uwar wani, kanwar wani,Matar wani haka Allah zai turo wanda zai lalata naka, sai kayi danasani abinda ka aikatawa yaran mutane, dan nasan ba ita kaɗai kalalata ba, kuma kar nakuma ganinka a area ɗin idan ba haka zansa amaka dukar kawo wuka."

Cikin sauri na iso gida, inda nashiga tabayan ɗakinmu.Har lokacin su Aunty basu shigo ɗakinmu ba, cire kayana nayi inda naraba gashina biyu nakwanta, ina tuna irin abinda Ashow yayi min, tabbas naji daɗi haka, ji nake kaman nafi kowa sa'a a cikin gidanmu.

Naiha Ibrahim daura shine cikaken sunana, mahaifina ɗan katsina ne, amma haifafen daura, Mahaifiyata ce ba yar kasan nan ba, ita yar nijar ce, ina da yayu hudu Ya ishaq shine babba yanzun yake service ɗinshi a zamfara, sai Aunty Zubaida tana karatunta a KSU, Aunty Hajra tana karatunta, A Poly, Ramla kuma tana Ss3 makarantarmu ɗaya ni kuma ina Ss1, Duk hudu Yaran Innaji ce, nikaɗai Mahaifiyata ta haifa sannan tarasu, Kasancewa Iyayen Mamata, suna nan katsina suka karɓeni, har zuwa yanzun da nagirma sai na koma gidanmu, Kakata Annah tana masifar sona haka yayan Mamata duk suna sona, kuma basu ganin laifina duk abinda zanyi dai-daine, duk yayuna mata suna da mutunci da nutsu uwa uba kamun kai, sanin ya kamata idan kacire ni kuwa na cire tuta a kafta rashin mutunci shigan banza kuwa ai ba sauki, ga tarin rashin kunya, a gidanmu, Ya Ishaq nake shakka dan kuwa yayuna mata ba tsoro, zabga musu rashin M nake, Ashow shine saurayina da nake ji dashi kuma shima yake jidani, mun haɗune, a birthday din kawata, tundaga ranar da yasa idanunshi akaina magana ya kare, kusan haɗuwata dashi idanuna suka buɗe, da farko baya taɓa ni, amma daga baya ya fara taɓani, tun ina kin yatabani har nafara jin daɗin abinda yake min, dukda nasan babu kyau toh yana iya, Karkuyi mamaki dan shekaruna sha shidane, amma idan kaganni zaka ɗauka nakai 20 sabida girman jiki, kuma bawani abu bane, Boons ɗina da button ɗina yake sakawa ake ganin na girma,

Lumshe idanuna nayi cikin jin dadin abunda ya faru dana tuna da wacce me tsukeken wandon ya hanamu cigaba da bidirinmu sai naji raina ya ɓaci.

***
Koda ya kori Ashow, gida ya koma daman abinci yake, ya mike fito gurinmu kallon Uwar gidanshi yayi cikin nutsuwa yace.
"Ina Jameesha take?" ya jefa mata tambaya cikin sanyi murya,
"Tana ɗakinta" ta bashi amsa.
"Kira min ita." yace hankalinshi nakan abinci da ya saka agaba, wanda tunda yakai loma ɗaya ya ajiye cokalin, bai sake bin takan abincin ba, koda ta isa kofar kwankwasa kofar tayi, buɗe kofar tayi, cikin isa da gadara tace.
"Lafiya kike min knock,"

karamin murmushi Zahira tayi sannan tace.
"Zauji yake kiranki bani ba"
tana gama faɗin haka ta juya tabar gurin, Sai da janeesha taɓata lokaci sannan tafito cikin yauki da yanga, ta isa falon, zamata tayi tare da cewa.
"Gani nan Yaya."

Tun shigowarta ya kalleta bai sake kallonta ba har tace gani nan Yaya bai ɗago ba saima watsa mata tambayar da yayi, cikin sanyin murya yace.
"Mi kike nufi da taliyar da kika dafa, da rana makaroni yanzun kuma taliya dake da Zahira baku da wani baiwar sarrafa abincine, sai taliya nan idan kukayi tuwo mutum sai ya gwamaci kwana da yunwa da yaci abincinku har sai yaushe zaku iya sarrafa abinci."

Tunda suke dashi bai taɓa musu magana akan abinci ba sai yau, dole sugyara kafin damarsu ta kwace masu, gyaran murya Zahira tayi sannan tace.
"Yaya kayi hakuri Insha Allah zamuyi kokarin mun gyara kurakuranmu, nd idan kabamu dama zamu shiga makarantan koyan girki,"

"Tab wallahi bazan shiga ko ina ba, gwarama ki daina niman suna, babu inda zan shiga." haka tagama fitsaran sannan tafita dafe goshinsa yayi cikin ɓacin rai. Zahira ma ganin halin da yake ciki tafita tabar falon tunda ba isa bace da girki, duk sai yakoma kalan maraya.

•••°°°^ΔΔΔ^°°°•••
Washi gari da safe cikin sauri na gama karyawa sannan nafito sanye da kayan makaranta, yayinda Ramla tasaka, riga da wando ni kuwa riga da siket nasaka, kafinshi wani bakin skintie ne a jikina baki sannan na ɗaura bakin siket ɗina, akai bayan nasaka riga me dogon hannun, nasaka butirin rigar, sannan na ɗauko hulata bakin nasaka, tufke gashina nayi cikin nutsuwa nafito, da Abbanmu muka, haɗu har kasa na gaisheshi, shafa kaina yayi cikin jin daɗi yace.
"Uwata Allah kin tashi lafiya, Allah yayi miki albarka, ga kuɗin break nan banda wasa."

Nodding kaina nayi cikin jin daɗi, na ɗauki skullbag ɗina na rataya, itama ramla haka tayi muka fito daga gida muna tafiya cikin sauri, duk inda muka wucce sai anbini da kallo haka ba sabon abu bane, muna isowa majalisin Imam Usman jikina yayi sanyi sakamakon abinda ya faru ya dawo min, wani shashi na zuciya tace _Akan me kike damuwa manta dashi karki ɗaurawa kanki abinda zai dameki_ take duk wani tsoro ya kau daga zuciyata, sai ma ɗauke kaina nayi ina hura hancina,

Kamshin turarena na perfume crown shiya sanar masa na gifta, ɗago kanshi yayi yaga yanda nake taku cikin isa da yanda nake shaky jikina yasa ya sunkuyar da kanshi cikin mamaki yanda na iya sarrafa jikina, cikin sanyi murya yakalle ɗalibanshi yace.
"Ina son sanin wancan yarinyar daga wani gida take,ne."
Aikuwa Nura yayi tsagal yace.
"Ai yar gidan Alhaji Ibrahim me katako ce, itace karamarsu kuma itace shaiɗaniyarsu,"

gyada kanshi yayi cikin gamsuwa yace.
"Shekarunta nawa"
Wani magidanci wanda yana cikin ɗaliban Imam yace.
"Akarmakalla ai yarinyace karama sosai dan sha shida ce, sa'ar yar wajenace da suna tare amma daga baya narabasu, sabida ita wannan idanunta a buɗe yake, sha'anin yau kar ta lalata min yarinya yasa nayi mata kashedi da barazana, tundaga lokacin ko a hanya suka haɗu basa ga maciji."

"Gaskiya ka kyauta malam Ali amma me yasa iyayenta basu saka idanun akanta ba yarinya karama haka ai zata lalace fa." Inji Imam,

Nura da yake can yace.
"Ai...


Read / Download MATAR MALAM

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

3 Comments On MATAR MALAM
avatar
rahma-2-7

6 months ago

Reply

Thanks

avatar
rahma-2-7

6 months ago

Reply

Thanks

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to rahma-2-7

Goods thanks keep with us for more interested novels

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album