Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

SANADIN KADDARATA Book 2 The Conclusion Complete Hausa Novel Document by SANADIN KADDARATA Book 2 The Conclusion


SANADIN KADDARATA Book 2 The Conclusion

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 114611



SANADIN KADDARATA Book 2 The Conclusion

Reading Time: 9 Hours

Added On: 30, Jun 2024

Author: Mhiz Innocent ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08124818273

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 600.13 kb

File Type: txt

Views: 340+

Download: 406+

Last download: 1 day ago

Description/Story: 
✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION21*

____Cikin azama da zafin nama Dad ya sauke masa wani gigitaccen marin daya dakatar dashi daga fad'in abinda yayi niyyar fad'a d'in, ya dafe kuncin sa yana kallan mahaefin nasa har lokacin 'kwayar idanunsa bata koma aenahin colour d'in ta ba, Cikin fushi wanda Dad d'in ya dad'e be nuna shi ba yace

"Ashe baka da hankali Adnan? Baka da kunya baka da kirki? Saki? Adnan!! Toh ka tabbatar yau ba se gobe ba ka d'auki matarka kun barmin gida na, ni ba 'karamin mutum bane..." Daga haka ya juya ya kalli Mami data gama mutuwar tsaye yace yana wucewa

"Ki sameni a d'aki na" be jira tace komae ba yayi gaba, Mami ba tace komae ba tabi bayansa tana jin yadda zuciyarta ke farfari, Ko second 1 be 'kara ba bayan fitar Mamin ya fice daga d'akin fuuuu kamar ze tashi sama.... Lumshe idanun ta tayi tana jin yadda wasu zafafan hawaye suka samu damar zuba a kuncinta, ta sake lumshe idanun nata a karo na 2 sannan ta kwasa da gudu zuwa cikin d'akin da aka sauke ta ta fad'a kan gado tana fashewa da wani gigitaccen kuka, tamkar zuciyarta zata fito haka take kukan, kukan data dad'e ba tayi irinsa ba haka ta dinga yinsa a ranar babu me lallashinta "Se yaushe ne za tayi farin ciki a rayuwarta? Anya kuwa ranar nan zata zo? Wannan mutumin shine mijinta? Ta yaya hakan ta kasance? Bayan akwae tazara me nisa a tsakaninsu wanda suke da yawa? Akwae banbancin asali, dukiya, nasaba da abubuwa da dama wanda ba zasu fad'u ba, abubuwan da suka kasance banbanci ne me tsayi kuwa a tsakaninsu, toh ta yaya kenan akayi wannan auren? Lallae akwae wani cukurkud'ad'd'en al'amari wanda daga ita har shi basu sani ba" seta sake lumshe idanun ta tana sake fashewa da wani sabon kukan, tana jin yadda tsanar mutumin ke ninkuwa a cikin zuciyarta, bata jin duk yawan tsanar da tayi wa iyayenta takae wadda tayi wa wannan mutumin da besan darajar d'an adam ba, wanda burinsa kawae shine ya wula'kanta d'an adam, A hankali taji an d'aga kanta an d'ora akan cinya, tana shirin d'agowa taga mamallakin cinyar Ammi tace tana shafa kanta

"Ya isa haka Azrah! Kukan ya isa haka uhmm?" Seta sauke ajiyar zuciya ta cigaba da sheshshe'ka tana ajje numfashi a hankali, Ammi tace

"Kiyi ha'kuri da halayen Adnan, don Allah Azrah karki gaji dashi kinji? Yanzu kece kika fi kowa kusanci dashi kuma ina fatan kece zaki chanja shi da taemakon ubangiji" Shiru tayi tana sauraran Ammin badan tana fahimtar abinda take fad'a ba, Ammi ta d'ora da fad'in

"Inaso ne kuyi sabo da Adnan badan wani abun ba, a'ah..inaso ne ku saba kamar kowanne ma'aurata dan kuwa ina muku kallan 'ya'yan dana haefa ne" Ammi ta d'an dakata tana jin yadda Azrahn ke sheshshe'ka har lokacin sannan ta d'ora da

"Ina iyayen ki?" Runtse idanun ta Azrah tayi dan har cikin 'kwa'kwalwarta taji tambayar Ammin, Ammi ta sake tambayar ta a karo na biyu, se a lokacin ta bud'e bakin ta da yayi mata nauyi tace

"Bansan su ba!!" Ammi tace

"Baki sansu ba kuma?" Azrah ta mi'ke daga kwancen da take a cinyar Ammi ta kalle ta tace

"Ammi na tsane su, na tsane su, don Allah Ammi ki dena min maganar su, zuciya ta tana gab da bugawa wallahi" ta fad'a tana fashewa da wani sabon kukan, Ammi ta tsura mata ido tana kallan yadda take maganar har cikin ranta, Se tace cikin lallashi

"Ya isa haka nan toh!" Azrah ta kifa kanta akan gwuiwoyinta ta cigaba da kukan cikin rashin sanin abinyi........ Kae tsaye d'akin sa ya nufa da wani irin sauri ya fad'a d'akin be wuce ko'ina ba se kan mirror yayi wancakali da kayan dake kae gaba d'aya sannan ya zube kan gado yana yamutsa sumar kansa

"Noooo!!" Ya furta bayan ya furzar da wata zazzafar iska daga bakinsa, seya lumshe idanun sa yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da 'karfin gaske saboda tsananin 'bacin rae, he wish yana shigowa da taba gidan yasha yanzun ko damuwarsa zata kau (Subhanallahi), ya sake ri'ke kansa, how? Wannan abun ya faru ne ba tare da ya ta6a tsammani ba, ta yaya? Lallae daga Dad har Mami nasan su tarwatsa masa 'kwa'kwalwa ne, shi kuma kome za'ayi baze ta6a yarda wannan er 'kauyen ta zama matarsa ba, toh waema ta yaya? Sunyi abinda suke so ae shikenan koh? Toh shima zeyi abinda yake so.....


..........A sukwane tayi sallama cikin parlourn, Dad dake zaune hannayensa biyu cikin juna ya d'aga kae ya kalleta sannan ya amsa sallamar, Mami ta 'karasa cikin parlourn ta nemi waje ta zauna kanta a 'kasa tace

"Gani ranka ya dad'e" shiru Dad yayi yana tunanin ta ina ma ze fara? Seya d'ago ya kalleta a hankali yace

"Meyasa kika min haka hadeeza?" Mami taji jikinta ya 'kara yin sanyi dan tunda taji ya kira sunanta gatsau haka toh fa yau kam babu kanta, seta d'ago ta maraeraece fuska tace

"Kayi ha'kuri ranka ya dad'e..wallahi akwae dalilin da yasa nayi hakan!" Dad ya kalleta sosae bece komae ba dan haka Mami ta cigaba da fad'in

"Yalla6ae nayi duba, nayi duba sosae wallahi naga babu wadda zata auri Son ba dan dukiyarsa ba..shiyasa na nemo wadda bata da wani wayewa..."

"Ita wannan d'in kin san halin tane?" Dad ya katseta da fad'in hakan, ta d'anyi jimm kad'an sannan tace

"In Sha Allah dae ina kyautata mata zato" Dad yace

"Ba wannan ba, meyasa kika saka 'karya a cikin lamarin?" Mami ta sake maraeraece fuska tace

"Yalla6ae..'karya kuma? Kawae dae nasan idan kasan gaskiyar al'amarin nan ba zaka amince da za6awa Son mata ba tare da amincewarsa ba, shiyasa nayi hakan, banda wannan babu komae.." Ta 'kare maganar tana kallansa, Dad yace

"Shikenan...Allah ya kyauta..and.." Dad ya d'an dakata wanda hakan ya bawa Mami damar sauke ajiyar zuciya ta cigaba da kallan Dad d'in wanda ya cigaba da fad'in

"Babu wanda ze maeda ni 'karamin mutum, 'kafa da 'kafa naje na nemarwa Adnan auran nan haka kuma na kar6ar masa, saboda haka baze yiwu ya 'kas'kantar dani ba, dan haka ki fad'a masa ya tabbatar ya d'auki matarsa a yau base gobe ba su barmin gida" Mami tace

"Toh yalla6ae amma don Allah ka sassauta abin, duk yadda ka d'auka fa ba haka yake ba, plss ka basu ko nan da sati 1 ne kafin nan komae ya daedaeta In Sha Allah" Dad ya juyo da sauri yana kallan Mami, se kuma ya girgiza kae yace

"Ba shawarar ki nake nema ba pls, tunda ance gaggawa aekin shed'an ne amma In Sha Allah daga yau ba zasu sake kwanar min a gida ba, karatun ma ta 'karasa a gidan nasa" Mami tace

"Amma ginin fa?"

"Wannan ba matsala bane" ya bata amsa, seta shiga neman wata maganar da zata fad'a, can tace

"Amma yalla6ae kafi kowa sanin halin Son" Dad ya sake juyowa ya kalleta yace

"Zan nuna masa ni na haefeshi ba shi ya haefe ni ba" daga haka ya mi'ke ya wuce bedroom d'insa, Mami ta bishi da kallo kafin ta dawo ta sauke ajiyar zuciya.......


..........Ranar gaba d'aya babu inda yaje yana cikin gidan ya kulle d'akin nasa gaba d'aya, yana nan kwance har lokacin idanun sa a lumshe haka zuciyarsa bata bar tafasa ba ya jiyo ringing d'in wayarsa, ko kallan inda take beyi ba ballanta me kiran ya saka ran za'a amsa masa, kiran na katsewa wani ya sake shigowa, seya bud'e lumsassun idanun sa a fusace ya janyo wayar ya d'aga ba tare daya kalli me kiran ba yace a fusace kamar ze rufe me kiran da duka

"How dare u?, Allow me to rest ahbeg" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace cikin lallashi

"Son.." Yana jin muryarta ya sauke wayar daga kunnensa yama kashe wayar gaba d'ayanta ya jefar da ita gefe ya koma kwancen da yake yana sake dafe kansa ya lumshe idanun sa, so after all dis kuma me za tace masa? Mami bata ta6a 6ata masa rae irin na yau ba, meyasa zata aekata masa haka? Ita d'in data kasance koda yaushe me son farin cikinsa yau kuma taso akasin sa? Ranar dae gaba d'aya be runtsa ba yana kan gadon yana tunanin yadda ze 6illowa wannan lamarin da ko a mafarki be ta6a tunanin kasancewar sa ba, "Dad!" Ya fad'a akan la66ansa bayan ya sake ri'ke kansa......


....Mami ta sakko daga stairs ta 'karaso cikin parlourn tana kallan Ammi tace

"Plss ki sanar da ita gobe zasu tafi!" Ammi tace

"In Sha Allah" daga haka ta 'karasa cikin d'akin Azrahn, ta tura 'kofar a hankali tana kallan yadda har lokacin tana kwance kamar yadda ta batta, ta 'karasa tana kallan ta tace a hankali bayan ta matsa kusa da ita

"Azrah" Seta d'ago jajayen idanun ta ta sauke su akan Ammi ba tare da tace komae...


Read / Download SANADIN KADDARATA Book 2 The Conclusion

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album