Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

WANNAN CE QADDARARMU Complete Hausa Novel Document by WANNAN CE QADDARARMU


WANNAN CE  QADDARARMU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 262457



WANNAN CE QADDARARMU

Reading Time: 21 Hours

Added On: 06, Apr 2023

Author: Aisha A Bagudo ,Faiza Hammadu Barau ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.49 mb

File Type: txt

Views: 3724+

Download: 4667+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: DARLING)

WATTPAD@HAU'ESH

PAGE 1

Kwance ummita take a kan doguwar kujera mai zaman mutun uku a parlourn mahaifiyarta mairo, idanunta sanye da farin glass wanda ya zame mata jiki , hannunta riƙe da littafin bulugul-maram tana nazarin karatun da malamin islamiyyar su ya koyar da su jiya, sosai tayi zurfi cikin nazarin, dan bata son ta zama koma baya a duk abinda ya shafi ɓangaren karatunta, bata son malamin ya yi tambaya a kan darasin sa bata kasance cikin mutum ta farko da zata soma d'aga hannunta domin ba da amsar tambayar da yayi ba.

Shiru ɗakin baka jin motsin komai sai bugun zuciyarta da iskar fankar parlour'n dake kad'awa a hankali, tana cikin karatun ta ja numfashi ta tsaya tare da sauke nannauyen ajiyar zuciya had'e da Jan tsaki a cikin ranta , saboda jin motsi da sautin muryar wanda yake ƙoƙarin shigowa ɗakin ,yaya Ma'aruf ne tsaye a bakin dokin kofa ya d'age labulen parlour'n, shi bai shigo ba, shi bai koma ba, yana faman cicciza lip's dinsa na ƙasa, sanye yake cikin wani had'ad'd'en farin yadin Aba , ɗinkin rigar dai-dai gwiwarsa, hannunsa d'aure da agogon fata baƙi sajen fuskarsa na kwance sai sheki yake zubawa, ga wani mayataccen kamshin turare da ya cika mata hanci tun tsayuwarsa, gashin kan nan nasa ya sha gyara tare da askin afro kamar Ko da yaushe, yayin da idanun shi ke kallon cikin ƙuryar parlour'n yana fuskantarta, ku san minti biyu ya d'auka tsaye a gurin sannan ya ƙarasa shigowa ciki parlour'n bakinsa d'auke da sallama wanda yayi a ciki shi ma ta san yayi ne ba dan ita ba.

Kallo ɗaya tayi masa ta d'auke idanunta a kanshi tana sake sauke ajiyar ba tare da ta amsa masa sallamar da yayi ba, haka da tayi yayi bala'in taɓa zuciyarsa, take yaji wani duhu ya gilma a saman zuciyarsa dama gangar jikinsa, kamar yayi mata magana sai kuma ya shareta dan ya fita jin duk wani abinda take ji dashi, idan takamarta miskilanci ne to shi ya doketa, kuma idan da sabo ya riga da ya saba da wannan mugun halin nata kamar na mutanen farko, tunda ba yau ta saba yi masa ba, sai dai duk sanda tayi baya sanya gurin cin ƙaniyarta, ko yanzu ma tunanin abinda zai mata yake wanda zai dagula mata lissafi , zuciyarsa ke umartarsa da ya ƙarasa gareta ya soma da yayyaga littafin da ke riƙe a hannunta, sannan yayi mata dukan mutuwa ya nuna mata bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, Amman tunawa da yayi a cikin ɓangaren su yake yasa ya ɗauke idanunshi a kanta yana jan dogon tsaki, sannan ya samu guri can nesa kaɗan da inda take kwance ya zauna yana cewa "Mamana kina ina idan ba kya ciki nasan inda dare yayi min, dan bana kaunar zama muhalli ɗaya da wannan fat lion din?
Maganarsa ta doki kunnuwanta sannan ta wuce har cikin tsokar dake maƙale da zuciyarta sai taji tamkar ta tanka masa, amman tayi shiru dan ta san mama tana ciki ɗakin, ƙarshe ta sha duka a gaban wannan mugun azalumin, dan haka ta ja tsaki a cikin ranta ta juya masa baya, ta ci-gaba da karatunta, tayi tamkar bata san da wani halitta zaune a gurin ba, shi kuwa sai girgiza ƙafarsa ɗaya yake yana ciccin magani da jan tsaki .


Ko cikakken minti biyar bai yi ba sai ga mama ta fito daga uwar d'aka "A'a a she ma'aruf ne saukar yaushe a garin kai da muke sa ran ganinka gobe?
Sai da ya gaisheta sannan yace
"Ban Dad'e da dawowa ba nace na shigo mu gaisa da mamana"
"Madalla ɗan albarka ka kuwa kyauta da kazo gare ni, ya ka baro mutanen Kano fatan duk suna lafiya?


"Lafiyarsu lau duk sun ce a gaishe ku "Mama ta fad'ad'a fuskarta da murmushi
"muna amsawa"
Bayan sun gaisa da mama ma'aruf ya ɗan tsaya yaji ko ummita zata gaida shi kamar yadda sauran kannensa ke rawar jikin gaida shi a ko da yaushe, abin mamaki ya ji tayi shiru taƙi cewa komai bare ta waiwayo inda suke , hakan ne yasa ya tattara hankalinsa da idanunshi inda mama take, sai dai ransa yayi bala'in ɓaci.
"Har yaushe zata daina mishi kallon gani-gani?

"Tabbas lokacin yayi da zai tsananta cin ƙaniyarta, yayi wa kansa alqawari sai ya gyara mata zama, lumshe idanun shi ya yi har sanda yaji sautin muryar mama cikin kunnenshi.
"Ke ummita maza tashi ki kawo wa yayanki abinci ki had'o Masa da ruwan zafi " wacce aka kira da ummi ta zunburo baki ta ajiye littafin hannuta tana ƙoƙarin mi'kewa, taji yace "No mama Karki damu kanki a koshe nake fa, Sai da na cika cikina ɓangaren jiniya sannan na shigo nan"
Ya fad'i haka ne saboda baya bukatar ummita cikin lamarinsa, shi asalima baya son kasancewarsa a duk inda take kallonta kawai na haddasa masa ciwon kai da ɓacin rai mara misaltuwa, duk cikin family's dinsu babu wacce ya tsana kuma baya son kasancewa tare da shi kamarta, ko kaunar ganinta baya son yi, yana jin da yana da hali da ya gogeta a cikin ahlinsa ..



"To ai shikenan Wani abincin zaka ci da rana a dafa maka ? Mama ta fad'i haka tare da zama tana Janshi da hira.
"karki wahalar min da kanki mamana daga nan gidan big sister zani ba kuma zan dawo ba Sai dare "
"Tou shikenan idan kaje ka gaishe min daita"

Cike da sanyin jiki ummita ta miƙe tsaye ta d'auki littafinta ta nufi d'akin mama tana cewa
"Aikin banza kawai malam, ai ko ba kace a barshi ba, daman ba wahalar da kaina zanyi gurin wani kawo maka abinci ba, dan mai iyayin tsiya kawai taja tsaki ta zube a kan bed tana sakin numfashi ..
Ma'aruf ya dad'e a ɓangaren Mama suna zantawa sannan yayi mata sallama ya bar part din, Kai tsaye gidan big sister ya nufa a nan ya wuni zur sannan ya koma gida .

******
Kamar kowane dare, karatu take a parlour'nsu har sai da taji kanta yayi mata nauyi alamun yana buƙatar hutu, sai faman hamma take zubawa idanunta sun Kad'e sun yi jazir sai kace wacce tasha kayan maye.
"ya dai?
"Lafiya kuwa Ummita yau ma ko ciwon kan ne ?
"Ki fa dinga sararawa kanki da yawon karatu, kallon yaya rayhan tayi, dan tuni har ta soma ganinsa dishi-dishi.
"wallahi yaya ba ciwon kan bane amman dai ina jin kaina yayi min nauyi ba kaji yadda nake jina ba yanzu, tayi maganar tana hamma yayinda ta miƙe tsaye domin shiga d'aki, tsaki yaya rayhan ya ja "ba dole ki yita Jin kanki yana miki nauyi ba, ta ɗan tsaya had'e da juyo wa suna fuskantar juna kafin daga baya ta sakar masa murmushi.
"ya kake son nayi yaya ?
Dole nayi karatun nan da, domin bana son na zamo koma baya,nafi son komai aka tambaye ni na zamo farko gurin bada amsa ko baka jin daɗin yadda sakamakona yake fitowa?
"Ina ji mana amman duk da haka kina buƙatar hutu ko dan ki dinga dan bani lokacinki"
Murmushi ta sake sakar masa "shikenan zan yi kokari yaya yanzu dai sai da safe ta furta da wani guntun munafikin murmushi wanda iyakarsa gefen baki "okay my wife sai da safe Allah tashe mu lafiya daga inda yake ya huro mata iskar bakinsa murmushi kawai tayi tana juya masa baya shima y asan bazata maida masa Marta ni ba"
A hankali ya miƙe ta nufi waje inda mazan gidan dana unguwa ke zaune suna shan iska har ma'aruf wanda shi yake riƙe da wayarsa yana charting da budurwa meenah...


*******

Washe gari ummita a hankali take d'aga kafafunta tana tafiya Kamar bata son taka ƙasa dan ku san duk sauran yan uwanta sun dad'e da dawo daga makaranta, tana shigowa harabar gidan da yaya ma'aruf ta soma cin karo, tana ganinsa tayi tsalle kamar wacce aka tsinkara ta manne a jikin bagon tana jiran ya wuce sannan ta shige ciki ..

kallonta Kawai yayi kana ya girgiza kai duk da sauri yake saboda abokansa da ke waje zaman jiransa hakan bai sa yaji zai iya barinta ba, dan haka ba zato ba tsammani taji ya cafki tsintsiyar hannunta cikin nasa,cikin tsoro ta juyo suna fuskantar juna dan dama ta kawar da fuskarta gefe saboda bata son ganin fuskarsa , ranta a matuƙar ɓace tace.
"Wai meye haka malam?

Bai ce mata komai ba ya soma ja hannunta da ƙarfin tsiya tana turjewa."Wai meye haka yaya ma'aruf nifa bana son wulakaci, ta yaya ban shiga shirginka ba...


Read / Download WANNAN CE QADDARARMU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On WANNAN CE QADDARARMU
avatar
amina-4

1 year ago

Reply

Interesting novel

avatar
amina-4

1 year ago

Reply

Interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album