Join Our WhatsApp Group

MK MIJIN DELU Complete Hausa Novel Document by MK MIJIN DELU


MK MIJIN DELU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 21426



MK MIJIN DELU

Reading Time: 1 Hours

Added On: 09, Aug 2023

Author: Zainab Habib Mom Islam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : _Elegant online writers_

Author Phone : 08141799224

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 116.41 kb

File Type: txt

Views: 669+

Download: 230+

Last download: 7 days ago

Description/Story: 🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hatsabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂





*_Zainab Habib(Mom Islam_*





Elegant online writers


*Tabbas banso ƙarayin rubutu ba nace sai bayan sallah , wani labari ne ya faɗomin cikin bazata ,shine nakeson amaryar dashi amma bashi da yawa sai ɗan karen daɗi😊muje zuwa*.



Page 1-2


Zaune take gaban wata bishiyar kanya hannunta riƙe da zabgegiyar sanda .Maganar da taji ne ya sata juyowa tare da kallon mai maganar ,ta galla masa harara kana tace "Muhammadu yaushe zan gaya maka ni binni zani saboda in samo miji ɗan gaye amma ka wani nacemin sai kace ni kaɗaice mace a faɗin ƙauyen nan "
Ta ƙarashe maganar tare da murguɗa masa baki .

Wanda aka kira da Muhammadu ya sharce zufar data karyo masa ya nemi guri nesa da ita ya zauna kana yace "haba delu kullum nazo gurinki sai kin tozartani kodan kinga Allah ya jarabceni da sonki ?".

Wani mai keke ne ya tsaya nesa dasu kana yace "Delu ta Haladu maza zomuje in siyo miki kifi " ,
Ba tare da ɓata lokaci ba Delu tabi mai keke tana tafiya tana gantsarewa harda yiwa Muhammadu dariya .
Cikin sanyin jiki Muhammadu yabisu da kallo tare da girgiza kai yana ambaton innalilahi ,sbda yanda soyayyar Delu tayi masa mugun kamu yanajin bazai iya rauwa ba idan babu Delu ,amma abin tambaya anan shine ,tace binni zata mai ya haɗata da Haladu ɗan gidan mai Gari ? bashi da mai bashi amsa dan haka ya nemi hanyar da zata sadashi da gidansu .

Saida su Delu sukayi nisa sosai ,Haladu ya kalleta kana yace "ƴar fara kinƙi bani izini in turo da iyayena koh? "
Farr Delu tayi da manyan idanunta masu ruɗar samari tace "nan bada jimawa ba zan baka izini amma kafin nan inaso ka bani kuɗin zuwa cin kasuwa "ta ƙarashe maganar tare da shagwaɓe fuska .

Hannu Haladu yasa a aljihun koɗaɗɗiyar rigarsa data yayyage ya ciro ɗari biyar ya miƙa mata kana yace "ki haɗo harda hoda da janbaki saboda suna yimiki kyau "
Washe jajayen haƙoranta tayi kana tace "to bara inje inyi wanka sai mu wuce nidasu Salame "

Shima dariyar yayi wacce ta baiyanar da jajayen haƙoransa yace "to adawo lafiya zuwa dare ina nan zuwa shira ".

Bayan rabuwarsu Delu ta shige gida kasancewar tsakanin inda suke da gidansu babu nisa.

Tunda ta shiga take cewa "Barira !Barira ! amma shiru ba'a amsa ba ,hakan ya bata damar zama ta miƙe ƙafafunta a ƙasa ta fara lissafin abin da zatayi , da sauri tace "yau Kano zani wlhi babu fashi tunda Kawu Inusa yace inzo zai sani a jirgi mai juyi wlhi yau bazan zauna a ƙauyen DASHI BA .

"Delu tashi ki kai ɓarjin fate saboda malam zeyi baƙi yau "
Da sauri Delu ta kalli mahaifiyarta Barira kana tace "nifa babu inda zani wlhi Kano zan tafi fan kiji",
Baki buɗe Barira take kallonta tare da tafa hannu ,sai kuma ta juya ta ɗauko kwanon masaran ta kawo gaban Delu ta ajiye ,kana tace "maza tashi ko inci gidanku bana son shashanci "
Delu na bubbuga ƙafa ta ɗauki niƙan tana cewa "wlhi zakiga niƙa dan bama zan dawo gidannan ba bare a sake aikana ".
Tana fita ta haɗu da Hansatu mai ɗanwake ,ta sauke buhun masarar dake kanta tare da kunce ɗanƙwalin kanta ta ɗaura a ƙugu tana girgiza tace "dan ubanki wa na kama ?
Ajiye bokitin ɗanwake Hansatu tayi kana tace "ubanki kika kama "Delu ta cakumo wuyan Hansatu tare da kai mata naushi tana cewa "azo ayi warwaso ga ɗanwake da zafinsa "da sauri Hansatu ta miƙe ta kaiwaDelu naushi ta ɗauki bokitinta ta ruga da gudu.
Ƙwafa tayi kana tace "kinci bashi wlhi sai naci uwarki zamu haɗu ".
Delu tayi tafiya mai nisa ,a bakin kasuwa ta tsaya tare da ƙwalawa wata yarinya kira a ƙallah zatayi shekara goma tace "ke Abulle ina zaki ?"
Yarinyar da aka kira da Abulle tace "masara zan siyo mudu biyu " da sauri Delu tace "kawo kuɗin in baki wannan mudu biyu ne harda rabi sai kice mai shagonne ya kyauta miki ,amma kawo kuɗin nawa ne ?"Abulle tace "ɗari biyar ne ai bazaki bani canci ba ".
Da sauri Delu ta miƙa mata masarar tare da haɗa kuɗin harda na Haladu ya zama dubu ɗaya ,tace "yawwa tabar gurin .
Kai tsaye tashar mota ta wuce ,tana zuwa taji ana cewa "Kano _Kano da sauri ta shige mota tare da cewa idan munje babana zai baka idan yazo ɗaukata .....!


Tofa yawan comments yawan typing idan ya sami karɓuwa zanyi farinciki over 😍

Mom Islam

🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hatsabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂



*Zainab Habib(Mom Islam*





_Elegant online writers_



Page 3-4

Gyara tsayuwa dreba yayi kana yace "ke kinga wasa a idona ? kuka ta fashe dashi tare da haɗe hannuwanta biyu tace "wlhi Allah babana zai biyaka sarkin Kano ƙanin ƙaƙan babana ne "
Da sauri dreba yace "to shikenan nasan kanawa da cika alƙawari maza rufe ƙofa ".
Dreba na shiga ya tada mota suka hau ƙwararraɓaɓɓen titin su , tunda suka fara tafiya Delu take bacci har aka iso Kano bata sani ba , wani bafulatani ne ya zunguri ƙafarta cikin muryarsa da hausa bata isheta ba yace "kai ka tashi munjo Kano ka shami mota kamar katifar ubanka 😂 , naushin da bafulatanin yaji ne yasa shi kallon wacce tayi naushin yace "dan ubanka daga tashinka a bashi shine jaka naushemu a shiki ?Delu dake huci tace "ubanwa ya aikeka zagin ubana yana kwance a kabari ?,yau zamuga mai ƙarfi cikin ni dakai ".
Waro ido bafulatani yayi mutanen mota kuwa sai cewa suke wannan yarinya akwai tsaurin ido.
Ko tasha dreba bai ƙarasa ba ya tsaya a gefen titi yace "walhi kowa ya sauka babu wanda zankai tasha ke kuma kiyiwa babanki waya ya kawomin kuɗin mota sauri nake ".

Bayan kowa ya fito ya rage Delu ita kaɗai dreba ke jira ,a hankali ta fito tare da gyara mayafin data rufa a kanta tace "ka jirani ai matambayi baya ɓata ,kai kuma ɗan filani wlhi sai na koya maka hankali "
Hannunta dreba ya riƙe tare da cewa "wlhi ina nan dake yau ko ki kirashi ya kawomin kuɗi kokuma in kaiki gurin ƴan sanda kisha duka "jiki na rawa Delu ta kunce gefen zaninta ta ɗauko ɗari biyar ta miƙa masa tare da cewa "Allah ya isa taja ƙafar bafilatani ta ruga da gudu , tana cikin gudu wata mota sharon tayi gaba da ita.
Da gudu mutane sukayo kansu mai motar yayi parking tare da fitowa cikin firgici yana mai-maita innalilahi wa inna'ilaihi raji'un Allah yasa tana da rai " .
Ihun da Delu keyi ne zai tabbatar maka da tana cikin mawuyacin hali .
Lokaci guda mutane suka taru a gurin suna jajanta abin daya faru , shiko saurayin idanunsa sunyi jajir ya kalli Delu dake kwance cikin jini yace "Allah kasa tanada rai ".
Wani dattijo dayazo yanzu yace "kuyi maza ku kaita asibitin murtala ,amma wannan bazai iya tuƙi ba, a nemo mota "batare da ɓata lokaci ba aka tsayar da mai napep ya wuce dasu asibitin murtala , koda suka isa cikin asibitin aka ƙi karɓarsu sai da suka zo da police ,
Dreban daya ajiye su Delu ya ɗora hannu a kai tare da ambaton hasbunallahu wani'imal wakil ,yace duk mai zuwa asibitin yazo su tafi ,harda saurayin daya bigeta aka tafi .
Suna isa sukayi tambaya aka nuna musu ɗakin da aka kwantar da ita ,
Samunta sukayi tana bacci ,dreba da sauran mutanen da suka biyota suka ajiye kuɗaɗe tare da yimata fatan Allah ya bata lafiya saurayin yace "amin ".
Dreba ya kalli saurayin kana yace "nidai a ƙauyen DASHI na ɗaukota ina tunanin idan ta farka zata gane inda zata ".
To kawai saurayin yace sbda burinsa yaga ta farka ,tunda yake a duniya bai taɓa buge koda kaza bace ,amma yau ikon Allah ya kaɗe mutum .
Har suka fice bai san sun fita ba hankalinsa na gurin Delu dake kwance kamar matacciya .
Kasancewar idonsa na kanta yasa shi ganin motsin data farayi da hannunta ,cikin sauri ya tashi tsaye tare da ƙarasowa bakin gadon ,a hankali ta fara buɗe ido ,ganin mutum na tsaye a gaban gado ya sata waro idanunta duka tana mai ƙare masa kallo ,
Fari ne tass dogo yana ɗauke da dogon ganci da matsakaicin baki idanuwansa ƙanana shiyasa lumshesu yafi komai yi masa sauƙi , fuskarsa na kewaye da baƙin saje , gashin girarsa luf-luf lips ɗinsa kuwa pink ne masu taushi sosai daga kallonsu zaka tabbatar da hakan.
Yunƙurawa tayi tare da dafe kanta dataji yayi mata nauyi kasancewar an ɗaureshi saboda ciwon dataji .
Ɗaukar filo yayi ya jingina mata a jikin gadon kana yace "sannu baiwar Allah "kallonsa kawai Delu keyi sabda komai da Allah yayiwa wannan saurayi ,a zuciyarta kam tana tantama kodai ba 'a duniya take ba ,sbda shidai wannan saurayi sanye yake da farar shadda babu aiki a jikin rigar tasa ,hannunsa na riƙe da wata faskekiyar waya mai bala'in kyau gashi asibitin ma komai fari anya ba acikin aljannah take ba ?"
Maganar da saurayin yayi ne ta dawo da Delu daga duniyar tunani yace "me kike da buƙata a siyo miki ? duk da zafi da kanta keyi mata bai hanata yin magana ba tace "tsire da lemu da abarba da kankana da balangu da kilishi da danƙwalwliyar kaza idan ka sami awara mai zafi dan darajar iyayenka ka haɗo min dashi "

Waro ido saurayin yayi kana yace "tom insha Allah zan taho miki dashi koma ki kwanta ".
Ba tare da tayi masa musu ba ta kwanta shi kuma ya fita .
Yana fita ya tari napep ,bayan ya shiga yayiwa mai napep bayanin inda zai kaishi , cikin ikon Allah suka iso inda motarsa take ya bawa mai napep kuɗi ,ya shiga motar shi yawuce inda ake siyar da kayan marmari ,
Yana daga cikin mota yayi wa mai lemo magana ya haɗo masa na dubu uku , yayiwa mai gashin kaza akawo masa na dubu biyu da tsire na dubu ɗaya ,aka ciko masa leda babba ,aka miƙo masa ya miƙa kuɗi ,yayi musu godiya yabar gurin....!


More comments more typing


MOM ISLAM
🤣🤣🤣🤣🤣

*MK MIJIN DELU*
(Hatsabibiya)
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂



*Zainab Habib(Mom Islam*






Dan girman Allah idan kina grps ɗina karki shiga wannan pls🙏👆



_Elegant online writers_



Page 5-6

Yana shiga asibitin bayan yayi parking ɗin motarshi yaji wayarsa na ring ,sai da yaɗan yi jimm kana ya ɗauka tare da cewa "Hajja B wlhi tsautsayi ne ya samemu amma ina tunanin zamu dawo yau "
A firgice wacce aka kira da Hajja B tace "gwaron namiji mekuma ya faru ?dakai ɗazu fa na fito daga gidanku "
Saurayin ya lumshe ,ƙananun idanuwansa kana yace "karfa ki damu zan dawo anjima "
Hajja B tace "ka faɗamin asibitin da kazo in biyoka "
Yana shirin magana yaji muryar mara lafiyarsa tana cewa "kai ɗan farin saurayu wlhi ka fito ,danma ance a aljannah ba'a zuwa ɗakin kowa wlhi dana tafi yawo amma a hakan ma bazan rasa mai jin tausayina ba gara ka fito "
Murmishi kawai saurayin yayi kana yace "zo gani kice ma kin warke ?"
Sunkuyawa tayi ta dafe ƙafarta tare da fara ɗingishi tace "nifa ban warke ba bani ledar "
Kai tsaye ya miƙa mata ledar tare da wucewa ciki itama ta bishi , waigowa yayi ya ganta tana tafyarta normal ,hakan ya sashi yin dariya mai sauti .
Delu ta juyo tare da galla masa harara tace "wllhi yau zan tafi gida "saurayin yace "dama yau za'a sallameki insha Allah ,
Suna isa ɗakin ta haye kan gado ta bubuɗe ledojin , kallonsa tayi kana tace "ina awarar ?saurayin yace "afuwan idan muka fita zan siya miki "
Batayi magana ba tafara cin abin dake gabanta ,babu abin da bata ci ba amma duk iya mugun cinta takasa cinyewa , ta turo cikinta tare da duba ɗaurin zaninta tace "yanaji babu kuɗina a jiki wlhi anyimin sata kuma dole a biyani "cikin gaji da surutu saurayin yace "me aka sace ?"Delu dake shirin yin kuka tace "wlhi kuɗina dubu uku suka kwashemun kuma na sautu ne Allah "ta ƙarashe maganar tana share hawaye .
Nisawa saurayin yayi kana yace "karki damu zan biyaki amma dai babu inda yake miki ciwo ko ? gyaɗa kai tayi alamar eh shikuma yace "good "
Shigowar likita ne yasa hankalinsu ya koma gurinshi bayan yayi wa saurayin ya mai jiki ,ya kalli Delu yace "jiki yayi kyau kinci abinci kenan ? Delu ta murguɗawa likita baki kana tace "meya shigo dakai ?ko ka mance a 'aljanna ba'a zuwa yawo ?dariya ce ta kufcewa likita sbda yaga harga Allah take maganar yace "to ai nan a Kano kike ,kuma a asibiti yau ma zan sallameku amma dai yamma tayi tunda yanzu ƙarfe 6:20 shida da ashirin ".
Delu ta sakko daga gadon ta durƙusa har ƙasa ta kama rigar likita tace "dan Allah kayimin rai ,karka salamemu kaji ni wlhi nan jinake kamar a wata duniyar nake yanzu fa kayan marmarin can sai dai ku zubar ko ? ta ƙarasa gadon tana kwashewa ta riƙe ledar a hannunta ,ta kalli wanda ya bigeta tace "kai ɗan kyakkyawan saurayi kace "ban warke ba "
Daga likita har saurayin dariya sukayi ,saurayin yace "ai babu mai son cuta inba dole ba ,gashi danaga kin sami sauƙi harnaji daɗi sosai bari ya kawo sallama sai mu tafi ki nunamin gidanku "
Hannunsa likitan ya kama tare da cewa "muje office "
Bayan sun shiga office sun zauna likita ya kalli saurayin kana yace "idan ban mance ba sunnanka Muhammad Kareem ko ? murmishi saurayin da aka kira da Muhammad ɗin yayi kana yace "eh hakane "amma ana kirana da MK "masha Allah likita yace "kana ya miƙa masa takarda da magunguna a leda yace "na rubuta inda zata shasu saboda ciwon dake kanta ya warke da wuri insha Allah "
Godiya MK yayi kana yace "to nawane kasan bamuyi maganar kuɗi ba, likita yaɗanyi juyi a kujerarsa kana yace "15k ne " okay MK yace kana ya ƙirgo ya bashi sukayi sallama ,
Ɗakin da Delu take ya shiga ya sameta ta narke har wani numfarfashi take "shi dariyama ta bashi yasan ba gaskiya bane tace "maza tashi ko ayi miki allura "da sauri ta tashi harda sauka ƙasa tace "gani kaji?"
Duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yayi kana yace "taɓɓ har ana kiran magrib ya ilahi " sai kuma yayiwa Delu alama da su tafi "babu musu tabi bayansa suka nufi gurin motarsa ya shiga ya buɗe mata gaba itama ta shiga .
Bayan ya tada motar suka fice daga asibitin ,kallonta yayi kana yace "ina zan kaiki ? ma'ana gidanku " Delu tace "nifa ba anan garin nake ba , dama na fito mota ta kaɗeni ne saboda bani da kowa a duniya sai akayi sa'a kaine ka bigeni gashi ban mutu ba "a gifice ya taka burki sbda firgici da ya shiga akan maganar da Delu keyi ,dole tayi...


Read / Download MK MIJIN DELU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album