Join Our WhatsApp Group

AMINIYA TACE Complete Hausa Novel Document by AMINIYA TACE


AMINIYA TACE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33266



AMINIYA TACE

Reading Time: 2 Hours

Added On: 01, Sep 2023

Author: Maryam Alhassan Dan Iya (Maryam Obam) ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08060860886

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 173.55 kb

File Type: txt

Views: 709+

Download: 245+

Last download: 18 hours ago

Description/Story: ο»ΏAMINIYA TA CE
Na Maryam ALhasan Dan iya mrs Nura Kuriga
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf

[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’
(Mrs nura kuriga)😘🌹

Dedicated this page to fatima zarahπŸ’ƒπŸ»
1⃣to5⃣

Da sunan Allah mai rahma mai jin qai, da ya sake bani dama na sake rubuta wani sabon littafi, Ina rokan Allah daya bani ikon kammalawa dan alfarman annabi Muhammad (s a w)

"Zeena ce zaune a class tayi uban tagumi, ta rasa maike mata dadi, mlmn maths nata musu bayani amma bata ma San yana yiba, kaman daka sama taji ana kiranta da sauri ta d'ago kai, ta saki murmushi da kara, suka rungume juna ita da Mysha, Zeena tace haba friend why are you late today,I though you are not coming today, Mysha tayi murmushi tace sorry Zeena na raka daddy airport ne daka nan driver ya Kawo ni, mlmn maths ne Ya katse su tare da fadin Zeena nd Mysha keep quick please, kasan cewan makarantan kudi ne, ba'a takura ma yaran sannan teachers din kaman tsoran student din suke, domin skul din sai dan wane da wane, kowa na tsoran ya bata ma student rai, kar allura ta janyo garma, Zeena tace sorry sir, yaji gaba da gudanar dasu, har ya fita, wani ya shigo, har aka fita break, Zeena suka je, yin break suna tafiya suna fira har suka karasa restaurant din skul din, ga snacks nan kala2 sai wanda kaga daman ci, Zeena ta dauko musu ice cream Mysha kuma ta dauko, cookies suka nufi kan wani table suka ajiye kayan sannan suka zauna, suna ci suna fira, Mysha tace Zeena kin San wani Abu kuwa? Zeena tace a'a sai kin fada, Mysha taci gaba da cewa daddy dazu muna hanya zan raka shi airport yake cewa wai ina Gama secondary skul zai min aure, Zeena ta zaro ido tace what? Sai kace a zamanin da, may be he is joking, mysha tace no Zeena he is not joking, Ya dade yana yin wannan maganan, kuma daddy inya fada Abu toh he is serious, Zeena tayi shuru tare da tausayin kawar tata, can tace toh ke Mysha bakya kula kowa, yanzu wa zaki aura, Mysha tace nima abunda nake tunani kenan, yasa koda yaushe nake jin wani iri idan na tuna bani da saurayi wanda nake so, Zeena tace toh ke yanzu mai zaki fada ma daddy dinki inya tambayeki akan wanda zaki aura, Mysha tace nima ban San amsa din ba, ke gwara ke ko yanzu akace ki fito dashi zaki Kawo shi, duk da ban taba ganinshi ba, har yanzu, Zeena tayi murmushi taji an Kawo zan cen prince dinta, Mysha tace wannan murmushin fah, a dai2 lokacin wani yaro mai suna afraz yazo kusa dasu ya kafa ma Zeena ido kaman tsohon maye yace sannunku yan mata, Mysha ce ta amsa, yace ya naji kunyi shuru, yaci gaba da fadin Zeena wai mai yasa koda yaushe indai kika ganni saiki canza fuska, ki duba duk skul din nan ko wace yarinya so take yau ace ina kulata, amma ke na rasa dalili da yasa bakya so inzo inda kike, Ya kalli Mysha yace please Mysha am I not handsome, Mysha tace you are, infact ma babu macen da zata ganka bata kuma kallonka ba, yayi murmushin jin dadi yace thank, sannan ya kalli Zeena wanda ranta ya Gama baci da Mysha yanda take wasa shi, ta mike da nufin ta wuce, ganin haka yasha gabanta, Ya tare ta, tare da fadin Zeena you better stop this nonsense, how dare you ina magana kina wani tashi zaki wuce, duk wanda suke wajan hankalinsu ya dawo garesu, ta kalleshi ido cikin ido tace you have to know 1 thing I really hate you, I hate everything about you, infact ma bana son ganinka, tsayawa yayi yana kallonta da mamaki, dama zaiga irin wannan ranan har mace ta tsaya tana gaya mishi magana duk yanda yake da kyau ga kudi ga aji, yan mata suke rubi binshi, amma yau y'a mace take wulakanta shi, a gaban mutane, ihun da akeyi a wajan yasa ya dawo daka tunanin daya fada, a dai2 lokacin Zeena ta wuce Mysha ta rufa mata baya, yayin da afraz yaji kafanshi yayi mishi nauyi wani irin kunya ya rufe shi, amma haka ya fita, kai tsaye wajan motanshi yayi yashiga ya tada ta, Ya fita daka skul din,Sheraton hotel ya nufa ya kama d'aki, Ya kwanta idonshi yayi ja babu abunda yake tunani sai abunda Zeena ta mishi, Ya kasa komai Ya tashi dakyar yaje motanshi ya dauko kwalban codein ya kwankwade, sannan ya samu bacci ya dauke shi, a lokacin da Zeena da Mysha suka nufi class, Mysha tace Zeena kin San mai kikayi kuwa? Zeena cikin tsiwa tace mai nayi, tell me, Mysha tace Kin San afraz kuwa kin San waye shi kuwa, Zeena tace ban sani ba ban kuma fatan in sani, plz indai kin San maganan shi zaki min, plz leave me alone, jin haka Mysha tayi shuru, amma a cikin xuciyanta tana tsoran abunda afraz zai mata domin hatsabibi ne, gashi ta wulakanta shi gaban mutane, skul din duk an baza labarin, a lokacin da aka tashi Mysha tabi Zeena dan ta ajiye ta a gida, yau bada matan ta tazo ba, kasancewan ta raka daddy dinta airport, dukansu babu mai magana, can Zeena tace Mysha mai yasa kikayi shuru baki cewa komai, Mysha tayi Dan murmushin yake tace mai zance Zeena wlh ina tsoran afraz, ban San mai zaiyi ba, Zeena tayi dan murmushi tace plz Mysha kinga ni harna manta shidin banza wlh bai isa yamin komai ba, nafi karfinshi, ita dai Mysha jinta kawai take, domin afraz bama a skul dinsu ba, kaf garin Abuja dakyar ne kaji wajan da ba'a sanshi ba, baya ji gashi idan yana son abu, ko miye sai yasan yanda ya mallake shi, kota halin 'ka' ka wannan kenan da haka har suka karasa gidansu Mysha ta ajiye ta, ta wuce gida,

Wacece Zeena?

Zeenat abubakar yan asalin garin katsina ne, su uku iyayensu suka mallaka, akwai yayanta adeel wanda yake karatu a kasar Japan sai ita dake aji hudu a famaks sai kanwarta mai suna aysha, suna kiranta da abda, sun taso cikin gata duk da irin gatan da suke ciki suna karatun islamiya kuma sun San addini dai2 gwargwado, mahaifinsu senator ne sau biyar yana ci saboda mutum ne mai rikon Amana kuma dadtijo ne, duk irin kudin da Allah ya mishi bai bar yayanshi sun lallace ba, yana tsaye akan iyalinshi, mutum ne mai son yaga yara sunyi ilimi sai yasa Zeena bata tunanin aure duk da, tana da saurayi wanda yake matukar sonta itama tana sonshi amma baya kasan nan yana China yana kula ma mahaifinshi da wasu aiyuka wajan shekara biyu, kullum suna makale a waya kaf gidansu babu wanda bai San zaheer ba, Zeena mutane da yawa suna mata kallon miskilanci don bata cika son yima mutane magana ba, in kaga ta kula ka toh babban dalili ne, sabanin kanwarta Mysha mai son magana, har wasu na mamakin kaman can nasu, sun hadu da Mysha a skul suka kulla kawance har suka hada iyayensu kawance.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’
(Mrs nura kuriga)😘🌹

Dedicated this page to zee babyπŸ’ƒπŸ»
6⃣toπŸ”Ÿ

"sai wajan shabiyu da wani abu afraz ya farka daka baccin daya dauke shi, Ya tashi tare da mika, komai daya faru duk ya manta, amma ganinshi a hotel yasa ya fara tuno abunda ya faru, lokaci daya yayi tsaki tare da fadin, Zeena you will regret it, toilet ya fada yayi wanka, Ya fito ya shirya ya nufi gida, kai tsaye dakin shi ya nufa, Ya fada kan gado yayi ruf da ciki, yana ta sake2 a ranshi, da haka bacci ya kuma dauke shi,

Zeena ce zaune akan dinning suna breakfast ita da abda, tana yi tana kallon agogo, har mahaifiyarsu wanda suke kira da ummi ta karaso, tace Zeena wannan saurin fah, tace ummi banso inyi late ne, muna da test yau ban samu nayi karatu ba jiya, so inna shiga skul da wuri zan Dan karanta wani abu, ummi tace yanzu na rasa dalilin da yasa bakya daukan karatunki da mahimmanci, kwata2 kinsa wasa inda dane aida kin San abunda kika taka, wai maike damunki ne Zeena? Tayi shuru ganin ummi din ta kafeta da ido yasa tace ummi nima kaina ban sani ba, ummi ta kuma kafeta da ido tana son ta fahimci wani abu daka yar tata, amma ganin babu abunda zata fahimta yasa ta canza maganan da fadin yau in kin dawo daka skul zaki rakani wani waje, ta amsa da toh ta Mike, abda tace ummi nima dani zaki koh? Tayi Dan murmushi tace yes my dear tasa dariya a dai2 lokacin skul boss din su abda yayi horn ta fita da sauri ta wuce.

Mysha da Zeena suna zaune a study room suna ta karatu gefe kuma wasu student ne suma suke ta faman karatun, jin kaman tsayuwan mutum a kanta yasa ta d'aga kai, hada idon da sukayi saida gabanta ya fadi, amma ga mamakinta sai taga yana mata murmushi, ta tashi zata bar wajan, yace haba Zeena mai yayi zafi haka, tace afraz please ka fita daka harka na, bana son kana shiga cikin harkoki na, Ya kafeta da ido yace Zeena dan na miki magana nayi laifi ne? Tayi banza dashi ganin haka yasa ya kwace littafin dake hannunta, ta waigo cike da masifa amma ganin ya tamke fuska gashi sun hada ido, yasa tace plz kaban book dina, Ina karatu, kaman bazai bata ba, komai Ya tuna kuma oho, Ya mika mata littafin, tana amsa tabar wajan, Mysha ta tashi itama, amma jin ya kira sunanta yasa ta tsaya, yace ina son magana dake, tace ina jinka, yace wai mai zanma Zeena ta soni, ni inma samu ta dinga kulani, Mysha tayi shuru can tace afraz mai yasa baza ka barta ba tunda bata sonka, akwai wanda take so, tana fadin haka tabar wajan, Ya bita da kallo tare da wani murmushi wanda shi kanshi yasan dalilin yinshi.

Ummi ce cikin wani tsadaddan leshi mai kalan milk colour flower din jikin leshin kuma purple, yayi mata bala'in kyau, ta nufi dakin Zeena taga itama ta shirya cikin wani material red nd golden, dinki doguwan riga, yayi mata kyau sosai, ummi tace muje Dan Allah kin cika bata lokaci, Zeena tayi murmushi tace na gama ai, ta dauko wani karamin gyale ta yafa, suka fita, cikin wata mota suka shiga mai Kiran Prado, driver yaja su, Zeena tace ummi wai ina zamu haka ne, ummi tayi murmushi tace Mrs hakeem ce ta gaiyace ni dinner gidanta, tace owk, tun daka nan ta kama bakinta tayi shiru, Mrs hakeem wata kawar ummi ce mijinta minister ne na agricultural, sun karasa gidan, sunga motoci da yawa na mutane a gidan daka gani gidan cike yake da mutane, sun shiga falon makil da jama'a Ana ta ciye2, Mrs hakeem na ganin ummi tazo da sauri ta rungumeta sannan suka zauna, Zeena ta gaida ta, ta amsa cike da fara'a, ummi tace wai miye na hada wannan taron? Mrs hakeem tayi dariya tace yau 35yrs da auranmu, ummi tace wow har kun kai haka gskiya lokaci na gudu, anci ansha kowa ya watse daka gidan.

Wayan Zeena keta faman ringing, tayi dan gajeran tsaki ta dauka, ganin sunan mai Kiran yasa tayi sauri ta dauka, tare da fadin hello, ta dayan bangaran ya amsa da gimbiya ta, Ina kika shiga inata kira? Tace sorry dear bacci nake yi, karan Wayan nema ya tashe ni, yace kina bacci kin manta dani, tayi dan murmushi tace ni na isa, yace gest watch, tayi shuru can dai tace fada min, yayi dariya yace ina naija, dazu na sauka, tace what a surprise, amma baka kyauta min ba, shine baka gaya min ba, yayi dariya yace amin afuwa, cikin shagwaba tace anyi ma, yace gobe ina nan tafe, tace sai Kazo nayi missing dinka sosai, yayi murmushin jin dadi yana mamakin jin kalaman nan daka bakin Zeena, wanda ya tabbata baza ta iya gaya mishi tayi missing dinshi a gabanshi ba.

Washe gari Zeena anata shirye2 na taran adeel, Ana ta girke2 kala2 dasu drinks kala daban2, duk wanda yaganta yasan tana cikin farin ciki, bayan ta kammala komai taje tayi wanka ta shirya cikin wani leshi mai ruwan Zuma, da zanan baki a kai, yayi mata kyau sosai, tayi kwalliya na kece raini, duk wanda ya ganta saiya yaba da irin suranta da kyau da Allah yayi mata, ta zauna tana jiran zuwan gwarzon nata don tun dazu ya mata waya yace yana hanya, komai an jera a falon saukan baki, sai kamshin turaran wuta yake.

Wayanta ne yayi kara ta dauka, da sauri ji tayi yace gani a gidansu, tace gani nan, da sauri ta fita, ta iskeshi a mota, yana jiran zuwanta, ta karasa gareshi, Ya kafeta da idon nan nashi, wanda yake rud'a ta, itama kallon nashi ta tsaya yi, Ya kara kyau da wani haske, yace wow my princess kin kara kyau da girma 2yr rabon mu da ganin juna, tayi Dan murmushi tare dajin kunya, tace mai fito mu shiga ciki babu musu yabi bayanta, har falon baki, Ya zauna cikin daya daka kujerun falon, Ya kafe ta da ido, yana mamakin irin girman data kara, da kyau, wani irin sonta yaji yana kara shiganshi, tare da burin yaga ya mallaketa, ta matsa kusa da jerin kayan ciye2 da aka ajiye a falon ta zuba mishi coconut juice, ta mika mishi ya amsa tare da murmushi yasha, sannan ya kalketa yace Zeena har yanzu kina sona kuwa? Ko an kwace min ke, sai taji nauyin maganan daya mata, tayi kasa dakai, a dai2 lokacin Mysha ta shigo falon da sauri tare da fadin ina bakon namu, gabaki daya komai nata ya tsaya ta kasa ko motsi, sai dai a zuciyanta take ta nanata wa, tsarki ya tabbata ga Allah wanda yayi wannan hallita, adeel ne Ya katse mata tunani da fadin Mysha right?mai makon amsa sai tayi murmushi wanda ita kanta bata San tana dashi ba, ta karasa shigowa falon ta zauna, Zeena tace ya akai ka gane ta? Yayi dan murmushi yace nasan itace daka yanayin yanda ta shigo, Zeena ta kalli Mysha wanda ta kafe adeel da ido, tace sai yanzu koh, tace kiyi...


Read / Download AMINIYA TACE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album