Join Our WhatsApp Group

KYAUTAR ALLAH Complete Hausa Novel Document by KYAUTAR ALLAH


KYAUTAR ALLAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 278111KYAUTAR ALLAH

Reading Time: 23 Hours

Added On: 19, Sep 2023

Author: Sa'adatu Bintu Abdullahi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.54 mb

File Type: txt

Views: 3827+

Download: 9183+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: [8/4, 19:30] +234 913 133 0334: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺
*KYAUTAR ALLAH*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺


Alhamdulillahi am back


SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽 (Marubuciyar boyeyyen al'amari)

Dedicated to hauwa'u mmn little saudiya and mom amatullahi.

Inama kowa barkada sallah.💃🏽


Page 1

A garin katsina safana lacal government, a wani dan madaidaicin kauye, me dauke da gidaje ginin kasa. Sede wani gini dankarere, wanda ya amsa sunansa gini bulo na gugar bulo, a gaskia ginin ya tsaru, kai inkaga ginin ka rantse da Allah a birni yake, duk garin babu gini dayakaishi kyau, da tsaruwa, domin kuwa kofar gidan dankareren getne me mugun kyau, yayinda a saman get din gidan aka rubuta *SAFANA HOUSE* da Ruwan gold Kai tsaye na dannakai cikin gidan, ma aikatane taf a bakin get din gidan masu sanye da kakin sojoji.

Ginine hawa biyu sama da kasa, a farfajiyar gidan akwai motoci biyar na alfarma, DUK CIKI BABU MOTAR MILIYON, sede zillions.

A falon kasa naga wata tsohuwa zaune a kan lallausar kujera, hutu da kwanciyr hnkli ya rasata.Farace Sol tsohuwar kai daganinta kasan bafullatanace dukda ta tsufa tukuf amma hkn be hana kyawunta ya boyuba, hajiya Annah kenan ikon allah. Benu, baki tsufa sede ki sake sabon gashi. Shine kirarin da Jikanta *muhammadu raslan* yakeyi mata.
Daga gefen Annah wata kyakyawar yarinya na hango kwance a kn cinyarta, idanuwanta a rufe, yyinda tunanin abbahnta fall ranta, dukda kuwa jiya ya tafi amma sam se takejin kmr tayi shekara bata ganshiba. yatsu ne ke bakinta tana tsotso, hutu ya ratsa yarinyar dagani. Sanye take da riga da wando kalar peach irin na yan hutunnan, luf kyn suka kwanta a kn kalar fatar yarinyar, wato ita kalar chocolate ce irin me shining dinnan.a kallah yarinyar batafi 12yrs ba.


A gaskia kujerun falon sun tsaru, sunyi kyau ainun tsayawa fadar kyaun falon is a west of time fans. Amma komi yaji. Hotunane manne a duk inda na wurga idona a falon hoton wani saurayi da wannan yarinyar dana gani a kwance, saurayin dasuke hoton matashine fari sol dashi, kmr ka taba jini ya fito. Saurayin nada cikar kamala da zati da haiba. ita kuma yarinyar kalar chocolate ce irin kalarnan me mugun sheki, yayinda duk suna dariya a hoton, hannunshi cikin nata, tanada wushirya sama da kasa, yayin kyaunta ya gigita lissafina, tuni tunanina ya dauke na wasu yan dakiku. Shikam matashin dimples garesa gefe da gefe, a gaskia ya hadu, kmr balarabe.

A wasu hotunan kuma tana karama, wani kuma tana jaririya wani kuma tanada girmanta amma da yatsa a bakinta tana tsotso, se abin ya daureminkai, wai yar 12yrs ce ke tsotson yatsu biyu, ammafa se naga tsotson yatsar ya kara mata kyau ainun. Wani hotone yafi daukar hankalina wanda take kwance a kn kirjinsa, da yatsa a bakinta, a jikin hoton an rubuta *KYAUTAR ALLAH* da mnyan harufa kalar gold, sanye take da riga da skeet na lace a hoton.

Zaune suke sanyin ac na ratsasu. dayake akwai wuta a kauyen dalilin hajiya aisha har yan kauyen suka samu wuta, domin kuwa Yayanta duk sunada budi, musamman ma Alhaji umar safana.

A duniya yara hudu Allah ya mallakawa aisha da jibril sudin haifaffun garin katsinane (Katsina ta dikko dakin kara) cikakkum fulanine na ainihi, auren zumunci aka yima jibril da shatu. Jibril a jeji suke a wancan lokacin, kowade yasan sana'arh fulani kiwon shanu domin shanaye sune dukiyar fulani.

Da mahaifin jibril da mahaifiyar shatu yanwa da yan kani suke, a haka akayi musu aure, jibril nada 15yrs shatu nada 7yrs, tinde ba asan inda rayuwa takeba' ba amasan meye aurenba har Allah yasa akazo aka fahimci meke tafiya a duniyar. Allah ya azurta jibril da shatu da yara hudu, uku maza se autarce mace, wadda seda suka cire rai da haihuwa,se kuma allah ya basu ita. Domin kuwa har shatu ta cire ran samun diya mace , don ada anama tunanin haihuwar tata ta tsayane. Se gashi allah yayi ikonsa.

aikou nan ta dauki son duniya ta dora mata, haka shima jibril a bangaren kakanninsuma sunfison auta rukayyah wadda taci sunan mahaifiyar jibril ake kiranta da *KYAUTAR ALLAH*.

Dukda a kauye suke hakan be hana jibril tsayawa yaransa mazaba sukayi karatuba sosai, domin kuwa a cikin gari suke fita karatunsu, su mazan kenan. Na farkon sunansa harun se na biyun musa sena ukun umar. Yaran sun tashi da hazaka kan kace kwabo Allah yasa musu hannu, yayinda umar ke karantar harkar kasuwanci, shi kuma harun acouting ya karanta shikam musa, harkar siyasa ya karanta.

Auta rukayyah wato *KYAUTAR ALLAH* itama daidai gwargwado tayi iya nata karatun.wato Allah yasa mata wani irin kyaune na mamaki, itadin yar madaidaiciyace, tin tana 7yrs maza ke kawo hari amma ina ainan shatu ta tsaya tsayin daka kan ba wanda ya isa yayima yarso dinta abinda akayi mata wato auren wuri.

Yayinda dukkanin mazan kowa ya kama ma tsaya Allah ya daukakasu fiyeda tunanin me karatu, amma Allah yafi daukaka alhaji umar wato na ukun. Allah ya azirtasa da dukiya taban mamaki, dominshi dan kasuwane, ya shahara kwarai da aniya, duk fadin nigeria da niger da ghana babu wanda besan da *Alhaji umar jibril safana* ba.

Alhaji harun yayi aure ya aura fulani, ta haifa da daya namiji wanda yaci sunan jibril. Wato mahaifin harun.

Musa kam tini ya samu mukamin govenor a garin kaduna a ynzu hk. Yanada mata biyu dayace ta haihu yara uku duka maza amma dayar sam bata haihuba.

Toufa Annah shatu da anyi haihuwa taji ance namiji, se murna ta koma ciki. itakam Allah yasa mata son mace, gashima yarannata basuda yawan haihuwa abunna damunta, Annah macece me fada fada ga surukanta musammanma in bata sonka toufa ka bani, jika kuwa sam bayashan ruwa a gabanta, Dan ita tafison danta bawai jikaba.

Nanfa ta matsawa umar kan dole shima yayi aure kou Allah zesa shidin ta hanyarsa tasamu jika mace. Ai data tasa sa agaba dole tasa ya aura wata shuwa'arab dasuka hadu a garin barno yaje business dinsa. Mace me natsuwa ya aura me suna zainab, zainab tanada kyau domin kuwa duk a cikin matan babu macen data kaita kyau da haduwa, farace soll. Amma kuma se akayi rashin sa'arh sam Annah bata kaunarta. Hakan yasamu nasabane da yadda, zainab ta iya rike mijinta, kunsande yadda matan shuwa suke da iya rike miji ladabi da biyayyah etc.

Duk wannan labarin danake muku ita KYAUTAR ALLAH batafi 15yrsba a lokacin domin kuwa tsakaninta da wanda takebi shekara Goma sha biyarne ne.

Ana haka, zainab tasamu ciki. Ainan Annah ta fara sonta da tattalinta a tunaninta, kou mace zata haifa. Amma kashe ranar haihuwa ta santalo santalelen danta namiji me kyau. wanda yaci sunan mahaifin Annah wato, Muhammad ake kiransa da *Raslan* tou yaronde yaci darajar dande kawai yanada sunan mahaifintane yasa Annah ke daga masa kafa. Amma kullum adduarh Annah daya Allah yasa tasamu jika mace.

Ana haka dukkaninsu kowa ya koma inda yake aiki dazama harun ya koma garin kano, yayinda musa ke garin kaduna, shikam goga alhaji umar da matarsa zainab suna garin abuja.

Annah da alhaji jibril sun more yaya, domin duk shekara se sunje hajji da umra, a kallah bazasu iya kirga adadin, sau nawa sukaje, dakin allah ba.


Ana hk Allah yayima, mahaifinsu alhaji jibril rasuwa bayan yayi doguwar jinya, a china. na ciwon sugar, tou a nan se muce Allah ya jikansa mukuma Allah yasa mucika dakyau da imani. Annah tayi kuka ta gaji *KYAUTAR ALLAH* kan seda ta kwanta asibiti domin har lokacin batayi aureba, dan Annah tace sam aure ba ynzuba ita indama son samuntane kada KYAUTAR ALLAH ta matsa daga inda take, bakaramin so Annah keyi mataba, haka suma yayyun nata ji suke kmr zasu lasheta, yar gatace gaba da baya.

Daman alhaji jibril ke takawa Annah burki tou ynzu babu shi dan haka duk yadda ta tsara hakanne ke faruwa a family din, dukda basa kusa amma Annah tasa musu ido a hkma dan KYAUTAR ALLAH na taka mata burki shiyasa abubuwan ke sauki. Daman tin kafin mutuwar malam jibril yarannasa sukayi sukayi su dawo birni amma Annah tayi fir tace aah dayake jibril mutumne me hkri dan hk duk abinda Annah tace kouda yakeda rai sede yabita da tom. Dole sede Suka siya gabaki daya anguwar suka graya musu, sukayi musu ginin zamani me hawa biyu nanma Annah nata fada wai almubazzarancine, tin kafin mutuwar jibril akayi hkn, a ynzu hk kullum cikin gyaran gidan suke.

Autan family's din shine *MOHAMMED RASLAN* seda yakai shekara sha biyar , duk jikokinma sun tasa yayinda babban jikanma keda matarsa nanma Annah tasa ido taga tattaba kunne mace, amma ina se maza biyu itama ta haifa. Jikokinma sun samu ilmi sosai. Yayinda *RASLAN* ya tashi da kwanya taban mamaki, shima burinshi ya gaji mahaifinsa wato fannin kasuwanci. Nan da nan arziki ya habbaka a family din jikokima arziki,tom daman ai cikin arzikin suka taso.

Ana hk KYAUTAR ALLAH tasamu miji dan niger buzune, alhaji Abdallah yanada rufin asiri, yana kasuwancinsa, da kyar Annah ta bari akayi auren a lokacin KYAUTAR ALLAH nada 25yrs, a garin katsina nan KYAUTAR ALLAH take zaune daman nan kasuwancin mijinnata yake. Nanfa hajiya aishatu wato Annah ta zuba ido tana jiran ganin cikin diyar tata kullum cikin adduarh take Allah yasa KYAUTAR ALLAH ta haifa mata diya mace. A hakade aka kwashe shekaru uku KYAUTAR ALLAH kou bari bata tabayiba,

Duk a family din jinin KYAUTAR ALLAH yafi haduwa da Dan yayanta RASLAN domin RASLAN yana respecting dinta, ta dauki son duniya ta dora masa tin yna qarami harya girma,shima ya dora mataso fiyema da iyayensa hk yakesonta dukda tayi aure kullum yna hnyar zuwa katsina duk weekend a gidan KYAUTAR ALLAH yakeyinsa. A haka yazo yabar kasar zuwa ingland Dan Karo karatu a fannin kasuwanci, a lokacin ynada 20yrs.

Bayan tafiyar *RASLAN* da shekaru biyar Allah ya bawa KYAUTAR ALLAH ciki, aikou zokaga murna gun Annah rnr ai batayi bacciba kwana tayi tna ibada tana godewa ubangiji da fatan Allah yasa a haifa mata mace me albarka wadda zatayi alfahari da ita dama duniya gabaki daya. Washe gari kuwa ta fara shela ga iyalan nata babu wanda bata gaya mawaba hatta Raslan da baya kasar seda ta kirasa ta gaya masa, shima yayi murna sosai, harda azumi yayi na godiyar ubangiji shima adduarh dayace Allah yasa macece me albarka kuma Allah yasa tayi kma da KYAUTAR ALLAH.

Annah tasa anyi sadaka da dukiya ta fitar hankali duk dan saboda samun cikin KYAUTAR ALLAH ji takeyi kmr rnr ne zata fara samun jika.

Family kam wasu na murna wasu na bakin ciki wasukam adduarh sukeyi Allah yasa a haifa namiji suga ta tsiyar Annah, kou ince suga iyakarta.

A bangaren KYAUTAR ALLAH Kam tinda tasamu cikinnan shikenan tayi bye bye da lafia, kou ruwa tasha seya dawo duniya babuci babusha wani irin laulayine Allah ya jarabceta dashi me mugun azaba, ji takeyi kmr ta cireshi ta huta, bata kara tabbatr dacewar uwa mace nada darajaba seda tasamu wannan cikin, kullum cikin kuka take, ganin hkn yasa Annah taje da knta ta daukota ta dawo da ita gidanta, toufa nanmadin kullum suna hnyar zuwa asibiti kullum hannun KYAUTAR ALLAH na daure da drib domin shine abincinta shine abinshanta don bataci batasha. A haka cikin yakai wata biyar ana tsammanin chanji amma ina kullum se cigabama whlar keyi Annah dukta sare dabadan tasarai da cikinnanba data haqura a zubar kawai domin autar ta KYAUTAR ALLAH ta huta, ji takeyi daman ana amsa ta amsar mata ta huta, domin wata rana ita da knta Annah tasa KYAUTAR ALLAH takeyi a gaba tayita kuka, gabaki daya rayuwarsu tass takoma a asibiti, KYAUTAR ALLAH dukta lalace ta kode ta canza kamanni setayi wani irin fari, kuma ita ba fara bace chocolate colour ce,irin kalarnan me shekin tsiya baka ganin komi a jikinta se karan hanci da dara daran idanuwanta, dukta koma kashi.

A haka wata rna Raslan yazo hutu yaje ya ganta, yna ganinta ya fasheda kuka, dukse yaji murnarsa ta koma ciki, yazo ya rungumeta yna kuka Annah Kam ta zabga uban tagumi.

KYAUTAR ALLAH tayi murmurshi ta shafa kan Mohammed Raslan din cikin sanyin muryarta tace, "My son...kaga yadda kanwarka ke wahalar dani kou..."

Wani irin hawaye me zafi yashiga bin kuncin Raslan ya shafa cikinta daya dan tasa, se kuma yaji sanyi a rnsa, yace" am sowie sweet mother a gaskia kanwarnan tawa bata kyautaminba...kiyi hkri pls mother zaki samu sauki very soon..."

Smiling kawai KYAUTAR ALLAH tayi ta zubawa Raslan ido tana masa wani irin kallo, shima dago kai yayi yna kallonta.

Rnr daze koma ingland haka ya dawo asibitin domin yayi mata sallamah domin yna tunanin inya tafi baze dawoba har zuwa lokacin dazata haihu. Kwance yasameta,tna sanye da riga doguwa maroon domin daman duk a kala tafison maroon kowa yasani a family,. Lokacin Annah na toilet tana wanka.

Ido KYAUTAR ALLAH ta zuba masa, kna tasakar masa murmurshi naso da kaunah, matsowa yayi yaja kujera ya zauna daf da gadonta, ya dora hannu a cikinta, haka kawai yakejin wani irin matsifaffen so da kaunarh yna ratsa bargon jikinsa da jijiyoyinsa yayinda zuciyarsa ke amsar sakon kaunar cikin dake jikinnata, ji yakeyi duk duniya be tabason wani halittaba kmr yadda yakeson cikin dake jikinnata. "Allah yasa ki sauka lafia mother in dawo in ga kanwata..." Ya krshe mgnr da murmurshi.

Itama murmurshi tyi ta damke hannunsa cikinnata, tace "Hmmm son inajin wani abu a game da rayuwata..."

Dam yaji gabanshi ya fadi, yynda jikinsa yayi sanyi, yace "kmrya mother.." Ya fara a firgice.

Murmurshi tasakar masa na kwantrda hnkli tace. "Dan Allah zan baka amana zaka amsa..."

Cikin hanzari yace "ki bani amana kota menene wallahi nayi alqawarin zan riqe miki kouda hkn ze zama silar rayuwatane..."

"Na baka amanar abinda zan haifa walau mace kou namiji..."

Be dauki komi a rnsaba yy murmurshi yace"na dauka..."

Dam ta kara rike hannunta cikin nasa, ta maimaita masa amanar har sau uku yace ya amsa, kna sukayi sallamah ya tafi yna waiwayenta,hk kawai yakejin jijiyoyinsa duksun sage.

Cikin *KYAUTAR ALLAH* yacika watannin haihuwarsa Seda tajera sati biyu tana labour se haihuwa tazo gadan gadan se kuma tayi shiru dif, hankalin iyalan safana dukya tashi. Ana shirin shiga dakin tiyata da ita allah yasa ta sauka ta sambalo diyarta katuwa wadda taci ta koshi bul bul da ita kamarta sak kmr uwarta harma tafi uwar tata kyau, dukkanin jikinta gashine, gashi dukya baibaye fuskarta yayindaya kwanta luf a fatar jikin jaririyar tinda nake ban taba ganin jaririya me gashiba kamar yarinyar domin tsaf za a iya kitsa sumar dake kanta, ga kyau, ga farin jini dashiga zuciya.

Toufa ga murna ga bakin ciki. Yayinda iyalan safana suka samu labarin haihuwar diya macen murna fal cikinsu annah kam baki har kunne, hatta raslan da bayanan ana haihuwar aka sanar dashi lokacin yna masallaci yanata ibada a...


Read / Download KYAUTAR ALLAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On KYAUTAR ALLAH
avatar
maryam-8-8-3

7 months ago

Reply

Aslm

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to maryam-8-8-3

Wslm

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album