Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»ΏAMINIYA TA CE
Na Maryam ALhasan Dan iya mrs Nura Kuriga
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf

[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’
(Mrs nura kuriga)😘🌹

Dedicated this page to fatima zarahπŸ’ƒπŸ»
1⃣to5⃣

Da sunan Allah mai rahma mai jin qai, da ya sake bani dama na sake rubuta wani sabon littafi, Ina rokan Allah daya bani ikon kammalawa dan alfarman annabi Muhammad (s a w)

"Zeena ce zaune a class tayi uban tagumi, ta rasa maike mata dadi, mlmn maths nata musu bayani amma bata ma San yana yiba, kaman daka sama taji ana kiranta da sauri ta d'ago kai, ta saki murmushi da kara, suka rungume juna ita da Mysha, Zeena tace haba friend why are you late today,I though you are not coming today, Mysha tayi murmushi tace sorry Zeena na raka daddy airport ne daka nan driver ya Kawo ni, mlmn maths ne Ya katse su tare da fadin Zeena nd Mysha keep quick please, kasan cewan makarantan kudi ne, ba'a takura ma yaran sannan teachers din kaman tsoran student din suke, domin skul din sai dan wane da wane, kowa na tsoran ya bata ma student rai, kar allura ta janyo garma, Zeena tace sorry sir, yaji gaba da gudanar dasu, har ya fita, wani ya shigo, har aka fita break, Zeena suka je, yin break suna tafiya suna fira har suka karasa restaurant din skul din, ga snacks nan kala2 sai wanda kaga daman ci, Zeena ta dauko musu ice cream Mysha kuma ta dauko, cookies suka nufi kan wani table suka ajiye kayan sannan suka zauna, suna ci suna fira, Mysha tace Zeena kin San wani Abu kuwa? Zeena tace a'a sai kin fada, Mysha taci gaba da cewa daddy dazu muna hanya zan raka shi airport yake cewa wai ina Gama secondary skul zai min aure, Zeena ta zaro ido tace what? Sai kace a zamanin da, may be he is joking, mysha tace no Zeena he is not joking, Ya dade yana yin wannan maganan, kuma daddy inya fada Abu toh he is serious, Zeena tayi shuru tare da tausayin kawar tata, can tace toh ke Mysha bakya kula kowa, yanzu wa zaki aura, Mysha tace nima abunda nake tunani kenan, yasa koda yaushe nake jin wani iri idan na tuna bani da saurayi wanda nake so, Zeena tace toh ke yanzu mai zaki fada ma daddy dinki inya tambayeki akan wanda zaki aura, Mysha tace nima ban San amsa din ba, ke gwara ke ko yanzu akace ki fito dashi zaki Kawo shi, duk da ban taba ganinshi ba, har yanzu, Zeena tayi murmushi taji an Kawo zan cen prince dinta, Mysha tace wannan murmushin fah, a dai2 lokacin wani yaro mai suna afraz yazo kusa dasu ya kafa ma Zeena ido kaman tsohon maye yace sannunku yan mata, Mysha ce ta amsa, yace ya naji kunyi shuru, yaci gaba da fadin Zeena wai mai yasa koda yaushe indai kika ganni saiki canza fuska, ki duba duk skul din nan ko wace yarinya so take yau ace ina kulata, amma ke na rasa dalili da yasa bakya so inzo inda kike, Ya kalli Mysha yace please Mysha am I not handsome, Mysha tace you are, infact ma babu macen da zata ganka bata kuma kallonka ba, yayi murmushin jin dadi yace thank, sannan ya kalli Zeena wanda ranta ya Gama baci da Mysha yanda take wasa shi, ta mike da nufin ta wuce, ganin haka yasha gabanta, Ya tare ta, tare da fadin Zeena you better stop this nonsense, how dare you ina magana kina wani tashi zaki wuce, duk wanda suke wajan hankalinsu ya dawo garesu, ta kalleshi ido cikin ido tace you have to know 1 thing I really hate you, I hate everything about you, infact ma bana son ganinka, tsayawa yayi yana kallonta da mamaki, dama zaiga irin wannan ranan har mace ta tsaya tana gaya mishi magana duk yanda yake da kyau ga kudi ga aji, yan mata suke rubi binshi, amma yau y'a mace take wulakanta shi, a gaban mutane, ihun da akeyi a wajan yasa ya dawo daka tunanin daya fada, a dai2 lokacin Zeena ta wuce Mysha ta rufa mata baya, yayin da afraz yaji kafanshi yayi mishi nauyi wani irin kunya ya rufe shi, amma haka ya fita, kai tsaye wajan motanshi yayi yashiga ya tada ta, Ya fita daka skul din,Sheraton hotel ya nufa ya kama d'aki, Ya kwanta idonshi yayi ja babu abunda yake tunani sai abunda Zeena ta mishi, Ya kasa komai Ya tashi dakyar yaje motanshi ya dauko kwalban codein ya kwankwade, sannan ya samu bacci ya dauke shi, a lokacin da Zeena da Mysha suka nufi class, Mysha tace Zeena kin San mai kikayi kuwa? Zeena cikin tsiwa tace mai nayi, tell me, Mysha tace Kin San afraz kuwa kin San waye shi kuwa, Zeena tace ban sani ba ban kuma fatan in sani, plz indai kin San maganan shi zaki min, plz leave me alone, jin haka Mysha tayi shuru, amma a cikin xuciyanta tana tsoran abunda afraz zai mata domin hatsabibi ne, gashi ta wulakanta shi gaban mutane, skul din duk an baza labarin, a lokacin da aka tashi Mysha tabi Zeena dan ta ajiye ta a gida, yau bada matan ta tazo ba, kasancewan ta raka daddy dinta airport, dukansu babu mai magana, can Zeena tace Mysha mai yasa kikayi shuru baki cewa komai, Mysha tayi Dan murmushin yake tace mai zance Zeena wlh ina tsoran afraz, ban San mai zaiyi ba, Zeena tayi dan murmushi tace plz Mysha kinga ni harna manta shidin banza wlh bai isa yamin komai ba, nafi karfinshi, ita dai Mysha jinta kawai take, domin afraz bama a skul dinsu ba, kaf garin Abuja dakyar ne kaji wajan da ba'a sanshi ba, baya ji gashi idan yana son abu, ko miye sai yasan yanda ya mallake shi, kota halin 'ka' ka wannan kenan da haka har suka karasa gidansu Mysha ta ajiye ta, ta wuce gida,

Wacece Zeena?

Zeenat abubakar yan asalin garin katsina ne, su uku iyayensu suka mallaka, akwai yayanta adeel wanda yake karatu a kasar Japan sai ita dake aji hudu a famaks sai kanwarta mai suna aysha, suna kiranta da abda, sun taso cikin gata duk da irin gatan da suke ciki suna karatun islamiya kuma sun San addini dai2 gwargwado, mahaifinsu senator ne sau biyar yana ci saboda mutum ne mai rikon Amana kuma dadtijo ne, duk irin kudin da Allah ya mishi bai bar yayanshi sun lallace ba, yana tsaye akan iyalinshi, mutum ne mai son yaga yara sunyi ilimi sai yasa Zeena bata tunanin aure duk da, tana da saurayi wanda yake matukar sonta itama tana sonshi amma baya kasan nan yana China yana kula ma mahaifinshi da wasu aiyuka wajan shekara biyu, kullum suna makale a waya kaf gidansu babu wanda bai San zaheer ba, Zeena mutane da yawa suna mata kallon miskilanci don bata cika son yima mutane magana ba, in kaga ta kula ka toh babban dalili ne, sabanin kanwarta Mysha mai son magana, har wasu na mamakin kaman can nasu, sun hadu da Mysha a skul suka kulla kawance har suka hada iyayensu kawance.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’
(Mrs nura kuriga)😘🌹

Dedicated this page to zee babyπŸ’ƒπŸ»
6⃣toπŸ”Ÿ

"sai wajan shabiyu da wani abu afraz ya farka daka baccin daya dauke shi, Ya tashi tare da mika, komai daya faru duk ya manta, amma ganinshi a hotel yasa ya fara tuno abunda ya faru, lokaci daya yayi tsaki tare da fadin, Zeena you will regret it, toilet ya fada yayi wanka, Ya fito ya shirya ya nufi gida, kai tsaye dakin shi ya nufa, Ya fada kan gado yayi ruf da ciki, yana ta sake2 a ranshi, da haka bacci ya kuma dauke shi,

Zeena ce zaune akan dinning suna breakfast ita da abda, tana yi tana kallon agogo, har mahaifiyarsu wanda suke kira da ummi ta karaso, tace Zeena wannan saurin fah, tace ummi banso inyi late ne, muna da test yau ban samu nayi karatu ba jiya, so inna shiga skul da wuri zan Dan karanta wani abu, ummi tace yanzu na rasa dalilin da yasa bakya daukan karatunki da mahimmanci, kwata2 kinsa wasa inda dane aida kin San abunda kika taka, wai maike damunki ne Zeena? Tayi shuru ganin ummi din ta kafeta da ido yasa tace ummi nima kaina ban sani ba, ummi ta kuma kafeta da ido tana son ta fahimci wani abu daka yar tata, amma ganin babu abunda zata fahimta yasa ta canza maganan da fadin yau in kin dawo daka skul zaki rakani wani waje, ta amsa da toh ta Mike, abda tace ummi nima dani zaki koh? Tayi Dan murmushi tace yes my dear tasa dariya a dai2 lokacin skul boss din su abda yayi horn ta fita da sauri ta wuce.

Mysha da Zeena suna zaune a study room suna ta karatu gefe kuma wasu student ne suma suke ta faman karatun, jin kaman tsayuwan mutum a kanta yasa ta d'aga kai, hada idon da sukayi saida gabanta ya fadi, amma ga mamakinta sai taga yana mata murmushi, ta tashi zata bar wajan, yace haba Zeena mai yayi zafi haka, tace afraz please ka fita daka harka na, bana son kana shiga cikin harkoki na, Ya kafeta da ido yace Zeena dan na miki magana nayi laifi ne? Tayi banza dashi ganin haka yasa ya kwace littafin dake hannunta, ta waigo cike da masifa amma ganin ya tamke fuska gashi sun hada ido, yasa tace plz kaban book dina, Ina karatu, kaman bazai bata ba, komai Ya tuna kuma oho, Ya mika mata littafin, tana amsa tabar wajan, Mysha ta tashi itama, amma jin ya kira sunanta yasa ta tsaya, yace ina son magana dake, tace ina jinka, yace wai mai zanma Zeena ta soni, ni inma samu ta dinga kulani, Mysha tayi shuru can tace afraz mai yasa baza ka barta ba tunda bata sonka, akwai wanda take so, tana fadin haka tabar wajan, Ya bita da kallo tare da wani murmushi wanda shi kanshi yasan dalilin yinshi.

Ummi ce cikin wani tsadaddan leshi mai kalan milk colour flower din jikin leshin kuma purple, yayi mata bala'in kyau, ta nufi dakin Zeena taga itama ta shirya cikin wani material red nd golden, dinki doguwan riga, yayi mata kyau sosai, ummi tace muje Dan Allah kin cika bata lokaci, Zeena tayi murmushi tace na gama ai, ta dauko wani karamin gyale ta yafa, suka fita, cikin wata mota suka shiga mai Kiran Prado, driver yaja su, Zeena tace ummi wai ina zamu haka ne, ummi tayi murmushi tace Mrs hakeem ce ta gaiyace ni dinner gidanta, tace owk, tun daka nan ta kama bakinta tayi shiru, Mrs hakeem wata kawar ummi ce mijinta minister ne na agricultural, sun karasa gidan, sunga motoci da yawa na mutane a gidan daka gani gidan cike yake da mutane, sun shiga falon makil da jama'a Ana ta ciye2, Mrs hakeem na ganin ummi tazo da sauri ta rungumeta sannan suka zauna, Zeena ta gaida ta, ta amsa cike da fara'a, ummi tace wai miye na hada wannan taron? Mrs hakeem tayi dariya tace yau 35yrs da auranmu, ummi tace wow har kun kai haka gskiya lokaci na gudu, anci ansha kowa ya watse daka gidan.

Wayan Zeena keta faman ringing, tayi dan gajeran tsaki ta dauka, ganin sunan mai Kiran yasa tayi sauri ta dauka, tare da fadin hello, ta dayan bangaran ya amsa da gimbiya ta, Ina kika shiga inata kira? Tace sorry dear bacci nake yi, karan Wayan nema ya tashe ni, yace kina bacci kin manta dani, tayi dan murmushi tace ni na isa, yace gest watch, tayi shuru can dai tace fada min, yayi dariya yace ina naija, dazu na sauka, tace what a surprise, amma baka kyauta min ba, shine baka gaya min ba, yayi dariya yace amin afuwa, cikin shagwaba tace anyi ma, yace gobe ina nan tafe, tace sai Kazo nayi missing dinka sosai, yayi murmushin jin dadi yana mamakin jin kalaman nan daka bakin Zeena, wanda ya tabbata baza ta iya gaya mishi tayi missing dinshi a gabanshi ba.

Washe gari Zeena anata shirye2 na taran adeel, Ana ta girke2 kala2 dasu drinks kala daban2, duk wanda yaganta yasan tana cikin farin ciki, bayan ta kammala komai taje tayi wanka ta shirya cikin wani leshi mai ruwan Zuma, da zanan baki a kai, yayi mata kyau sosai, tayi kwalliya na kece raini, duk wanda ya ganta saiya yaba da irin suranta da kyau da Allah yayi mata, ta zauna tana jiran zuwan gwarzon nata don tun dazu ya mata waya yace yana hanya, komai an jera a falon saukan baki, sai kamshin turaran wuta yake.

Wayanta ne yayi kara ta dauka, da sauri ji tayi yace gani a gidansu, tace gani nan, da sauri ta fita, ta iskeshi a mota, yana jiran zuwanta, ta karasa gareshi, Ya kafeta da idon nan nashi, wanda yake rud'a ta, itama kallon nashi ta tsaya yi, Ya kara kyau da wani haske, yace wow my princess kin kara kyau da girma 2yr rabon mu da ganin juna, tayi Dan murmushi tare dajin kunya, tace mai fito mu shiga ciki babu musu yabi bayanta, har falon baki, Ya zauna cikin daya daka kujerun falon, Ya kafe ta da ido, yana mamakin irin girman data kara, da kyau, wani irin sonta yaji yana kara shiganshi, tare da burin yaga ya mallaketa, ta matsa kusa da jerin kayan ciye2 da aka ajiye a falon ta zuba mishi coconut juice, ta mika mishi ya amsa tare da murmushi yasha, sannan ya kalketa yace Zeena har yanzu kina sona kuwa? Ko an kwace min ke, sai taji nauyin maganan daya mata, tayi kasa dakai, a dai2 lokacin Mysha ta shigo falon da sauri tare da fadin ina bakon namu, gabaki daya komai nata ya tsaya ta kasa ko motsi, sai dai a zuciyanta take ta nanata wa, tsarki ya tabbata ga Allah wanda yayi wannan hallita, adeel ne Ya katse mata tunani da fadin Mysha right?mai makon amsa sai tayi murmushi wanda ita kanta bata San tana dashi ba, ta karasa shigowa falon ta zauna, Zeena tace ya akai ka gane ta? Yayi dan murmushi yace nasan itace daka yanayin yanda ta shigo, Zeena ta kalli Mysha wanda ta kafe adeel da ido, tace sai yanzu koh, tace kiyi hakuri Zeena baki mukayi sai yasa banzo da wuri ba, haka suka zauna suna ta fira cikin nishadi, har adeel ya tafi yaba Zeena tsaraba da yawa, itama Mysha ya bata nata.

Mysha ta kasa tsaye ta kasa zaune sai kaiwa da kawowa take a dakinta, tabbas adeel ya hadu kalan namijin da take mafarkin samu kenan, ko wace mace zatayi burin yau ace ta mallake shi, a matsayin miji, wata zuciyan tace mata Mysha mai kikeyi haka, saurayin aminyar ki ce wanda take matukar so, kaman ranta, Ya kamata ki cire wannan tunanin a ranki, dan bai kamace ki ba.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’
(Mrs nura kuriga)😘🌹

Dedicated this page to hafsy (mamani) 😘
1⃣6⃣t2⃣0⃣

Adeel ne zaune cikin gidansu Zeena a falon baki yana jiran zuwanta, duk da baya kallon kofa, kanshin turaranta yaji yasa yasan ta karaso, da murmushi ya dago ya kalleta, amma ga mamakin shi, ba ita ya gani ba, Mysha ce, cikin wani Riga da wando yan kanti, tace barka da hutawa, Ya amsa da yauwa ya kike, cikin lallausar murya ta amsa da lafiya, kaifa? A dai2 lokacin Zeena ta shigo, ganin Mysha a wajan yasa ta tsaya tare da mata tambayan yaushe kika shigo? Tace yanzu ban dade ba, naga falon nan a bude na dauka kina ciki saina nufo nan, ashe baki riga kin iso ba, suka samu waje suka zauna, adeel ya kafe Zeena da ido, Mysha tana lura dashi duk sai taji wani iri, tunda take wannan ne rana na farko data fara kishi da Zeena sannan kuma rana na farko data yarda zata iya komai dan ta samu adeel, sai a yanzu ta kare mishi kallo, adeel namiji ne wanda ya hadu, Shiba dogo ba kuma ba zaka kirashi da gajere ba, sannan idonshi ma kanshi abun burgewa ne, dan inka kalla idonshi kaman mai jin bacci, (sexy eye) gashi yana da faffadan kirji, gashi yana da haske kaman balarabe, Zeena ce ta katse ta tare da fadin Mysha ya kikayi shuru, tayi firgit tace ina jinki, Zeena ta kafeta da ido tace wai mai kike tunani haka? Tace babu komai, adeel yace Zeena ya maganan mu? Taji gabanta ya fadi, tayi shuru, ganin haka yace Zeena plz kimin magana, tace adeel na fada Maka tun farko kudiri na akan karatu, bani da burin inyi aure yanzu, Ya kalli Mysha yace plz kisa baki, Mysha harga Allah taji dadin jin amsan Zeena, amma a fili sai tace haba Zeena aure ai shine darajan y'a mace, kuma babu abunda yafi ma mace mutunci face yau ace tana d'akin mijinta, kuma koda karatun zakiyi idan kina da aure za'afi mutunta ki, ada ina tunanin kaman mahaifina baimin adalci ba, nason inyi aure daka na kammala secondary school, amma da nayi nazari akan abun sai naga wannan shine babban gata daya nunamin, tunda Mysha ta fara magana adeel ya kafeta da ido tare da mamakin jin irin wannan kalaman a bakinta, yaji ta burgeshi, Zeena tace Mysha hakane, amma kawai bana ra'ayi ne, jin haka adeel ya tashi tare da fadin owk babu damuwa indai kin canza ra'ayi zaki iya nema na, yabar gidan ta bishi da kallo.

Mysha nata jin dadin abunda ya faru yau, tabbas tasan halin Zeena indai tace abu da wuya kuma ta canza, lokaci daya wani haushin Zeena taji yana shiganta, tare da fadin Zeena ba kyau kika fini ba, sai dai ki nunamin hasken fata, hasalima da kadan kika fini haske, kowa yace ke yake so jiba afraz yanda ya mutu a kanta, yaro hadadde sai dai matsala daya bashi da hali, ga adeel shima kowa yace ke, why not me, dole sai na sami adeel at any cost.

Wasa2 yau satin adeel biyu baya zuwa wajan Zeena inta kirashi kuma sai yaga dama yake dauka, koda ya dauka dinma tambaya daya yake mata kin amince, tace adeel kamin hakuri, baya bari ta karasa saiya kashe Wayan, tayi bala'in shiga damuwa tabbas tana son adeel amma bazata iya yarda da kudirishi ba, tana burin tayi karatu mai zurfi kafin aure, domin tana ganin in tayi aure da wuya ta samu cikan burinta.

Yau Monday Zeena da abda suna dauke da kayan skul, abda ta kalli Zeena tace yau ke zaki Kaini skul plz, Zeena ta mata harara tace tunda nice driver koh, gwara ma ki nemi mai kaiki, jin muryan daddy dinsu sukayi yana fadin zo mamana ni dakai na zan kaiki, tayi dariya cike da jin dadi ta nufi mahaifin nata, tana yima Zeena gwalo, Zeena tace ina wasa dake koh, daddy yayi dariya yace haba Zeena mai mamana tayi miki da safen nan kike mata haka, ta dan turo baki irin na shagwaba tace daddy kana taking side dinta koh, babu komai, Ya karasa kusa da ita yace no Zeena dukan ku ina tare daku, jin haka yasa tama abda gwalo itama, ganin haka yasa abda tasa kuka Zeena ta fita da sauri tana dariya, daddy ya kalli abda yace lah kuka zaki sa tace ke raguwa ce, jin haka yasa tayi shuru, yace muje in kaiki, sai in wuce office,.

Alokacin da Zeena takai skul a tare sukayi parking ita da afraz, yayi sauri ya fito ya bude motarta yace fito mu shiga tare mana, ta sakar mai harara, yayi dariya yace in kika bata rai kinfi kyau, tayi tsaki tace wlh afraz kana da naci, wai mai zan Maka ka daina kulani, yace babu, dan komai zaki min bazan daina kulaki ba, tunda ina sonki kuma ke zan aura, ta saki dariya tare da tafa hannu, tace aiko maza sun kare wlh ban auranka, balle ma kai ba namiji bane, Ina maka kallon d'an daudu ne, tana fadin haka ta wuce, ranshi yayi mugun baci yace saina nuna miki ni a cikin mazan ma daban nake, Ya cije lebe u will regret it wallahi Zeena kota wani irin hali saina sameki, shima ya shiga cikin skul din.

Maryam obam ✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my kawata ta rai da rai nana fidaddusyπŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
2⃣6⃣to3⃣0⃣

"adeel ya aika gidansu Mysha an tsayar da komai na aure amma iyayenta sunce saita kammala secondary skul za'ayi bikin, mahaifin adeel ya yarda da hakan tunda ance bai kai shekara daya ba, zata kammala, kuma yaji dadin ganin gidan da d'an nashi ya nemo aure

Please Login or Register in order to submit comment