Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata nasiha sosai akan ta zauna lafiya ita da mijinta da abokiyar zamanta, aka fito da ita aka kama hanya, har aka karasa gidan tana kuka, abda dake gefe tace Zeena fito kiga gidan da aka Kawo ki, ya hadu sosai, tama abda harara sai kace tana ganinta, a cikin masu Kawo ta harda mum, tace ta fito da bismillah, hakan ko tayi suka shiga ciki, babu kowa da yake sun san dakin Zeena din suka bude suka shiga, tsarin dakinta yayi kyau sosai, itama da falo da 3bedroom ne a ciki, sun dan zauna kadan kafin suka wuce tana ta kuka, bayan sun tafi ta kifa kanta a giwa tana ta kuka,

Adeel wajan karfe goma ya shigo gidan, kai tsaye dakin Mysha ya nufa, yaga tana ta rafsa kuka, duk sai yaji ta bashi tausayi, ya zauna yana ta rarrashinta, yace taci abinci, ta girgiza mai kai alaman a'a, ya dauko daya daka ledan daya shigo dashi ya bude kaza ne a ciki, ya bata yace gashi taci, ta amsa, ya tashi tare da fadin saida safe, nan ta kuma sakin kukan haka ya fita ya barta, cikin kunci da bakin ciki, yanzu adeel zai kwana da Zeena a matsayin matarshi, wani bakin kishi taji yana dibanta,.

A lokacin daya shiga d'akin Zeena da sallama, yaga tana ta kuka, ya zauna kusa da ita, yace haba Zeena wannan kukan fa, na tabbata tun dazu kikeyi, ya kamata kiyi shuru kibar wannan kukan, jin bata kulashi ba, kuma bata daina kukan ba, yasa ya d'aga mata kai tayi sauri ta matsa baya, ganin haka yace ga abinci kici karki zauna da yunwa, ya fara bude mata, kaza ne da yogurt, ya mika mata ta amsa, ya fita daka d'akin ganin haka yasa tayi sauri ta rufe kofan ta da key, shima falo ya nufa ya kwanta kan kujera, ya daura hannunshi akan kanshi, babu abunda yake sai tunani, wai yau shida Zeena suna matsayin mata da miji, ranan da suke ta buri, amma ranan tazo Zeena kwata2 bata murna, yanzu Zeena bata sona kenan mijinta take so, wani irin kishi yaji ya rufe shi.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my fans πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
1⃣1⃣0⃣to1⃣1⃣5⃣

Ga kanshi dake ta sara mishi, a falon ya kwanta har bacci ya dauke shi, ita kuma Zeena bayan fitanshi itama kwanciyan tayi abunta, sai wajan asuba ta farka taje toilet tayi alwala tazo tayi sallah, bayan ta idar taji kaman ana mata nocking, taso ta share komai ta tuna kuma ta tashi ta bude kofan, taga adeel ne Ya shigo tare da fadin kinyi sallah, ta d'aga mai kai alaman eh, ya bude daya daka cikin d'akin ya shiga wanda ya ware nashi, bayan ya shiga tayi dan tsaki ta nufi d'akin ta itama,

Mysha tun jiya ta kasa bacci sai aikin kuka, babu abunda take gani sai adeel da Zeena, tana ganinsu a tare a matsayin ma'aurata, tace ni nayi sake ya kamata in dau mataki, tayi dariya tare da fadin Zeena nasan ko ke wacece, nasan yanda zan miki keda kanki zaki bar gidan nan, wannan tunanin da tayi shi yasa bacci ya dauketa

Zeena tunda ta koma bacci sai wajan 10 ta farka, ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin wani doguwar rigan material, duk da batayi makeup ba tayi kyau, ta zauna ta zabga tagumi tace koya twins suke yanzu oho, duk kewarsu ya kamata, ta dauki wayanta ta kira mum, bugu daya ta dauka, Zeena ta gaidata mum ta amsa cikin fara'a, bayan sun gama gaisawa tace ina twins mum tace sun fita da dady yanzu, tace to a gaidasu, mum tasan Zeena kewarsu take domin bata taba tafiya koda na wuni daya bane ba tare dasu ba, tace in sun dawo zata kirata, ta amsa da toh sukayi sallama, a dai2 lokacin adeel ya shigo cikin kananan kaya ya mishi kyau sosai sai kamshi yake tashi, ya kalleta yace an tashi lafiya, ta amsa da lafiya, yace muje muyi breakfast, taji gabanta ya fad'i, don bata san wani irin tarba Mysha zata mata ba, yace let go, tace no bana jin yunwa, ya kafeta da ido ganin irin kallon da yake mata yasa ta daure fuska tare da tashi tasa hijab, yayi dan murmushi yace mai kika ci, ki tashi muje ban San musu, ta mike suka fita tare sun sami Mysha a falo tasa wani top mai hannu daya da 3quater jeans, ta daure fuska kaman bata taba dariya ba, adeel yace Mysha ina breakfast ban gani a dining ba, tace breakfast banyi ba, yace saboda me, tace bashi aka Kawo ni in dinga yiba, ita wanda kaje ka kwana a wajanta ta baka mana, ranshi ya baci sosai amma saiya dake, ya kalli Zeena yace bari in Kawo miki abunda zaki ci, tace no kabarshi kawai, yace akan me kinci wani abu ne, Mysha ta kwashe da dariya tare da fadin yau ina ganin ikon Allah, ganin haka yasa Zeena ta juya tayi dakinta, shima ya bita, bayan sun shiga d'akin ya rasa mai zaice mata, can dai yace kiyi hakuri Zeena bari inje in dawo, ta amsa da toh sannan ya fita, Mysha na falon har yanzu tana ganin shi ta fara bala'i tana fadin an dai zama mijin tace, kana wani binta kana kaudi ko kunya baka ji, yayi banza da ita ya fita, har yaje ya dawo ya sameta a zaune a falon tana kad'a kafa tace Malam nima fa yunwa nake ji, ya mika mata leda daya sannan ya wuce ta bishi da harara, a lokacin daya shiga d'akin Zeena ya ganta a kwance amma idonta biyu, yace ki tashi kici abinci, bata amsa ba amma ta tashi, ya mika mata, ta amsa sannan ya fita, dakinshi ya shiga ya kwanta, ranshi ya baci akan abunda Mysha ta mishi, ina kyaleta ne kawai saboda Zeena, amma duk da hakan zanyi maganin ta, yayi dan tsaki wayanshi dake gefe ya fara kara ya dauka yaga Mysha ce, yayi rejecting Kiran, ta kara kira, da yaga hakan saiya kashe Wayan gaba daya,.

Sai wajan karfe biyu ya fito ya shiga d'akin Zeena, ya ganta tana ta aikin kuka, nan ya zauna yana tambayanta akan mai nene, mai aka mata take kuka ko Mysha ce, ta girgiza mai kai alaman a'a, ya matsa kusa da ita tare da janyota kirjinshi, nan gabanta ya hau bugu, yace kiyi shuru Zeena bana son wannan kukan, ta dan tsagaita da kukan da takeyi, yace ta tashi su shirya suje suyi lunch, tace a'a taci sauran abincin safe, yace ok, ya fara wasa da gashin kanta, wani irin sonta yake shiganshi tare da wani sha'awarta, jin bugun kofa sukayi anayi kaman za'a balla, da sauri ya tashi ya bude kofan yaga Mysha ce tana huci, tace toh Malam saika fito ka nemo min abincin da zanci, yace kina da hankali kuwa Mysha, tace ban sani ba, in banda wulakanci Kazo ka ajiye mutum babu abinci, yace wani kalan abinci ne babu miye babu a gidan Nan, tace ni dafaffe nake so, dan bazan iya girki ba, yace ok ya rufe kofan ya barta a nan waje tana ta bala'i, Zeena tana ta kuka dama abunda take tsoro kenan irin wannan abun, gashi kuma an fara, yace dan Allah Zeena kibar wannan kukan, bata kulashi ba taci gaba da kukan, dakyar ya rarrasheta tayi shuru, tace ya tashi yaje ya siyo mata abincin, yace babu inda zashi tunda akwai abinci a gidan, ganin ta bata rai yasa yace bari yaje, bai sami Mysha a falo ba ya fita,

Yau Zeena zata bar girki, Mysha zata amsa, ya kirasu dukansu falo akan su tsara yanda zasu dinga kwana, ranan Mysha ta sake kaman ba ita ba, itace ma ta yanke tace kwana biyu2 ya kalli Zeena yace kinji hakan yayi, jin haka yasa tace inma bai mata ba ni haka na tsara, yace Mysha ki dawo cikin hankalinki bake nake tambaya ba, jin haka yasa tayi shuru tana hararan Zeena, Zeena tace duk yanda kuka tsara yayi, Mysha ta tabe baki, sannan yace ya maganan abinci ya zakuyi, Mysha tayi caraf tace duk mai girki zata dinga yi, ita dai Zeena bata ce komai ba, sai bugun da zuciyanta yake mata, ita kwata2 bata son wannan zaman jinta take kaman akan wuta take, domin irin kallon da Mysha take mata abun ya isheta, adeel yace shikenan hakan yayi, jin haka Zeena ta tashi tayi ciki, ya tashi da nufin ya bita, Mysha ta shiga gabanshi tace ka manta yau nice dakai, Ina kake kokarin zuwa, yace kaman ya dan yau girkin kine banda iko inga matata, tace hakane, yace ok hakan ko akayi, ya fasa shiga, Zeena ko tana shiga d'aki ta dau wayanta taga misscall din mum da sauri ta kirata, ta dauka suka gaisa sannan take tambayanta komai lafiya tace eh, ta bata afraz yana ta mata surutu wani ta gane wani kuma tayi dariya, mum taba small Zeena itama suna ta surutu tana dariya, tayi kewan yaran ta sosai, sun dauki lokaci suna ta surutu, sannan sukayi sallama.

Bayan Mysha ta gama dinner, ta jera a dining adeel yace taje ta kira Zeena, tace toh, ta nufi d'akin Zeena din ko nocking batayi ba ta bude kofan ta shiga taga bata falo dinta, taje wata kofa ta buga jin kaman ana buga kofa yasa ta fito, taga Mysha ce,ganin kayan dake jikin Zeena din yasa ta daure fuska tare da wani bakin kishi, wani top ne mai gajeren hannu da skin tie tasa ribbon ta kama kanta, ganin kallon da take mata yasa tace lafiya kuwa, tace ke ko kunya bakya ji, kin auri mijin kawarki, tir da halinki, Zeena tayi dariya tace ni ko ke, jin haka Mysha ta kuma tamkewa tace karki fad'amin magana dai, Zeena tace ni banda ma lokacin ki ta bude kofa ta shige, tabar Mysha da bakin ciki, ta fita ta sami adeel akan dining yace ina Zeena din, tace tana d'akin ta, tace ta koshi, yace kaman ya mai taci, tace oho aiba gadinta nake ba, ya tashi ya nufi d'akin Zeena din ya ganta a kwance yace Zeena ki tashi kizo kici abinci, ta amsa da toh, ganin bata tashi ba yace ina jiranki, ta tashi ta dauki hijab, tasa suka fita tare, Mysha tayi tsaki, ta zuba ma adeel abinci ta zuba nata, Zeena itama tasa kadan, bata wani ci da yawa ba, ta ajiye tare da mikewa, adeel yace ina zaki baki gama cin abinci ba, tace na koshi, tayi gaba abunta, Mysha tace ikon Allah yau ina ganin abunda yafi karfina, yayi banza da ita, dan duk abunda take yana tara tane, yau yake so yayi maganin ta.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my fans πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
1⃣1⃣5⃣to1⃣2⃣0⃣

Bayan adeel ya kammala ya tashi daka kan dining din, ya nufi gefen Mysha, itama ganin haka yasa ta bishi, don ta zauna ne taga ko zaije d'akin Zeena, bayan ya shiga ya bude dakin shi ya shiga, toiled ya fad'a yayi wanka ya fito yaga Mysha daka ita sai night gown, kallo daya ya mata ya kauda kai gefe, bayan ya gama shiri ya kwanta ta gefen gado, ganin bai kulata ba yasa tayi tsaki tare da fad'in ikon Allah, ya tashi fuska a daure yace ta tashi tabar d'akin, tace kaman ya, wlh babu inda zani in tashi in fita kaje d'akin wancan munafukar koh, ranshi ya kuma baci yace bari kiji Mysha duk abunda kikeyi na gaji dashi bazan dauka ba dan haka kije gidanku na gaji, tace toh, ta juya baya tare da fadin Allah ya kaimu gobe zan wuce,

Ranan Mysha kasa bacci tayi domin ba zata iya komawa gida ba, koda lokacin da adeel yake bata wuya bata koma ba, balle yanzu da take ganin ya kara aure, wato ta basu waje suyi abunda suke so, tace no way, lokaci daya tayi dan murmushin takaici, ta tashi da sauri ta fara hawaye tana rokan adeel akan yayi hakuri bazata kara ba, yayi banza da ita don har ya fara bacci ta tashe shi, ganin bai kulata ba, yasa tace duk abunda take mai zata daina sannan zasu zauna lfya ita da Zeena, jin haka yasa yace shikenan, tace mai ta gode ta koma ta kwanta tana goge hawayen tare da dan murmushi.

Washe gari Mysha tun wajan 7 ta shiga kitchen ta had'a breakfast, ta jera akan dining, ta koma d'aki tayi wanka sannan ta tashi adeel, shima ya shirya, bayan sunje kan dining, ta tashi bari inje in kira Zeena hakan yamai dadi, ya amsa da toh, kai tsaye d'akin Zeena din ta nufa ta bude kofan, taje kusa da kofar da taga ta fito jiya tayi nocking Zeena ta bude kofan, Mysha taya mutsa fuska, tare da fadin ki fito muyi breakfast, kina wani kasa2 dakai kaman wata munafuka, Zeena tayi shuru, Mysha tayi tsaki ta fita, Zeena ta koma ta dauki dankwalin atamfan ta, ta daura, sannan ta fito, bayan Zeena ta zauna ta gaida adeel ya amsa tare da fadin kin tashi lfya, ta amsa da eh, Mysha ta zuba ma adeel breakfast sannan tasa ma Zeena tace ga naki in yayi kadan sai in kara miki, Zeena da mamaki take kallon ta,tace yayi haka, suna ci Mysha tana dan Jan Zeena da fira, wani Zeena ta amsa wani kuma tayi murmushi, adeel shiko yau yana cikin nishad'i, bayan sun kammala Zeena tayi d'akin ta, adeel da Mysha suka zauna suna dan taba fira jefi2 yin firan kawai yake amma kwata2 hankalin shi da tunanin shi, yana wajan Zeena yana son zuwa wajanta, ya tashi yace bari inje mu gaisa da Zeena ta amsa da toh, yaji mamaki dan baiyi zaton haka daka gareta ba, amma saita amsa, yace ya kamata ma ki dauko ahmad, tace toh anjima zan dauko shi, ya nufi d'akin Zeena, bayan ya shiga ya ganta tana waya da mum, bayan sun gama ta kalleshi tace nagode mum tace ka kaima su twins kaya, yace dan na kai musu kaya shine kike min godiya dan nama yarana hidima, taji dadin abunda yace, tayi dan murmushi, ya kafeta da ido wani irin shaukin sonta ke shiganshi, ganin yanda yake kallon ta yasa taji wani iri, yayi murmushi yace mai kike bukata, ta amsa da babu komai yace ok, ya fita daka d'akin, har lokacin Mysha tana falo, tana ganin shi tace dama kai nake jira ka fito in wuce, yace ok ki gaida mum nd dad ta amsa da toh sannan ta wuce tare da fadin yace ma Zeena ta fita, d'akin Zeena ya koma a lokacin tana toilet, bai dade da shigaba yaga ta fito da alama wanka ta karayi dan towel ne a daure a jikinta, ya kafeta da ido, ta dauko hijab dinta da nufin tasa, yazo yayi hugging dinta ta baya, tare da amsan hijab din, ya fara wasa da gashin kanta wanda ta jika da ruwa, yayi dan murmushi tare da fadin very soon zaki bani cute baby kaman ki, jin haka yasa ta matsa da sauri tare da daure fuska, ya kuma janyota, ta fad'o jikinshi, ya fara kokarin cire mata towel din jikinta gaba daya ta sandare ta kasa ko motsi haka ya dinga wasa da ita, yasa jikinta yayi sanyi, ta saki kuka, ya fara magana kaman yana rad'a yace Zeena mai nene, tace ka kyakeni bana so, jin haka yasa ya sake ta, tare da barin d'akin, tana ganin ya fita ta tashi dakyar tasa ma d'akin ta, key, ta dawo ta kwanta,

Mysha tunda ta fita ta kasa sakewa dan gani take kaman Zeena da adeel suna tare yanzu tayi dan tsaki, ta dauki ahmad tace ma mamanta zasu wuce, tace tun yanzu tace mum zanyi dinner a gida inna koma, Ina so ki samo min mai aiki wacce ta iya girki nan da kwana2 na gaji da wannan girkin, maman tayi dariya tace toh shikenan zan sa a samo miki, ta amsa da to suka wuce, a lokacin da suka shiga gida taga babu motar adeel, tayi ajiyan zuciya cikin jin dadi, tace yauwa basa tare, lokaci daya kuma ta gimtse kodai tare ma suka fita, da sauri ta dauki ahmad sukai ciki, d'akin Zeena din tayi, tana ta nocking kaman zata balla kofan, Zeena ta fito tace lafiya kuwa, Mysha ta mata kallon sama da kasa, tace lafiyan ya Kawo haka, Zeena tayi dan murmushi tace toh Allah ya karo lafiyan, nan Mysha ta kumbura tare da fadin mai kike nufi kina nufin banda lafiya, ko mai, Zeena tace ni bance haka ba, keda kike da lafiya dan nace Allah ya karo ai ba laifi bane, Mysha ta matso kusa da Zeena kaman zata daketa, nan Zeena tayi sauri tayi baya tace badai fad'a zaki dani ba, rufamin asiri, kiyi hakuri, Mysha tace aikin banza ai wlh idan kika fad'a abun da yafi karfin bakin ki saina zane ki a gidan Nan, suna cikin haka saiga adeel Mysha tana ganinshi tace Zeena muje kitchen ki tayani muyi dinner yau a gajiye nake wlh, Zeena da mamaki take kallon ta, ta kasa furta komai, ganin haka yasa Mysha ta kuma cewa kiyi hakuri inna takura miki ki barshi zanyi, adeel yace zama ta taya ki ko Zeena, sai a sannan tasan adeel yana wajan, tace lallai Mysha makira ce, amma a fili sai tace kanta na ciwo, Mysha tace Allah sarki ban sani ba, Allah ya sawake bari inje inyi in barki ki huta, adeel yanda yaga Zeena tayi mata baiji dadi ba, amma saiya basar ya mata uziri, Zeena ta koma d'aki, shi kuma ya dauki ahmad yana mai wasa, ya shiga d'akin Zeena din yaga tana danna waya, yace kinsha magani ta amsa da eh fuska a daure ganin haka yasa ya fita, ita kuma tayi dan tsaki ta kwanta abunta,

Yau Zeena ita zata karbi girki dan haka, tun wajan 4 tayi kitchen taga duk yayi 'kura ta zauna ta goge ko ina, ta maida komai wajan shi, sannan ta daura girki, tayi tuwo miyan danyan kubewa, da yaji nama da kayan ciki, tayi Mango juice ta jera akan dining sannan ta fad'a toilet tayi wanka tasa wata doguwar riga na yan kanti, ta kama gashinta da ribbon, sannan tasa wani karamin gyale ta daure kanta dashi tayi kyau sosai, ta fito falo din taga Mysha da adeel, Mysha tace yanzu nake kokarin tashi in kiraki, yunwa nake ji, Zeena tace aida kinci basai kin jirani ba, adeel tunda ta fito ya kafeta da ido, ji yake kaman yaje yayi hugging dinta, amma babu dama, tazo ta zuba musu, ita kuma ta koma kan kujera tana kallo, adeel yace kizo kici abinci mana, tace no na koshi, yace mai kikaci tace babu komai, ya tashi tare da plate din abincin yazo inda take, ya zauna ya fara bata tana ci,tana kallon Mysha wanda ta kumbura kaman zata fashe, dama tayi hakan ne dan ta nuna mata itama ta iya makircin,shi kuma adeel din kwata2 ya manta da Mysha tana wajan.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my fans πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
1⃣2⃣0⃣to1⃣2⃣5⃣

Mysha ta tashi da sauri tabar wajan, ganin haka Zeena yasa itama tace ma adeel ta koshi, yace ki kara ci kad'an, tace no, ka barshi jin ihun Mysha sukayi, da sauri adeel yayi d'akin, yana fadin lafiya Mysha mai nene, tace ciki na, yace mai ya sameki tace murd'a min yake, yace tashi muje asibiti, tace bazan iya ba ka taimaka min, yace ina zuwa yana fita tayi dariya tare da fadin yau kwanan kine Zeena amma ni zan amshe, Jim kadan sai gashi da Zeena din sun shigo, ta kuma langwabe wa, adeel yace Zeena ta dauki ahmad ta kaishi d'akinta ta amsa da toh, ta daukeshi ta kaishi, shi kuma adeel ya dauki Mysha yayi mota da ita, kai tsaye asibiti suka nufa, an duba ta, aka bata magani suka dawo gida wajan karfe goma da wani abu, a lokacin Zeena harta fara bacci, taji kaman ana taba ta, da sauri ta tashi taga adeel tace har kun dawo ya jikin nata, ya amsa da sauki sannan ya dauki ahmad, ya fita, tunda ya fita bai dawo ba, daka yazo zai fita Mysha taita nishi, ganin haka saiya dawo ya zauna da ita, ita kuma Zeena baccin ta tayi abunta, sai wajan asuba tayi bacci sannan ya fita masallaci, yayi sallah, bayan ya dawo ya duba ta yaga tana ta bacci, kai tsaye d'akin Zeena ya nufa, yaga tana sallah,ya zauna akan gado, harta idar bata tashi ba taci gaba da zama akan dadduman, ganin bata da niyan tashi yasa yazo inda take ya zauna a 'kasa ya kamo hannunta da take wasa dashi, yace Zeena kiyi hakuri kin jini shuru sai yanzu ta samu tayi bacci, tace babu komai ta tashi ta haye gado, ganin haka shima ya haye gadon ya janyota jikin shi,ya manneta kaman zata gudu, da haka bacci ya dauke shi, ganin yayi bacci yasa ta zame jikinta cikin nashi ta nufi kitchen don ta had'a breakfast, ta had'a farfesun fresh fish, tayi sandwich da tea ta jera kan dinning ta koma dakinta taga har yanzu yana bacci, ta fad'a toilet tayi wanka ta shirya cikin wasu kananan kaya Riga da wando tayi kyau sosai duk da batayi makeup ba,ta fashe jikinta da turare sai kamshi ke tashi, ta koma falo dinta ta zauna tana kallo, sai wajan 10 ya farka yaga bata kusa ya shiga toilet shima ya fito ya shirya, ya ganta a falo tana kallo wani sonta yake shigar shi, musamman shigan da tayi wanda ya rud'a shi, tabbas Zeena ta hadu, jin kaman ana kallon ta yasa ta waigo, suka had'a ido ya sakar mata murmushi tayi sauri tayi kasa dakai, ya matso kusa da ita tare da janyota jikin shi, suna shakan numfashin juna, ta kasa ko motsi, yasa hannunshi ya d'ago mata kai, ya kafeta da ido itama ta kasa, 'kasa da kanta jin bakinshi tayi cikin nata sun dauki lokaci cikin haka kafin ya sake ta, ta fara mayar da numfashi ta kasa ko tashi dan gaba daya ya kashe mata jiki, jin hannunshi tayi cikin kirjinta tare da kara rungumota, ganin dagaske yake yasa tace breakfast is ready, yayi dan murmushi ya matsa kusa da kunne ta, yace kece abinci na, ta dan tureshi ya kuma yin dariya ganin yanda take daure fuska, yace Zeena ina sonki, nan taji gabanta yana bugu da sauri ta tashi tayi bedroom dinta nan ta saki kuka, jin ta dade bata fito ba, yasa ya bita yaga tana kuka yace lafiya kuwa Zeena tayi shiru babu amsa, ya matsa kusa da ita tare da fad'in ban San kukan ki Zeena plz, nan ta kuma jin wani hawayen sau da yawa adeel yana mata abubuwa shigen na afraz, dakyar ya samu tayi shuru, suka fita falo don yin breakfast,baiga Mysha ba yasan tana bacci har yanzu dan haka baiko leka d'akinta ba suka fara yin breakfast.

Mysha itama tuntuni ta farka taga adeel baya wajan tayi dan tsaki yanzu saida yaje d'akin waccen mayyar, wani bakin ciki taji yana damun ta, yanzu duk abunda na shirya a banza tayi tsaki ta tashi, ta fito falo taga Zeena da adeel suna cin abinci suna fira cikin Jin dadi, nan ranta ya kuma baci ji take kaman ta shage Zeena dan takaici, adeel yace Mysha har kin tashi ta amsa da eh, nan Zeena tace ya jikin, tace da sauki kiyi hakuri naso in taso in taya ki aiki, bacci yaci karfina, adeel yace keda baki da lafiya Mysha ina ke ina tayata aiki, Zeena tace lallai Mysha ke daban kike, nan Zeena ta dan fahimci wani

Please Login or Register in order to submit comment