Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan mutunci,bayan an gama komai suka wuce tare da fatan Allah ya kaisu lokacin,

Su Zeena an kammala jarabawa na zuwa ss2 sunyi hutu, yanzu babu skul, sai a yanzu take kewan adeel sosai kasan cewan suna hutu babu skul, kullum sai zaman gida, duk ta rame tayi dan duhu, gashi number din adeel din duk basa zuwa, tayi mugun shiga damuwa, har ummi ta fahimci hakan tayi tambayan duniya akan mai yake damunta, amsan dai kullum daya ce babu komai, ta dai zuba mata ido ta rabu da ita,

Yau an tashi garin Abuja da sanyi sosai yawanci mutane na dauke da rigan sanyi wasu harda hula, Zeena ta fito daka dakinta duk ta rame jikinta sanye take da Riga da wando ta daura suwaita akai, da hula kalan pink, hannunta dauke da key din mota, ta nufi falo ta tarar da ummi, tace ummi barka da Safiya, ganin yar tata kaman tana cikin ni shadi hakan ya mata dadi, tace yauwa Zeena ina zaki? Tace ummi wajan Mysha zani tace toh sai kin dawo, ta amsa da toh ta fita.

Lokacin da Zeena ta karasa gidansu Mysha tayi parking motar ta, ta nufi cikin gidan, ta tarar da mumy din Mysha a falo ta gaidata, ta amsa cikin fara'a har tana dan tsokanan ta, kin mana yaji dai Zeena kwana biyu bakya zuwa, tayi dan murmushi tace Amin hakuri mumy, tace Mysha tana dakinta, ta amsa da toh, ta nufi dakinta a kwance ta sameta cikin blanket, taja mata kafa, ta dan bude ido, Zeena ta sakar mata murmushi, ganin Zeena yasa ta tashi tare da dan yin gajeran tsaki, Zeena tace baki da matsala Mysha, ta dan ya mutsa fuska kaman bata son magana tace toh mai zai hanani bacci ai wannan sai ke, Zeena tace kaman kin sani wlh bana iya bacci wlh adeel kwata2 bana samun shi a waya, Mysha tace kai Zeena dan Allah kema ki rabu dashi nifa bazan dauka wulakanci ba, mutum ya shareki amma ke kullum kina nan cikin tunanin shi, Zeena tace Mysha wlh ba zaki gane ba, son adeel yamin yawa, yana da irin abubuwan da nake so mijin da zan aura ya kasance dashi, Mysha ta tabe baki tace toh yanzu miye abun yi? Zeena tace nazo muje gidansu ne ko Allah zai sa in ganshi, jin haka Mysha tace haba Zeena kin bada mata wlh akan mai zaki gidansu inya wulakantaki fa, tayi shuru, tabbas Mysha tayi gaskiya hala ma wata ya samu ya manta dani, lokaci daya taji wani bakin kishin adeel ya lullubeta, anya zan iya juran ganin adeel da wata mace kuwa, Mysha tace kinyi shuru, Zeena tace toh Mysha mai zance abun ne duk ya zama wani iri, Mysha tace Zeena ya kamata ki cireshi a ranki tun yanzu, kar nan gaba abun ya zaman miki matsala, Zeena tace Mysha kina ganin kaman Abu mai sauki ne in cire adeel a raina, kin San so kuwa Mysha? Bari kiji so ba wasa bane wani abu ne da yake shiga ran Dan Adam ba tare da notice ba, sai dai kaji ka fada wlh Mysha inda inada halin da zan cire son adeel toh zan cire saboda abu daya, a rayuwa ta banso in kira mutum ya kashe min waya, kinga adeel tunda haka ta faru ya daina daukan wayana kwata2, naso in shareshi inyi fushi dashi amma na kasa, Mysha dai kallonta take tana ganin duk sonda Zeena take ma adeel bata kaita ba, Mysha tace toh dazu da kikeso muje gidansu kin janye kudirin karatun ne, Zeena tace eh zan janye dan banso in rasa adeel dan naga idan nayi wasa zan rasa shi, Mysha tayi dariyan mugunta tare da fadin ai kin rasa adeel Zeena har abada, amma a fili sai tace kai kawata amma naji dadin hakan, yanzu tashi muje gidan nasu muga in yana nan, Zeena cikin murna tace suje, kai tsaye gidansu adeel suka nufa, da suka karasa sun tarar da mai gadi a zaune a wajan gidan suka mai sallama, Ya amsa sannan sukace dan Allah adeel muke nema, yace ai baya nan yana China wajan sati biyu kenan, gaban Zeena ya fadi, yace cikin ku wacece Zeena? Tace gani nan ya dauko takarda ya bata, yace ance in baki inji shi toh ban samu naje ba sai gaki, tace toh amma taya akai ka gane akwai Zeena a nan, Ya dan fara dan in ina, dama ya fada min kina da haske toh ganin haka nace hala cikin ku baza'a rasa Zeena din da yaban sako in bata ba, tace toh nagode suka wuce, saida suka karasa gidansu Mysha ta bude letter din rubutu ne kaman haka,. "Zeena ada naso ki naso in kasance dake a matsayin mata kuma uwar y'ay'ana kin nuna baki ra'ayina toh ina farin cikin shaida miki Zeena nima a yanzu babu sonki ko daya a raina, na samu wacce nake so Dan haka kiyi hakuri kar ki batama kanki lokaci, nagode. Sakin takardan tayi Mysha ta dauka ta karanta tace yanxu haka adeel zai miki lallai namiji badan goyo bane, ko jin abunda Mysha take fada batayi, ta shiga motar ta, ta wuce tuki take amma bata San maike gabanta ba idonta har rufewa yake bata gani sosai, ji tayi garab ta bugi wani mota, mai motan ya fito rai a bace amma ganin Zeena yasa yace Zeena what happen with you hope you are OK, kai kawai ta iya d'aga mishi tana ganin jiri2, mutane keta musu horn ganin ko daga hannu ta kasa yasa ya zagaya ya daukota dakyar ta iya fadin afraz ka daina taba ni, amma ko a jikin shi, yasa ta cikin motanshi sannan ya koma nata ya matsar gefe, Ya dauke nashi a hanya ma, ido ya kura mata tare da wani mugun sha'awanta, tabbas Zeena ta hadu, Ya tada motar ya figa, wani gidan gonanshi ya nufa da ita, bayan sun karasa ya dauketa cak ya kaita wani d'aki, Ya ajiye ta kan gado, yana wani murmushi, Ya fara kokarin cire mata riga..

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to waleeda luv😘
2⃣1⃣to2⃣5⃣

"wasa2 yau wajan wata daya adeel yana fushi da ita, ga Mysha ta rasa gane kanta, ta gefe daya kuma gashi zasu fara exam duk tunani ya mata yawa, ga afraz irin abubuwan da yake mata yayi yawa,

Zeena ta kalli Mysha tace muje study room muyi karatu, Mysha ta dan yamutsa fuska tace no kije kaina yana min ciwo, Zeena tayi dan sororo tana kallon ta, tace muje kisha magani mana, tace ki barni plz Zeena am ok, ganin haka Zeena ta fita, ta nufi study room din tare da tunanin maike damun Mysha kwana2, a lokacin data karasa taga afraz a kofan study room din, shida wasu abokan shi, ta daure fuska ta nufi ciki, shima bai kulata ba, hakan ya mata dadi, inta tuna ya kusa barin skul dinma sai taji wani farin ciki.

Mysha ce zaune a cikin Millennium Park, tana jiran adeel, tana shan drink, bata wani dade ba, yazo, bayan ya zauna ya kalleta babu yabo babu fallasa, yace Mysha lfya kika kirani nan, ko Zeena ta amince ne, ta dan yamutsa fuska jin an kira sunan Zeena, tace nop dama ina son magana dakai ne, yace ok ina sauraranki, ta dan saki murmushi tace adeel kai yanzu kana ganin zaka tsaya jiran Zeena har sai ta kammala karatun ta? Ya danyi shuru can yace bazan iya ba wlh Mysha alhaji na ya dameni yanzu ma yaban nanda wata daya in Kawo mata koya aura min duk wacce yaga dama, plz Mysha kima Zeena magana ko zata tausaya min wlh ina son Zeena kullum da tunaninta nake kwana nake tashi, Mysha tace indai Zeena ce ba zata amince dakai ba, tana da kafiya, babu yanda banyi da itaba amma taki yarda, sai yasa na kiraki in shawarceka, yace ina jinki, tace adeel nima mahaifina yace ina gama secondary school zaimin aure, yace gwd haka yana dakyau ai domin shine ya dace da y'a mace, gidan mijinta, tace haka ne, toh amma akwai matsala yace name kenan, tace bani da saurayi wanda nake so, yace aiya Allah ya baki, tayi dan murmushi tare da kara make murya tace adeel mai zai hana ka nemi aure na, yace what Kin San mai kike fada kuwa Mysha, tace eh na sani adeel, kaga kai an baka 1month ni kuma yanzu gobe zamu fara exam na zuwa ss2, anan kuma zanyi waec, nasan kana San Zeena ita kuma tana da burin karatu mai zurfi kafin aure, kaga nima ina da burin karatun amma dady na yace a d'aki na zanyi, kaga inka aure ni, zamu taimaki juna, zanyi karatu na, idan Zeena itama ta gama saika sakeni ka aureta, yayi shuru can yace sorry Mysha I can't do it, Ya tashi yabar wajan, tayi tsaki tare da fadin wlh adeel kota wani hali saina zama matarka, taji wani tsanan Zeena a ranta.

Su Zeena an fara exam yanzu ba kaman da ba Mysha an dan sake ma Zeena kadan, afraz an bar skul suma sun kusa fara waec,sai dai yakan dan zo jefi2,

Wayan Mysha kema ringing tayi tsaki ganin sunan adeel yasa tayi sauri ta dauka tare da fadin hello, bai jira ta gama fadin abunda zata ceba, yace ina kofar gidanku, tayi sauri ta tashi ta dauki gyale ta fita, ta sameshi cikin mota ta bude ta shiga, da murmushi a fuskanta, Ya kalleta yace Mysha na amince da kudirinki zan aureki amma zan sakeki bayan Zeena ta Gama karatu, don ita nake so, I tace zabi na, tayi dan murmushi tace babu komai, amma da sharadi yace name, tace karka fadama Zeena yanda mukayi, yace babu komai. Sukayi sallama ya wuce, ta shiga gida tana murna ta sami adeel, tace ai adeel kaida Zeena har abada tayi wani dariya wanda ita tasan mai take nufi.

Yau Zeena tayi mamakin canjin Mysha ganin haka yasa take fada mata adeel ya daina kulata, Mysha tace ki shareshi kema tunda ba'a dole, Zeena tace baki San yanda nake son adeel ba Mysha wlh ina son adeel fiye da komai, duk na rame ko abinci bana iya samun ci in koshi saboda tunanin shi, yaki yamin uzuri, wlh Mysha ban so inyi aure ban kammala karatu ba, domin bazan iya ba mijina kulawan daya dace ba, ga karatu ga hidiman mijina, kinga inna Gama karatun in mukayi aure zai samu kulawa sosai, Mysha tayi shuru amma ji takeyi kaman ta shake Zeena dan haushi, tace Zeena tunda kin dage karatu zakiyi sai kiyi ni bari inje inada abunyi.

Maryam obam ✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to huda babyπŸ’ƒπŸ»
3⃣1⃣to3⃣5⃣

"Ya cire cardigan din dake jikinta, sai yar riga karama ya rage mai gajeran hannu, Ya kurama kirjinta ido, har wani hadde miyau yake, Ya fara kokarin cire rigan itama, ta dan sa hannu ta rike tare da fadin ruwa2 ya tashi da sauri yaje ya dauko ruwa ya zuba mata maganin bacci a ciki sannan ya juya ya bata tasha duk idonta na rufe, bata san wake mata wannan aikin ba, bata dade dasha ba, bacci mai nauyi ya dauke ta, Ya cire mata rigan ganin kirjinta yasa ya kara rudewa, Ya fara wasa da kirjinta gaba daya ya fita hayyacinshi, afraz yayi nasaran raba Zeena da budurcinta, har ya gama komai bata farka ba, jini keta zuba a jikinta ganin haka yasa mata kayanta ya dauketa cak, Ya Sata a mota kai tsaye inda ya parka motan ta, Ya nufa, yako tarar da motan a wajan ya bude yasa ta a ciki yaja nashi motan ya wuce,

Gaba daya hankalin iyayen Zeena ya tashi, tun dazu aketa nemanta amma ba'a ganta ba, ga wayanta yana ta ringing ba'a daga ba, ganin haka dady dinta ya fita ko za'a dace, amma babu labari, hankalinsu yayi mugun tashi, gashi Mysha tace tun dazu ta wuce, an sanar gidan radio da tv ko Allah zai sa a dace, police sunzo suma an bada report, ummi ganin wajan karfe goma shiru yasa tace bari dai taje gidansu Mysha taji ko wani abu ya faru kafin tabar gidan, jin haka dadyn Zeena shima yace suje tare, suna tafiya suna duba hanya ko Allah zaisa su ganta, driver ke tuka su, ummi tace tsaya2 kaman ga motan Zeena can, bayan driver ya tsaya da motan, da sauri ummi ta fita, ta bude motan sai ganin Zeena tayi cikin jini gabanta ya fadi ta fara salati, ta rike mijinta ta saki kuka mai karfi tare da fadin mai ya sami Zeena na shiga uku, dady yace ba kuka zakiyi ba, mu dauketa mu kaita asibiti, dady ya dauketa suka nufi asibiti da ita, likitoci sun an sheta anyi emergency room da ita, ummi ta kasa samun nutsuwa sai kaiwa da kawowa take yi, ita da dady an rasa mai bama wani baki, kowa yana cikin tashin hankali, likitoci sai wajan shadaya saura suka fito, ummi taje da sauri tace Dr maiya sameta? Dr yace muje office, suka nufi office dinshi bayan sun zauna, daddy yace Dr maiya sameta, dr yace anyi mata fyade ne sannan an bata maganin bacci wanda zai iya kaita nan da kwana biyu bata farka ba, dady yace what? Ummi babu abunda take iya fada sai innalillahi wa inna ilaihira jiun, wani hawaye mai zafi ke zuba daka idonta, dakyar daddy ya samu ta dan nutsu.

Police sun zo bincike akan abun amma ummi tace subar maganan dan bata son tonan asiri, domin bincike akan wannan abun kaman an tozarta yarta ne, ta dai ce koma waye shida Allah.

Kwanan Zeena uku ta farka daka baccin da take, a lokacin data bude idonta wani jiri2 take gani, ganin ta farka ummi ta kira Dr yazo ya kuma dubata yace ma ummi sai su godema Allah tunda ta farka, sannan a hankula komai nata zai koma normal domin kwayar da aka bata mai karfi ne.

Zeena anata samun sauki kwananta goma a asibiti aka sallameta, Mysha tazo sau biyu tana dubata, amma bata San mai aka mata ba, iyayen Zeena din ne kawai suka San mai ya faru da ita, ita kanta Zeena din ta kasa tuna komai, sai dai tana ganin kaman hatsari tayi lokacin da tabar gidansu Mysha.

BAYAN WATA BAKWAI

Alokacin su Zeena an fara waec tunda abun nan ya faru mahaifinta ya hanata zuwa ko ina ita daya saida masu bata kulawa harda skul, anata shirin bikin Mysha da adeel ba tare da sanin Zeena ba a kwana a tashi babu wuya su Zeena an kammala jarabawa, sai a ranan Mysha take fada mata maganan auran ta, Zeena tace haba Mysha aure zakiyi shine sai yanzu kike fad'a min kina ganin kin min adalci, Mysha tace kiyi hakuri Zeena abun ne yazo da haka, tace shikenan wa zaki aura, Mysha tace surprised nake son miki sai ran bikin zaki sani, tace Allah ya kaimu, kin ga da adeel na nan nema daya fito, Mysha tace Allah sarki ai adeel bai kyauta miki ba, Ya miki halin maza da haka dai suka wuce.

Anata shirin bikin Mysha kasan cewan angon baya farin ciki da bikin yasa bai dawo Nigeria ba yace sai Ana gobe bikin zai dawo andai yi komai daya dace, wani abokinshi mai suna ahmad shiya tsaya akan komai kuma shiya sallama yan matan amarya, a ranan da ango din zai dawo suka shirya kamu wanda ya hada manyan mutane, masu ji da Kansu anyi kamu lafiya kowa ya watse.

Yau sati aka daura auren Mysha da adeel, wajan karfe goma, mutane sun taru sosai, anyi kalanda dasu memo an raba ma mutane, a lokacin da Zeena ta gani ba karamin shock tayi ba na ganin adeel tare da Mysha, wani hawaye ya zubo mata wanda bata San yana zuba ba, waje tayi cikin motan ta, tana kara kallon Hoton tana ganin kaman idonta ke nuna mata adeel, amma bashi bane, ta dai tabbatar adeel din ne, tace driver ya kaita gida, yace toh suna tafiya tana ganin jiri2 dama Mysha haka take zata iya cin Amana na, wani hawaye mai zafi ya kara zubo mata, AMINIYA TA CE yau taci Amana ta, ta rabani da abun da nake so, ashe dama haka aminci yake yanzu na aminta da ita amma taci Amana ta dama shine surprised din da Mysha zata bani.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to zee babyπŸ’ƒπŸ»
3⃣6⃣to4⃣0⃣

"wani azababban ciwon kai ne Ya kamata lokaci daya, inda ita take tuki toh da komai zai iya faruwa, shi kanshi driver din dake janta ganin yana yinta ta bashi tausayi duk da bai San maike damunta ba, Mysha why are you doing this to me, u are my best friend, why Mysha, I trust you but you break the trust that I have for you, inda kin fadamin kina son adeel zan iya hakura dashi in bar miki Mysha am not a selfish, you hurt me alot Mysha, ta saki kuka mai karfi, driver yace hajiya Zeena lafiya kuwa? Ta kasa ko motsa baki balle tayi tunanin bashi amsa, jin bata kulashi ba, yasa yaci gaba da tuki, har suka isa gida, da gudu ta shiga gidan kai tsaye dakinta ta shiga, iyayenta suka bita suma dan ganin yanda ta shigo da gudu, amma ta rufe kofan ta, suna ta buga kofan amma taki ta bude, haka suka barta.

Zeena komai Ya tsaya mata kwata2 ta tsani komai, ko fita batayi kullum tana gida, bata komai sai kuka, tare da bakin cikin abunda Mysha ta mata, ta rabata da farin cikin ranta, har yanzu tana mamakin abun, iyayenta na tausaya mata, sun dai yanke hukuncin su turata wajan yayanta zaheer kasar japan ko Allah zaisa ta manta komai, ummi ta shigo d'akin ta ganta tana ta faman hawaye kaman kullum, tace Zeena kiyi hakuri ki cire wannan abun a ranki dan Allah, ta kalli ummi tace haba ummi AMINIYA TA CE, fa Mysha taci Amana ta, ta rabani da masoyi na, ummi dama haka kawaye suke dacin Amana, yanzu babu mutane masu Amana, masu amana sun kare kwata2 ban taba tunanin Mysha zata min haka ba, ummi inda Mysha ta fadamin tana son adeel ni zan iya bar mata, amma ta yanda tamin is painful, ummi ni daya nasan abunda nake ji a raina yanzu babu mai fahimta na, ta saki kuka ummi ta janyo ta, ta rungumeta tana tausayin yar tata, tace Zeena ki daina fadin haka, akwai masu amana kar kiyi judging mutane ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai mutane masu aminci, tace ummi amma yanzu sunyi karanci, plz ummi ban San zama a kasar nan, Ina so in bar Nigeria gobe dan ina ganin kaman yanzu abun ya faru, ummi tace shikenan Zeena dama nida dady dinki mun yanke hukuncin ki tafi Japan wajan zaheer kiyi karatun ki a can, tace toh ummi I want to leave tomorrow, ummi tace shikenan amma kibar wannan kukan tace toh ummi ta fita daka d'akin.

Mysha ce zaune a falonta da yasha kayan ado na more rayuwa masu tsadan gaske, tana tunanin ta yanda zata bullo wa adeel, Ya dinga kulata, jin motsin shi tayi, yasa tayi saurin tashi ta nufeshi tare dayin hugging nashi, yayi sauri ya tureta, tare da daure fuska, yace Mysha karki manta nida ke fake marriage mukayi, lokaci kawai muke jira mu rabu, so plz ki daina shige min, domin bazan taba kallonki a matsayin wacce zan iya zama da ita ba, tace haba adeel nifa matarka ce kuma inada hakki a kanka, yace what, hakki matata, yayi wani murmushi tare da fadin dnt you ever think of this thing, you are not my wife, lalle Mysha har kina tunanin hakki, kina da hankali kuwa, kin manta yarjejeniyan mu nida ke, tace no adeel ban manta ba, naji na canza ra'ayi, bazan iya rabuwa dakai ba ina so ka daukeni a matsayin matarka wanda mukayi aure na soyayya, Ya kalleta a wulakance yace Mysha kinyi kuskure you are selfish kinci amanan kawance, but zan nuna miki kuskuranki, tace adeel baka isa kamin komai ba, sonka yasa nayi haka na rasa hanyan da zan sameka saida nabi ta wannan hanyan, yace Mysha sai kinyi dana sanin sani na, kin rabani da Zeena akan selfishness naki, zan zauna dake amma ki sani sai kin gwammace gwara mutuwa akan aurena, domin nan gidan daka yau zai koma miki gidan azaba, babu ke babu farin ciki,. Yana fadin haka ya fita, bai dade ba ya dawo, tare da masu aikin gidan duka, yace duk ya sallamesu, tace haba adeel wa zai dinga aikin? Yace ke, don shine abun daya dace dake, ta saki kuka haba adeel yanzu abunda zaka min kenan, yayi banza d ita ya haura sama, Ya barta a nan, cikin bakin ciki.

Zeena tabar Nigeria ta tafi Japan, da yake acan kasar daddy dinsu nada gida anan yayanta yake zama, toh itama a can zata zauna ummi ta had'a ta ita da wata yar dattijuwa dan ta dinga kula da ita, gashi kuma an kammala mata komai na skul, ta sami course din da take burin samu kuma, doctor, Zeena dan kwana biyu da tayi a kasar taji dadin kasar sosai, zaheer shi yake kaita skul ya dauko ta, kafin ta saba da kasar,.

Afraz zaune a d'akin hotel dake kasar nijar, shida wata mata, ta manne shi, amma ba komai yake tunani ba, sai Zeena tabbas mata suna suka tara, babu irin macen da bai nema ba, amma ya rasa dalilin da har yanzu bai sadu da wanda yaji ya gamsu da ita ba sai Zeena, duk da a lokacin shi daya yayi kadan shi yayi rawan shi, balle ace na sadu da ita cikin son ranta ya zan kasance, wani abu yaji yana to karan zuciyan shi tabbas Zeena ina sonki kuma zanyi farin cikin in mallake ki a matsayin matar aure na, ada ba sonki nake ba sha'awar ki nake amma yanzu, babu komai tare dani face soyayyan gaskiya, Ya lumshe ido, matar dake manne dashi tace Afraz inata magana kayi shiru, Ya dan tureta ya tashi, Ya fara sa kaya, tace ina zaka kuma yace zan koma skul, ban son in kara kwana a kasar nan.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to yasmin darling πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
4⃣1⃣to4⃣5⃣

Zeena an fara sabawa da garin duk da ba fita takeyi ba, daka skul sai gida, koda tana son abu zaheer zai Kawo mata, kuma tana karatun ta cikin kwanciyan hankali, amma har yanzu ta kasa mantawa da adeel kullum dashi take kwana take tashi, duk yanda tayi kokarin ta cire shi a ranta amma abun yaki yi, ji take kaman kullum ana kara mata sonshi ne, ta dai barma Allah zabi akan ya zaba mata mafi alkairi.

Afraz ya dawo London amma kwata2 baya jin dadin kasar, ji yayi babu abunda yake son gani sai Zeena, har mamaki yake, kuma yakan tambayi kanshi wai mai yake damunshi, Ya lumshe ido tare da tuna surar Zeena, wani ni shadi yaji yana shigarshi, Zeena you are the best, kinfi ko wace mace, ke daban kike, burina in mallake ki.

Adeel yana zaune a cikin bedroom dinshi daka shi, sai singlet da shortener, yana danna laptop dinshi yana kallo yana murmushi, Hoton Zeena yake kallo, yana fadin Zeena ke tawa ce, saina mallake ki, you are my, bazan bari in rasa kiba, Mysha ta shigo d'akin harta zo kusa dashi

Please Login or Register in order to submit comment