Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waje ta hangota tace ta shigo suje, babu musu ta shiga, gidan su afraz din suma suka nufa, sun shiga falon gidan sunga ummi da mum suna ta karatu gefe kuma afraz ne kwance an rufe shi, da sauri ta karasa wajanshi ta bude shi, taga fuskanshi kaman mai yin bacci, tace afraz mai yasa kamin haka ka tashi in fad'ama abun da kake so kaji, afraz ina sonka ina sonka afraz, baby dinka yana son ya rayu dakai plz ka tashi kar ka maida baby dinka maraya, ummi ta matso kusa da ita, tace Zeena ta rungume ta, tana kuka ummi afraz ya tafi ya barni, saida nace karya fita ummi amma yaki, inda bai fita ba da hakan bai faruba, ummi tace Zeena kiyi shuru ki daina fadin haka koda bai fita ba indai kwananshi ya kare bazai kara koda kwana daya ba, tace ummi bazan iya rayuwa ba tare da afraz ba ummi ina sonshi ummi mai yasa haka yake faruwa a kaina, ta kuma sakin kuka, ummi tace ta daina kuka tamai addu'a ne, ta matsa kusa dashi tana tamai addu'a tana kuka, duk wanda yake wajan saida ya tausaya mata.

Mutane sun taru a kofar gidansu afraz din sosai daka gari2 mutane keta zuwa, anyi mishi wanka an mai sutura dama an barshi sai wajan 8:30 za'a kaishi gidanshi na gaskiya hakan ko akayi, a lokacin da aka dauko shi Zeena kuka take kaman ranta zai fita, ta kankame gawan, dakyar aka banbare ta, aka wuce dashi, rayuwa kenan, afraz yayi mutane sosai, Allah yasa mu cika da imani,

Ana ta zuwa musu gaisuwa kota ina, Zeena kwata2 taki cin komai, anyi2 taki ci, saida mum din afraz tazo da kanta sannan ta yarda taci, shima ita take bata a baki, ci kawai take amma bata jin dadin komai, inta kalla cikin ta saita fashe da kuka, tana fadin afraz ka tafi baka ga baby dinmu ba.

A yau akayi addu'an uku, mutane kowa ya watse, an barsu su kadai, ciki harda ummi wanda tun da akayi rasuwan itama tana gidan ita da abda, yanzu daka Zeena sai mum din marigayi afraz da dad dinshi, suka rage a gidan sai masu yi musu hidima, Zeena duk ta rame tayi baki kullum tana cikin hawaye, mum taita bata baki akan tayi hakuri ta rage damuwa ba ita daya bace, inta kiyin shuru saita ce mata da afraz yana nan ba zaiji dadin wannan kukan ba, inta ji hakan sai tayi shuru.

Wata ranan juma'a da yamma Zeena tana zaune tana karatun alkur'ani mum ta shigo d'akin ta zauna a gefe, Zeena ta saki kara tare da fadin ciki na, mum tace Zeena sannu tashi muje asibiti, ta kira daya daka cikin masu aikin gidan suka kama Zeena din aka sata a mota sukai asibiti da ita, tana ta faman fadin ciki na, nan da nan akai labour room da ita, mum ta kira ummi ta fada mata bata dade ba tazo, tare da abda, sun dauki wajan awa uku amma shiru babu labari sai azaba da Zeena din kesha, akace dole sai an mata operation domin ba zata iya haiyuwa da kanta ba, suka ce sun yarda ayi, nan da nan likitoci sukayi kanta aka fara aiki, su ummi babu abun da ake sai addu'a, wajan karfe goma da wani abu Dr ya fito yana murmushi tare da fadin congratulations an sami twins, baby girl nd baby boy, mum ta d'aga hannu tana ma Allah godiya, suka cewa Dr din zasu iya shiga yace eh, da sauri suka nufi dakin, Zeena tana kwance yaran na gefe, babu abun da take sai hawaye, mum ta dauki yaran duka yaran kaman afraz kaman an tsaga kara, kaman yayi yawa sosai, mum itama ta fara hawayen tace Allah sarki afraz, Allah yaji qanka, ummi tace Zeena ki daina wannan kukan, tace ummi naso afraz yaga wannan ranan inga wani irin murna zaiyi, ya dade yana burin zuwan wannan ranan, ta kuma zubo da wani hawayen wani son yaran taji yana shiganta tare da tausaya musu.

NOTE: masu cewa afraz bai kamata ya mutu ba, inya mutu novel din ya baci, kufa tuna Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, kuma karku manta duk mai rai mamaci ne. Rayuwa akwai mutuwa akwai tsufa kar ko da yaushe mu dinga mantawa da mutuwa, duk da novel ne wannan ya kamata mu dinga sawa akwai mutuwa a ciki ba kullum ace sun kasance tare cikin jin dadi da kwanciyan hankali ba, indai akace kullum haka ne Ya zama babu amfani rubuta littafi tunda ana mantawa da mutuwa ya zama shirme, sau da yawa ina rubuta akan abun da yake faruwa ne, Allah yasa mu dace

Maryam obam✍✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to aysher likymo πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
9⃣5⃣to1⃣0⃣0⃣

Ganin haka yasa yace kar suyi kuka zai dawo, yaja motarshi ya fita, ganin ya fita din suka saka kuka, ta fara rarrashin su, har Suka shiga ciki, mum tace mai aka musu, tace kawai daka sunga zai tafi suke wannan kukan, tace aiya yaro kenan ta tashi ta janyo jikokin nata ta fara rarrashinsu, sukayi shuru suka mika mata ledan daya basu, su chocolate ne dasu biscuit, kalan na waje dinnan sune kala2 a ciki, mum tace harda tsaraba dole kuyi kuka dan zai tafi, Zeena ta danyi murmushi,.

Bayan Zeena ta shiga d'aki ta kwanta yanzu twins wajan kakarsu suke kwana, ita a yanzu adeel baya cikin tsarin rayuwanta tunda ta rasa mijinta ta cire komai a ranta, take ganin ba zata iya kara kallon wani namiji ba da sunan so ko aure ba, yayanta ma sun isheta rayuwa, wannan abun Zeena tasa a ranta.

Adeel tuki yake amma yana ganin Zeena, ya rasa wani irin azababban so yake mata, ga yaranta wanda suka shiga ranshi jinsu yake kaman yaranshi, har yakai gida yana wannan tunanin, a lokacin daya shiga cikin falon gidan yaga Mysha tana cika tana batsewa, yace ina ahmad, tayi banza dashi, ganin haka yace ba dake nake magana ba, tace na kaishi gidan mu, ya daure fuska tare da fadin bana hanaki fita ba, ba tare da izini na ba, ta yamutsa baki tare da fadin duk ka gama abunka fita ne dai sai nayi, dama tunda naji kace mu dawo nja nasan akwai dalili, dama mijin waccen yar iskan ne Ya mutu wato shine ka dawo ka jajubota, toh wlh..... Saukan mari taji, ta rike wajan tana hawaye, yace ki dinga sanin abunda zaki fad'a akan Zeena, domin Zeena ta fiki itace macen da nake so kuma har gobe nake burin aure, darajan Zeena din kikeci shi yasa nake jure duk wani abu naki nake zama dake, inda badan ita ba, dana dade da rabuwa dake, tace adeel akan wata mace kake fadamin haka, ta shige dakinta da gudu tana rusa kuka, yayi tsaki ya kuma barin gidan.

Tunda Mysha tasan Zeena bata da aure, ta shiga cikin damuwa, ta takura ma adeel akan su koma China amma yaki, yace mata ya dawo kenan, haka suke zama kullum ita bata jin dadinshi shima baya jin dadinta, duk abubuwan da takeyi mai da dan yaji dadi duk ta daina, kullum sai mita, inya gaji ya bata waje, shi yanzu babu abunda yake damunshi illa ace yau ya sami Zeena.

Zeena tana falo suna wasa da twins saiga mai gadi nan yayi sallama ta amsa sannan ya shigo, yace gashi wai inji adeel yace abama twins, leda ne manya2 guda uku, ta amsa tare da fadin kace angode, yace aiya wuce, ta amsa da toh, mum ta fito tace a'a wa innan kayan fah, tace adeel ne yace a Kawo masu afraz, mum tayi dariya tare da fadin Allah sarki baya gajiya da hidima, tunda yazo mata gaisuwa bai kara zuwa ba, sai dai yaba mai gadi kaya ya Kawo ma yaran, mum ta bude ledan taga kaya ne masu tsadan gaske ya siyo da takalmi masu kyau, mum ta kalli Zeena tace ya kamata dai nima in mishi godiya, Zeena tayi shuru bata ce komai ba, mum tana son duk wanda yake son jikokinta bata iya boye son su ako ina, ko 'kuda bata so ya taba mata su, sai yasa bata cika son suna fita sosai ba.

Adeel ya yanke hukuncin turawa wajan iyayen Zeena, don wannan karan dagaske yake, bazai bari ya kuma rasa taba, hakan ko akayi iyayenshi sunje sun sami dadyn Zeena sun mai magana, yace Su bashi dan lokaci kadan zai kirasu sukayi godiya tare da sallama, a lokacin daya je, gida ya sanar da ummi, a lokacin zaheer yana wajan, yace ma dady ai Zeena tana son adeel domin kuwa a ranan da suka dawo da maganan zai turo ta dawo, sai kuma ta tarar da ana bikinta, dady yayi shuru tare da tuna lokacin tabbas Zeena tace tana son fada mai magana, duk sai yaji tausayinta ya kamashi, yace Zeena kin min biyayya kin auri mijin dana baki, ya aiyana a ranshi akan wannan karan zai cika mata burinta ya aura mata adeel.

Dadyn Zeena Yama mahaifin afraz bayani yayi na'am da abun yace dama ya kamata tayi aure, a lokacin da Dady afraz ya fada mum din afraz yanda sukayi da mahaifin Zeena ba karamin dadi taji ba, nan ta fadama dady irin hidiman da adeel yake ma twins, shima yaji dadin hakan, dady yace yasan baban Yaron sosai dan gidan mutunci ne,.

Dadyn Zeena ya kira magabatan adeel ya fad'a musu akan su turo ayi komai, sunyi godiya sosai, cikin kwana uku suka Kawo komai da komai da ake bukata, duk wannan abun da akeyi Zeena bata San wainar da ake toyawa ba,

Adeel yasa anci gaba da gina mai gidanshi, wanda da ya tsaya, ya tafi China, yanzu anci gaba da gina gidan a ciki yake son saka matanshi dan yace wanda suke ciki yayi karami, ummi ta kira mum tace Zeena tasan da batun auren kuwa mum tace a'a bata sani ba, ummi tace mum ta fada mata, tace shikenan, hakan ko akayi Zeena tana zaune a d'aki tana karanta wani littafi mum ta shigo tace Zeena ina son magana dake, tace to mum, tace Zeena ansa bikinki keda adeel nan da wata biyu, tace what mum aure, mum tace eh, tace dan Allah mum kar kumin haka babu aure a tsari na ta saki kuka, mum tana ta rarrashi tace kiyi hakuri Zeena ba zaiyu mu barki haka ba, dole kiyi aure Zeena, tace no mum bazan iya auren kowa ba mum, bana son yin aure mum, jin haka taba mum din tausayi tasan duk macen da mijinta ya rasu yawanci ana samun irin wannan matsalan kafin su sake aure, tace kiyi shuru Zeena in bakya so babu mai miki dole, jin haka yasa tayi shurun,

Mum ta kira ummi washe gari ta fada mata Zeena bata son auren, ummi tace zata zo ta sameta suyi magana, ko awa daya basuyi ba ummi tazo, ta sami Zeena din tace miye dalilin ta nakin auren tace ummi kawai banso inyi aure ne, jin haka ummi tace toh bari kiji ko kina so ko bakya so sai kinyi wannan auren, so kike mu ajiye ki kita zama a gida babu aure to gwara ma ki canza tunani, babu abun da take sai kuka, har ummi ta gama ta fita, mum tana ta bata baki har tayi shuru, ta dai yanke wannan karan ba zata bari a mata dole ba, domin yanzu ta cire shi a tsarinta.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my fans πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
1⃣0⃣0⃣to1⃣0⃣5⃣

A lokacin da ummi ta koma gida tama dady magana akan a daura auren nan da sati biyu, in yaso saita tare daka baya, dady yace akan wani dalili kuma, bayan an tsaida rana kuma yanzu a canza, ummi tayi shuru bata kuma cewa komai ba, jin haka dady yace akwai wani matsala ne, tace a'a babu, naga kaman ansa lokacin ne yayi yawa, dady yayi shuru can yace ai kaman yanzu ne, zaki ga yayi, abda ta shigo falon da fara'a a fuskanta, ummi tace anyi nasara kenan, tayi dariya tare da fadin eh ummi, ta mika ma ummi takardan tace lallai abu yayi kyau, dady tace mai nene, ummi tace waec din tane, yace har ya fito, yanzu sai shirin zuwa high instuition kenan, tace eh dady, tana dariya, nan suka zauna suna ta fira cikin sha'awa,.

Tunda ummi tazo gidan tama Zeena magana, babu wanda ya kuma mata maganan auren, hakan ya mata dadi dan tana ganin kaman an fasa ne, ita kwata2 yanzu adeel baya cikin tsarinta, domin kuwa ba zata iya kishi da Mysha ba, domin yanda taga Mysha a saudiya ta musu, Ina ga in sun hada miji, wani hawaye ya zubo mata tare da fadin afraz ka tafi ka barni gashi yanzu ina cikin kunci, babu mai rarrashi na, Ina ma kana nan da duk haka bai faru ba, mutuwa ta rabani dakai masoyi na, a lokacin da nake son kasancewa dakai, lokacin da nake bukatanka, ta kuma zubo da wani hawayen afraz ka tafi ka barni da sonka, a raina, naso ace tare muka mutu, duk wannan maganan da takeyi a fili take, mum ta shigo d'akin taji duk abunda take fad'a, taji tausayin Zeena din sosai, ta matsa kusa da ita, tace Zeena ki daina fadin haka, afraz ya tafi yabar miki yaranshi Zeena ki daina sa wannan abun a ranki, afraz addu'a yake bukata, sannan kuma yaranshi duk da basu sanshi ba, ki fad'a musu waye babansu su taso suna mai addu'a indai kikayi haka kin mai babban gata, kuma kin nuna mishi dagaske kina sonshi, ta kuma fashewa da kuka ta rungumi mum din,.

Yau an tashi garin Abuja ana zafi, Zeena tama twins wanka tasa musu kaya mara nauyi, tana zaune taji zafin itama ya isheta duk da a.c a kunne yake, ta tashi ta sami mum tace zata wajan ummi, mum da fara'a tace kai yau wani rana, tunda afraz ya rasu sau biyu taje gidansu, itama tayi murmushi, mum tace ai kin kyauta Zeena amma zama waje daya babu dadi, shi yake sama mutum yaita tunani, tace hakane, tace ma mum ta wuce ganin zata fita twins suka bita da gudu, suka makale ta, abun ya bata dariya tace ku koma ku taya mum fira, suka ki sakinta, mum tace haba ya zaku min haka, dawa zaku barni a gida, kuzo muje muma anjima zamu fita, ganin mum zata zo inda suke suka sa kuka, mum tace kuyi shuru tare zaku, jin haka sukayi shuru suna dariya, suka fita suna ma mum bye2, tace zaku dawo ai ku sameni,

Kai tsaye gidansu Zeena ta nufa, bayan tayi parking ta shiga, taga motar dady a gidan alaman yana gida kenan, sun shiga falon gidan da gudu abda tazo ta kamo hannun twins, tana fadin what a surprise yanzu nake son kiranki ince zanzo sai gaku, Zeena tace kedai abda kin iya tsara zance, tayi dariya tare da fadin ki tambayi dady kiji, a gabanshi na fada, jin haka dady yace to ai tunda tazo shikenan, nan ta gaida dady ya amsa cikin fara'a ya kira jikokin shi, suka zo wajan shi yana musu wasa, ummi tace ma afraz yazo ya noke alaman a'a, tace au niko to yau babu auren na sallameka, dady yayi dariya yace kishin ne ya motsa kinga amarya tazo ko, sukayi dariya, Zeena da abda suka shige ciki,

Bayan sun shiga Zeena take tambayan abda akan maganan bikin da ake shirin yi, yana nan ko an fasa, abda da mamaki tace a fasa kuma, aike zaki fi kowa sani ai, tunda kuna waya da adeel din, ni nasha mako kinzo mu tattauna akan bikin ne, Zeena ta sakar mata harara tare da fadin sai ki tattauna dashi ai, abda tace mai yayi zafi kuma, Zeena tace abda Kin San wani abu, kin dai San yanda abubuwa suka faru a baya toh ina so kiban shawara, ada naso adeel Mysha ta aure shi, daka baya na gano, abunda yasa ya aureta, a lokacin Allah yasa bani zai aura ba, nima na auri afraz bana sonshi amma daka baya Allah ya dauramin sonshi, har ya rasu ya barni da mugun sonshi a raina, wanda a yanzu nake kallon bazan iya kallon wani namiji da sunan so ba, ko aure ba, gashi su ummi sun tsaida ranan aurena da adeel, abda bazan iya kishi da Mysha ba, taya zan rusa wannan auren, abda tace haba Zeena ban taba tunanin haka daka gareki ba, dady yasan ba zaki bashi kunya ba shiyasa ya amsa musu, kuma bros zaheer ya fada mishi kina son adeel, shi yasa ma harya amsa maganan auren kuma dady yayi hakan ne dan ya faranta miki, bama haka ba idan kince baki son auren haka zaki bar yaranki babu uba, ai ya kamata yau ace sun taso da wanda zasu dinga kira da mahaifinsu,kuma na tabbata yanda adeel yake sonki zai rike miki yaranki, tace abda banki taki ba adeel fah mijin Mysha ne AMINIYA TA, abda tace to sai me dan mijin tane, idan ita bata ji kunyan aurenshi ba, taci amana toh kece zaki ji kunyan aurenshi, aiba zamanta zaki yiba, Zeena tayi shuru tabbas maganan abda hakane kuma gaskiya ta fad'a, toh amma yanzu taya zata kalli adeel a matsayin mijinta, harta iya zaman aure dashi, wata zuciyan tace don yaranki zakiyi, sai wajan 5 Zeena suka koma gida, da gudu twins suka shiga suka fad'a kan mum dake zaune a falo tace oyoyo, suka saki dariya da murna na ganin mum, nan suka nuna mata kudin da dady ya basu,tace to su bama mamansu ta ajiye musu, suka nufi Zeena suka bata, nan suka zauna suna ta fira da mum,

Bikin yana ta gabatowa, ita Zeena harga Allah bata murna da auren, dan tana ganin kaman taci amanan afraz idan ta sake wani auren, gashi a yanzu babu daman tace ta fasa domin bikin baifi sati daya ba, ga adeel tunda yazo mata gaisuwa bai kara zuwa wajanta ba, sai dai twins da yake aiko ma da kaya, kala2 hakan yana mata dadi sosai, tana zaune a waje kan kujera ta gaban swimming pool dan zafin yau yayi yawa, aka bude gate din gidan aka shigo, motar tayi packing ta bayanta, ya fito yazo inda take yace barka da hutawa, ta waiga taga adeel, ta amsa babu yabo babu fallasa, ganin hakan yasa ya sami karfin giwa, yace Zeena nazo muyi magana ne, bata amsa Shiba, shima hakan bai dameshi ba, yaci gaba da magana, Ina so inji mai kike bukata, ta dan tabe baki tare da fadin bana bukatar komai, yace ok babu damuwa ya ciro kudi yan dubu daya2 ya bata bandir biyar yace ga wannan ki saima su twins sweet, tace no ka barshi an gode, ya danji wani iri, amma sai yace ai bake naba ba, so baki da right din da zaki ce a barshi, tace amma ai...... Ya katse ta tare da fadin na wuce.........

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my fans πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
1⃣0⃣5⃣to1⃣1⃣0⃣

Ganin haka yasa ta diba kudin, ta shiga ciki itama, tare da fadin ni wannan auren ba sonshi nake ba, kawai dai so ake amin dole, tayi tsaki, tare da tausayin kanta,..

Anata hidiman biki, ango shi daya yake hidimar shi, amma Zeena ko a jikinta, itama Mysha bata San da batun ba, yadai ce mata zasu koma sabon gidansu ta shirya kayanta hakan ko akayi, tana ta shiri suka koma, a lokacin da suka koma taga yanda yayi tsarin gidan abun sha'awa, gidan babba ne, falon gidan ya hadu sosai, ya nuna mata wani kofa yace nan ne dakinta, ta bude taga falo sannan taga kofofi guda uku taga bedroom ne ko wanne akwai toiled a ciki, kuma duk dakunan ansa kayan gado a ciki, sannan falon ma data gani shima an hada shi, tace wancan shine babban falo kenan,ta fito ta nufi wata kofar taganta a rufe, ta matsa wanda yake kusa dashi shima a rufe, tayi dan tsaki to miye na rufe kofofin ma toh, ta koma babban falon ta ganshi yana tama ahmad wasa, yana dariya tace sauran kofofin can fa, mai yasa aka rufe, ya tamke fuska tare da fadin ainan ba hurumin ki bane, tace kaman ya, yayi banza da ita, ganin haka ta fara surutu ta inda take fita ba tanan take shiga ba, jin haka ya tashi yabar wajan.

Yau ranan laraba kuma a ranan aka kai akwatin auren Zeena, gidan su ummi aka kai, mum ta tafi can aka bar Zeena da twins, akwati 24 aka kai mata ko wanne cike da kaya masu tsada, abun dai ba'a magana, sai San barka, a ranan itama yakai ma Mysha nata akwatin, tace adeel wannan akwatinan fah, yace nama nama amarya tane, kema na miki, komai kala daya nasa muku, sai dai colour din na ban banta, tunda ya fara magana tasa mai ido tana kallonshi, wani hawaye yake zuba a fuskanta dama tasan za'ayi haka, tun zuwan su gidan Nan take zargin hakan, tace adeel wa zaka aura ba tare da fargaba ba ko tsoro yace Zeena, tace what Zeena kake nufi zaka auro ka Kawo ta cikin gidan Nan, yace yes, tace wlh baka isaba ba adeel dan rashin adalci ka rasa wacce zaka auro sai Zeena, ta saki kuka, yace Mysha ke har kina tunanin banyi miki adalci ba, ai bai kamata kima cemin hakaba, kanki ya kamata ki kira da hakan, tace adeel ka auro koma wace ce, bazan damu ba, amma dan Allah karka auro Zeena, yace Mysha kiyi hakuri Allah yasamin son Zeena, bazan iya fasa aurenta ba, tace adeel ka tausaya min nima ina sonka adeel, nasan kayi hakan ne dan ka rama abinda nama, duk sai yaji ta bashi tausayi yace Mysha badan in rama abunda kikamin ba yasa zan auri Zeena, keda kanki kin San yanda nake son Zeena, Mysha bazan wulakantaki ba dan na auri Zeena ba, taci gaba da kuka yana ta bata baki ganin bata da niyan yin shuru yasa ya bata waje, ganin ya tashi taci gaba da kukan ta, tasan idan Zeena ta shigo gidan nan zata koma bora, yanzu ma yata kare balle Zeena tana gidan, tace Zeena sai nasa adeel ya tsaneki.

Yau juma'a aka daura auren Zeena da adeel, ranan Zeena kuka take tayi tana fadin ita bata son wannan auren, amma ina babu mai sauraronta, tun Ana saura kwana biyu bikin ta koma gidan ummi, abda cema mai bata baki, ummi ta shigo d'akin taga tana ta kuka, nan ummi ta mata ta tas, tare da fadin in batayi shuru ba saita saba mata, ganin ran ummi din ya baci yasa tayi shuru, mum ta shigo d'akin ta tarar da ummi tana huci tare da fada, nan tace ma ummi ta daina mata fad'a haka ai rarrashinta za'ayi ba fad'a ba, ummi tace wani rarrashi ne ba'a mata ba, amma dan iskanci tazo tana ta kuka da yake ta raina mutane, ki duba ko wanka taki tashi tayi, jin yanda ummi take ta fad'a yasa ta tashi da sauri tayi toilet nan taci gaba da kukan ta, tayi mai isarta sannan tayi wanka ta fito, abda ta mata makeup tare da taya ta sa kaya, tayi kyau sosai, ta fito falo suna ta gaisawa da mutane, ummi ganin haka yasa ta saki ranta,.

Mysha tun safe itama take aikin kuka a d'aki tana fargaban a Kawo mata Zeena gida, amma babu yanda ta iya domin aikin gama ya Riga daya gama, son adeel dinne yasa ta kin barin gidan, dan har mahaifiyarta tace ta dawo gida, amma taki,

Wajan karfe 8 a Kazo daukan Zeena, tana ta rusa kuka, iyayenta sunyi

Please Login or Register in order to submit comment