Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mahaifin nata ya baci sosai, yace ma adeel ya gode saiya neme shi sukayi sallama, yana zuwa gida ya kira Mysha ita ma mamanta ta fito, nan ya zayyane mata abun da Mysha tayi, itama taji mamaki tace Mysha ce take hakan, gaban Mysha sai fad'i yake dan tasan yau ta bani, mahaifin nata yace kin kyauta tunda zaman gida kika zaba saiki zauna, kin samu yaro mai hakuri kinje kina mai abunda kika ga dama, inda wani ne daya dade da koranki ko kuma ya miki dukan tsiya, tunda baki da kirki daka yau zan kafa miki doka bake ba fita, ki zauna a gida tunda shi kike so mutuniyar banza, mamanta tace Mysha ina kika koyo wannan bakin halin wanda ban sanki dashi ba, ke kin taba ganin inama babanki haka, babu abunda Mysha take sai kuka, domin tasan tunda dad dinta yayi fushi da ita, tasan yanzu bata ba wani jin dadi, dad dinta yace ta tashi ta basu waje, ta tashi da gudu tayi d'aki tana aikin kuka,

Bikin zaheer ya matso anata shirye2, dakyar adeel ya bar Zeena taje gida tayi sati daya, anata shagalin biki gidansu Zeena ya cika da mutane sosai, an daura auren zaheer da amaryan shi Zaynab yar garin adamawa, washe garin daurin dauren zasu koma Japan domin ya samu aiki a can haka ko akayi ango da amarya suka wuce yan biki kowa ya watse, adeel ya kira Zeena yace yaushe zaki dawo, tace nan da 2week dan na gaji da hidiman biki, Ina so in dan huta, ya kashe Wayan Jim kadan ya kuma kira yace fito ina kofar gidanku, yana gama fadin haka ya kashe Wayan,sai gata ta fito ta zagaya ta shiga cikin motan tana shiga yaja suka wuce, tace ya zaka wuce dani banyi ma ummi sallama ba, yace ki kirata a waya, tun daka lokacin bata kuma cewa komai ba har suka isa gida, ranan Zeena tasan mijinta yayi kewanta kaman itama yanda tayi,

Mysha ce zaune ahmad nata wasa ta rame da danyi duhu, kullum tana cikin tunani ga iyayenta sun daina sakan mata sosai, mu samman ma dady dinta, gashi bata fita ko ina, inta kira adeel baya dauka, sai dai ta mai text tana bashi hakuri akan ya maidata, shima babu reply, sai a yanzu take nadaman abunda tayi, wani hawaye ya xubo mata, adeel sanka da kuma kishinka yasa nayi duk wa innan abubuwan, gashi yanzu ya tashi a banza tunda ka sakeni, lokaci daya taji tana nadaman abunda tayi, domin tasan nata kishin ya wuce musali,cikin wannan halin mum dinta ta sameta a ciki, ta tausaya ma yar tata, tace Mysha ki daina wannan kukan domin bashi da amfani, kuma komai Ya faru ke kika jama kanki, tace mum wlh ina son adeel dan Allah mum kisa dady ya mishi magana ya mayar dani, mamanta tayi shuru, tace Mysha dad dinki yayi fushi sosai dakyar in zaima adeel magana amma zan jaraba bashi hakuri.

Cikin Zeena yakai wata7 tana samun kulawa wajan adeel, kullum yana nuna mata so da kauna, itama tana iya kokarin ta wajan nuna mishi kulawa, suna zaune a falo wayanta yayi ringing ta dauka taga number ne, ta kara a kunne jin muryan Mysha tayi tana kuka, tace Zeena dan Allah kiyi hakuri akan abunda na miki, Zeena tace babu komai, sannan tace dan Allah kisa adeel ya dawo dani, wlh Zeena Allah ya jarabce ni da sonshi, Zeena tayi dan murmushi wanda bai kai ciki ba, tace zan mai magana duk yanda mukai zaki jini, ta kashe Wayan sannan ta kalli adeel wanda ya bata rai, tace lafiya kuwa naga ka daure fuska, yace banso kimin maganan Mysha plz, tace haba adeel karfa ka manta akwai yaro a tsakaninku ko danshi ya kamata kayi hakuri ka dawo da ita, yace Zeena bazan iya dawowa da Mysha ba, domin Mysha ba macen aure bace, Zeena tayi kaman za tayi kuka tace adeel ka dawo da ita saboda Allah, badan halinta ba, kuma na tabbata tayi nadama tunda harta kirani tana kuka akan inyi hakuri akan abunda tamin, nan yayi shuru dakyar Zeena ta samu ta shawo kanshi ya yarda,..

Adeel da Mysha sun dawo matsayin mata da miji Mysha ta canza kaman ba ita ba, komai ita take ma Zeena tace bata so tana komai tunda ba ita kadai bace, adeel har dan kiba yayi saboda yanzu ya sami kwanciyan hankali a gidanshi,

Adeel shi ya dauke biya masu twins karatu yana musu hidima kaman yaran daya haifa, Zeena kullum tana kara godewa Allah akan baiwar da yayi mata, ita da Mysha sun fara business Ana Kawo musu kaya daka waje suna sai dawa, Mysha da Zeena Ana zaune Ana fira, Zeena taji kaman ana tsungulinta a mara, tun tana ji kadan harta fara ji sosai, nan ta saki kara Mysha tayi sauri ta riketa tana fadin Zeena lafiya maike damun ki, tace Marana, dakyar Mysha tasa ta a mota sukai asibiti suna zuwa akace haiyuwa ne, akai labour room da ita ko minti talatin ba ayi ba ta haifa yarta mace, sai a sannan Mysha ta kira adeel take fad'a mai, zo kuga murna nan da nan yazo asibitin, yaga yar kaman Zeena sai dai ta dauko kalan hancin shi, yarinyan kyakyawa,

Zeena da baby dinta suna samun kula wajan Mysha sosai, ranan suna yar taci sunan ummi habiba, suke kiranta da ma-ma, mum tasai ma yarinyan kaya da yawa, haka itama ummi, ga wanda Mysha itama tayi, abda itama tayi aure ta auri wani saurayinta wanda suke san juna sosai, a dubai zata zauna saboda karatun ta.

BAYAN SHEKARA BIYAR

Zeena zaune da yaranta su uku, ma-ma da sadeeq sai anan, suna ta wasa, Mysha ta shigo ita da yaranta da gudu yaran suka tashi suna tsalle na ganin yan uwansu, Zeena tace har kun dawo kunyi sauri, Mysha tace wlh kuwa duk na gaji, itama yaran Mysha biyu, ahmad da saudat, nan yaran sukai waje suna wasa, ita kuma da Mysha suna ta hira, har adeel ya dawo, shima ya zauna anayi dashi, yace yanzu dai kun daina bani kulawa aure zan kara, jin haka Zeena ta tamke fuska, Mysha tace ai babu wacce ta isa ta shigo wannan gidan, yace haka kika ce, zaku gani ai jin haka Zeena tabar wajan, Mysha ta saki dariya tare da fadin sai kaje kaba aminiyata hakuri, yayi dariya shima sannan ya tashi ya nufi d'akin Zeena din, tana ganin shi ta kawar dakai gefe, yayi dariya yace haba amarya ta, jin haka ta saki kuka tana fadin ni ka daina cemin amarya wanda zaka aura ita zaka kira da haka, yayi dariya tare da fadin kece amarya ta, tunda na sameki na cire ko wace mace a raina, taji dadin abun da yace, yace ashe dai ana kishi na, ta rufe fuskanta da hannu, yayi dariya nan suka fada faranta ma juna nima dai a nan zan tsaya.
ALHAMDULILLAH

Zaku iya samun novels dina a grp dina :maryam obam novels

Maryam obam ✍✍
08060860886

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment