Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata sani ba, ganin Hoton Zeena a laptop din yana kallo yasa ranta ya baci, ta fisge laptop din tayi jifa dashi, Ya tashi rai a bace ya tsinka mata mari har sau biyu tare da fadin Mysha I hate you, you are evil, tace adeel ni ka mara? Ya daure fuska yace get out tare da nuna mata kofa, yace sai kin San kin fasa laptop din nan, ta fita da gudu tana kuka, toilet ya fada yayi wanka ya fito cikin kananan kaya ya mishi kyau sosai, Ya nufi d'akin ta, Ya ganta kwance kan gado tana rusa kuka, Ya tabe baki, Ya daka mata tsawa tare da fadin ke naki kukan najin dadi ne, sai na d'an d'ana miki irin radadin da kika sani a ciki, yana gama fadin haka ya fita.

Afraz yazo Nigeria, Ya samu labarin Zeena tana Japan karatu wajan mai gadin gidansu, Ya tambayi number dinta yace baida shi, Ya bashi kudi da yawa yace ga wannan plz ka samo min bayani akan inda take karatu a Japan din, mai gadi ya washe baki yace an Gama, Ya amsa number din Afraz din, akan zai kirashi idan ya samu information akan batun, Afraz ya wuce.

Zeena tana cikin class sun gama lecture, tana jiran zaheer yazo ya dauketa, sai ga wani bature yazo inda take, yace mata hello, Ya sakar mata murmushi ta amsa da hi,tana fadin haka ta tashi da nufin fita, yace mata please I want to talk to you, ta dan tsaya tare da fadin ok, Ya kalleta yace please sit down, batamusa mishi ba, ta zauna, Ya kalleta yace, na ganki a skul din nan, so ina lura dake kaman kina da damuwa, naga baki kula kowa, duk da harshen turanci yake mata maganan, ta kalleshi ta dan daure fuska, tayi shiru, ganin haka ya kuma tambayanta ya kikayi shuru, ganin ya matsa mata da tambaya yasa ta tashi tabar class din, tako ci sa'a ta hango zaheer da sauri ta nufeshi ta bude motar ta shiga, tace bros mai yasa kayi late din zuwa dauka na, Ya kalleta yace sorry little sis, naje amso abu ne, ta dan turo baki, irin na shagwaba, yayi dariya yaja motar suka wuce,

Mai gadin gidansu Zeena ya fad'a ma Afraz komai da komai na wajan da Zeena take karatu, yaji dadin labarin, Ya fara shiri na zuwa Japan,

Afraz an sauka a kasar Japan, bai bari ya huta ba, Ya nufi skul din, amma harya gama yawonshi baiga mai kama da Zeena ba, haka ya koma masaukin shi cikin takaici, haka kullum yake ta sintiri a skul din amma shuru kake ji, babu Zeena balle mai kama da ita, wajan sati daya kenan, yayi tsaki tare da fadin kodai mutumin nan wrong address ya bani, mai ma yasa na yarda dashi, Ya tada motarshi, da nufin ya wuce a dai2 lokacin Zeena ta fito daka class zata mota ya hango ta, da sauri ya fita, amma kafin ya karasa ta shige mota sun wuce, Ya koma da sauri yabi bayansu, har suka nufi gida, toh amma wani abu daya tsaya mishi a rai waye wannan namiji din daya dauko ta, miye halakan su, da yaga tana mishi dariya shima yana mata, wani bakin kishin Zeena din yaji yana shiganshi, wannan ne karo na farko daya taba jin kishin y'a mace.

Maryam obam ✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to yasmin darling πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
5⃣1⃣to5⃣5⃣

"tunda mum din afraz tayi mai magana akan zata neman mai auran Zeena ya cire duk wani fargaba da yake yi akan zai rasa ta, wannan ne Ya bashi da man yin karatu har suka kammala exam dinsu, kuma shine final year dinshi, zai zama cikakken engineer a quantity survey, a ranan daya gama exam din ji yayi kaman yayi tsalle ya gashi a Japan wajan Zeena domin yayi mugun kewanta, shi koda bata kulashi inya ganta ma dadi yake ji, amma dole yayi hakuri gobe tayi, yayi dan gajeran tsaki yaga dare ya mishi nisa ranan, washe gari da asuba ya tashi yayi sallah, sannan aka fara shiri, duk da wajan 10 zasu tashi yana Gama shiri ya nufi airport, Ya zauna kafin lokaci ya cika.

Zeena tana gida yau bata je lecture ba, ta online take dubawa, wayanta dake gefe yayi kara, ta dauka taga abda, tace little sis yakike, abda ta amsa da lfya tare da fadin ya skul, ta amsa da lafiya, wai yaushe zaki zo Zeena, nayi missing dinki, Zeena tayi dariya tace kaman da gaske, abda tayi dariya tace dagaske nake, Zeena tace in mun gama exam zan zo, mun kusa farawa, jin haka abda tayi kara tare da fadin kizo keda bros zaheer, kice na mishi mata, Zeena tayi dariya tare da fadin wa innan kananan kawayen naki, a ciki kika zaban mai, ta dan turo baki kaman Zeena din tana gabanta, tace haba Zeena yanzu fa ina jss3 going to ss1 kinga ai ba za'a kirani da karama ba, Zeena tayi dariya sosai tace abda baki da dama, tace ina ummi abda tace tana kitchen Zeena tace takai mata Wayan, ta amsa da toh, ta nufi kitchen din taba ummi, bayan ta amsa suka gaisa tace ummi daddy ya fada miki wata magana, tace a'a maganan mai nene, tace akan adeel, ummi tace Zeena har yanzu baki cireshi a ranki ba, tayi shiru, ummi taci gaba da fadin ya kamata kima kanki fad'a, kara girma kikeyi Zeena ya kamata kisan abun da zai yiwu da wanda bazai yiwu ba, ki cireshi a ranki ki fara kema rayuwanki, tace toh ummi, tana fadin haka ta kashe Wayan, tabbas abunda ummi ta fad'a haka ne, Ya kamata ta cire adeel a ranta, amma ta yaya hakan zai faru taya zata cireshi, bayan kullum son shi kara karuwa yake a ranta, wani hawaye ya biyo kuncinta, adeel ka cuceni kaida Mysha kuna can kuna jin dadin rayuwanku kun barni cikin kunci da bakin ciki, sonka yamin yawa, mai zanyi sonka ya fita a raina, Allah sarki Zeena rashin masoyi babu dadi.

Afraz an sauka a kasar Japan, wani farin ciki yake ji tare da nishad'i yazo kasar da masoyiyarshi take, kai tsaye hotel ya nufa ya ajiye kayanshi, Ya fad'a toilet yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin kananan kaya, yayi kyau sosai, kai tsaye gidansu Zeena ya nufa, yayi nocking, aka bashi izinin shiga, fatima ya gani wacce take kula da Zeena, Ya gaidata cikin harshen hausa da mamaki take amsa wa, don a zaton ta baya jin hausa don baiyi kama damai jin hausa ba, zata iya kiranshi da bature ko balarabe, Ya katse ta tare da fadin dan Allah Zeena nake nema, tace tana baya, ta nuna mai hanyan da zaibi, Ya shiga ya ganta cikin wani yar bukka, ta zabga uban tagumi, duk sai yaji wani kala kasancewan ya ganta a haka ya tabbata tana cikin damuwa, Ya matsa kusa da ita, Ya cire mata hannun, ganin afraz yasa tayi saurin tashi tare da fadin maiya Kawo ka nan, yace Zeena dan Allah ki tausayamin wlh Zeena ina sonki, tayi tsaki tare da fadin nace bana sonka wai afraz dole ne, ya kafeta da ido tare da fadin Zeena nasan abun daya faru da kike tunawa wlh Zeena na canza yanzu ba haka nake ba, tayi shuru bata kulashi ba, Ya matsa kusa da ita, tare da daura hannunshi kan kafadan ta, Zeena kece farin ciki na kece komai nawa, ganin bata kulashi ba ya janyota tare da rungumeta, babu abunda kake ji sai saukar numfashin su, sunyi wajan minti uku a haka, yace Zeena plz ki soni kaman yanda nake sonki, taja da baya tare da fadin afraz you will never change, who give you the right to touch me, let me tell you one thing, niba kalan yan iskan yan matanka din nan bane, so you better respect your self and leave, idonshi ya canza kala, Ya kuma matsawa yana fadin Zeena plz kiyi hakuri ki soni, tace nace bana sonka I hate you, yayi dan murmushi yace Zeena ko kina sona ko baki so na saina aureki kota wani haline, this is a promise, Ya fara tafiya tace afraz ya tsaya ba tare daya waigo ba, tace kace saika aureni koh, to bari kaji dana aureka gwara in mutu, ya waigo tare da matsowa kusa da ita, Ya janyo ta, ganin yanda ya daure fuska yasa ta kasa magana, Ya matsa da bakinshi kusa da nata kaman zaiyi kissing dinta, komai Ya tuna kuma ya fasa ya tureta ya fita, ta fashe da kuka tare da fadin wai mai yake shirin faruwa da ita ne, ta gefe daya ga adeel wanda take mutuwar so, tunanin shi ya hanata komai, ta dayan bangaran kuma afraz wanda yake takura mata, haka ta zauna taci kukanta, ta tashi ta shiga d'akinta.

Tunda wannan abun ya faru bata kara ganin afraz ba, hakan ya mata dadi, shima afraz din a washe garin ranan ya koma Nigeria, domin yaga inya biyema Zeena zai iya rasa ta, iyayenshi sunyi mamakin ganin yanda d'an nasu ya rame lokaci daya, sunyi mai tambayoyi afraz ya taso bai saba da karya ba, komai munin abu indai yayi in suka tambayeshi yana fada musu gaskiya, yace mum Zeena nake so ku nemo min auran ta, dady dinshi yace wannan wani irin sone afraz haka, wannan ne karo na farko daya ma iyayenshi karya tare da boye musu abu, Ya fada musu yanda suka hadu da Zeena amma bai fad'a musu ya mata fyade ba, daddy dinshi yace karka damu yar gidan waye, yace yar gidan senator abubakar daura ce, yace ok shikenan zanje gobe muyi magana dashi, yace thank daddy, Ya tashi yabar wajan cikin murna.

Zeena ta fito daka wanka taji karan wayanta da da sauri ta dauka, taga number ne, ta dannna tare da fadin hello, ta dayan bangaran aka amsa da Zeena, jin muryan tayi ya bugan mata dodon kunne, muryan da take burin ji take son ganin mai muryan, yace Zeena plz kiyi min magana, mai makon magana sai ta fashe da kuka, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, yace Zeena dan Allah ki daina wannan kukan, tace adeel mai yasa ka kirani, yace Zeena na kiraki in fad'a miki har yanzu ina sonki, son da nake miki bazan iya yima ko wace mace ba, plz Zeena ki yarda dani banci amanarki ba, jin haka tace adeel plz ban son wannan maganan, yace shikenan Zeena, amma ina so ki sani ina jiranki har ki gama karatun ki, Zeena ke daya ce macen da nake so kuma nake so in mallaka, kullum da sonki nake kwana nake tashi ta kashe Wayan da sauri, Zeena tayi shuru ta kasa furta ko kallama daya, wai mai yake shirin faruwa ne, Don son adeel tana yi amma mijin AMINIYA TA CE, hmmmm muje zuwa.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to sayyada darling πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
5⃣6⃣to6⃣0⃣

Mahaifin afraz bayan ya shiga d'aki ya dauki waya ya kira mahaifin Zeena, a lokacin mahaifin Zeena yana zaune a bedroom dinshi yana kallon news, yaji karan wayanshi, Ya dauko ganin sunan mai Kiran yasa ya dauka da sauri tare da fadin ranka ya dade barka da dare, mahaifin afraz ya amsa da yauwa, bayan sun gaisa mahaifin afraz yace mai gobe kana gida, Ya amsa da eh ranka ya dade, yace insha Allah gobe zanzo da yamma, mahaifin Zeena yace ranka ya dade lafiya dai koh, yace eh lafiya, mahaifin Zeena yace aida ka bari ni nazo da kaina, yace a'a karka damu zanzo da kaina, yace toh ranka ya dade sai na jika, sukayi sallama, bayan ya kashe Wayan yace lafiya kuwa alhaji umar na sidi yake son gani na, mahaifin afraz yana daya daka cikin manyan mutane a Nigeria, bama Nigeria ba kawai duk Africa, babu inda zaije yace yana son abu ba'ayi mishi ba, baya ga siyasa da yayi shi babban dan kasuwa ne, ranan mahaifin Zeena da tunanin zuwan alh umar na sidi yayi bacci.

Zeena na kwance karar wayanta ne ya tashe ta, ta dauka tare da fadin hello cikin muryan bacci, jin muryan adeel yasa ta watsake, yace Zeena badai ni na tashe ki ba, tace a'a dama yanzu nake son in tashi, jin kaman ta dan sake, yasa yaji dadi, tare da fad'a mata yana so yazo Japan akwai maganan da yake so suyi, tace no adeel plz karka zo ka zauna kawai, yace Zeena kin San yanda nayi missing dinki kuwa? Tayi shuru yaci gaba da fadin da kin San yanda nayi missing dinki da baki cemin haka ba, Zeena na tabbata kema kina kewa na, tayi shuru dai bata kulashi ba, shi daya yake ta maganan shi, yace Zeena plz kimin magana, tace ina jinka, ta rasa mai yasa ta kasa fushi da adeel har take sauraranshi, ganin kaman bata son magana yasa yace gobe yana nan tafe, bai jira mai zata fad'a ba ya kashe wayan, wani farin ciki taji,tare da son ganin adeel, domin itama tana son ganinshi, lokaci daya kuma ta canza fuska, tare da tuna abun da ya faru, adeel kamin nisa yanzu ka auri AMINIYA TA, bazan iya auranka ba, tayi shuru na wajan minti biyar, can tayi tsaki tare da shirin zuwa skul.

Wajan karfe biyar mahaifin afraz yazo gidansu Zeena,tare da wani abokinshi aka saukesu a falon baki, sannan aka cika su da kayan ciye2, bayan sun gaisa cikin girmamawa, mahaifin afraz yace alh abubakar, nazo neman alfarma ne, Ina nema ma d'ana afraz auran yarka Zeena, mahaifin Zeena yace haba ranka ya dade ai kai ka wuce wannan, na bama danka auran Zeena, sukayi godiya sannan abokin mahaifin afraz yace a yanke musu sadaki su biya mahaifin Zeena yace Su bada dubu hamsin, nan da nan yaje mota ya dauko wani akwati da kudi cike a ciki, yace ga wannan 50million ne ni na kara akan sadakin, sukayi godiya sannan mahaifin afraz ya kuma neman alfarma akan yana son a daura auren nan da sati biyu, mahaifin Zeena yace babu matsala, sukayi sallama suka wuce.

A lokacin da dadyn Zeena ya shiga gida, Yama mahaifiyar Zeena din bayani kuma hakan ya mata dadi, domin tana ganin idan tayi aure hakan zai sa ta cire adeel a ranta, sannan tace kar'a fad'ama Zeena din maganan auran, domin karta sama kanta damuwa, tunda ta kusa zuwa in ta dawo sai mu mata bayani, daddyn Zeena ya yarda da shawaran matar tashi.

Adeel ya sauka a kasar Japan, kasancewan yana da address din gidansu Zeena din, Ya nufi gidan amma yayi rashin sa'a tana skul, yace bari yaje ya dawo, hotel ya nuna ya fada toilet yayi wanka, yasa kananan kaya, sannan ya fashe jikinshi da turare, Ya zauna tare da jiran anjima kadan yayi ya koma gidansu Zeena din, sai murmushi yake shi daya.

A lokacin da Zeena ta dawo fatima ta fad'a mata anzo nemanta bata nan, bata damu da ko waye ba, tace ok, ta nufi dakinta tayi wanka, tasa wata doguwan riga, ta dauki littafinta ta nufi bukka, don karatu gobe zasu fara exam, littafin dai yana hannunta kuma inka ganta zaka rantse shi take karantawa, amma tunani take, ganin adeel tayi ta gabanta yana murmushi sai taga kaman gizo, yake mata, tasa hannunta tare da taba fuskanshi, taga bai bace , ta tabbata dai shi dinne, tayi sauri ta cire hannunta, tare da fadin adeel yaushe Kazo? Yayi murmushi tare da fadin tun dazu, ya kura mata ido, yaga ta kara girma da kyau wani sonta ne yake kara shigarshi, itama ta nata ban garan, wani sonshi ne yake kuma shiganta, dukansu sunyi shuru suna kallon Juna, ya katse shurun tare da fadin Zeena kina sona kuwa kaman yanda nake sonki, jin haka yasa ta fashe mishi da kuka, hankalinshi yayi mugun tashi, yace Zeena plz kibar wannan kukan kar ki sani cikin damuwa, tace adeel mai yasa ka gujeni, a lokacin da nake bukatan ka, sannan kuma yanzu ka dawo zaka kara yaudara na, yayi sauri ya rufe mata baki da hannunshi yace Zeena ban yaudareki ba, Zeena kece macen dana fara so, kuma har yanzu banga wacce nake so ba sai ke, Zeena Mysha ce ta rabamu akan selfishness nata nan ya bata labarin yanda sukayi da Mysha, tayi shuru babu abunda take sai hawaye, ta kasa furta komai, ganin haka shima yayi shuru yana kallonta, ganin yanda take kuka bazai iya jure ganin kukan ba, Ya matsa kusa da ita, Ya fara share mata hawayen, tare da fadin plz kibar wannan kukan, jin haka tayi shuru, wani sonshi taji ya kuma karuwa a ranta tare da tausaya mishi, tabbas komai Ya faru laifina ne, inda ban Kawo maganan karatu ba da yanxu munyi aure, da hakan bai faru ba, a yanzu ta yarda bazata iya auran ko wani namiji ba inba adeel ba, domin shi daya take so, shima yana sonta, a ranan Zeena ta sake da adeel kuma tace mishi a shirye take data aureshi, hakan yamai dadi, sannan tace karya sake ya saki Mysha domin tana sonshi kuma komai tayi sonshi yasa tayi hakan, yace babu komai duk abunda tace shi zaiyi, daka karshe yayi mata sallama ya wuce masaukin shi, ranan su duka sun kwana cikin farin ciki.

Maryam obam✍✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to yasmin darling πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
6⃣1⃣to6⃣5⃣

Su Zeena an fara exam, cikin kwanciyan hankali, kullum suna tare da adeel, ji take kaman bata taba shiga wani matsala ba, haka shima ta ban garan adeel din, Ya manta da komai, jira yake ta gama exam su dawo Nigeria tare ayi maganan bikinsu, har zaheer yasan adeel kuma ya yaba da hankalinshi, Zeena ta fito daka lecture ta hango adeel ta wajan wata bishiya ya kura mata ido, harta karaso kusa dashi bai daina kallonta ba, tayi dan murmushi tare da fadin yaushe Kazo, yace tun dazu suka sami waje suka zauna, Ya kuma kafeta da ido, tace adeel lafiya kuwa, yace Zeena tun jiya nake jin wani kala a jikina, tace muje asibiti mana, yace no ba abun asibiti bane, tace toh miye adeel, yace inaji a jikina kaman za'a raba mu, tace adeel wannan wani irin magana ne haka, yace Zeena jikina yana bani haka, ta dan daure fuska tare da fadin sai dai in Kaine zaka gujeni, yace haba Zeena komai zai faru bazan taba gudun kiba, kece farin ciki na, tace toh adeel ka daina wannan tunanin ni taka ce, babu mai raba mu, yace Allah yasa, suka d'an taba fira sannan suka tashi suka wuce.

Anata hidiman bikin Zeena da afraz, ba tare da sanin taba, harta zaheer bai San mai ake shiryawa ba, abda kuma daddy dinsu ya gargadeta akan karta fad'a ma Zeena din tace toh taja bakinta tayi shiru.

A lokacin da dadyn afraz ya fad'a mishi yanda sukayi wani farin ciki ne Ya kamashi tare da kara godema iyayenshi, kuma yana alfahari dasu akan komai yake so suna bashi, tunda yaji wannan labarin bai kara neman Zeena ba, yana ganin ya riga ya gama samun ta, ya rasa wani irin so yake mata, bai taba tunanin zai so mace tace bata sonshi ba sai Zeena, Ya lumshe ido tare da fadin Zeena you are special, zan iya yin komai a kanki Zeena.

Yau Thursday su Zeena an gama exam, ta fito tana murna don gobe zata Nigeria taba dady dinta surprise akan sun dai daita da adeel, kuma a shirye take data aureshi, tayi dan murmushi ta tabbata idan dady dinta yaji wannan labarin zaifi kowa murna, kai tsaye gida ta nufa, tana shiga ta fad'a toilet tayi wanka, ta fito falo ta tarar da zaheer yana kallo tace yaushe ka shigo bros, yace ban dade da shigowa ba, yace ya exam din tayi dan murmushi tare da fadin alhamdlh, yace gobe sai gida, tayi dariya tare da fadin ai wutun ma ba wani mai yawa bane, yace inye hutun wata nawa kikeso a baku, tace kaman 3month yayi dariya tare da fadin Zeena baki da dama, tace goben kaima zaka bimu yace eh tare zamu tafi, fatima itama ta fito kana ganinta kasan tana cikin murna domin ta kosa ta ganta a Nigeria itama, taga yan uwanta da abokan arziki, nan suka zauna suna ta fira gwanin sha'awa,

Adeel ya kira Zeena yace yana gidansu ta wajan bukka, tace tana xuwa, ta tashi da sauri ta dauki dan karamin gyale ta yafa a kanta kasancewan gown ne a jikinta na yan kanti, ta fito ta hango shi a zaune, wani dadi taji tare da kara sonshi ta aiyana a ranta adeel ka hadu, babu macen da zata ganka taji bata sonka, wani kishin shi taji data tuna yana da mata, ta karaso kusa dashi ta zauna ta gefe suna kallon Juna, Ya sakar mata murmushi tare da fadin gobe sai gida koh, ta daga mai kai alaman eh, yace ya exam din, ta amsa da alhamdlh, ya kuma kura mata ido yace Zeena bana gajiya da ganinki, kullum sonki kara karuwa yake a raina, tayi murmushin jin dadi, tace nima haka Kaine mai sani farin ciki, koda ina fushi inna tuna dakai sai inji farin ciki, ya sakar mata ido yana kallonta, tace wannan kallon fah, yace ina mamaki ne Zeena, tace name, yanda kike fad'amin wa innan kalaman da bakin ki, jin haka ta dan rufe fuska tana dariya, sunyi fira sosai daka karshe sukayi sallama akan sai gobe,

A yau juma'a aka daura auren Zeena abubakar da afraz umar na sidi, wajan karfe biyu na rana, daurin auren ya tara manyan mutane sosai, ranan afraz yayi kyautar naira kaman za suyi kuka, domin duk wanda ya gani a masallacin indai mai bukata ne saiya bashi kudi, ranan ji yake kaman an mai bushara da gidan aljanna, mahaifinshi duk yana kula dashi, hakan ba karamin dadi ya mishi ba, na ganin danshi cikin farin ciki, duk wanda suka zo daurin aure sun watse,

Su Zeena sai wajan karfe biyar suka sauka, kowa yaga driver dinshi yana jiranshi adeel ya shiga mota akan sai yazo, suma suka shiga nasu motar, kai tsaye gida suka nufa, Zeena taga gidansu makil da mutane, gabanta ya fadi tace mai yake faruwa, driver na parking ta shiga da sauri tana Kiran ummi abda dady, ga mamakin ta sai ta gansu dukansu, da gudu ta nufi ummi, tace ummi wannan taron fa, ganin bata, bata amsa ba ta nufi dady tace dady wannan taron fah, yayi dariya kije ki huta Zeena kafin muyi magana bata musa ba, ta nufi dakinta, tayi wanka ta fito taga an ajiye mata abinci kala2 a d'akin tayi murmushi ta zauna taci tayi nak, ta kwanta abinta,

A lokacin da adeel yaje gida, yaga Mysha shi harga Allah ya manta da tunda ya tafi bai kirata ba, ta rame tayi duhu, tana ganinshi ta taso da kuka, tana fadin adeel kamin adalci kenan, ka tafi wajan sati biyu amma babu waya, baka San ya nake ba, Ina matsayin matarka, duk sai yaji ta bashi tausayi, bai kuma dace ya mata haka ba, amma saiya dake yace ai bance dole ki zauna ba, yana fadin haka ya haura sama, ta zauna tana ta kuka, d'akinshi ya nufa, Ya fada toilet yayi wanka, ya fito cikin wata shadda dinkin kaftani yayi mishi kyau sosai, sai kamshi ke tashi, yaganta a inda ya barta tana ta aikin kuka, jikin shi yayi sanyi, a gaskiya baya mata adalci matarshi ce, kuma ko babu komai tana da hakki a kanshi, zama yayi ya kira sunanta ta amsa da na'am cikin muryan kuka, yace kinyi abinci ta

Please Login or Register in order to submit comment