Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa da eh, yace Kawo min, wannan ne karo na farko daya taba tambayanta abinci, jiki na bari ta nufa kitchen ta Kawo mishi, farfesun kayan ciki da fried couscous, da coconut juice, Ya zauna yaci sannan yace mata ya gode, hakan ya mata dadi sosai, Ya kuma Kiran sunanta ta amsa, yayi shuru can yace mata inaso inyi miki magana tace toh inaji, yace ina so in kara aure, gabanta ya fadi tare da tausayin kanta, ta daure dakyar tace wa zaka aura, yace Zeena ta Mike tsaye tare da fadin Zeena, yace yes ta fashe da kuka tare da rokan shi akan ya auro ko wacece, amma banda Zeena, yayi dan murmushi tare da fadin bazan iya kallon ko wace mace ba inba Zeena ba, ita nake so, itace farin ciki na, yana fadan haka ya fita, ta zauna tana tausayin kanta, tabbas idan adeel ya auri Zeena bazata iya zama a gidan ba, duk irin son da take mishi .

Zeena sai wajan 7 ta farka a lokacin dady dinta ya shigo d'akin, yace Zeena bacci kikayi bayan kin San babu kyau baccin bayan la'asar, tace daddy wlh gajiya ne yasa nayi, Ya nemi waje ya zauna akan wata kujera dake d'akin, tayi murmushi tace daddy wai taron miye akeyi haka, yace Zeena ta amsa da na'am ina so in fad'a miki wani magana, tace toh daddy nima zan fad'a Maka wani magana wanda zai saka farin ciki, yayi dariya tare da fadin mai nene Zeena, tace daddy ka fadamin kafin sai in gaya ma, yace toh Zeena, yayi shuru na wani lokaci can yace Zeena ina so ki zama mai biyayya, sannan ki zama y'a mai bin umarnin iyayenta, tayi dariya tace haba daddy baka taba sani abu naki yima ba, daddy wlh komai kake so indai bai sabama shari'a ba zan yima shi, yaji dadi tare da samun karfin giwa, yace Zeena wa innan mutanan da kike gani sun taru ba dan kowa suka taru ba sai dan ke, taji gabanta ya fad'i, tace daddy dan ni kuma, yace eh, a yau aka daura miki aure, inaso kimin biyayya duk da baki San da auren ba sai yanzu, ta Mike da sauri tare da dafa kirjinta tace aure, ta fara yin baya kaman zata fad'i.

Maryam obam ✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to yasmin darling πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
6⃣5⃣to7⃣0⃣

Daddy yayi sauri ya riko ta, tare da zaunar da ita akan gado, yace Zeena baki son auren? Tayi shiru babu abunda take sai hawaye, tabbas bana son wannan auren amma taya zan iya kallon daddy ince mai bana so, daddy ya katse ta tare da fadin Zeena kiyi magana nasan ba zaki bani kunya ba, tace daddy Kaine mahaifina baza ka, zaba min abunda zai cutar dani ba, jin haka yace Allah ya miki albarka, yana ta mata godiya, tare da fadin yana alfahari da ita, yace ta tashi ta shirya yanzu za'azo daukanta, ta amsa da toh, sannan ya fita, kuka ta saki mai karfi yanzu na rasa adeel a karo na biyu, a lokacin da muka dai daita, mai yasa haka ya faru dani, jin kaman karar bude kofan d'akin yasa ta goge hawayen fuskanta, ummi ce ta shigo ita da abda, ummi ta zauna ta gefenta tare da fadin Zeena naji dadi da kika yarda da wannan auren kika mana biyayya, yanda kika mana biyayya kema Allah ya baki masu yi miki, ta amsa da ameen, sannan tace abda ta taya ta shiryawa don anzo daukanta, jin haka hawayen da take boyewa suka zubo mata, yanzu wa aka aura mawa ni, Ya zanyi da son adeel, abda tace muje ki shirya, bata musa ba, ta shiga toilet tayi alwala tazo tayi sallah bayan ta idar abda ta taimaka mata ta shirya, ummi da daddy suka kuma shigowa suka mata nasiha akan tabi mijinta tayi mishi biyayya, domin aljannarta yana karkashin kafan mijinta, komai naki yanzu ya koma kan mijinki a yanzu Muda muke iyayenki bamu da iko dake, sai mijinki dan haka kimai biyayya yi nayi bari na bari, babu abunda take sai kuka, ummi ta kama hannunta suka fita falo, a nan yan daukan amarya suka amsheta da yan uwan ummi din akai mota da ita, motocin daukan amarya sun kai hamsin, Zeena kuka take kaman ranta zai fita, abda nata faman rarrashi, hankalinta bai tashi ba sai da taga an kunna mota an fara tafiya, har suka karasa gidan da za'a kaita tana Manne jikin abda, maitama aka kaita wani katoton gida ne suka shiga, gidan ya hadu fadan haduwan gidan ma bata lokaci ne, wata kanwar ummi ta zagayo tace ta sauka da kafar dama tare da bismillah, hakan ko tayi suka shiga cikin gidan, akai sama da ita, cikin wani d'aki aka kaita wanda yaji kayan alatu, wanda suka Kawo amarya suka duba gidan tare da San barka, aka fara shirin tafiya anan hankalin Zeena ya kuma tashi ganin harda abda za'a wuce dakyar ta saki abda suka wuce, aka barta ita daya, tana ta aikin kuka, kanta ya fara ciwo dan taci kuka ta kwanta bata dade ba bacci ya dauke ta.

Wajan karfe goma afraz ya shigo gidan shida wasu abokanshi, yace Su zauna a falo yana zuwa kai tsaye sama ya haura, Ya nufi dakinta ya bude yaga tana bacci, Ya matsa kusa da ita yaga fuskanta ya kumbura da alaman taci kuka, duk sai yaji ta bashi tausayi, ya fita ya kashe mata wutan d'akin, yace ma abokanshi tana bacci bazai kuma iya tashin ta ba, sukace ai dole ma ka tashe ta, yace haba ai tunda ta kwanta sai dai wata rana kun hadu, daya daka cikin abokan mai suna jabir yace inma mu anki taso mana ita ai kai dole ka tashe ta, suka saka dariya sannan ya rakasu suka wuce, bayan ya dawo dakinshi ya nufa ya kwanta amma kwata2 ya kasa bacci, sai tunanin Zeena yake,

Zeena ta farka wajan karfe dayan dare jikinta ya rufeta da zazzabi, ta tashi ta nufi toilet, tayi wanka amma jikin dai sai zafi yake mata, ta kwanta akan carpet din d'akin ta dauko blanket ta rufe kanta tana rawan sanyi,ga yunwa da take ji.

Afraz dai shima ya kasa bacci ya tashi ya nufi d'akin Zeena din ya kunna wutan d'akin ya hangota a kasa tana rawan sanyi, da sauri ya nufeta yace Zeena maike damun ki, jin kaman muryan afraz yasa ta dago da kanta tace afraz, Kaine wanda ka aure ni, bai bata amsa ba, ya dauketa cak ya daura ta kan gadon d'akin sannan yaje ya kashe a.c din d'akin, fita yayi a d'akin Jim kadan ya dawo da cup a hannunshi tea ne a ciki da paracetamol, ya bata taki amsa, ganin haka yasa ya kafa mata kofin a baki, ta fara sha, duka ta shanye sannan ya bata paracetamol tasha, sannan ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauke ta, shima a gefenta ya kwanta yana kallonta tare da kara godema Allah daya mallaka mishi Zeena a matsayin mata, ranan afraz kasa bacci yayi, bini2 ya duba Zeena yaga ya take ciki, can yaga jikinta ya fara zufa ya cire mata blanket din, sai wajan karfe biyar ta farka a lokacin afraz ya nufi masallaci, itama toilet ta fada tayi alwala tazo tayi sallah, bayan ta idar ta zauna akan dadduma din, tana tunani yanzu afraz shine mijin da daddy ya zaba min, zan iya kallon afraz a matsayin miji kuwa, wani haushin afraz din taji ya kamata, a lokacin afraz ya bude kofan ya shigo ya ganta kan dadduma yaje kusa da ita ya kira sunanta Zeena bata amsa ba kuma bata d'ago ba, hakan bai dameshi ba yaci gaba da magana ya jikin naki, tace ina ruwanka da jiki na, Malam ka fita ka barni dan Allah, jin haka ya fita dakin shi ya nufa, Ya kwanta, dan jiya baiyi bacci ba.

Tunda adeel ya fita jiya da daddare yaje gidansu wajan alhaji amma yayi rashin sa'a baya nan, sai mahaifiyar shi ya tarar da kannan shi, suka d'an taba fira, mamanshi ta tambayeshi Mysha yace tana gida, tace in gaidaku tace muna amsawa rannan tazo ta wuni a nan ai, yace eyya ya tashi sukayi sallama,

A lokacin daya koma gida yaga Mysha a falo tana gyangyadi, ya matsa kusa da ita wato da bana nan kullum fita kike koh, tayi shuru ya daka mata tsawa bada ke nake ba, tace babu inda naje gidanku kawai naje da gidanmu, yace uban wa yace ki fita, tace kayi hakuri, yace daka yau in kika kuma fita ban sani ba saina bata miki rai, Ya haura sama,.

Wayan shi ya dauka ya kira Zeena amma a kashe hankalinshi duk ya tashi, ya tuna yana da number din zaheer ya kira bugu daya yayi ya dauka, bayan sun gaisa yace mai yakira Zeena number dinta yaki shiga, zaheer yace eh Zeena tana gidanta, yace ban gane ba, zaheer ya fadama adeel abunda ya faru, sakin Wayan yayi tare da zama a kasa, yanzu Zeena tayi aure, kai wasa zaheer yake min, hakan bazai faru ba, Zeena tawa ce, he is joking daukan key din motanshi yayi ya nufi gidansu Zeena din, amma abunda idonshi ya gani ya tabbatar mishi da haka din, ganin motoci yayi da mutane birjik a kofar gidan, Ya tambayi wani a kofar gidan yace mai yar sanata ce take aure yace wacce a ciki, mutumin yace Zeena, hankalin adeel ba karamin tashi yayi ba, ya shiga motarshi yana tuki kwata2 baya ganin gabanshi, bai ma San mai yake yiba, shidai ya farka ya ganshi a asibiti jikin shi duk ansa flasta a jikinshi, yaga alhaji da mamanshi, ga Mysha dake gefe tana ta kuka, alhaji yace sannu adeel ya jikin ya amsa da sauki, kwanan shi biyar aka sallame shi, a asibitin, Allah ya taimake shi babu karaya, sai dai bugawa da yayi a bayan shi.

Zeena tana dakinta a kwance afraz ya shigo d'akin ta daure fuska ya matso kusa da ita ta tashi da sauri ya janyo ta, ta fada kanshi, yace ina zaki, tace ka sake min hannu, yayi dan murmushi tare da kuma janyo ta, suka had'a ido tayi sauri tasa kanta a kasa, yasa hannunshi kan kirjinta ya fara wasa da wajan, ganin haka yasa ta fara kuka, Ya cire hannun shi tare da fadin Zeena plz ki bar wannan kukan, ganin haka yasa ta tashi da sauri tayi wajan toilet, tace afraz I hate you bazan taba sonka ba tana fadin haka tayi sauri ta shige toilet, yayi murmushi ya fita tare da fadin zanyi maganin ki.

Maryam obam ✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to basma darling πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
7⃣0⃣to7⃣5⃣

Jin karan kofan d'akin yasa ta fito, tare da rufe kofan ta da key, tayi tsaki yanzu wannan ne miji na, ai wlh ba zaka taba samun abunda kake soba a waje na.

Afraz tunda ya fita daga d'akin ta, gidan ya bari gaba daya, bai dawo ba sai wajan karfe tara, a lokacin tana falon kasa tana kallo har ya shigo bata sani ba, ji tayi an rukota ta baya, ta saki ihu, duk ta tsorata, ta bashi dariya amma saiya dake, ta fara kokarin kwace kanta daka rikon daya mata, ya sake ta, ganin haka yasa ta tashi zata gudu ya kuma kamo ta, tace ka sake ni, yai kaman bai jita ba, ya kuma janyo ta, Ya zaunar da ita kan kafanshi, ta daure fuska, ganin shima ya tamke fuska yasa ta kasa cewa komai, yace kinci abinci, ta daga mai kai alaman eh, ya janyo wani leda, ya bata, bata musa ba ta amsa, ta tashi daga jikinshi tayi sauri tayi sama, ya bita da kallo harta bace sannan ya kauda kanshi, yayi murmushi ya rasa wani irin so yake ma Zeena.

Bayan taje d'aki ta bude ledan taga kaza ne da ice cream da abinci, ta bude kazan taci da ice cream, tayi nak, ta fad'a toilet tayi wanka ta fito tana shafa mai, a lokacin ya shigo d'akin ya kura mata ido, ta waiga ta ganshi ta tashi da sauri tare da fadin miye na shigo min d'aki babu neman izini, yayi dan murmushi tare da fadin nida d'akin matata saina nemi izini, ganin yana matsowa yasa tayi shuru, tana matsawa baya, har ta hade da bango, shima ya karasa ya manneta, suna shakan numfashin juna ganin yanda yake kallonta yasa tayi kasa dakai, wani nugun sha'awanta yake ji, wanda bazai iya hakuri ba a wannan lokacin, daukanta yayi cak, ganin haka ta fara wintsil2 amma ko a jikinshi dakinshi yayi da ita, ya ajiyeta a kan gadon d'akin sannan ya rufe kofan, ganin haka ta fara kuka tare da fadin dan Allah afraz karka min komai kayi hakuri, yace Zeena nifa mijinki ne, kuma ina bukatanki, tace bana so bana sonka dan Allah karka min komai, yace bakya sona koh, tace eh, yace owk shikenan bari in kira daddy dinki saiki fad'a mishi ni kuma saina sauwake miki, jin haka tace karka had'a ni da iyayena bana so, yace toh ki bani hakki na, tun daka lokacin bata kuma magana ba, nima ganin haka na fita daka d'akin, na koma da asuba naga Zeena tana ta kuka shi kuma afraz yana ta rarrashi yana bata hakuri, dakyar ya shawo kanta tayi shuru ya kaita toilet yace ta shiga tayi wanka, ganin kaman bata da niyan shiga ya dauketa yasa ta cikin ruwan zafi, ya kura mata ido wani sonta yake kara shiganshi, ganin kallon da yake mata yasa ta kuma sakin kuka, duk ya rud'e yana tambayanta mai nene, tace ka fita, yayi dariya ya tashi ya fita.

Adeel ya yanke hukuncin komawa China da zama domin bazai iya zama a nja ba, yaga Zeena tare da wani mijin, tunda ya tabbatar tayi aure komai nashi ya canza abu kadan, yaita fad'a akai, ga saurin fushi da yake yi yanzu wanda duk bayayi da, itama Mysha ta samu labarin Zeena tayi aure hakan ya mata dadi domin tana ganin yanzu zata samu mijinta, tayi alkawarin ko zuciyan dutse gareshi saiya sota, wannan kenan.

Zeena inta tuna abun daya faru tsakaninta da afraz sai tai ta kuka, yanzu ya rabata da adeel kenan, yayi nasara akan ta, ta tuna lokacin daya mata alkawari saiya mallake ta, gashi yanzu ya sameta, wani takaici taji tare da bakin ciki, tace afraz zaka iya samu na, amma ba zuciya na ba, bazan taba sonka ba,

Afraz tunda ya sami Zeena duk ya daina harkan mata, domin duk yawon barikin da yayi bai hadu da wacce takai Zeena ba, tunda ya sami Zeena yanzu bashi da wani buri illa ace Zeena ta fara sonshi, shine abunda yake fata.

Yau watan Zeena uku da aure, tana zaune a falo, afraz ya fito, ta kalleshi tace ina son magana dakai, yace inaji, tace inaso inje gida yau yace ba yanzu zaki fara fita ba, ta dan marairaice tace plz, yace in kina so kije gida sai kin min kiss a baki, jin haka yasa ta daure fuska tare da kau dakai gefe, yace ok ni na fita ganin zai fita yasa ta tashi da sauri ta shiga gabanshi, yaso yayi dariya yanda yaga tazo da gudu amma saiya dake, ta rufe idon ta, yace ai bani zan miki ba, ke zaki min, ta dan turo baki, ganin yana kallonta tace toh ka daina kallo na, Yayi dariya yace in ban kalleki ba taya zaki min, tayi shuru tana kallon kasa yace ni zan fita in ba zakiyi ba, da sauri tayi mishi kiss din sannan ta ruga da gudu, Ya bita da kallo yana dariya, ya koma ya zauna a falo din, Jim kadan ta fito cikin wani material mai kalan c green ya mata kyau sosai, yace Zeena yanzu haka zaki fita babu mayafi, tace toh ba'a mota bane, yace koma a miye ban yadda da hakan ba, ki koma kije kisa hijab muje, kaman za tayi kuka ta koma ta dauko hijab din, yace kinga yanda kikayi kyau kuwa, ta turo baki, suka fita, wani super market suka je, yace suje tayi musu tsaraba suka shiga ta dauka abubuwan d zata dauka ya biya suka wuce, bayan ya sauketa yace wajan 5 zaizo daukanta tace toh, ta shige, masu gadin gidan yasa suka shigar da kayan tsaraban,Ya wuce.

Da gudu ta shiga cikin gidan ta fada jikin ummi dake zaune akan kujera tana kallo, ummi tace miye haka karki karyani, tayi dariya tace kai ummi bakiyi missing dina ba, tace banyi ba, ta turo baki tare da fadin bari daddy yazo dama shine yake sona, jin haka ummi tayi dariya abda ta fito da gudu sukayi hugging juna, tace wow zee zee dina kinga yanda kika kara kyau da haske, Zeena tayi dariya tare da fadin haba, abda tace dagaske, tun shigowan Zeena ummi ta lura da hakan, tana zargin kaman ciki take dashi, nan suka zauna suna ta fira, har daddy ya dawo shida zaheer, shima daddy yaji dadin yanda yaga yar tashi cikin kwanciyan hankali, wanda ada yake farga akan idan Zeena tayi aure, babu wanda yasan fyade aka mata, amma a yau ya cire ganin yar tashi cikin jin dadi, zaheer yace ya maganan skul dinki tace ina yi ta online, yace ok sai a kara bada himma, tace toh bros,sai bayan magrib afraz yazo daukan Zeena, a lokacin ya shigo suka gaisa da mahaifin Zeena din da ummi, mahaifin Zeena nata sa mishi albarka, ummi tace ma Zeena tazo zata mata magana kafin su wuce, tace toh ta tashi suka nufi d'akin ummi din, ummi tace Zeena ciki kike dashi, tace a'a ummi banda komai, jin haka ummi tabar maganan, tace gaskiya kinyi dacen miji, ji yanda yake kula dake sosai ki rike mijinki dakyau, ada ina fargaban idan kikayi aure duk mijin da kika aura bazai ga darajarki ba, tace ummi kaman ya, nan ummi ta fad'a mata abun daya faru, ta tashi da sauri tace fyade tare da fadin afraz.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my fancy habiba πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
7⃣5⃣to8⃣0⃣

Ummi tace ki zauna Zeena amma ina tayi hanyan waje, ganin haka itama ummin ta rufa mata baya, falo ta nufa taga daddy shi daya, yace Zeena kije mijinki yana jiranki tun dazu, dan Allah Zeena ki zauna da mijinki lafiya, yaron yana da kirki, wani hawaye ne Ya zubo mata na takaici yanxu idan daddy yasan afraz shine wanda ya mata fyade ya zai dauka abun, tace toh daddy nagode, tayi waje ta sameshi a mota yana jiran ta, da murmushi yace sai yanzu kika fito, ganin tayi banza dashi yasa ya lura da hawayen da takeyi, hankalinshi ya tashi a duniya babu abun daya tsana kaman yaga Zeena tana kuka, yace Zeena mai nene, mai akayi miki, waya taba ki, ganin bata da niyan yi mishi magana yasa yaja motar, tuki yake amma zuciyan shi yana tafarfasa, gani yake kaman an mata wani Abu ne, har suka karasa gida, suna shiga ta fita da sauri ganin haka shima ya bita, yana fadin Zeena Zeena amma ko ta waigo ta kalleshi harta shiga d'akinta, Ya bita shima ya kamo mata hannu yana fadin haba Zeena mai ya faru kike ta kuka, plz ki fad'a min, ta waigo cikin kuka tace afraz wlh ka cuceni ka cuci iyayena sun daukeka mutumin kirki amma basu San ko kai waye ba, na tsaneka bana son ganinka, jin haka duk ya rude yace Zeena maiya faru wai don Allah, tace afraz ka rabani da budurcina kayi min fyade, jin haka yasa gaba daya ya dauke wuta, har d'aci yaji bakinshi yana mishi, ganin yana yinshi yasa ta tabbatar dashi dinne, dakyar ya iya cewa Zeena kiyi hakuri, wlh nayi nadama akan abunda nayi miki, tace afraz wlh ba zaka taba canzawa ba, ka cuceni duk da abun daka aikata sai da kaje ka nemi aurena domin wani manufa naka, yace Zeena wlh na aureki ne tsakani da Allah, Zeena nayi miki fyade ne dan in rama wulakancin da kika min a gaban mutane, amma bayan haka sai Allah ya jarabceni da sonki, Zeena wlh son da nake miki na gaskiya ne bazan iya rayuwa ba tare dake ba, tace afraz ban taba sonka ba bazan kuma taba sonka ba, kana da son kanka ka, kai da kanka kasan ban dace dakai ba, rayuwa na ba kalan naka bane, na tsare kaina amma saida ka tozartani, bazan taba yafe Maka ba, yace Zeena kiyi hakuri nima nasan ban kyauta ba, koda son da nake miki aka barni, nasan wannan babban sakayya ne, ta toshe kunnenta, tace dan Allah ka fita ka barni, yace zan fita Zeena amma dan Allah kibar wannan kukan tace ina ruwanka dani, jin haka ya kama hanyar fita har yazo bakin kofa ta kira sunan shi afraz, Ya waigo tace bazan iya zama dakai ba zan fad'ama daddyna abun da kamin na tabbata bazai barni in zauna dakai ba, jin haka ya matso yana fadin Zeena ki tausayamin ina sonki inna rasa ki, banga amfanin rayuwa na ba, wani jiri takeji yake dibanta tace afraz wlh ka.... Ta fad'i kan gadon d'akin da sauri ya nufeta yana fadin Zeena Zeena duk ya rude ya rasa abun yi, Ya dauketa cak ya nufi waje da ita, cikin mota yasa ta, kai tsaye asibiti ya nufa da ita, aka shigar da ita cikin emergency room,

nan da nan likitoci suka tsaya a kanta Ana ta aune2, afraz ya kasa tsaye ya kasa zaune kanshi keta sara mai, duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali, Jim kadan Dr din ya fito yace afraz ya sameshi a office, bayan yaje office din Dr din yace mai congratulations your wife is pregnant, afraz cikin murna yace what ciki, you mean Zeena tana da ciki, dr yace yes harna wata biyu, yace zan iya ganinta Dr yace ka barta ta huta, kuma sannan ku daina tasar mata da hankali yanzu jininta ya hau, kasan mace mai ciki bata son damuwa, afraz yace insha Allah, Ya fito sai a sannan ya samu nutsuwa, abda ya kira ya fad'a mata Zeena tana asibiti an kwantar da ita, ta rude tare da fadin maiya sameta, yace karta damu ciki take dashi da murna ta kashe Wayan ta nufi d'akin ummi ta fada mata, ummi tayi dariya tare da fadin ai dama na sani, taje ta fad'a ma daddy yace toh su shirya sai suje, ummi tace in sunje ita zata kwana da ita, daddy yace babu damuwa, hakan ko akayi suka nufi asibitin sun tarar da afraz a reception, ya nuna musu d'akin da aka kaita, suka shiga, kwata2 shi ya kasa shiga d'akin domin a yanzu kunya had'a ido yake da Zeena, koda suka shiga tana bacci bata farka ba, dady da abda suka fito zasu wuce afraz ya raka su, sannan ya dawo dakyar ya daure ya shiga, ganin bata farka ba yayi ajiyan zuciya, ummi tace afraz kaje gida ka huta, ya amsa da toh sannan ya fita,.

Sai wajan karfe biyun dare ta farka taganta a gadon asibiti, ga ummi kuma a gefe tana sallah, abubuwan daya faru suka fara dawo mata, jin muryan ummi tayi tana fadin kin farka Zeena sannu, ta amsa da yauwa, ummi ta had'a mata tea amma tace bata sha, ummi tace ai kodan abunda ke cikin ki kyasha tace ummi ciki na kuma, tace eh tunda yanzu bake daya bace, a nan ne ta gane inda ummi ta dosa, tace ciki nake dashi yanzu cikin afraz a jikina, ummi ta mika mata kofin ta amsa tasha.

Afraz shima daya

Please Login or Register in order to submit comment