Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

je gida kasa baccin yayi yana fargaban kar Zeena ta fad'a ma iyayenta, ta gefe daya kuma yana farin cikin zai samu d'a, Ya janyo wayanshi ya kira mum dinshi har sau biyu ba'a dauka ba, Ana ukun ne ta dauka tace afraz lafiya kuwa, yace mum Zeena nada ciki, cikin murna tace wow tana ina, yace tana asibiti, tace gobe zata ita da daddy dinshi, mum din afraz taji dadin wannan labarin zata samu jika, tana son yara sai kuma Allah ya bata kwaya d'aya,

Washe gari afraz tun wajan karfe 7 ya nufi asibiti amma duk sammakon shi, daya je ya tarar da mum dinshi, tana kusa da Zeena tana bata abinci, suka hada ido da Zeena din ta sakar mai Harara, sannan tayi kasa da kanta, yace ya jikin ta amsa da sauki, sannan ya gaida ummi ta amsa cikin fara'a, yace mum ina daddy tace anjima zai zo, mum din afraz tace ma ummi taje gida ta huta zata zauna da Zeena din, babu yanda ummi ta iya dole ta wuce driver din mum din afraz ya kaita gida,..

Kwanan Zeena uku aka sallameta, mum din afraz tace gidanta zata tafi da Zeena afraz bai so hakan ba, amma dole ya hakura, aka wuce da Zeena din, Kwanan ta biyu gidan mum dinshi shima yace ya dawo gidan, yana tsoran kwana shi daya, mum ta Harare shi, tace toh da bakai daya kake kwana ba, yayi dariya tare da Sosa kai, afraz shima ya tare a d'akinshi na gidan, Zeena ta lura da yanda afraz yake zumudi akan cikin, hakan ya mata dadi don tana ganin ta sami hanyan da zata Rama abun daya mata, idan suna zaune mum ta Kawo abinci sai taki ci, tace ta koshi ta lura da hakan yana bata mishi rai, amma idan baya wajan tana ci,

Satin Zeena biyu gidansu afraz, Ya matsa ma mum dinshi akan zasu koma gidansu, dakyar ta yarda aka samar ma Zeena wata yar dattijuwa,mai suna jamila don ta dinga kula da ita.

Tunda suka dawo bata sakar ma afraz, hakan bai dameshi ba, shi abun daya dameshi yanda bata son cin abinci, yana zaune a falo jameela ta haura sama da abinci, sai gata ta sauko dashi, yace wannan ba abincin Zeena bane tace eh tace bata ci, ranshi ya baci yace mai taci, jameela tace babu abunda taci, Ya amsa abincin ya haura sama rai a bace, tana zaune akan gado tana game a wayanta, Ya shigo cikin fushi ya fisge Wayan tare da mika mata abincin, yace Zeena wannan wani irin abune ni na miki laifi a kaina zaki rama ba akan yaro na ba, wanda bai San komai ba, zan iya juran komai amma bazan jura wannan ba, ko kallo bai isheta ba, yace Zeena ki amsa wannan abincin kici, taki amsa babu yanda baiyi da ita ba, amma taki amsa, ganin haka ya fita rai a bace Jim kadan sai gashi da ummi, ummi tama Zeena ta tas, tace da badan kina da ciki ba wlh dazai nayi mugun bata miki, babu shiri ta dauki abincin taci, ummi tace ma afraz ai duk shine yake mata wasa sai yasa take iskanci, ummi ta wuce, afraz ya dawo tana ganin shi ta saki kuka, nan ya zauna yana ta rarrashi.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my fancy habiba πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
8⃣0⃣to8⃣5⃣

Adeel yana kwance a bedroom dinshi, Mysha ta shigo da plate dauke da kayan fruit a ciki, ta ajiye mai a gefe, tace adeel ka tashi kaci, ya amsa da toh, ya tashi ya faraci ita kuma ta koma gefe tana kallonshi tana murmushi, ci kawai yake amma yana tunanin Zeena ya rasa mai yasa kullum son Zeena yake kara karuwa a ranshi, duk yanda yayi kokarin ya cireta a ranshi amma abun yaki, wani zubin har tausayin Mysha yake yanda take bashi kulawa sosai amma bai taba jin sonta ba, tunda suka zo China ya dan sakar mata, domin yana tsoran kar Allah ya kamashi da hakkin ta, itama kanta tasan ba sonta yake ba, tasan Zeena yake so, sai yasa har gobe take jin haushin Zeena, kuma take kishi da ita.

Afraz tunda Zeena ta sami ciki kullum Ana gida Ana kula da ita, baya zuwa ko ina, daka tayi motsi kadan yace miye, ganin haka yasa da gangan ma sai tayi abu, shi kuma sai ya rude yaita tambayanta mai nene, mai kike so, tace wannan tace wancan sai ya Kawo tace bashi ba, ga abunda take so, haka zai koma ya nemo mata, inya Kawo kuma tace ta koshi, haka kullum suke,

Zeena tana kwance a d'aki, tana tunanin yanda zata Japan, tana tunanin dakyar afraz ya barta, jin karan bude kofan da yayi ne yasa ta rufe ido kaman mai bacci, ya zauna akan gadon kusa da ita, yasa hannunshi a bakinta yana wasa dashi, ta dan bude ido daya, suka had'a ido yayi dariya tare da fadin har kin tashi, ta dan turo baki tare da fadin mutum yana baccin shi, Kazo kana damu na, yayi dariya tare da fadin ai ba zaki iya bacci ba in ina kusa, ta daure fuska tare da turo baki, yayi dariya yace idan kina fushi kinfi kyau, ya Mike bari inje in dawo, tace afraz ya amsa da na'am tace exam din mu a Japan kasan dole inje, yayi shuru can yace bari in dawo sai muyi maganan, tace toh har ya kusa fita tace ina zaka, da mamaki yake kallonta wannan ne karo na farko data taba tambayan shi ina zashi, hakan ya mishi dadi yace zani wajan budurwana ne, abun ya bata mata rai amma sai ta dan dake, duk yanda ta dake saida fushin ya fito, yayi dariya yace ashe Ana sona, ta sakar mishi Harara, ya fita yana dariya,

Tunda afraz ya fita ta kasa zaune ta kasa tsaye yanzu afraz dagaske tad'i zaije, wani bakin ciki taji ya taso mata, tayi tsaki inma yaje tadin ni ina ruwana, wata zuciyar tace da ruwanki mana mijinki nefa, ta dauki wayanta ta kira shi, bai dauka ba, ranta ya baci ta kuma kira bai dauka ba, ta zauna tana huci, ya bude kofan d'akin ya shigo ta sakar mai harara, yace bakiyi bacci ba, wani haushi ya kamata ya zauna a kusa da ita tare da fadin ance in gaidaki, ta daure fuska tace ka fitar min a d'aki, yace haba Zeena daka fadan sako ki bari in baki labarin abunda ya faru jin haka yasa ta fara mishi kuka, yace Zeena kin San ban San wannan kukan naki plz kiyi shuru, ya janyo ta ya kwantar da ita kan kirjinshi, yace Zeena ke bakya sona dan nace naje tadi shine kike kuka, ta kuma sakin kukan ai dole kaje tadi tunda ni ka cuceni kamin ciki shi yasa kake min haka, yaso yayi dariya amma saiya dake, yace haba Zeena ba haka bane so nake in Kawo miki wacce zata dinga taya ki aiki, tace bana so ai inada jamila, inma mutum daya yayi kadan ko masu aiki nawa ne ummi zata iya Kawo min, yayi dan murmushi najin dadi ya tabbata yanzu Zeena ta fara sonshi tunda har ta fara kishin shi, yace ni ban cika son masu aiki ba kinga idan ko matata ce zata fi kula dake, a matsayinki na yayarta, tace Allah ya kiyaye in zama yayarta taje ta nemi yayarta bani ba, ta tashi daka kan kirjin nashi cikin fushi, yace come on Zeena ina zaki kin San ban San fushin ki, tayi banza dashi, ganin haka yace kin San banso inga kina damuwa kar kisa babyna shima cikin damuwa, tace wato wannan bata ni yake ba, ta baby dinshi yake ba, ta kwanta ta baya tare da juya mishi baya, abun ya bashi dariya shima ya kwanta ta gefenta,.

Zeena yanzu indai taga afraz ya fita toh haka zata zauna cikin fushi da kunci, taita tunanin ya fita tad'i ne, shi kuma afraz din yana mata hakan ne don yaga ko tana sonshi, ya fito cikin kananan kaya ya mishi kyau yana ta kamshi, ya kalleta yace Zeena nayi kyau kuwa, ta kauda kai gefe, yayi dariya tare da fadin plz ki fad'amin in banyi kyau ba, in canza kaya kar inje tad'i taki fitowa, tayi tsaki tare da tashi ta haura sama ya bita da kallo yana dariya, Jim kadan sai gata ta fito dauke da key din mota a hannunta, yace ina zaki tayi banza dashi, ya tare ta, ta saki kuka tace ni ka matsa min in wuce gidan mu, yace haba Zeena akan wani dalili zaki gida, jin haka tayi shuru ya kuma tambayanta tayi shuru, ya kamo mata hannu yace zo muje na fasa fitan, jin haka yasa taji dadi harta yarda suka koma ciki.

Adeel yana office amma duk ya kasa komai, yana tunanin Zeena wanda ya zaman mishi aiki kullum, ya lumshe ido tare da fadin Zeena Allah ya jarabce ni da sonki, na rasa yanda zanyi in cireki a raina, na kasa yarda da na rasa ki, kullum zuciya na tana yaudara na, akan ban rasa ki ba, karan wayanshi ne ya katse shi, ya dauka yaga Mysha ce, yayi dan tsaki sannan ya dauka, tace adeel yaushe zaka dawo ina so muje hospital inga Dr, yace anjima tace toh sai Kazo bai bata amsa ba ya kashe Wayan,.

Afraz yace ma Zeena ta shirya suje Japan din,ta hada kayanta sukaje suka ma kowa sallama, washe gari suka cala harda jameela, wani gida suka sauka, gidan duk da bashi da girma sosai amma ya hadu, afraz yana ba Zeena kulawa sosai, ita da kanta yanzu ta yarda tana son afraz, amma ta kasa nuna mishi, bata san ya Riga ya ganota ba, satinsu biyu suka dawo Nigeria, afraz yayi siyayyan kayan yara sosai na mata da maza, d'aki daya aka ware aka shirya komai yasa ansa na mace dana miji, yace duk wanda aka haifa ga kayanshi nan.

Cikin Zeena yakai wata takwas, amma inka ganta zaka ce haiyuwa yau ko gobe ne, don cikin yayi girma sosai, afraz yace in kika haifi mace sunanki zan sa Zeena, tayi dariya tace saboda me, yace Zeena saboda ina sonki, kullum sonki kara karuwa yake a raina, tayi dan murmushin jin dadi, yace amma ni har yanzu ba'a sona, ta dan turo baki suka hada ido tayi sauri ta kawar da kanta gefe, yayi dariya yace idan namiji kika haifa sunan wa zaki sa, tace ka bari saina haiyu sai in fad'ama, yace shikenan Allah ya kaimu wannan ranan Zeena, ji nake kaman yanzu inga kin haiyu, ki haifar min mace mai kama dake, tayi dariya tace in namiji ne kuma yayi kama dakai, ya kalleta yace Zeena kina son ki haifa mai kama dani tace eh, a ranta tace afraz kana da kyau, inna haifa mai kama dakai ba karamin kyau zaiyi ba, nan suka zauna suna ta fira cikin so da kauna, aka kira afraz a waya ya dauka tare da fadin gani nan zuwa, bayan ya kashe yace Zeena bari inje in dawo, tace ina zaka yace wasu kaya dana bada oder dinsu aka Kawo, tace daka bari gobe mana afraz yace bazan dade ba ta dan turo baki, yayi dariya tare da fadin Zeena say you love me, ta turo baki yayi dariya sannan ya fita, ita dai bata so wannan fitar ba, dan yanzu bata son afraz yana nisa da ita.

Tunda afraz ya fita har wajan karfe goma bai dawo ba, duk ta rud'e, ta kirashi baya shiga, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ta fito falo ta zauna, taji ana buga kofan falo din da sauri ta nufi falo din tare da fadin sai yanzu ka dawo koh, amma abunda ta gani yasa ta tsorata police ta gani guda biyu, suka ce kece matar afraz koh, ta amsa da eh, sukace yayi accident a halin yanzu yana asibiti, tace innalillahi wa inna'ilaihira jiun, da sauri ta koma ta dauko hijab tabi su, kai tsaye asibitin suka nufa, a lokacin suma su mum din afraz din suka zo da daddy dinshi, Zeena ganin yana yin afraz yayi mugun bata tsoro, duk jikinshi ansa flasta kuka take kaman ranta zai fita, tana fadin afraz saida nace karka fita amma kaki, mai yasa ka fita afraz, yayi mata dan murmushi yana son yin magana amma ya kasa, tace afraz ina sonka, yayi murmushi a dai2 lokacin oxygen din da aka samai ya tsaya.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my fancy habiba πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
9⃣0⃣to9⃣5⃣

A lokacin da dady din afraz yazo asibitin yaga yaran, yace namijin Sak afraz a lokacin yana yaro, ya tambayi Zeena akan wani suna take so a musu huduba dashi tace asa ma namijin afraz, mumy sai da tayi hawaye don jin dadin sunan, macen kuma tace asa sunan mumy din afraz, jin haka mum din tace a'a marigayi ya taba fad'a mata indai ya haifi mace sunan matarshi zai sa, jin haka yasa Zeena ta saki kuka mum ta rarrashe ta tayi shuru, anyi ma macen huduba da Zeena, tana ta samin sauki kwananta biyar aka sallameta daka asibitin suka koma gida, tana ta samun kulawa wajan mumy din afraz, idan ta zauna taita kallon yaran tana jin sonsu na shiganta, tana fadin ina ma afraz yana nan yaga yaranshi, wani hawaye mai zafi yake fita daka idonta, idan mumy ta sameta cikin wannan halin taita mata nasiha akan ta daina sa damuwa karta jama kanta matsala.

Yau juma'a kuma ranan sunan Zeena da afraz, mutane sun taru sosai an hada gagarimin biki, mum ba karamin kudi ta kashe ba wajan siyayyan kayan yara, itama ummi din Zeena tayi siyayya sosai, Zeena babu abun da take sai kuka, har ummi tayi fushi da ita, tana ta fad'a yau ranan suna amma kin zauna kina ta kuka, sai kiyi tayi, mum tace haba ummi aiba fad'a zakiyi mata ba, ai ba'ama yaro haka, tace yi shuru Zeena kinji ki daina wannan kukan, ganin yanda mum take rarrashin Zeena yasa abun ya bata haushi tace aiki ya ganku, ita kuma Zeena tana kuka ne tare da aiyana wa dama mijinta yau yana raye yaga wannan ranan, da wani irin taro zai had'a inta tuna hakan sai taita kuka, anyi suna kowa ya watse duk wanda yazo sunan yaga yaran sai yaji kaman ya wuce dasu dan kyau.

Mysha tana zaune da dan cikinta na wata Bakwai, adeel yana ta mata hidima, duk abunda tace shi yake mata, don adeel Allah ya yishi da son yara, duk ya tare gida wajan kula da Mysha don yana burin shima yaga danshi na cikin shi, itama ganin yana son cikin yasa take amfani da daman take kara tusa mishi kanta, kuma babu laifi yana biye mata, ba kaman daba,

Zeena tana zaune tana karatu ta cikin system dinta afraz da small Zeena suna ta wasa, yaran yanzu watan su goma sai wayau, gashi basu da kiriniya, harta nono bai dame suba, ganin haka yasa aka fara basu abinci, a lokacin da suka cika shekara daya da wata biyu ta yaye su, a lokacin suka shirya tafiya umra ita da yaranta da abda, sunje umra sun gama aikin su, suna ta yawo suna siyayya yawanci siyayyan duk kayan yaran ne, sun fito daka wani shagon kayan yara a lokacin Mysha da adeel suka zo shiga shagon suma, tare da yaransu wanda adeel ya rike a hannunshi, ganin Zeena yasa ya tsaya ita kuma Mysha ta daure fuska ta shiga cikin wajan tare da fadin sai dai ka kalleta amma tama nisa tunda tayi aure, Zeena ta bita da ido da mamaki, ya matsa da murmushi yace Zeena kece a nan tace eh, abda ta gaida shi, ya amsa da fara'a, yace yaranki ne wa innan abda ce ta bashi amsa da eh, ya kamo hannun small Zeena yace wow so cute, ganin haka shima afraz ya matsa kusa dashi yana dariya, yaji yaran sun birgeshi, ya aiyana dama ace yaran shine, yace ina dad dinsu fa, dukansu sukai shuru Zeena tayi gaba, yace ma abda ya naga kinyi shuru tace dad dinsu ya rasu, yace INNALILLAHI'WA INNA'ILAIHIRA JIUN, nan yama abda gaisuwa sannan yace ta bashi number dinta zai kirata yama Zeena gaisuwa ta amsa da to ta bashi number dinta na nigeria don gobe zasu wuce,ta kama hannun yaran suka wuce suna ta mishi bye2 shima yana musu, harga Allah yaji mutuwan mijin Zeena ya kuma tausaya mata tare da yaranta,

A lokacin daya shiga cikin shop din yaga Mysha tana cika tana batsewa, tace kai abun da kayi kana ganin ka kyauta kenan, dan wulakanci kaje ka tsaya kana musu magana, ni ka shareni ina jiranka a nan, ya daure fuska tare da fadin na tsaya kiyi abun da zakiyi, ya juya tare da fadin in kin gama abun da kikeyi ki sameni waje, wani bakin ciki ne Ya kamata tare da tsanan Zeena,.

Ranan adeel kasa bacci yayi daka ya rufe ido Zeena yake gani,tare da yaranta wanda yaji yana matukar so, yaran abun burgewa, toh amma mai yasa Zeena ta kasa tsayawa su gaisa ma dakyau, take ta daure fuska, Mysha tace inafa ta magana kayi banza dani, ya d'aga kai yace inaji, tace daka nan zamu dubai dinko, yace no Nigeria zamu wuce, tace Nigeria, da mamaki take mai tambayan, yace eh, jin haka yasa ta zauna tare da tunanin mai zai kai adeel Nigeria, bayan babu zuwa nja a tsarinshi yanzu, kai akwai wani abu, haka ranan dukansu suka kwana tare da tunani ita da adeel din,.

Su Zeena sun koma gida, ita Zeena tunda mijinta ya rasu take zaune wajan mum din afraz din, yanzu haka ma gidansu afraz din suka sauka, abda ita ta wuce gida, kwanansu biyar da dawowa adeel suma suka dira a Nigeria, an gyara musu gidansu, a nan suka sauka, a ranan ya kira abda ta dauka bayan sun gaisa yace ina Zeena, tace tana gidan iyayen mijinta, anan take yanzu, yace a ina kenan, ba tare da wani abuba abda ta fada mai gidan yayi godiya tare dayi mata sallama,

Washe gari adeel ya nufi gidan, ya samu masu gadin gidan yace yazo wajan Zeena, suka cemai injiwa zamu ce, yace adeel kace mata nazo yi mata gaisuwa, jin haka suka bude mai gate din ya shiga gidan, a lokacin Zeena da mum suna falo suna fira, mai gadin yayi sallama bayan sun amsa yace Ana sallama da Zeena taji gabanta ya fadi tace waye yake nema na, yace wai adeel yazo miki gaisuwa, tace kaje kace bana nan, Jin haka mum tace mai gadin yace tana zuwa ya amsa da toh ya fita, mum tace waye shi, tayi shuru can tace wani friend dina ne, mum tace haba Zeena shine ba zaki fita ba, ai babu kyau wulakanci, maza ki tashi kije, ta amsa da toh badan ranta yaso ba, ta dauki dogon hijab tasa sannan ta fita, ta sameshi cikin mota ta zagaya ta inda yake ta tsaya yayi dan murmushi shima ya fito daka motan, yace Zeena ya gida ta amsa da lafiya, sannan ya mata gaisuwa ta amsa data gode, ta fara tafiya yace haba Zeena ina zaki muna magana, tace gida zan shiga, tunda kamin gaisuwa din, yace Zeena wai mai yasa kike haka ai ya kamata ki Kawo min yaran mu gaisa dasu, ta daure fuska tare da fadin toh, ta shiga cikin gidan ya bita da kallo, Jim kadan sai gata ta fito tare da yaran, ta tsaya ta gefe yana ma yaran wasa suna ta dariya gasu da baki suna ta mai surutu yana dariya ya dauko leda guda biyu ya basu suka amsa suna murna, ya kalli Zeena da tasha mur yace to ni zan wuce sai wani lokacin, ta amsa da toh an gode, ta kama hannun yaran suka fara kuka ganin adeel zai wuce.

Maryam obam✍✍
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©AMINIYA TA CEπŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©

πŸ’…πŸ’… NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA πŸ’πŸ’

Dedicated this page to my fans πŸ˜˜πŸ’ƒπŸ»
8⃣5⃣to9⃣0⃣

Shima komai nashi ya tsaya, ganin haka ta fara girgiza shi, tana fadin afraz, dr ya shigo da sauri yace Su bashi waje, nan ya fara yan dube2 amma ina rai yayi halinshi, Zeena ta bude kofan ta shigo da sauri itama mum ta biyo ta, tace Dr ya tashi, dr yace sai dai kuyi hakuri Allah ya mishi rasuwa, Zeena ta saki dariya tare da fadin no afraz bazai mutu ba, ta matsa kusa dashi tana fadin afraz ka tashi ka karyata wannan Dr din, nasan ba zaka mutu ka barni ba, get up afraz, taja hannunshi taga yayi nauyi, ta saki ya fadi sharaf, ta saki kuka afraz why mai yasa ka tafi a lokacin da nake bukatan ka, afraz saida sonka yamin yawa sannan zaka tafi ka barni, ka tashi your unborn child is waiting for you, ba haka mukai dakai ba afraz ka tashi ta fara girgiza shi, mum dinshi ita Suman tsaye tayi ta kasa ko motsi, a dai2 lokacin dad dinshi shima ya shigo cikin rudewa ganin afraz din yasa ya tabbatar ya rasu, hawaye ke zuba a idonshi, ya matsa kusa da matarshi wanda ko digon hawaye yaki ya zubo mata a ido, gaba daya ta shiga cikin d'imuwa, Zeena ta taso da sauri tace dad kace ya tashi, yace Zeena kiyi hakuri afraz bazai tashi ba, addu'a kawai zamu mai, tace dad afraz ya mutu dagaske, yace eh Zeena ta fara baya2 tana fadin no no he will not die and leave me lokaci daya jiri ya dauketa ta fadi kasa, da sauri dad din afraz ya fita ya kira Dr, nan da nan aka fara dubata, shi kuma afraz aka daukeshi akai gida dashi da safe za'a kaishi gidanshi na gaskiya, labarin mutuwan ya baza ko ina, su abda suma sun zo asibitin, ita zauna da Zeena ummi kuma tana gidansu afraz din, kwata2 hawaye yaki zuba a idon mum sai zuciyanta dake faman buga mata, ummi tana ta mata maganan da zata danji sanyi, kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne, kar ki zama mai butulci a lokacin da Allah zai baki shi bai fad'a miki ba, har kika sameshi kika nuna farin cikin ki, yanzu Allah ya dauki kayanshi sai ki zama mai hakuri duk son da kike mai Allah yafi sonshi, sai a sannan kukan yazo mata tace shine daya dan dana haifa yau na rasa shi, don me bazan damu ba, afraz shine komai nawa shine kwai na dana mallaka yau na rasa shi, mutuwa mai yasa baki daukeni ba, ummi ta to she mata baki, tare da fadin kar kima Allah butulci karki manta rayuwa akwai mutuwa kuma koda afraz bai mutu yanzu ba zai mutu wata rana, ki zama mai hakuri da dan gana, a yanzu babu abun da afraz yake so sai addu'a wannan kukan bashi da amfani, tayi shuru tare da fadin haka ne, ta tashi da sauri ta nufi dakinta sai gata da alkur'ani ta matsa kusa da inda aka ajiye afraz din ta fara karatu tana kuka,

Zeena wajan karfe hudu ta farka, ta bude idonta tare da fadin afraz ta tashi zaune, taga ansa mata drive, ta tsige abun ta tashi da sauri, jin kaman motsi yasa abda ta farka taga Zeena na kokarin bud'e kofa da sauri ta tashi tace Zeena ina zaki, tace abda ina afraz, tayi shuru, tace abda dagaske afraz ya rasu, abda tace Zeena kizo ki zauna, tace no ta bude kofa ta fita abda ta rufa mata baya tana kiranta ganin bata da niyan tsayawa yasa ta koma da sauri ta dauki jakanta ta fito bata ga Zeena din ba, da sauri ta shiga motarta, tayi

Please Login or Register in order to submit comment