Join Our WhatsApp Group

RAYUWAR MADINA PART 1 Complete Hausa Novel Document by RAYUWAR MADINA PART 1


RAYUWAR MADINA PART 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 95977



RAYUWAR MADINA PART 1

Reading Time: 7 Hours

Added On: 05, Nov 2023

Author: Nafisat Isma'il Lawal ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 480.22 kb

File Type: txt

Views: 688+

Download: 522+

Last download: 35 minutes ago

Description/Story: [08/06, 3:56 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎

_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*CONTINUE... STORY OF MEEMA FARUKH*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 1*
_____ *ZARIA CITY*
Ƙaramar ƙauye mae cike da albarkatu kala-kala, yanki ne da ake shuke-shuken kayan gona waɗanda ake samun iri masu ban sha'awa da burgewa, wanda hakan ne ya zamewa ƙauyen abun dogaro kuma sana'a a gare su, da noma suke ci suke sha kuma suke siyarwa a garuruwa mabambanta saboda Allah ya basu wadataccen fili mae kyau; ga kuma ƙorama da ke fitar da ruwa sosai, da lokacin damina da lokacin rani gaba ɗaya idan suka yi shuka suna ganin albarkan abun sosai. Sai dai kuma wannan ƙauye tana ɗaya daga cikin ƙauyukan da har yanzu basu waye ba a cikin al'umma, al'adun su sun sha bamban da sauran na mutane, har yanzu kansu a duhu yake wanda su sun ɗauki wasu al'adu tamkar addini a wajen su, karatun Boko ma har yanzu basu wani yarda dashi ba, iyakan su karatun Arabia da suke yi a zaure, da zaran kuma kayi sauka shikenan sai kuma ka ci gaba da sana'a ko kuma a aurar da kai, shiyasa su a tsarin su Mace tana kai wa shekaru 13 suke kaita ɗakin Mijin ta

A cikin ƙauyen akwai wani babban gida wanda a gaba ɗaya cikin ƙauyen shi ne Babba domin babu kamar shi, gida ne babba da sassa kusan goma sha biyar a ciki, kuma duk wannan gidan ahali ɗaya ne domin Mutum ɗaya ya haifi yaran gidan, waɗanda su kuma sun yi aure a cikin gidan sannan suka hayayyafa. Sai dai a yanzu Allah ya yi wa Malam Umaru rasuwa wanda ya kasance shi ne Kakanmu kuma mai Ahalin nan gaba ɗaya, tare da Matarsa guda ɗaya mai suna Faɗime da ta haifa mishi Yaransu goma sha uku cif, kuma gaba ɗaya babu wanda ya rasu face Mutum ɗaya, wanda shi ne ɗa na uku a cikin yaran gidan, Malam Sule. Ya rasu tun da ƙuruciyarsa, ya bar yara guda biyu dukka Mata, yayinda Matarsa ta fita tayi aure a cikin Zaria

Yanzu haka Babban ɗan Malam Umaru shi ke jagorantar gaba ɗaya Ahalin nan, Malam Abubakar. Muna kiran shi Baban Sasa; wanda shi ne Babba sannan kuma ya fi kowa iyalai a gidan. Matansa su huɗu ne ko wacce da nata zugan Yaran, wasu sun yi aure wasu kuma suna nan sun fantsama ƙauyaku suna sana'a

Sai kuma mai bin masa Malam Ali; da muke kiran shi da Baffa, shi kuma Matan shi biyu ne da nashi zugan Yaran shima, domin shima Allah ya albarkace shi da yara da yawa

Sai Malam Sule wanda ya rasu da jimawa, kamar yanda na faɗa muku Yaran sa biyu ne tal a duniya, kuma shi ne Mahaifina

Sai sauran waɗanda yawancin su Mata ne suna aure a sauran yankuna na ƙauyakun, wasu kuma sun samu ci gaba suna aure a cikin birnin Zarian. A taƙaice dai Iyayenmu Maza a gidan su takwas ne, sai Mata su biyar kuma kowanne Allah ya albarkace su da Yara da dama. Duk da akwai wayewa yanzu sosai a cikin rayuwarmu amma har yanzu muna da al'adun da muka kasa barin shi, duk wani ci gaba bamu yarda mu watsar da al'adun nan ba sabida muna ganin shi ne tushenmu tun iyaye da kakanni, idan za'a yi wa yarinya aure Iyayenmu da kansu suke zaɓa mana Mijin aure, sannan kuma dole ne ko wacce Mace sai an yi mata kaciya. Eh kaciya, su Iyayenmu sun mayar da al'adunmu ba namiji kaɗai ake yi wa kaciya ba har da Mata, kuma har yanzu suna nan a kan bakansu sun ƙi dena wannan al'adan sabida sun ɗauke shi da matuƙar muhimmanci. Suna ganin ta wannan hanyar ce zasu natsar da ƴaƴansu Mata wajen kamewa da riƙe budurcin su har sai sun yi aure, kuma suna ganin hakan na ƙara wa Mijin jin daɗin Matarsa wajen kwanciyar Aure; ko kuma taimakawa wajen samun ciki da sauƙi. Wannan al'ada an laƙanta shi da auren wuri kuma duk mutanen da ke cikin wannan ƙauyen zaka tarar Mace ba'a ɗauke ta a bakin komai ba kuma bata da daraja ko kaɗan, suna yin wannan kaciyar ne da zaran Mace takai shekara goma sha ɗaya sannan sai ayi mata, bayan shekaru biyu kuma sai a aurar da ita, duk da a yanzu ya sha bamban da rayuwar baya, ada can ana yi wa yarinya kaciya ne da zaran takai shekaru biyar a duniya, amma yanzu kai ya waye an samu ci gaba dole sai yarinya takai shekaru 11 sannan za'a yi mata

Duk yadda Mutum ya so ya dubi al'ada; ba ta wani ɓangare da ya cancanta sam. Cin zarafi ne na ɗan Adam da bai cancanta sam ya zama yana wakana koda a kan kowa ba, domin wannan ɗabi'a na sanya wa Mata da aka yi musu kaciya; zasu kamu da matsaloli da suka shafi lafiyar Mace (mental and physical health challenges) a gaskiya ba Macen da ya kamata ayi mata kaciya. Haka wannan al'umma suke alaƙanta kaciyar Mata da addini, musamman addinin musulunci. Haka ma a wasu ƙasashe da dama suna amfani da addini domin yi wa Mata kaciya; kuma suna kafa hujjarsu mara tushe a kan wannan aika-aikan, duk da cewa basu da hujja kuma basu da takamaiman inda zasu kama a cikin Al'ƙur'ani ko hadisan Manzon Allah. Wannan na faruwa ne saboda rashin cikakken ilimin addini da kuma mabiya da basu san alƙiblan su ba, wanda ya kasance abun da suke aikata wa Mace daban da abun da yakamata su cire mata, sam kaciya bata dace da Mace ba, hanyar da suka dauko ba shine wanda ya dace ba, a ganin su daidai ne. A dalilin haka wannan al'ada ta samu shiga sosai a wannan ƙauyen, kuma babu wanda ya isa ya tsallake wa hakan.







⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

_____Kamar yanda kowacce shekara ake samun waɗanda ake musu wannan kaciyar, hakan ta kasance a cikin wannan ƙauyen. Mata da yawa waɗanda aka shirya domin aiwatar musu da wannan al'adan a gobe juma'a

Inda a babban gida kamar yanda muke kiran sunan gidan mu, Mata shida su ne waɗanda za'a yi wa kaciyar suma, shiyasa kowacce Uwa take tausayin ɗiyarta sabida abun da zai faru gobe, suna ganin daga yau kuma ɗiyar su ta zama babbar Mace, ta tashi a ƙaramar yarinya, da zaran an yi kuma sai maganar aure da zai fara tashi, inda za'a zaɓawa kowacce Mace Mijin da zata aura, wannan dalilin ne yasa Idan ka shiga babban gida zaka ga kowa jigum haka suke zaune duk babu karsashi a jikin su, musamman ma Yaran da su za'a yi wa kaciyar kana kallon fuskokin su zaka ga rashin walwala a tattare da su, ko kaɗan ba sa ƙaunar gobe tayi sabida azaban da zasu sha.
ƴan uwanmu suna bamu labarin wahalar da ake sha, mu ma kanmu muna gani, amma kuma wacce ta tsallake shikenan, bamu da yadda zamu yi dole ne mu fuskanci wannan ranan kamar yanda ƴan uwan mu suka fuskanta a rayuwar su.

Da yammacin ranan ne Baban Sasa ya yiwa ƴan uwan shi kira suka zauna suna tattaunawa a kan gudanar da al'adar tasu a gobe, wanda a cikin jawabin Baban Sasan ne yake cewa, "tunda yanzu Madina ta kawo girma itama, babu wani sa'ar ta a cikin gidan nan sauran duk yara ne, to, sai a haɗa ta da sauran Yayyinta da za'a yi musu kaciya gobe itama ayi mata, ai ina ga babu matsala tunda da shekara ɗaya suka girme ta, kunga mun huta ma."

Jin zancen Baban Sasa babu wanda ya musa, kowa ya ga dacewar hakan, sai kaɗa kai suke yi suna cewa, "ƙwarai kuwa hakan ya kamata, ai itama tana da girman jiki ta kamo su a girma, babu wanda zai ce sun girme ta, za'a haɗa su kawai ayi musu."

Ana haka sai gani na shigo cikin falon riƙe da kwanon sha da aka aiko Ni in kawo musu farau-farau. A hankali na ajiye kwanon shan tare da durƙushewa na soma gaishe su cikin girmamawa irin nawa, sannan na isar da saƙon kamar yanda Matar Baban Sasa ta aiko Ni, Matarsa ta farko wacce muke kira da Inna Lami

"Yauwa Madina, ajiye." Cewar Baffa da yayi maganar yana kallo na, domin a cikin su duk shi ne wanda yake da sakin fuska da wasa da Yara sosai

Har na miƙe Baban Sasa ya tsayar da Ni yana cewa, "zauna Madina akwai maganar da zamu yi da ke."

Hakan yasa na samu wuri na zauna a saman ƙafafu na yayinda kaina ke ƙasa na kasa ɗagowa. Baban Sasa ya soma sanar min da hukuncin da suka yanke a kaina wanda lokaci ɗaya na ɗago kai ina kallon su ɗaya bayan ɗaya, duk da ba wani wayau ne da Ni ba domin a lokacin shekaruna goma ne cif; amma kuma ina sane da wannan Shegiyar al'adan tamu wacce ina ɗaya daga cikin waɗanda suke matuƙar tsoron zuwan wannan rana a gare mu, musamman yanda naga Yayata ta sha wahala a lokacin da aka yi mata, tayi ciwo sosai kuma ta sanar min akwai wahala sosai, daga ƙarshe dai Allah ya bata lafiya har aka yi auren ta, yanzu shekara ɗaya kenan kuma har da ƴarta guda ɗaya da ta haifa ko kwana hamsin ba'a yi ba. Jin cewa da Ni za'a yi kaciyar gobe zuciyata tuni ta cika da tsoro wanda ya kasa ɓoyuwa a kan kyakkyawar farar fuskata da take ɗan tsut da ita, kullum a rame kamar ba na cin abinci, to kusan haka ne tunda dama rayuwar gidan yana matuƙar min wahala kasancewata marainiya babu Mahaifina, sannan kuma mahaifiyata ta fita tayi aure a can cikin Zaria anguwan ƙaya, shiyasa muke matukar shan wahala Ni da Yayata Haula, sai dai kuma yanzu ita tayi aure ta huta ba kamar Ni ba, kullum kamar Ni ce jakar gida ko wacce Mace Ni take sakawa aiki, babu damar aga wulƙawa ta sai ɗaya daga cikin matan gidan sun kira Ni sun saka Ni aiki, da su saka yaran su sun gummaci su sanya Ni, shiyasa a kodayaushe bani da lokacin kaina kullum cikin bautar Matan gidan nake yi, kuma dole inyi tunda bani da ƙyuya ko kaɗan, idan ma ban yi ba abincin da ake bani sai dai in rasa domin babu wacce zata bani ban yi mata aiki ba, shiyasa na zama tamkar Almajira a gidan kamar ba ƴar gidan ba, idan aka yi min wani abu sabo sai dai idan Baffa ne, ko kuma Baban Sasa wanda yake haɗa kowa na gidan da sallah yayi musu sabon kaya, to idan ba sallah ba Ni ba na samun me min komai koda biki ake yi a gidan namu, babu me min anko ko ya siyan min sabbin kaya, sauran yaran kuwa iyayen su mata suke siyan musu duk abin da suke so tunda duk suna sana'a suna samu, kasancewar rayuwar gidan mu yawanci matan su suke yiwa kansu hidima na yau da kullum, iyayen mu maza basu saba ba kuma baza su taɓa yi ba sai idan sun ga dama, yana ɗaya daga cikin uƙuban rayuwar da Matan cikin ƙauyen namu suke sha, har yanzu kai ya ƙi wayewa. A gaskiya na shiga tashin hankali jin cewa har da Ni za'a yiwa kaciya, na ruɗe sosai sai dai na kasa yin magana sabida kasancewar Baban Sasa ne mai maganar, domin shi ba ya ɗaukar raini kuma ba ya so yana magana ana katse shi, yana da son girma sosai duk abin da ya gindaya to babu me iya tsallakewa. Hakan yasa ya bani umarnin, "in je gidan Yayata in kira ta." Babu musu na miƙe na fita jikina na rawa kamar mazari, har ina jin tamkar ƙafafuwana baza su iya ɗauka ta ba, duk yanda na so na daure kar na fitar da halin da nake ciki amma hakan ya faskara, tuni hawaye sun soma sauka a kan dandamalin fuskata sai shatata suke yi kamar an kunna famfo, dole na miƙa hanya na fice daga gidan namu na doshi gidan Yayata da babu nisa sosai, tunda naga na fita cikin jama'a sai na soma kuka wi-wi kamar ana yankan naman jiki na, har ba na iya ganin gabana a yanda nake tafiya a haka nakai ƙofar gidan da Yayata take Aure. Gidan ba wani babban gida bane kuma su uku suke zaune, daga surukar su sai Wan Mijin Yayata; da Matarsa shima da yara biyu. Ina shiga babu kowa a tsakar gidan sai na nufi kaina tsaye ɗakin Yayata, ina shiga ɗakin kuka na ya janyo hankalin ta da har barci ya soma fizgar ta, tana rungume da jaririyar ƴarta me sunan Umman mu, Asiya, mu kuma muna kiranta da Ihsan

Yayata hankalin ta ya tashi ganin yanda na shigo mata ina kuka, shiyasa nan da nan ta ruɗe ta soma tambaya na, "Madina lafiya mene ne? Me aka yi miki? Faɗa min inji?" Dukka ta rungumo Ni jikinta tana kallon fuskata; yayinda ita nata fuskar cike da damuwa tsantsa

Ni kuma kukan nake yi na kasa denawa. Dole ta zauna bani haƙuri har nayi shiru sannan ta sake tambayata? A nan na bata labarin komai har da kiran da Baban Sasa yake mata

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..." Salati kawai take rafkawa lokaci ɗaya ta sake rikicewa wanda har hawaye ne suka soma sintiri a kan fuskarta me kama da nawa sak, cikin tsantsan tashin hankali tace, "yanzu kina nufin da ke za'a yi wa kaciya a gobe?"

Shashsheƙa na soma yi ina gyaɗa mata kai a hankali, yayinda wani kukan ya sake taho min sai na faɗa jikinta ina cewa, "shikenan Yaya Haula nima zan fuskanci wannan uƙuban rayuwar da ku ka sha? Ni yanzu ya zan yi wlh bazan iya jurewa ba, idan aka yi min mutuwa zan yi, don Allah ki kai Ni wajen Ummana ba na so ayi min, ki ce musu ba na so."

Haula ta kasa magana illa sake rungume Ni da tayi tana kukan itama sosai cike da tausayina, ta san kuma aikin gama ya rigada ya gama dama wannan ranan take gudun zuwan ta, tana tausayin ƙanwarta musamman kasancewar ta me rauni sosai, tana gudun zuwan wannan ranan ga ƙanwarta, amma babu yanda zasu yi dole ne itama sai an yi mata. Ta kasa rarrashina yayinda Ni kuma nake ta sambatu ina kuka ina faɗa mata, "Ni ba na so." Riƙo kaina tayi tana ɗago Ni tare da kallon fuskata da nake ta shatatar ruwan hawaye, haka itama nata tuni idanuwanta sun yi jawur tace,...


Read / Download RAYUWAR MADINA PART 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album