Join Our WhatsApp Group

Zumuncin Zamani Part 1 Complete Hausa Novel Document by Zumuncin Zamani Part 1


Zumuncin Zamani Part 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 40844



Zumuncin Zamani Part 1

Reading Time: 3 Hours

Added On: 04, Nov 2023

Author: Nazeefah Sabo Nashe ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08033748387

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 204.61 kb

File Type: txt

Views: 820+

Download: 323+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: Zumuncin Zamani

Na Nazeefah Sabo Nashe


(Ku karanta kyauta. Zai dinga zuwa muku a group d’in Sabon littafina Ya Abin Yake? Riba biyu kenan! Ku biya kud’insa ku karanta Kyauta.)

08033748387

A sunkuye kaina yake a tsakar gida, ina d’auraye kwanuka. Da sauri nake tayi don na san muddin Ummata ta dawo ban gama wanke-wanken nan ba tabbas kashi na ya bushe. Ai kuwa sallamarta na ji hakan ya sa ni saurin janyo ragowar kwanukan.


Umma dake tsaye a bakin k’ofa ta rafka salati “Sauda me zan gani haka? Yanzu da tun safe da na fita ba ki k’arasa wanke-wanken nan ba har yamma sakaliya? Anya Sauda ba zaki nutsu ki yi hankali ba, duk da gama secondary School da kika yi?”

Muryata cikin shagwab’a na ce “Umma wallahi wuni nayi kaina na ciwo.”

Ta zabgo min harara ta ce “Haka kika iya, ba ki da zance sai na cuta, shegen son jiki kamar mage, wallahi ki kiyayeni.” Ta bankad’a labule ta shiga cikin d’akinta.

Ni ko na saki ajiyar zuciya. A zuciya ta na ce “Umma kenan.”


A daidai lokacin wani yaro ya kwad’a sallama, na amsa masa ina nazarin inda na san fuskar yaron. Sai can na tuno d’an maigadin gidan Baba Hamza ne haka yasa na had’a rai na kuma bi shi da harara, don ko magen gidan na ga ni wallahi zan harareta. Na tsani ahalin gidan gaba d’aya. Wannan tabbas haka ya ke.

“Ina wuni?” Naji ya ce dani.

Ko kallon sa ban yi ba balle na amsa masa. Umma ce ta fito daga d’aki tana tamabayar “Waye mai sallamar ne?”
Da sauri yaron ya amsa, ko don ya fuskanci ni d’in ba zan amsa ba ne oho! Ya gaishe da Umma sannan ya mik’o mata chewing gum guda uku. Ta ce “ Na menene?” Ya gyara zamansa, sannan ya ce “Wai na sunan munirat ne gobe. kuma wai ta ce don Allah ki zo da wuri akwai aiki a can gidan.”

Umma ta amsa ba tare da wata damuwa ba. Ni kuwa zunduma ashar na yi na ce, “Gidan uban wa za ta zo? Saboda sun mayar da ke jakarsu, babu mai nemanki sai irin haka ta taso, saboda sun san za ki je ki wahalar da jikinki a wajen yi musu bauta da aikin banza aikin wofi.......

Wani kallo Umma ta wurga min ta kuma cillo min wani mafici cikin b’acin rai ta girgiza kai, ta kalli yaron da ya yi sugud’i yana yi min kallon mamaki da alama tijarata kawai ya ke ta’ajjabi. Ta ce “Kai yaro, ya sunanka?” Ya ce “Najibu”
“Yauwa Najibullahi, maza kaje ka ce Allah ya raya, sai mun zo insha Allah.” Ya mik’e ta mik’a masa Naira Ashirin, “Ungo wannan ka sha alawa kayi maza ka wuce gida.”

Ai yana karb’a na fisge cikin tsawa na ce “Wannan matsiyacin cingam d’in da suka kawo shine zaki ba shi har Naira Ashirin?”
Wannan karan cikin jin haushi Umma ta zabga min dundu a gadon baya na, tana salati ta ce “Sauda ina raba ki da wannan bak’in halin ba kya ji ko? Kin ba shi ko sai na mare ki shashashar yarinya har abada ana gaya miki amma kan ki ba ya d’auka? Wanda ka bayar har abada shine naka, zaki ba shi ko sai na mangareki?”

Fuskata a d’aure cike da k’unk’uni na mik’a masa Ashirin d’in idanuna har suna tara ruwan k’walla.

Shi kuwa ya karb’a ina kallon fuskarsa yana min dariyar mugunta. Hararar da na zabga masa ce tasa ya k’unshe dariyar da alama mamakin masifata ya ke.

Yana fita kuwa Umma ta hau kaina da masifa da bala’i tana cewa “y’ar banzar yarinya mai bak’in hali. So kike tilas sai kin yanke zumuncinmu da mutanen nan tamkar yarda suka yi, to bara na sanar da ke, ke ma kun zama d’aya da su. Ina ruwanki idan ma wahalar na musu, na yi d’in jikin ki ko nawa? Shashashar banza. Kuma ki sani, ki kwana da shirinki ke ma tilas sai kinje sunan tabbas! Sai dai ki kashe kanki don haushi.., shashashar yarinya mai d’abi’ar mutanen banza, duk mai yanke zumunci ai mutumin banza ne..”

Wai! Ai zuciyata tamkar ta fashe don tsananin zafi. Ba fad’an bane ya b’ata min rai sai cewa da ta yi ni ma sai na je gidan sunan. Ni ko da zuwa na wani sha’ani na danginmu wallahi gwara ta kwana tana yi min fad’a. Me za’a yi da danginmu Ko Dangin masifa da jaraba.


Har dare ina ta rok’on Umma a kan ta kyaleni da batun gidan sunan nan, amma Umma ta yi burus da ni. Kuma fuskarta babu alamun sassauci don ta d’inke tsaf ta had’e rai kamar hadarin kaji. Hakan yasa ko da na kwanta barci da batun na kwanta na fara tunanin su wanene Dangin mu?



***********

Alhaji Usman mai shadda shine sunan kakana da ya haifi ubana, mai kud’i ne a yadda tarihi ya nuna. An ce yana daga cikin k’irgaggun masu kud’in zamanin da.
Matansa uku da y’ay’a goma sha uku. A wancan lokacin shi kad’ai ne mutumin da aka san yake shigo da shadda daga waje.

Matarsa ta farko ita ce Hajiya tana da y’ay’a biyar biyu mata uku maza. Inna falmata, Inna Shukra, sai Baffa Hamza, Baffa Lawal, da Baffa Shu’aibu.

Matarsa ta biyu ita ce H.Saudatu. Ita ta haifi Babana, Malam Mustafa da k’annensa mata biyu. Inna Sabuwa, da Inna Mariya. Sai Hajiya Amarya, ita kuma y’ay’anta biyar, Baffa Amadu, Baffa Sa’idu, Baffa Umar, Baffa Nura da Baffa Iliyasu.

Wad’annan su ne zuriyar Alhaji Usman Mai shadda kakana, kafin mutuwar mahaifinsu, sam babu y’an ubanci a tattare da su, amma bayan mutuwarsa aka raba gado, sai zumuncinmu gaba d’aya ya koma ZUMUNCIN ZAMANI da wanda yake da shi ake yi don ni mahaifina a gefe aka saka shi sanadiyyar karayar arziki da ta samu mahaifinmu. Don kafin hakan ta sameshi suna zumuncin da shi sosai, tunda babu abinda zai nema a hannunsu. A lokutan baya shi ne, ya wahalta musu har da d’iyoyinsu don sam shi mutum ne ba mai raba d’aya biyu ba, ba ya y’an ubanci kuma sam abin hannunsa bai rufe masa ido ba.Koda yaushe hannunsa a bud’e yake, yana mi’kawa akwai kyauta atare dashi, sam bai zama igiyar giginya ba, kamar yadda wasu masu dashi d’in su ke yi.
Bayan anraba gadone karayar arzik’i ta same shi, ‘yan fashi suka yi masa tatas a hanyarsu ta tafiya kwatano wajen saro kaya, a zamanin baya mutane basu waye da yin transfer d’in kud’i ba idan zasuyi tafiya. shikkenan silar rukurkushewar arzik’in kenan da kad’an-kad’an komai yaja baya yana kwasar kadararsa yana sayarwa, yana jan jari amma rabon samun nasa ya k’are babu mamaki iya arzikin da ubangiji ya ‘kadarto masa kenan.

Tun muna private school(makarantar kud’i) har hakan ya zo ya gagareshi, sai da mu ka yi zaman shekara guda a gida, sannan ganin babu yadda zaiyi ya mayar damu makarantar gwamnati, duk fa ga ‘yan’uwansa nan sunxama gawurtattun masu kud’i don kam suna rik’e da manya -manyan kujerun gwamnati, amma sukayi burus damu, yakuwa za’ayi na manta?
Manyan makarantu suke saka ‘ya’yansu, wasu har ‘kasashen waje suka fitar dasu, mukuwa dagamu har yayyena ta gwamnatin ma wani lokaci nema take ta fi ‘karfinmu. Ta ya ya Umma take zaton zan manta da wannan bak’ar rayuwar da muka shiga?
Zamanin baya, bana fatan ko mak’iyina ya fuskanci irin halin da muka shiga na babu da Ta yi mana dabaibayi. sau tari muna wuni ba muci abinci ba, ko kuma garin kwakwi yazama abincinmu wuni guda tamkar ‘yan bursina. Wani lokacin garinma ko ‘kasa ko sama nemansa muke ruwa a jallo duk da a wancan lokacin store d’in ‘yan’uwana cike yake da kayan abinci. Yaushe ni sauda zan manta? Kada allah ya maimaita mana don wani abun ba shi fad’uwa.
Amma alhamdulillah, don kuwa Allah ya bawa mahaifina zafin nema da jajirtacciyar zuciya mai tsananin juriya,tak’awa da tawakkali. sam baya girgiza, duka lamarinsa yakan mik’ashi ga Allah, ba lallai ma Ka fuskanci halin da yake ciki ba idan ba ya fad’a maka ba, kai ko ya fad’a bai zama lallai a yarda ba. dalili, za ka ganshi tas, fuskarsa cike take da annurin k’aunar ubangiji.
Komai ya fara lafawa bayan mahaifinmu ya fara ‘yan buga bugar sa, ya kuma samu ya bud’e shagon siyar da kayan abinci anan k’asan layin mu. A yanxu kam babu abinda zamu ce sai godiyar ubangiji. Alhamdulillah.
Sai dai duk da haka bawai anayi damu a dangibane, a’a, ina! Ai karanmu bai kai tsaiko ba su danginmu ba sa zumunci da kowa sai mai naira. Ba sa alheri ga kowa sai wanda suka san zai ninka musu abinda suka yi masa. Haka yanzu rayuwa takoma zukatan al’umma sun mutu murus ba a kyauta don Allah sai na san zaki iya biya na.
Ga misali, a danginmu suna yin abin nan da hausawa suke cewa, dai-dai ruwa dai-dai tsaki Idan talaka na biki dari biyar, shima ana san ran zaibiya. zokisha kallo idan ana bikin mai kud’i a danginmu, yadda ake karawa mai ‘k’arfi, k’arfi saboda an san zai iya biya.
Fisabilillahi ina amfanin hakan, ga wanda zaka yiwa ya ji da’di’, Allah kuma yayi farin ciki da abin da ka yi, sai ka je ka yi a inda sam kud’in da ka bayar ba burge su zaka yi ba. Dalili? Suna da ni kin ba ninkin naka ka ga ka tashi a tutar babu ba lada ba gwaninta. Kai Allah ya kyauta! Ubangiji ka cika zuciyarmu da imani.
Mu biyar ne a wajen mahaifiyar mu, ina da yayye uku, maza biyu suna FCE biyu kuwa a management suke. Nikadai ce ‘diya mace, nida yaya sa’eed munfi kowa tsanar danginmu a gidan nan. Ni ko yawon sallah ba na zuwa, A kullum nasihar umma garemu mu yayyafa wa xuciyarmu ruwan sanyi, komai mai wucewa ne wata rana sai labari. Jin Ta kawai nake, Allah ne kad’ai yasan yadda nake ‘kinsu, K’iyayyar su ta zauna daram a raina.
Ko ‘ya’yansu babu wanda nake Huld’a dashi sai d’aya, itama sama-sama kawai ne tsakaninmu, ba wani mun sha’ku bane.

*** *** ***
Kashe gari tun safe nake ta nu’ku-nu’ku na ‘ki shiryawa don nasan Umma tace tun safe zamu tafi, ita kuwa sai mita take yi Koda nayi wanka, powder kawai na mitstsika wa idona , dama ni ba gwanar kwalliya ba.
Mutane da dama suna yimin kirari da kyau zalla, haka din ne duk da nidin ba fara bace, haka nan ba za’a sakani a layin bak’ak’e ba. Girar idona tana da yalwa,sannan tana da lan’kwasa, ina da dara daran ido masu yalwar gashi da rumfar ido. Hancina na da tsayi da tudu kad’an. Bakina kuwa ba k’arami ba ne ainun, haka kuma ba za’a kira shi babba ba, yana daga cikin tsaka tsaki dai. Jikina a murje ya ke ba rama babu kuma k’iba. Dogon wuya ne da ni wanda ya fallasa asirin tudun k’irjina. Haka nan ina da cikakken k’ugu a dire nake sosai, k’afafuna kuwa zan iya cewa sun fi komai kyau a jikina kasancewrsu luwai-luwai kamar na fatar jarirai don fatata mai kyau ce duk da ba fara ba ce ni sosai amma k’afata fara ce tas kamar ka latsa jini ya fito.


Da sauri na zira wani bak’in takalmina flat shoe half cover, nayi saurin ficewa daga d’akin jin Malam Mahaifina yana k’wala min kira.
Wani kallo ya bini da shi, kafin ya yi k’wafa ya ce “Wato ke uwata har yanzu zuciyarki ba za ta rusuna ba ko? Kin k’ullaci y’an uwana a zuciyarki. To ko ni da suka yi wa abin ban k’ullacesu ba, idan ma sun yi min d’in ina ruwanki ba tare ki ka gan mu ba? Shashashar banza. Ke ma kin zama su tunda kin yanke zumunci da su. Za ki wuce ki tafi ko sai na sab’ar miki. Sakaryar banza kawai.”
Tamkar na rusa ihu haka na ji, jikina babu laka. Haka na bi Ummanmu zungui-zungui a baya, fuskata a had’e tamkar an yi min bushara da mutuwar mahaifina. Na ayyana duk shegiyar da na je ta yi min kallon banza a gidan sunan nan wallahi sai ta kwashi hannunta a hannunta, don sai na lakad’a mata uban duka, don sun iya yiwa mutane kallon k’ask’anci da kallon baka isa ba, wanene kai?

Gidan ba kowa don san da muka je ba a cika ba, zan iya cewa ma mune farko-farkon zuwa. A zuciyata na ce na san kallon azarb’ab’i ake mana mun zo cin ta tsotse. Kamar kowane lokaci ba mu samu wani kallon maraba da
Manyan bak’i ba. A madadin haka ma kallon daman ku muke jira, ga aikinku can, shi aka bi mu da shi.
Umma kuwa dai washe baki take. Ba don uwa ba ce Allah ji na yi kamar na rufe mata bakin.

A hakimce uwargidan B. Hamzan take a kan kujera, ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya, ta bi Umma da kallo tamkar ba faccalarta ba, kai kace uwargijiya ce da mai aikinta. “Sa’ade, dama ke nake jira, ga kullin waina can a tsakar gida, suyar wainar za kiyi sai kin d’an hanzarta don da yawa kwano goma ce.”

ALK’ALAMIN JIKAR NASHE




Zumuncin Zamani

Na Nazeefah Nashe.

(Ku karanta kyauta. Abokin hira na dare)


📄 2


Umma ba abinda ya dameta da umarnin da aka bata, madadin b’acin rai ma a fuskarta sai fara’a take tana jaddada Allah ya raya d’iyarki Munira ya yi mata Albarka, alfarmar annabin Rahma.

Cikin shan k’amshi mai jegon take amsawa da kyar sai wani muzurai take tamkar Umman sa’arta ce sai kace Umman bata haifi wad’anda suka girme mata ba, kawai don dai ba ta da kud’i shi yass bata da wata daraja da k’ima a idanunsu. Ganin Umman ta mik’e sai ni ma Na mik’e na bi ta a baya, har na kusa k’ofa na ji muryar Muniran cikin gadara tana cewa “Ke Sauda ba kya gaisuwa ne? Saboda rashin mutunci kina ganin mutane ba za ki gaishe su ba?” Na juya na zuba mata wani kallo kafin na ce “Shi yasa naga kin gaida tawa uwar.. uwa ai ba tafi uwa ba..” A fisge ta d’ago ta zuba min na mujiya “Kan uban can ashe fetsararki da rashin mutuncinki yana nan? Shegiya kina y’ar talaka sai girman kan banza, ciki fal yunwa..” Na jiyo zan bata amsa...


Read / Download Zumuncin Zamani Part 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album