Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

RANAR BIYAN BUƘATA Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba Complete Hausa Novel Document by RANAR BIYAN BUƘATA Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba


RANAR BIYAN BUƘATA Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 61584



RANAR BIYAN BUƘATA Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba

Reading Time: 5 Hours

Added On: 11, Aug 2024

Author: The Nainarh KD ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08081129487

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 318.42 kb

File Type: txt

Views: 604+

Download: 536+

Last download: 1 day ago

Description/Story: 𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫


*SHIMFIƊA*
Akwai lokacin da wahala da tsananin azaba na wasu mutane ke saka raunannu daga cikin mutane gaza jurewa su tashi tsaye domin nemawa kansu ‘yanci. Akwai k'addara, Akwai son zuciya. Akwai K'addda ta Fyad'e, dake faɗawa wasu matan. Akwai tsananin zalunci da cin amana. Duka da suke taruwa wurin tagayyara Rayuwa su saka tsananin shakku da ruɗani a wasu zukatan.....

_


*💫...RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna.*
*A.k.a Nainarh KD.*
*A.k.a Nkd's ✍️*


*LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION...*


*بسم الله الر حمن الر حيم*

*Ep_1-2*

_2000_
*Shekara ta dubu biyu .*

*25, Idowu Martins Street, Off Adeola Odeku Street, Victoria Island, Lagos, Lagos State, Nigeria.*

*07:30, Na safe.*



Da sauri yaron da ba zai wuce shekaru goma a duniya ba, ya tashi a firgice daga saman kujerar Dining da yake kai yana ƙoƙarin fara karin kumallo. Jikinsa ne ya ɗauki rawa kamar mazari lokacin da ya jiyo sautin fashewar Gilashi daga kitchen da iyayensa ke ciki. Da kyar ya iya haɗiye yawu na tsoron abin da ke faruwa a ciki.
Saɗaf saɗaf ya fara taku a hankali, har ya ƙari sa ƙofar kitchen ɗin ya tsaya tsaye sannan ya leƙa kansa ciki kaɗan domin ganewa idanunsa abin da ke faruwa duk kuwa da yasan wannan abu da yake ƙoƙarin yi a yanzu ba abu ba ne mai kyau domin mahaifiyarsa ta taja masa kunne akan aikata wannan ɗabi'a ta laɓe musamman ga manya.


Juya masa baya tayi tana ci gaba da abin da take yi ba tare da ta kula shi ko sauraren magiya da yake ma ta, domin kuwa a halin yanzu bashi da wata kalma da zai kwace kansa a wurin ta har abada kuwa, da idanunta ta ganshi a wannan karon ba wai zargi da take yi ba, daurewa kawai take yi domin kuwa ji take kamar Zuciyarta zatayi bindiga ta fito waje kanta kamar zai tsage gida biyu tsaban tashin hankali da damuwa da take ciki da kuma kishi na ganin Mijinta da wata da ta yi a daren jiya da shi ne dalilin fushin nata a yanzu domin nuna masa kuskuren sa sai dai da alama ya yi nisa sam baya jin kira a harkar.....


“Haba mana Tawan kiyi haƙuri nayi alƙawari ba zan sake ba fa wannan ma aka si aka samu kinji.”
Shiru ta yi tana sauraren sa ba tare da ta tanka masa ba. Ganin taƙi magana kuma da alama har yanzu bata haƙura ba, ya yi Murmushi kaɗan irin na gefen baki sannan ya kai hannunsa ya zagayo da ita suna fuskantar juna kana ya fara magana.

“Na ranste ba zan sake ba, nayi Miki alƙawari ko dan wannan tilon Ɗan namu.”
Ya faɗa yana ma ta nuni da yaron nasu da zuwa lokacin yana tsaye jikin ƙofar kitchen ɗin.
Girgiza kai kawai ta yi ba wai don ta yarda da abin da ya ce gaba ɗaya ba domin ba yau farau ba.
Cikin sassanyar Muryarta mai cike da nutsuwa ta ce.
“Shikenan komai ya wuce a wurina na yafe maka.”
Murmushi ya yi cike da farin ciki ya kamo hannunta tare da kashe Gas da ta kunna ya nufa ƙofar fita daga kitchen ɗin.
“Ah ah Abu J ina ne kuma zaka kaini ina girka ne fa?.”
“Ke dai kiyi shiru kawai bazata ne.”
Ya faɗa daidai lokacin da suka fito daga kitchen ɗin ya kama hannun yaron nasa ya sumbata, bayan ya saki nata.
“J dama ba kace min kanason zuwa wurin wasa tare damu ba?.”
Ya tambaya yaron bayan ya rangwafa daidai tsayin sa.
Kallon Mamansa yaron ya yi. Ta yi Murmushi tare da kyaɗa masa kai sannan ya mayar da kallon sa ga Mahaifin nasa ya kyaɗa masa kai alamar e.
“Toh shikenan yau zan cika maka Burin ka zamuje duk Wurin da kake da buƙata a tare.”
Ya faɗa yana Miƙewa tsaye tare da kallon fuskar matar nasa da take baƙa wani abu yana tsaya masa a rai, amma ya daure tare da sakar ma ta murmushi kamar yadda ya saba a koda yaushe, ita ma ba tare da jinkiri ba ta mayar masa duk da tanaji gaban ta na tsananta buga wa ba tare da ta san dalilin ba...



_
*Fantasy Land Lagos*
*11:50 na safe.*



Yarda yaron ya saki jiki yana wasa da dariya da sauran yaran dake wurin ne ya bata mamaki domin tafi kowa sanin wanene J yaron ta. Akwai tazara sosai tsakanin su da shi domin shi yana kan lilo ne tare da wasu yaran yayin da ita da mijin nata suke can sama a wurin. Juyawa ta yi domin mayar da kallon ga mijinta, ta buɗe baki zatayi magana daidai lokacin da ta juyo garesa shi kuma ya sakar ma ta Kyakyawan Murmushi daman abin da yake jira ke nan. Hannu ya sa ya tura ta gaba ɗaya ai kuwa take ta yi ƙasa tun daga saman Benen ko shurawa batayi ba lokacin da ta faɗo ƙasa kanta ya fa she Sakamakon tsagewa na buguwan da ta yi, jini ne ya fara malala a wurin yayin da mutane suka zagaye ta. Murmushi ya kuma sakarwa tare da lumshe ido Finally ya kawar da ita burinsa ya cika saura kuma me ya rage⁉️



_____
*2024*
*Shekara ta dubu biyu da ashirin da huɗu.*

_Abuja, Nigeria_

*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja.*




“Wani abu ne da ya kasance sabo a gane mu gaba ɗaya sannan mai cike da ruɗani da kuma sarƙaƙiya mai ɗaure ciciyoyin kai lamari ne akan kisan babban jami'in ƙasar nan da aka yi wato Commissioner Of Police Mr Aashir Aasaal. An kashe shi ne a cikin Gidan sa na hutawa dake wajen gari. Nasan akwai tarin tambayoyi a tare daku game da wannan ruɗaɗɗen al'amarin na kisan kai mafi ɗaukar hankali da aka yi a ƙasar nan. Mai zaku ce game da hakan wani irin tunani kukeyi akan Wannan lamarin da binciken sa zai kasance a hannun ku?.”


The Director General of the state security service, Mr Bilal Yusuf Bilal ke nan da kansa cikin ɗakin tattaunawa na binciken mayan laifuka irin su Kisan kai Garkuwa Da mutane Fyaɗe da sauransu, yake kwararo wannan baya nan cikin kwarewa da sanin makamar aiki yake bayanin yana nuni da farin allon wanda hasken kwan wutan projector ya haskesa, mai ɗauke da hoto na gawar commissioner da aka kashe kuma zasu ɗaura ɗambar bincike akan case ɗin.

Ya kammala bayanin tare da mayar da kallon sa akan kwararrun jami'ai na musamman da yake ji da su ya kuma yarda da basirarsu tare da kaifin tunanin su da kwarewa a aiki. Wannan dalili ya sa ya haɗa su a team guda domin fara binciken....



“Sir a tunani da nazarina wannan kisan kai bai wuce ɓarayi ne kawai suka yi ba, wata ƙila sun shiga gidan domin neman wani abun shi kuma ya nema ya yi musu gardama a matsayin sa na jami'i wata ƙila shi ne ya sa suka kashe sa sannan suka gudu.”


D.G Bilal Y.B ya yi shiru yana sauraren abin da ɗaya daga cikin jami'an yake faɗa bayan ya miƙe.


Ba tare da ya ce komai ba ya kuma bawa ɗayar da take mace damar ita ma ta yi magana sannan ta fara kamar haka.

“Wannan bai yi kama da ace ɓarayi ne suka yi ba, a iya nazari na nafi danganta hakan da kisa ne da aka yi domin ɗaukar fansa.”


D.G ya yi Shiru kamar yadda sauran jami'an suka yi shiru tare da Nazarin abin da ɗaya daga cikin su ta faɗa.


Bayan shuɗewar wasu sakanni D.G ya Girgiza kai tare da kallon ta tun da aka fara tattaunawar bata kalla kowa ba haka zalika ba tace da kowa komai ba, sai ma ‘yar yatsar ta da take bubbuga wa akan Cup of coffee dake a je gefenta yayin da idanunta suke tar akan allon majigin tana nazarin hotunan gawar da suke maimaita kan su kasancewar da na'urar projector ake hasko hoton.



“Officer muna sauraren ki, shin kina da wani abun faɗa game da wannan case da zan damƙa a hannun ku domin binciken ko kuwa dai sai kin ƙara nazari akai?.”


Ya ma ta tambayar ba tare da saka ran samun amsa daga gare ta duba da sanin Wacece ita da ya yi.


Baya ta yi kaɗan tare da Miƙewa tsaye ta ɗan kurɓa coffee dake hannunta sannan ta a je Cup ɗin. Ta ƙari sa gaban farin allon tare da juyo da kallon ta gare su sannan ta fara magana cikin Muryarta mai cike da jarumta rashin tsoro fikira da basira tare da jajircewa.


“Wannan kisan kai sam bai yi kala da sheƙe kai ko na ɓarayi ba ko kuma domin wani ɗaukar fansa kamar yadda wasun ku suka yi tsammani”


Ta
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download RANAR BIYAN BUƘATA Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album