Join Our WhatsApp Group

BAKIN JININA YA JAMAN Season 2 Complete Hausa Novel Document by BAKIN JININA YA JAMAN Season 2


BAKIN JININA YA JAMAN Season 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 52852



BAKIN JININA YA JAMAN Season 2

Reading Time: 4 Hours

Added On: 10, Sep 2023

Author: Jameela Jameey ƴar mutan Kankia ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Manazarta Writers Association

Author Phone : +234 816 050 8316

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 296.88 kb

File Type: txt

Views: 525+

Download: 299+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: BAKIN JININA YAJAM S2 na YAR MUTAN KANKIA



*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


*Godiya ta tabbata ga Allah daya sake ara mana lokaci mai tsada da dimbin daraja inda zamuci gaba da labarin rayuwar Amina,yanda muka gama ALQALAMI Season One lafiya Allah yamu ikon gama BAKIN JININA YAJAMAN Season two ameen.*

_Naga sakonin ku dafatan alkhairin da kuka dinga yiman,Amina Caranci nagodiya Allah yabar zumunci._

*Muje zuwa🤸🏻‍♀️*

S2/E1&2


Na shiga tashin hankali tareda kalubale na rayuwa narasa duk wani farin cikina da sukunina kullin ina cikin zullumi da fargaba musamman halin dana tsinci kaina a Jami'a ga tarin fargaba marar misaltuwa a gefe guda kuma ga challanges na dangi da yan unguwa kowa da abunda yake faɗa akaina bayan kowa yasan yankema mutun hukunci akan abinda baka da ilimi akanshi haramunne,lallai nasan komai yake faruwa dani yana cikin Qaddarata amman ya zanyi bayan nasan koma minene yanada sila da *BAKIN JININA YAJAMAN!*

_Amina Caranci kenan wadda take cikin wani yanayi na rayuwa._

*Muje zuwa domin cigaba da labarin gadan gadyayi


_Cigaban Labari*******_


Fatash ta fito a cikin motar Ya Taufiq kallan dayake jifana dashi kadai yasa na sha jinin jikina hakan yasa a hankali nafara takawa zuwa inda motar shi take a tsaye kaina kasa nike tafiya saida na kusa isowa bakin motar ya figi motar shi har kura nadan tashi yai tafiyar shi wani irin mummunan faduwar gabane ya riskeni narasa dalilin jin hakan take na shiga damuwa.


musamman hudubar dayake yawan yi mani ta dawo mani cikin kwakwalwata jinayi duk ban lafiya,karfin hali kawai nayi jin Fatash ta kamo hannuna muka juya zamu koma hostel.

Amina pls kitsaya ki saurareni cewar Ahmad dan harna manta dayana wajen.
Cak na tsaya saidai ko kallan shi banba,saima wani irin haushin shi da naji ina blaming dinshi akan abinda ya faru.


"Amina ki saurari abinda nafada maki karkimin haka."
Daga mashi hannu nayi najiyo raina a dagule nace.
"Dan Allah Ahmad ka sauraramin kabarni da abinda yake damuna na rokeka kafita rayuwa karkayi gigin shigowa a cikinta dan baka da wani muhalli da zan iya baka,kabarni dan Allah karatu ke gabana ba wata soyayya ba."

Ina gama fadar haka na fisgi hannun Fatima muka tafi daki ji nike kamar inyi kuka,musamman da Ya Taufiq yatafi a fusace kuma nasan hakan ya nada nasaba na ganina da wani bayan alqawalin da nai mashi bazan kula samari ba,duk da Ya Taufiq yace yana sona amman nasan tunda har aka fasa sa ranar mu,zai hakura da sona,saboda hakan yake yimana fada kada mu kula samari mu dage akan karatu,sai gashi tunkan tafiya tai nisa ya ganni da saurayi.



"Haba Minal akan mi zaki zauna kina dogon tunani kin tisa abinci gaba kina kallo kuma kinki yin magana."


Hmmm Fatash kenan dan Allah kibari bakisan yanda nikeji bane,tunkan karatuna yai nisa nafara samun matsala ga wannan Ahmad din da Ya Taufiq ya ganni dashi na tabbata zaiga ban dauki maganar da mahimmanci ba kenan."


Aaa sam bakisan Ya Taufiq bane ko maganar da wahala yai maki ita saidai zai baki shawara,kuma tunda kince baki son shi ai komai ya wuce."


"Allah yasa,amman abin na damuna."
Da haka mukaci gaba dacin abinci amman saidai badan yai mani dadi ba,hankalina kaf yana wajen Ya Taufiq fatana Allah yasa kada yaiman maganar Ahmad dan bansan mi zance mashi ba,saurin cire hannuna nayi a cikin abinci tuna maganar Dr JJ ya zanyi dashi.



Kaina ya sara mani hakan yasa naje na kwanta da tunani iri iri araina,ko bacci na kasa jin ana kiran sallah natashi nai alwallah natada sallah.



****** Lecture Theater zaune muke bisa Chairs kowa yazo da wuri muna jiran shigowar Dr JJ dayake shike garemu kuma ka'ida idan kayi late bazaka shiga ba,ya iya disga mutun wannan dalilin yasa kowa ke shayin ya rigashi shigowa Class,zaune muke na kifar da kaina kasa inata nazari abubuwa sun mani yawa,domin bansan sadda Dr JJ ya shigo ba,kowa yai shiru annatsu harya fara lecture,saida ya duba gaba kamar yanda yasan nan nike yawan zama amman ba alamuna,saboda koda na shigo second to the last sit na zauna, dan bansan muna yawan hada ido dashi inyana mana lecture musamman dayace yana sona,shiyasa na koma baya na zauna.



Rufe idanuna nayi kamar mai bacci,fuskata ta tana kallan ƙasa na hada hannyena bisa desk na daura kaina saman hannuna nayi zurfi a tunani bansan mi akeyiba,jin ta kusa dani tana bubbugani a hankali hakan yasa na dago in kallan ta,murmushi tadan yimani,ganin ba wani abu tace mani ba hakan yasa na sake kifar da kaina kasa.


"Baiwar Allah Dr JJ na magana."
Wani abu naji ya keta cikin kunnena a hankali nafara ɗago da kaina jin hall din yai tsit kamar an mutu ga idanun kowa akaina hatta shi dake saman step yai holding hannayen shi.

Stand up."
Shine abinda yace mani,mikewa nayi duk na tsargu.
What are u doing?" sorry sir."
Abinda nace mashi kenan ina kara maida kaina ƙasa.
I say mikikeyi."
Nothing Sir."
Get out of my Class."
Jikina yai sanyi gashi ya hade rai,ganin idanun mutane akaina hakan yasa na dauki jikkata na fita duk nashiga damuwa dan bansan mi zaije ya dawo ba, nasan zaiyi tunanin saboda shi na koma last sit na zauna.


Ban wani batama kaina lokaci ba,na tafi hostel saidai Fatima bata dawo ba,abinci nafara kokarin girka mana.



******Baba Pov

"Maman Amina kinsan abin nan yana damuna yana ci mani tuwo a kwarya,musamman kananun maganganun mutane akan Mamana nagaji da al'amarin nan."


Ajiyar zuciya Mama ta sauke tace.
"Haba Alhaji hakuri shine zamuci gaba dayi kowa yasan wacece Amina baccin wannan kadararrar sa ranar da akai mata ai da bata shiga cikin wannan gutsiri tsomar ta mutane ba."

"Ni duk ba wannan ba dazun Hafizu ke mani magana wai yaji wasu samari nacewa wani saurayi yazo yana neman makarantar da take karatu, kowa yasan dagani saurayin tane,amman ni nasan ya'ta bata da wani saurayi kuma Taufiq aiba bako bane tunda yasan inda take karatu al'amarin ya dameni baki ɗaya."



Ba dadi amman haka Allah yaso komai zai zama labari,ni kaina kan wannan Jami'ar da tafi karkaso kaji kowa da kalar zancen da yakeyi sai kace kanta farau,koda yake kusan dai a cikin mata nan kusa damu ita kamar zan iya cewa tafara shiyasa abin ya zama zunubi Allah dai ya kyauta ya tsare mana ita da kariyar shi."


Ameen wannan itace addu'a ni nayarda da ya'ta kuma nasan wacece Amina Allah dai yai mata albarka."

Ameen ya rabbi.


*Fiction*

Taufiq ne cikin sashen shi yarasa mike mashi dadi musamman dayaga Amina tareda wani ,hakan ya taba mashi zuciya sosai shi kanshi har mamakin kanshi yakeyi tambayoyi yafara jefoma kanshi.


Miyasa Minal zatai mani haka? Waye shi,mi yake nema wajen ta?ya zatayi da karatun ta idan harta fara soyayya? Can kuma wata zuciyar tace miye ruwan ka tunda tana ganin wannan rayuwar itace dai dai da ita,karabu da itaTaufiq kaima kaje ga yan mata nan kala kala kanema ka aura,akan mi zaka tsaya batama kanka lokaci akan kankanuwar yarinya waddama ba sonka take ba,da bakinta tace bata sonka gashi Abba yace baka aurenta mizaisa ka damu kanka,ga dan uwanka can da matar shi sai kai,haba Taufiq kafarka daga baccin daka lula kullin fa kara shekaru kakeyi Hussein!

Can kuma ya girgiza kai kamar wani zautacce a zahiri ya furta.
Never bazan iya rabuwa da Minal ba itace zabina ina sonki so na hakika dake na shirya rayuwa Minal in kinga ban aureki ba kilan Allah baisa zan aure ba a rayuwata ba amman kece farin cikina Minal dan Allah kada ki kula kowa kiyi karatu Aminatu."


Ya ida maganar yana kallan picture dinta yana karajin sonta a cikin zuciyar shi.



Amina Pov


Tunda Dr JJ ya koreni Class dinshi duk ranar da yakeda Class idan har yari gani shigowa ina zuwa zai korani,idan kuma ya iskeni ciki koda ina gaba zaune yana fara lecture zaiyi sending out dina waje tun ban damuwa harna fara,domin kowa yasan indai yafara tsanar mutun shikenan bai kara daga maka kafa sunsa tun korar dayai mani ta farko ce tajawo mani wannan tsanar daga gare shi,ni kuma nasan dalilin sa nayi mani hakan.


Gashi course din shi babban ne yana dauke da 4 credit unit kuma kowa na shakkar course din wasa wasa ankai sati ukku bai barina ina attending lecture din shi,gashi next week zai mana test kuma duk banda attendence dinshi rabi da kwata,ba kadan hankalina ya tashi ba daurewa kawai nike ina karatu saboda ya bada handout.


Kullin hankalina da tunanina nakan test din da zamuyi ta Dr JJ wanda kowane dan course din mu ya maida hankalin shi kanta.


Ranar Monday a ranar zamuyi test din tunda muka tashi da wuri nacema Fatash zanje Class domin yau mukeda Dr JJ domin haka kawai muke cewama Course din nashi da kace Dr JJ kowa yasan abinda kake nufi addu'a taimani tace ita yau bata da komai hutawa kawai zatayi.
Murmushi nai mata nace damani wlh bokon nan ba dadi karfin hali kawai nikeyi.




Fita nayi zuwa school area akan hanyata nasamu Commercial motor na hau har gaban Department suka ajeni na karasa ciki,kai tsaye theater na nufa aiko rabi da kwata duk anzo banfi minti da goma da zamaba saiga Super Visors sun fara zuwa,ciki duk ya duri ruwa saboda first test dinmu ce a University,musamman yanda ake zuzzuta mana lecturer din da rashin mutuncin shi ga ya iya setling Questions,suna shigowa kowa ya nutsu haka suka gama setting arrangement dinmu jiran shigowar shi kawai ake yana shigowa ya tsaya daga baya aka fara raba Question Paper saida kowa ya samu sannan ya tafi dayan hall din saboda watsamu sukayi wara wara akai mana,duk da bawani karatun kwarai naiba amman dana duba Question din sai naga nasan wasu harda tambayar da yaimani a class ya dawo da ita ban wata wata ba,nafara answering hankalina kwance duk da akwai apply Question sai nafara amsa wadda nasani,ina cikin answering naji an fizge mani Paper saboda a Fullscape muke test.



A firgice na dago zuciya ta na bugawa naga Dr JJ yana mani wani killer smile dukar da kaina nayi nace.
"Sorry sir dan Allah kabani in ida pls."
"Get out."
Hankalina yai bala'in tashi kaina ya kulle ganin first test dita zanfara da kora kuma babban Course irin wannan wanda kusan shike rike da GP dinmu.
Bansan na duka ba nafara bashi hakuri har idanuna sun kaɗa,haka lecturers din suka fara bashi hakuri ganin yanda na rude na fita tunanina amman ya kafe saina fita karshe cewa yayi.

"Idan nayi counting one to three i swear i will give u a Carry Over (CO)."
Jiki mace na mike ina kwalla a gabana ya yaga mani paper din ya watso mani ita,bisa step naje na dauki jakata natafi ina kwalla,jikina yai masifar sanyi har banganin gabana tafiya kawai nike bisa titi bansan mike damuna ba hankalina bai jikina ga ciwon kai wanda tsananin damuwa harya zame mani jiki tsallaka titi nazoyi naji ana banka mani uban Horn na tashin hankali,har saida mota ta kusa gogata,a rude na dawo duniyar damuwa ganin wasu har sun aza hannun su,bisa kai alamun sallallami sukeyi dan dayawa an dauka motar tabi ta ruwan cikina,ni kaina jikina banda mazari ba abinda yakeyi na watsar da jikkata sai wayata dake yashe ƙasa ni kaina kasan nike zaune dabas banda rawar gabbai ba, abinda nikeyi kaina keta juyaman ina ganin mutane kashi kashi,suna juyawa bansan na aza hannaye na bisa kunnena ba na saki uwar kara mai rudarwa ina jijjiga kaina.


Shiko Driver din yai zaune yakasa fitowa duk tsoro ya kama shi ganin naki tashi wadda ke gaban motar ta fito tana sannu baiwar Allah tashi,Allah ya auna mana arziki,shima sai yanzun yajawo kafa ya fito ran shi abace yace.....






_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E3&4



"Wane irin sakarci ne wannan bayan kin hayema mota,Allah ya soni ban takeki ba,shine zakizo ki mana zaune akan titi, dallah malama kitashi bani wuri stupid.!"


Kaina na dago ina kallan shi ko keftawa banyi sai kwalla da suka samu damar cigaba da zirara bisa idona maganganun shi suka bani mamakia,sai yanzun juwar tasamu damar lafa mani,wato baima tambayar lafiya ta shine zai fara yimani bala'i.



Haba yaya bai kamata kai mata fadaba ai barka zamuyi ma juna tunda bataji ciwo ba,kamani tayi ta dagani ta miko mani jikkata da wayata harta dan fashe.


ina sakala takalmina nai saurin cire kafa saboda zugin da tai mani banjin zan iy takata sosai,godiya nai mata najuya ina tafiya a hankali tace,in shigo su rage mani hanya maganar Ya Taufiq ta fado mani arai yai mana kashedin hawa lift shiyasa naki yarda da kyal tasamu na amince har hostel suka kawoni sannan na sauka na tafi,ina dingisawa a hankali,ji nayi anrikoni kanwar shi tace dan Allah ya sunanki."
Amin Yusuf.
Ni kuma Zainab Sule Garko."
Bari inrakaki dakin ki naga kin razana bakida kwari sosai.



Ban mata musuba muka tafi a hankali nike jef kafata duk tai mani tsami muna tafiya tace.
" dan Allah Amina kiyi hakuri akan abinda Ya Hafiz ya fada maki saurin fushine dashi kinji."
Bakomai nace mata har muka shigo room dinmu,yanda nike tafiya hkan yasa Fatash tashi da sauri ta taroni,lafiya Minal miyasame ki.?"
A rude take tambayar mu,Zainab tai mata bayani tace
"Ai an auna arziki Allah ya kyauta gaba,level one kuke.
Eh muka ce mata."
Nima 100level nike ina karantar Pharmacy."
Kufa ni nace mata Medicine Fatash Enginearing."
Nan tai mana bankwana tace a gari take zaune.


Tafiya tayi nikam kamar jira nahau kuka ina cewa
Nabani Fatash kwanana ya kare ya zanyi."
Haba Minal kidaina kuka tunda abin yazo da sauki dan Allah.!"


"Ba wannan ba Dr JJ ya hanani yin test dinsa kuma over 40 zaiyita zanyi making wannan uban mark din da narasa mi nai masa da har ya tsane ni haka,dan Allah minene mafita ya zanyi ya tsaneni bai sona ni kadai yakema haka,wlh Fatima nafara zargin Bakin Jini gareni,inba hakaba akan mi zai hukuntani ta hanyar tsanata banci ban sha mashi ba kuma....



Kukan yaci karfina naita kuka tana lallashina tace.
"Ni banga wani bakin jinin da zakice shi yaja maki ba,kawai dai kije ki bashi hakuri zuwa gobe kiji mi kikai mashi insha Allah zai maki make up dinta kidaina kuka.

"Shiru nayi ina tuna yanda nayi dashi a office din shi gashi har an shiga wata ɗaya bankara bi kota kanshiba yanzun taya zanfara yi mashi maganar,nasan da whala ya hakura,ajiyar zuciya kawai na sauke ina gayama Allah kukana.


Saidai still kwalla nike tun Fatash nabani hakuri harta gaji ta kira Taufiq tagaya mashi na samu accident,inajin yanda yaketa jera salati yana fadin garin yaya hakan ya faru? tai mashi bayani da yace tabani wayar sai kuma naji yace wait ina zuwa i will call you.
Katse kiran tayi nace.
"Akan mi zaki gaya mashi bayan kinsan shima yanajin haushina dan Allah Fatima wlh da baki gaya mashi ba,in ya kiraki...


Read / Download BAKIN JININA YA JAMAN Season 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album