Join Our WhatsApp Group

AUREN SADAKA Complete Hausa Novel Document by AUREN SADAKA


AUREN SADAKA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 60376



AUREN SADAKA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 04, Apr 2023

Author: Safiyya Muktar Garba ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Elegant online writers

Author Phone : 09042684315

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 217.5 kb

File Type: doc

Views: 3288+

Download: 1139+

Last download: 2 days ago

Description/Story: NA WHATSAPP DA DAYA NUMBER YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI* *09042684315* *WANDA SUKA TURO MIN KUDI SU TURAMIN SHEDAR BIYA TA SABUWAR LAMBATA NAI ADDING NASU A PAID GROUP NGD.*


Saadatu shi ne asalin sunana amma ba a kirana da shi haka sai Wai aikun mutane ne suke kirana da hakan amma yawanci anfi kirana da Sa'ade saboda Sata suna irin na mutanen gari ma sai aka daina kirana da Sa'aden ake cemin Ade kawai haruffan ™arshen sunan kenan don haka duk ragowar sunayen Sa'adatun da Sa'adah da Sa'aden da Sa'a duk sai suka Sata aka koma Ade kawai saidai kawai wanda na tsira a gunsu Mamana da ´an uwana sune suke faWamin sunana mai daWi amma even haka bazasu faWi ba tun ina faWa da fishi bare da nake mai zafi har na gaji na sallama musu,
³an asalin garin Kano ne mu ta dabo timbin giwa ko da mai kazo an fika tsakiyar Birni cikin Unguwar ˜ofar Na'isa Mahaifina kenan shi ne haifafffen nan Mahaifiyata kuma ´ar asalin jihar kaduna ce cikin garin zaria kenan a nan ya Aurota ya kawota kano cikin ahinsa.
Gidanmu Babban Gida ne Family house da kakarmu wadda ta haifi mahaifinmu da yayyen mahaifinmu da ™annensa su da matansu facaloli duk haka ake cakuWe a gidan ana zaune kowa da sasanta amma kasancewar gidan kamar na gado tun da cancan tun mahaifinsu yana da rai ya bar musu gidan ya ce kowa yayi Aure ya sa matarsa a ciki bai yadda wani ya fita waje ya zama bare ba bayan babu ransa duk wanda ya fita to bai yafe ba, shi ne suka gyara gidan akai masa gyare gyare sosai kasan cewarsa Baban nasu mutum ne mai arzi™i na gaske tun a zamanin da yana zuwa fatauci gari gari ya tara arzi™i da dukiya mai yawa ya mutu ya bar musu Gado Da suka girma kuma sai arzi™insu ya daWa faWaWa don kaf cikinsu babu wanda bai bawa miliyoyi baya ba, kowa yayi Aure da matansu da ´a´ansu
Mahaifinmu Shi ne ™aramin cikinsu Baba Abdulhadi shine Babbansu ana kiransa da Alhaji Hadi, Sai na biyun Baba Musa ana cemasa Alhaji Kalla sai na ukunsu Alaji Isuhu, muna kiransa da Baba Isuhu sai na HuWunsu Baba Maigida ni ban ma san sunansa na Gaskiya ba don haka na taso naji ana cemasa sai Wan Autansu Abbanmu Salahu shi kansa baya son sunan Har yana faWama Kaka mahaifiyarsa ta ce to in bayaso yana iya zuwa ya sayo sabon rago ya yanka amma ita bazaya zo ya dameta ba saboda ya sha faWa mata haka ya kance Kaka bazan canza ba amma zan daina amfani da shi ba don da yawa ma bazasu sanshi ba Ya koma Alajin kawai sakamakon sauran ´an uwansa da sai an haWa da sunayensu Alhaji wane to har yai Aure mu ´a´ansa muke cemasa Abba don haka ma ko a makaranta sunan muke amfani dashi kamar ni Sa'adah Abba, don kowa da haka yasan ni indai ´an makarantarmu ne to Sa'adah Abba mutan gari Kuma Ade.
³a´an Mamanmu mu huWu ne maza uku nice Auta ta huWu Yaya Auwalu shi ne na farko sai na biyu Yaya Sani sai na ukunsu Yaya Salisu sai ni Auta Ade dukansu sun gama karatu suna taSa kasuwanci kafin Allah yasa aikin ya zo ni kuma ina University yanzu Level one hundred ban daWe da shiga ba,
Wan Abbanmu na farko Baba Hadi shima ´a´a huWu gareshi duk maza kusan saanin su Yaya Auwal ne saboda bai samu haihuwa da wuri ba Yaya Mahmoud sai na biyunsu Yaya Amin sai na Uku Yaya Umar da Yaya Walid,
Sai Baba kalla shima duk maza Yaya ishaq, Yaya Abdul hadi me sunan Baba Hadi ana cemasa Abdul, sai Yaya zakariyya,sai karaminsu mai sunan Abbanmu salahu Ana cemasa Yaya Deen,
Sai Baba isuhu da Baba mai gida suma maza kowa biyu su Allah bai basu haihuwa da wuri ba yayan Baba mai gida Yaya Junaid da Yaya Ubaid, Sai Baba Isuhu Yaya Safullahi da Yaya Abbas,
Wadannan sune rankatakaf yan uwana na gidan sai uban yawa kusan mu ashirin da biyar a gida daya bataliya guda kenan gashi duk maza, kaf yayan gidan maza ne dukkansu ni kadaice mace a yaran gidan, shiyasa na taso rayuwata kamar irin ta maza a tsaye nake babu alamun raini sam a tattare dani Babu wanda zai ganni ya kawo min raini don ni mace ce mai kama da maza Mamana tayi tayi ta gyarani na daina Halina amma ina na kasa to dakinmu maza duk yan gidanmu maza a cikinsu na taso tun ina yarinya cin abinci dasu zuwa makaranta dasu wasa dasu komai na, Mamata babu irin fadan da ban sha ba a wajenta ta ce Babu kyau wasa da maza Sa'ada duk wanda yake wasa da maza Allah zai konashi a wuta amma cikin ikon Allah ina fita wasa maganarnan zata zirare ta bayan kunnena,
Dambe kam babu irin wadda ban iya ba tamkar yar rustling da harbi da kafa da naushi ga iya hawa bishiya tamkar yar biri to da na girma ne ma na dan samu na rage da rokon Allah da Adduar Mama don lokacin na fara zama yan mata amma dai ina nan yadda nake,
Da na shiga secondary school banada kawaye mata sam sai Abokai maza kala kala daga wannan sai wannan bana tsoron malamai balle kuma ajega prepet in tamun cin ubanta nake babu abinda ya shafeni akai karata wajen malamai iyakaci nai kneldown ko tsallen kwado wannan ko ba sabona bane bana tsoron ta mutu Ballantana tai rai na fita sanda nakeso nashiga class sanda nakeso Babu mai sani balle ya hanani raina fes, school bus ma hanani shiga akai saboda masifata ake aiko driver daga gida ya tafi dani,

&&& &&& &&&

Bayan na dawo a makarantar Boko nai wanka a gurguje naci abinci nai sallah nashiga dakina nai wanka nasa JC kayan Ball dina nadau school bag katuwa na saba nasa cambers dina a ciki da Pcap na zura katon hijab na har kasa ruwan madara na zura slifas na fice falo,
Kamar yadda na zata Mama ita kadai na tarar a falo tana kallo nai mata sallama na ce " Mama na tafi makaranta" ta ce "to yar Albarka yau da wuri hakam"? Na ce "Eh Mama zan bada hadda ne inaso kafin ya sayyadi yazo naje nayi murajia", ta ce "To Allah yayi miki Albarka ya kareminke a duk inda kike ya shiryaki ya baki ilimi mai Amfani", na Amsa da "Amin Mamata" kamin nasa kaina na wuce,
Ina fita na tarar da Yaya Deen tsaye kan mashin dinsa yana jirana yana ta faman duba Agogo yana doka uban tsaki na karaso zai faramin fada "na dakatar dashi as kaga Yaya Deen dakatamin bakasan da yaya ma na samu na fito ba kasan Mama na nan zaka faramin Bala'i, sanin halina da yayi da naci da mita ya ce "hau hau ni mu tafi ana can an fara muna nan", na ce "to tsaya na cire wannan shegen hijabin kasandai bazan tafi da shi ba naje ya buga ni da kasa Babu gaira babu dalili", na cireshi na cukuikuye na danna a jaka nasa slifas din shima a jakar na dauko booth din takalmina da P-cap na sanya na goya school back din badon gashina da ya leko ba da kirjina da cewa zaayi namiji ce sak, na dare kan mashin din ya tayarda shi yai juyi ya zana kwabo da tayar da kura sananna ya fananoshi a dari da sittin sai filin kwallo na Abacha Youths Center.


Ba mu muka dawo ba sai magriba kuma yayi daidai da lokacin tashinmu makaranta, muna shigowa layin nace ya ajiyeni a bayan gida ya zagaya ya ajiyeni ya nufi masallaci nikuma na sanya hijabina na cire booth din da P-cap na maida slifas din nai bakin get, na tarar ma sun shiga sallah na wuce Sasanmu na leka dakin Mamana tana sallah na maza na shige dakina na kwabe kayan na canza wasu sannan hankalina ya dawo jikina nima nai Alwala nai sallah na,
Na janyo wayata na bude data na hau online, Group dinmu na yan Ball K/Na'isa United na shiga na dudduba sakonni ana ta nemana ma zanyi Adding mutane bana online saboda ni kadaice a group din mace yasa suka bani Admin, Sallamar Yayyena da naji yasa nai maza na boye wayar karkashin filon katifata na mike na fita nasan halinsu yanzu zaa fara ina nake ana kwadamin Kiran da babu dalili,



*PAID BOOK 300 ONLY*
*SEND VIA THIS ACCOUNT=ØGÜ*

*SAFIYYA GARBA MUKHTAR*
*JAIZ BANK*
*0007688753*
*EVIDENCE OF PAYMENT HHERE=ØIÜ 09042684315 siyan na gari maida kudi gida*


*AUREN SADAKA BY SAFIYYA MUKHTAR GARBA*

#Share 'þ
#comment'þ
#EditingL'




*AUREN SADAKA 3&4*





*AS.Episod one.pg3&4*. *E*O*W

*09042684315*=ØÞÜ

=Ø…Ü*FC'- 'D5/B)*

*AFUWA DA JINA SHURU LAYINA YA SAMU MATSALA AN MIN HACKING ACCOUNT DINA NA WHATSAPP DA DAYA NUMBER YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI* *09042684315* *WANDA SUKA TURO MIN KUDI SU TURAMIN SHEDAR BIYA TA SABUWAR LAMBATA NAI ADDING NASU A PAID GROUP NGD.*



Sun dawo dukansu su ukun Yaya Auwal Yaya Sani Yaya Salis Mama ta fito suna zaune a falo a kasan carpet Mama na kan kujera naje na gaishesu da musu sannu da zuwa aka amsamin ba yabo ba fallasa, na zauna kan kujera suka daka min tsawa harda hada baki wai suna kasa ni ina sama nai maza na sauko ina cuna baki dama sun tsaneni a cewarsu wai halina na banza suka tsana bani dinba,
Mama ta ce "to kun dawo zaku fara, kuyi mata a hankali mana in daya yace ta sauka ma zata sauka ba sai kun mata rubdugu ba",
Yaya Auwal ya ce "kinga irinta ko?kinga irinta ko Mama? Ke kike cewa Kanki yarinyar nan ta dameki amma da anzo zaai mata fada sai ki hau kakkareta tsakani da Allah ai rayuwa ba haka take ba, ni zan zare hannuna akanta wallahi haba shegiyar yarinya saikace Aljana?",
Mama ta ce "yi hakuri Babban Yaya ai mana hakuri nida Yar tawa, amma a daina aibatamin ita in baza ayi mata addua ba to mutum yai shuru falyaqul khairan au liyasmut",
Ya ce "shikenan Mama kin bata lasisi tayi duk abinda taga dama gaki nan gata",
Ta ce "au baka fasa ba kenan kunga ku bata abinda zaku bata ta koma daki ni banason hayyata",
Ya fito da lemon bawo da Ayaba ya dangwara min a hannuna Yaya sani ya bani fura damammiya a leda kulli daya shikuma yaya Salis ya bani tsire yanka uku, ya ce "jaka gashinan sai kije kitaci na tashi sum sum nabar wajen A zuciyata na ce "Allah ya isana kuma ni ba jaka bace", na shige dakina,
Dama sun saba duk dare kowa ya dawo daga kasuwa sai yayi tsaraba ya kawowa Mama a hadu a ci nikam saidai a sammin nawa na matsa inko na sake na zauna kusa da su sai sun kusa cinye ni da baki saboda masifa,
Akayi sallar Ish'i dama ina da Alwalata na mike nayi nai shafa'i da wutri Nagama komai na Al'adar rayuwata kafin na haye kan katifata na ja bargo na hau online na shiga Facebook, bani na sauka ba sai biyu saura na kashe na sake Addua na kwanta, Asuba ta gari

Washe gari kamar yadda take Al'adar gidanmu mudai a Sasanmu zamu hadu bayan an idar da sallar Asuba mu zauna muyi murajia da azhkar da Addua sannan a fara shiri masu Shirin makaranta nayi masu shirin kasuwa na yi, sannan kowane Sasa (part) saikaje ka gaishesu saikuma a hadu a dakin Kaka a gaisheta sai kuma a fito Haraban Get jiran Driver ya fito da mota a Garage mi ta shiga dake kusan kowa makarantar sa daban wasu Rumfa college wasu FCE wasu Legal Wasu SAS ta maza mune na karshen saukewa nida Yaya Deen saboda tamu ta fi nisa kuma kamar private ce maza da mata a hade dayake akwai Christan a ciki daga malaman har daliban don haka kowa ya zauna inda yaga dama bencin mu daya nida Yaya Deen,
Muna gama third period aka fito break dama a matse nake zaman class din duk ya isheni, capteria na nufa wajen Adamu mai shayi da bread yana ganina ya fara washe baki "Ade! Cau cau! Ranki ya dade zamanin ki ma ya dade Ade tamu ta gargajiya", ya dinga famfani da kirari naji kaina ya kara girma kaman zai fashe na danyi murmurshi na dunkule hannuna na bashi muka gaisa irin na gayun nan don shima haka hakane kura ce tai Lafiya, na samu gu na kyafe yace tanawa zaa sheko miki? Nace yimin hadin dari hudu komai da komai, in minute kuwa sai ga shayina hadin kauri bredi indomie da kwai na zauna na ci na gode Allah lokacin har an koma break dama 30mint ne nai maza na haura baya na fiddo da JC a cikin school bag dita na dora kan uniform din na dira ta katanga,
Filin kwallo ne cike yake da yan Ball ana ta tafka musu ana fafata wasa ana ganina akayo caa akaina suka dagani Sama ana ta murna da ganina ga raba gardama ta zo, suka gama dagani sannan suka direni kasa na ce "ya akayi yanzu? Akace akan me tsaron Raga ne ansa wancan Garan bai iya ba yasa anyimana ci biyu kwarara gashi bakizo da wuri ba", n an ce "aa kune dai kuka fara da wuri amma ni ai lokacin tashi na daidai nazo", suka ce " eh kuma hakane muje dai yanzu a fara", aka hura Usur aka fara.
Shigata sai da muka cinye Ball dinnan tas! Aikam hatsaniya ta tashi wai wallahi basu yarda ba basu yadda dani ba ni na daina zuwa kawai na fita basa sona in bahaka ba wallahi bazasu yadda ba nanfa dambe ya harke takaiga har anjiwa wani ciwo aka kira yan sanda nidai na silale na gudu don bazan bari a ritsa da ni ba na haura ta katanga na dira ta bayan ajujuwa na hango ma har an tashi masu tafiya a kafa wanda gidan su babu nisa da school wasu kuma suna shiga school bus,
Nai maza na shige rububi kar a ganni na samu gu kusada Admin block na zauna ina jirana driver, ina ta duba agogon hannuna tsaki kam nayishi...


Read / Download AUREN SADAKA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album