Join Our WhatsApp Group

TUNA BAYA SHINE ROKO Complete Hausa Novel Document by TUNA BAYA SHINE ROKO


TUNA BAYA SHINE ROKO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 34447



TUNA BAYA SHINE ROKO

Reading Time: 2 Hours

Added On: 05, Dec 2023

Author: Sumayya Abdulkadir Takori ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07030137870

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 180.45 kb

File Type: txt

Views: 1002+

Download: 516+

Last download: 1 day ago

Description/Story: TUNA BAYA SHINE ROKO!


1













SUMAYYAH ABDULQADIR
babbangoro2015@yahoo.com

Copy write: Takori
Hakkin mallaka: Takori

Shekarar Rubutu; 2004
An fara bugawa 2010
An sake bugawa a wannan shekara 2015

FATAN ALKHAIRI
Mal. Dr. Sani Lawal Malumfashi, (Dept. of Sociology), Sub-Dean SMS, BUK. Mallam Allah ya kara GIRMA.

SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafi ga marigayiya Haj. Hafsatu Tijjani Bichi, principal GGC Kano, wadda ta rasu 26/7/2004. Allah ya rahma mata ya inganta mata zuri’arta da ta bari Ameen.




KUNA RAINA
Nafisah Mohd. Dan kaura da Nafisah Adam Yola. Da biron ku na rubuta TUNA BAYA…Kenan dole in ke tuna kaunar da kuka nunawa rubuce-rubuce na..


















DAGA MARUBUCIYAR….
Littafin TUNA BAYA SHINE ROKO, kirkirarren labari ne dana kirkira domin fadakarwa da nishadantarwa kawai tun a shekara ta 2004, na rubuta shi da wani suna daban da wata siga daban ba wannan ba, rashin dab’I da wuri ya janyo sauye-sauye da dama a cikinsa. Ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba haka ba’a dauki rayuwar kowa ba don haka in kaji wani abu da yayi kama da naka to arashine kawai aka samu.
Suna, garuruwa da mukamai da akayi amfani da su acikin labarin, bana kowa bane. Asali ma kawai sakon littafin shine ya zamo nasiha ga iyaye mata irin Mubina kan muhimmancin rainon ‘ya’ya musamman daga shekarun daya zuwa biyar.



-Takori

‘YAN UWA RABIN JIKI
Dr. Aminah Ja’afar Musa Gombe ( Mrs Sa’ad kuma TAKORI na)
Furairah Ja’afar Musa (Maman AbdulBasid) da dukkan iyalin Alh. JafaruMusaGombe ALLAH kara zumunci har ‘ya’ya da jikoki.
.

KIYAYEWA
Kiyaye hakkin mallaka ga marubuciyar shi wajibi ne; Sake bugawa (reprinting), bada haya (renting) ko sarrafawa ta wata hanyar daban, kamar rubutawa a duk wani SOCIAL NETWORK (WHATSAPP, FACEBOOK) da ire-irensu ba tare da iznin marubuciyar shi ba, zai fuskantar da tuhuma daga Lauya na Barrister Sadiq Rufa’I Wali. Idan kunne ya ji…



KAUYEN KARAYE (1980)
A
garin mu KARAYE, mahaifina, Mallam Mamman, wanda aka fi sani da MAI KALWA, sananne ne akan sana’ar shi, ta saida kalwa, wadda ya gada tun iyaye da kakanni. Kowa ya taso a kauyen Karaye, da sana’ar da ya san shi kenan.
Kamilin dattijo, talaka tikis wanda bai aje ba, bai kuma ba wani ajiya ba. Mai wadatar zuci, bashi da kwadayin abin duniya ko kadan. Koda aka san shi a matsayin talaka, kowa yana girmama shi sabida mutuncin sa.
Ga wanda duk ya san Maikalwa, zai shaideshi akan gudun duniya, kyamar abin hannun mutane, in ba wanda gumin sa ya amso mishi ba.
Matar Maikalwa, tun ta ladan noma, Indo, ita ce uwar manyan ‘ya’yan sa maza uku, Auwalu, Sani da Salisu. Tun bayan haihuwar Salisu Indo bata sake haihuwa ba, sannan ya auro Lami, ta haifi Rabi’u da Atika, itama din kamar hadin baki daga kan Atika haihuwar ta tsaya mata cik.
Lami ‘yar babban gida ce, a garin Karaye kowa ya san Ubanta. Tun zuwanta ta kame gida, Indo ta zama ‘yar kallo, sai abinda tace za’ayi, wanda ta hana, shima ya hanu. Shi kanshi Mai kalwa, shayin Lami yake, sabida masifar ta, inda Indo ta kasance, jarumar Uwargida, babu abinda ya dameta kamar harkar cikin gida tana kuma ‘yan kulle-kullen Omo, suga, gishiri, barkono, kanwa, citta mai kwaya, masoro, kanimfari da sauran kayan kulli ta daurawa Sani da Salisu.
Don haka duk ranar girkin Indo, Maikalwa bai san kudin cefane ba, sai dai ya ci mai kyau shida iyalinsa, duka a aljihun, jarumar uwar gida, Indo. Wannan ya bata wata daraja ta musamman a idon shi, da jama’ar gidan duka, har ‘ya’yan Lami, suna mutunta Goggo Indo.
Allah kuma yasanya mata albarka cikin al’amuranta, har ta kai ga, Indo sai dai awo, kwano ko rabi. Ta nan ta samu ta tura ‘ya’yanta makaranta, bata ware ba, ta hada har da Rabi’u dan wajen Lami, dan shekaru takwas.
Tsakanin Indo, da mijinta Mallam Mamman Maikalwa, mutunta juna da darajja juna ne ziryan. Wannan ya haifar da kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin su da ‘ya’yansu duka.
Don haka koda ya kawo batun son karin aure, ya samu cikakken goyon baya daga Indo, da kyakkyawar addu’a daga ‘ya’yan sa.
A bangaren Lami, ta hana kanta zaune balle tsaye, yau gidan wannan mai rauhanai, gobe gidan wancan malami, wai a lalata zancen auren Maikalwa, da diyar Liman, yarinya Saudatu.
Amma da yake an ce matar mutum, kabarinsa, Saudatu ta tare a gidan Maikalwa, shekara na zagayowa ta haife ni, kamar mu daya da ita a komi.
Na ci sunan mahaifiyar Maikalwa, kasancewar an haifeni ranar litinin suke kira na, ‘Atine’.
Gidan mu ginin kasa ne gaba da baya. Gida mafi talauci da kaskanci a layin gabadaya.
Daga farko zaure zaka tadda, wanda ko rufi Allah baiyi zai samu ba, a cikin soron dakin Yayan mu Auwal ne, daga katifar audugar shi, sai akwatun karfen kayan shi, da tarin littafan karatun shi, kasancewar shi mutum ne mai kwazo a fannin karatu, sabanin Sani da yafi maida hankali ga bin Baba kasuwa.
Gefen dakin Awal buhunhunan kalwa ne fiye da talatin, in har da warin kalwa yana cutarwa, da nace cikin mu babu wanda ya kawo matsayin da muke a yanzu.
Faffadar tsakar gida mai dauke da katuwar bishiyar dalbejiya, wadda muke amfana daga ni’imar sanyinta, muyi wasa, mu ci abinci, muyi hira da Baban mu a karkashinta. Galiban, anan iyayen mu suke aikin surfen, masara da dawa, anan ne kuma ake aunar da kayan kullin, Goggon mu Indo.
Turakar Malam ce ta fari daga dama, sannan dakin Goggo ciki da falo, daga hagu dakin Inna Lami ne, sannan dakin Innata, da muke kira, (Amarya).
Rumfar dafa abinci na daga kudu maso gabas din gidan, sai makewayi daga can bayan dakin Inna Lami, wanda zaka suturta kanka, ta hanyar jawo langa-langa ka kare kofar.
Goggo Indo, ita ta daukeni a bakin nono, tun daga yaye kuwa na koma dakin ta kasancewar ita Allah bai nufeta da haihuwar ‘ya mace ba, ta dauki so, da kaunar duniya ta aza mani.
Duk wani dan abin yayi in ya taso, kamin ka gani jikin Atika, ka ganshi jikina. A da, ta so daukar rikon Atika, take-taken rashin kawaicin Inna ne ya tsoratata, ta kyale mata diyar ta, ita kanta Atikar, ba karamar fitinanniya ba ce tamkar Innar ta.
Mahaifiya ta Saude, diya ce ga Limamin Karaye, ‘ya daya jal, da ya mallaka; ma’abociyar sani a addini ce, sosai.
A bokon ma, tasan wani abu, domin tayi firamare. Kullun daren Allah matan anguwarmu (Limanci) take karantarwa littatattafan addini, irinsu ahlari, qawa’idi, sirah, balaghah, dasauransu, daga karfe takwas zuwa goman dare. Goggo na ma, tana zama ta dauki karatu, tayi mata tambaya tamkar sauran dalibai.
Babu zancen kishi a tsakanin su, ko ganin kyashin juna, sai mutumta juna. Bazaki taba tsammanin cewa kishiyoyi ne ba sai Yaya da kanwarta.
Wannan ne yake kara min kaunar Goggo na a kullum. Bani da kamar ta, bani da abokin shawara sai Goggo. Mahaifiyata tamkar kawaye muke, zamu je dakin ta, ni da Atika, muyi hira, muyi dariya, mu tafi dakin Goggo, mu bata labari.
Babu kunya, ko kadan a tsakanina da ita irin na mutanen kauye ga ‘ya’yan su na fari sai ‘kawaici’. Wato duk wani al’amari daya shafeni, baza ta yi ruwa tayi tsaki ba, wannan na Goggo ne.
Tsakani na da Atika, shekaru biyu ne kwarara ta bani. Duk wata huduba da Inna kewa Atika game da mu, Atika bata dauka, asali ma kwasowa take ta gaya mani, in yi mata fadan, don me zata ke dauko hirar su da mahaifiyar ta, tana gaya mani?
Sauda yawa, zata ce
“umh! Atine, kin ji Innata tace wai bakwa kaunar mu. Wai Amarya ta asirce Malam ya maiheta bora, wai ina karama, Goggo ta zuba mun shinkafar bera a koko, na kusan mutuwa, sai da anka kaini Birni naga bokan turai. Don haka in bar hige miki, watarana zaku kaheni”.
Irin wannan tsegumi na Atika, yana da yawa, sai in yi murmushi, in ce
“Atika,ba zan ce Innarki tayi karya ba, amma da kahekin, Goggo keda niyyar yi ai da baki kawo yau ba.
Kwanan ki nawa a dakin ta, bata kahekin ba? Ni kuwa ‘yar uwar ki ce, Uban mu daya, ina kaunarki, ban taba tunanin, cutar da ke ba.
Abinda ke tsakanin Iyayen me, kishi ne, irin na matan Sango, kada ki sake, ki tsoma baki, babu ruwan ki.”
To da haka nake kashe gulmar Atika, duka da nike kasa da ita ni kaina na san Atika “doluwa” ce.
Na fi ta wayo da hankali, na fita kamun kai, ta fini son kwalliya, gwalli da iyayi. Don haka koda muka dan tasa samari ta ko’ina ke kawo mata caffa.
Gata da ingarman jiki, girma take cikin dan lokaci, girman jikin ta ya fi shekarunta kai kace hurata a ke yi. A kauyen mu, Atikar gidan Maikalwa, tayi suna sosai a wurin samari, gata dai baka wuluk, amma kyakkyawa, mai ado da rangwada, Atikar Inna Lami kenan.

Al’adar mu a kullum, idan mu tashi da Asubahi, bamu komawa barci, zamuyi sallah tare da Baba, mu cigaba da lazumi, har zuwa ketowar alfijir.
Daganan ne Mai girki cikin su, zata tashi ta dama koko, ta dumama sauran tuwon dare. Idan aljihun Baba da albarka, ya aiki Ya Auwal, ya sayo mana kosai a hada da shi, ranar da babu kuwa, a sha koko, a ci dumame, cikin godiyar Allah.
Ni kuma in share tsakar gida, zaure, dakin Awal dana Goggo na. Watarana Atika, in ‘yan kirkin na kusa, ta share na Inna Lami, dana Amarya. Ta koma tabarma, ta ja filo ta mike, in ko basa kusa, da Baba ya fice kasuwa, zata koma sharar barci abinta.
Son barci irin na Atika, ko kasa sai haka. In hada kwanuka, in dau guga in jawo ruwa, in dauraye su, in kada dan jangabo, in dauraye kewayen mu tas, Goggo tayi tasa mun albarka, ita da Amarya.
Auwal, Sani, da Rabiu su tafi makarantar boko, mukuma mu tafi allo. Ina goye da ‘yar kanwar mu Sadiya da Amarya ta haifa daga baya.
Haihuwar gidan mu tamkar tsari, sai dai tsari ne daga Allah, kamar bata matan kauye ba, sai a haifi daya, sai bayan shekaru biyar, kamin wata ta zo. Baban mu bai amince muje boko ba, amma Amarya taso muje, haka goggo, tunda ya nuna ba ra’ayin sa ba ne, cikin su babu wadda ta sake tada zancen.
In mun dawo makarantar allo, sha biyun rana, muyi wanka, mu kullawa Goggo omo da suga, in tana aiki, mu zauna mu karbi ciniki, tun Inna na hantaran Atika akan mu, har ta gaji, ta saduda, ta kuma amince, ba’a raba hanta da jini. A kullum kara shaquwa da juna muke, ni da Atika, sai dai hali, kowa nasa daban.
Da yamma gidan kakana Liman muke daukar karatu wurin sa, na Al’qur’ani mai tsarki da sauran littattafan addini, irin su Bulugul-Maram, Barzanji, Sirah, Kawa’idi, Arba’una Hadith, Ishmawi da sauran su. Da daddare Atika kan je dandali, ko wasa gidajen kawayenta.
Ni ko haka nake; ba kawa ba abokiya, balle aminiya. Na gwammace in zauna wurin matan auren da ke daukar karatu ga Amarya. Duk da karatun ya fi karfina, amma yau da gobe, da aka ce tafi karfin wasa, kullum kwakwalwata kara budewa ta ke a karatun addini. In wani bai shigaba, wani na shiga. Ni kaina nasan, na fi Atika ilmi nesa ba kusa ba.
Duk wasu alhairai da take samu wurin samari, baya gabana, domin ba abinda Goggona, bata sai mun. Har kullum ina alfahari da Goggo Indo, matsayin uwar rikona na har abada.
Bana yin Sallah, in mike ban yi wa Goggo addu’ar, budi da nasaran rayuwa ba.

A wanan watan Inna ta haifi dan ta namiji, aka sa masa suna Jafaru. Na rungumi renon Jafaru, Inna Lami bata san cin Jafaru ba, balle shan sa, bata san kashin sa ba, balle fitsarin sa. Rainon ne ya zame min biyu, har ya so ya rinjayi karatuna.
Domin a da, ina hadda, tun bayan haihuwar Jafaru na daina sai dai bita. Ganin haka Amarya na yaye Sadiya, ta aike da ita gidan Liman, ni kuma na ji dana Jafarun da karatuna, don ta lura ZAN IYA BARIN KOMAI IN DAI A KAN RAINO NE.
Ina son kananan yara, ina matukar kaunar, in ganni goye da jariri, ina jijjiga shi, ina yi masa rawa, ina cilla shi ina cafewa, yana bangala mani dariyar ‘kauna’ irin ta ‘Uwa’. Don haka inda duk zan shiga a kauyen Karaye, an san da goyon Jafaru ko Sadiya za’a ganni.
Ko da aka kai Sadiya yaye wurin Luba Kakar mu, kullum kafata, bata rabo da hanyar gidan Liman, ina goye da Jafaru dan shekaru biyu.
Malam yayi ta tsokana ta da Uwar Biyu. Ina jin dadin sunan, ina farin ciki a ce ni UWA CE. A ganina, wanda duk Allah ya baiwa Da yayi masa babbar kyauta, wadda wani ko wata, ba zai iya bashi ba. Haihuwa ai kyauta ce daga Allah, don haka abin alfaharin kowacce mace ne.
*****







T
afe muke ni da Atika a gefen kwalbati, ina goye da Jafaru, Atika dauke da kwarya a kanta cike da Kalwa. Baba ne ya aikemu mu kai gidan wani mutun da ya bashi kudin a kasuwa, ta kare yace zai aiko mai da ita gida.
Atika ta dube ni, ta girgiza kai cike da takaici tace
“Atine, shin wai ke bayan ki bai gajiya da goyon yara?”
Nayi murmushi nace “amsar ki kenan” tace “wallahi ki rika aje Jafaru hakanan, ya girma, shekarun shi fa biyu, an yaye shi tuni yana gudunshi ko ina, tukunna ma, baki tsoron kirjin ki ya bude?”
“To idan ma ya bude Atika menene? ZAN IYA JURE KOMI IN DAI AKAN RAINO NE!”.
Atika tayi tsaki “Allah wadan wahalalle wallahi, ina kuwa za ki yi saurayi? Kullum sungume da yaro kina tafe sukutuf, babu dan karya kugu?
Ki duba ki gani, ni kullun zance, har layi a ke, kudi, sutura, kayan kwalliya, babu wanda samari basa bani. Amma ke ko ‘yar murtala, bana ce kin taba karba daga saurayi ba”.
Nayi murmushi “kudi, sutura, kayan kwalliya, don su zaka kula saurayi Atika? To ladan RAINO fa? Saurayi yana bayarwa? In gaya maki gaskiya ta Atika, burina ba samari ba ne, KARATU NA BOKO irin makarantar su Ya Auwal, in karanta raino, RAINO NA KANANAN YARA.”
Atika ta tuntsire da dariya har tana hawaye, irin ta kaga mahaukaci sabon kamu tace
“koda na ji ana karatun boko, ban taba jin wani KARATUN RAINO ba. Kai Atine, kin bani dariya, wai ma ina kika jiyo wani karatun...


Read / Download TUNA BAYA SHINE ROKO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album